Showing 45001 words to 48000 words out of 69765 words
shiyasa na kasance shalele awajen mai gidana saboda gabaki ɗaya sirrin gyaran jikina yana Tattare da gudun muwar UMSAD INCENSE shiyasa koda yaushe muke cikin walwala da farin ciki da mai gidana🥰.
Dan neman farin ciki akoda yaushe tsakanin ki da mijinki ki tuntuɓeta a wannan layin
Sayen nagari maida kudi
UMSAD INCENSE 080 288 27241
3️⃣9️⃣&4️⃣0️⃣
""Message ne ya shigo wayar shi hakan yasa shi sauke ajiyar zuciya kamin ya bude yaga itace kamar yanda yayi tsammani yaga ta rubuta.
" *Yah shekh kayi hakuri karkayi fushi* "
Murmushi kawai Yayi ya mayar mata da reply kamar haka.
*Bana fushi da abinda nikeso ki kwana lfy Mrs Habib*
Koda taga amsar daya bata sosai ta samu natsuwa har bacci yayi gaba da ita mai daɗi.
Shi kau Sheikh ya daɗe yana juyi gabaki ɗaya ya kasa control din kansa,daya tino girman auran dake kansa sai yaji son kaɗaicewa da matar sa, wani irin ciwo marar sa tamai lokaci daya wanda yasashi sakin dogon nishi, A haka Yayita juyi harya samu ɗan sukuni ya tashi ya shiga toilet ya tsarkake jikin sa ya dauro alwallah ya fito ya fara jera nafilfili kamar yanda ya saba,gabaki ɗaya sujjadar dayake addu'ar shi ta Allah ya tusama Husnah son shi mai tsanani yake ta yanda komi zaice zata amince da Addu'a Allah ya ciremata tsoron shi ga rai kamar yanda tace.
Saida yayi sallah Asuba kana ya hau gado ya kwanta yanajin kanshi na masa wani fitinan nan ciwo.
Koda ya kwanta cikin lokaci zazzaɓi mai zafi ya sakkomasa take ya fara rawar sanyi.
A'C ɗakin ya mike ya kashe da kyal kana ya dawo ya kwanta ya lulluɓe.
Istigfari kawai Shekh yakeyi yanajin ciwo amma baitabajin mai tsanani kamar wannan ba, gabaki daya ciwo ya haɗemai lokaci ɗaya .
Salati sosai ya saki lokacin da yaji marar sa tamai wani murɗawa kamar mai shirin fiddo Ɗah.
Lips dinsa ya kama da karfi ya tsotsa kana ya rintse ido yana Addu'a.
Azabure kuma ya kife yana damkewa .
Tsawon lokaci yana cikin wannan mawuyacin halin kamar zai shiɗe, kamin Allah yasa bacci yayi gaba dashi wanda daka kagani kason bana daɗi bane.
Husnah kau tana tashi da safe ta fito tayi ɗakin umma, Anan ta gaishe dasu Umma dasu Aunty meenah kana ta takure gefe guda tayi shuru tsawon lokaci sunata labari amma bata samasu baki ba.
Ummah ta dafata tace'' Husnah wai wannan Sanyi da kikeyi na miye ko baki da lafiya ne, kodai Auran ne bakyaso?.
Kai ta gilgiza tare da faɗin" Babu komi Umma.
Aisha ta kalleta cikin Damuwa tace" Umma infa Husnah tace haka zatai zata cuci kanta ta cuci mijinta, kuma Wallahi bazasu zauna lafiya baa .
Shikenan Sadam ya riga ya kashe maki rayuwa da tsoron kowa da komi , Dan haka in kikace haka zakiyi to ba baki naimaki ba wallahi azeem gashicen kina samun matsala da SHEIKH, saboda bazai yarda ki Cuceshiba akan abinda yakamata ace kinshafe tarihin sa,Inzaki shekara cewa ba komi ba kowa da kike tinani bazai yarda ba ,ke Shekh dinma zai iya tinanin Tsohon mijinki kike tinani,ki gyara rayuwanki kison abinda ya dace, Rayuwar da kikai gidan sadam ki ɗauketa a matsayin kaddara kisa aranki yanzu sabuwa zakiyi mai cike da farin ciki.
Anan suka zage sukaita bata shawara kuma sosai hakan yamata dadi takuma ɗauka,Tare da basu hakuri da subata lokaci komi zai wuce.
Aysha tace'' kije ki turamasa sakon barka da safiya kinga dai ya damu dake, Bai dace ace komi shi zai mikiba ke kuma kina nan kina Nonnokewa,Ki kula da wanda ya kula dake,Kiyima Sheikh biyayya koda bakyason shi, Domin shi din marufin Asirin kine.
Kai ta jinjina kana ta fita. Ɗakinta ta fada ta ɗauki wayar ta tafara mai text.
*Aslm Alaikum*
*Brk da safiya malamina da fataan ka tashi lfy ya ummy nah ina gaida su Amal ka wuni lafiya M.L*.
Ta turamasa.
Ganin sama da awa biyu ba reply yasa ta yanke shawarar kiransa kila dai fushi yayi bai huce ba, amma nan ma shiru ba amsa.
Wani iri taji kamar ta fashe da kuka da ba dan kunyar Ummy ba da saitaje gidan ta dubosa.
Hajjah ce ta buɗe kofar ta shigo tare da zama bakin gadon tace.
" Ya akai kiketa cika kina batsewa?.
Kamr jira Husnah keyi ta saki kuka .
Hajja ta kama haɓa tace.
" Danjan sharri minaimiki Husnah daga shigowata ko da wuka kika ganni ko Sanda?
Baki ta ɗan turo cikin shagwaba tace"Yo bashine niketa kiransaba yayi fushi yaki ɗauka,Nama fasa Auran nasa dan yaga ya sameni cikin sauki zaimun haka Hajja..
Shiwa Hajjah ta tambaya cikin mamaki.
YAH SHEKH mana Husnah ta bata amsa kai tsaye.
Dariya Hajja ta tintsire da ita tace" Kai yaran zamani, Allah ya shirya,duka fa ko goma bataiba,kikasani ko bacci yake,karki manta dole ya dinga zullumin inda iyayensa suke kullum, Yau kau ya kwana gabansu ai dole yayi bacci mai daɗi tinda dole susha firar yaushe gamo.
Jin furucin Hajja ba karamin farantamata yayi ba, Hakan yasa ta sauke ajiyar zuciya tare da sunkuyar da kanta tana share kwallah.
Hajjah ta buɗe ledar data shigo da ita ta fiddo wani abu kamar masara acikin yar kwalba,ta fiddo guda tara ,tare da warware wani ledar ta fiddo dabino tara ta kalli Husnah tace"Ma'u ,daga yau zanfara gyaran jikin ki kinji ko,bazance zaki koma kamar daba amma kuma babu wanda zai kiraki zawara Insha Allah,wannan abun da kike gani abune mai tattare da sirri irin namu na mutan da,Dakyal na samo miki shi yau tin asuba nabar gidan nan,Sunan sa *kaɗan mai aikin Alkhairi*(zaku iya samun sa kai tsaye wajen ummy Aysha ) kingansa nan,Hmm kedai maza kici,Inaso ya tsumi jikin ki cikin wata ɗaya nan ki canza kamanni,anjima ma zan karɓomiki na sanyi.
Cikin rashin fahimta ko miye Dan Husnah ba sanin kayan mata tayiba, ta dauki daya ta sanya a dabinon ta tauna a haka har taci tara.
Murmushi Hajja tayi tace mu kayan mu na da ba irin na yanzu bane,na yanzu cuta kawai suke saki.
Wata roba ta dakko ta wani abu mai Ya'ya shima ta zazzaga ta bata tace maza cinye.
Abakinta tasashi take bakinta ya gauraye da wani masifaffan Yauki kamar taci kuɓewa.
Fuska ta yamutse zatai magana Hajja ta Harareta kana ta tashi ta fita tace kinga wannn abun mai kamar masara ko,bazaki karacin irin saba sai nan da sati biyu dan yana dadewa jikin mace , Wayan nan kau zan dingabaki so dai-dai A rana.
Kai kawai ta jinjinamata tafiya.
Agidan su Yah Shekh kuwa murdawa da cikinsa ya sakeyine yasashi zabura ya mike yana salatai tare da matse cikinsa sosai yanacije lips.
UMMY ce ta turo kofar ta shigo ganin duk sun hadu Palo bandashi.
Da sauri ta ƙarasa matsowa indayake ganinshi karshen gado yana neman fadowa ƙasa.
HABIBIEEE miye haka ka gyara kwanciyar ka man.
Shuru taji yayi kamar ma baya numfashi.
Azabure ta sake Kiran shi tare da kwalama Daddy dasu sameer kira.
Aguje suka shigo Ɗakin, nan sukayi kanshi dai dai lokacin da numfashin sa ya fara ƙoƙarin tsayawa.
Kuka Ummy ta fashe dashi tana fadin" miye haka ,mike damunka Habib, Dan Allah karkamun haka,daga haduwarmu shine zaka kwanta jinya, Habibinah katashi tafita da gudu dai-dai sadda Inna ta shigo itama a kidime.
Sameer kau ciccibar SHEKH yayi ya fito dashi aguje Imran yaja mota aguje suka fita.
UMMY mah motar da Daddy yajawo tashiga ita da Inna sukabar Amal da mai aiki gida hankali tashe.
Kai tsaye Heritage Special Hospital suka nufa dashi,anan manyan Doctor suka rufu akanshi dan bashi taimakon Gaggawa.
Daddy kau da ummy duk sunbi sun ruɗe suna tsaye wayar Daddy ta shiga Ring.
Ɗagawa yayi cikin sanyi suka gaisa da Abbah.
Anan abba ke cemai lfy yaji fitar motar sa yana ta sauri ya shigo su gaisa?.
Fadamai abinda ke faruwa yayi tare da faɗin ya shirya zai turo Sameer ya kawoshi tinda baison Asibitin ba .
Sosai Abbah ya shiga tashin hankali anan shima ya fadama Umma, nan danan hankalinta ya tashi ta sanarma su Aysha itama ta fadama Husnah.
Anan fa ake yinta,kiri kiri Husnah ta cire kunya ta dinga ihu da fadin akaita ta gansa Dan Allah .
Dakyal umma ta lalalsheta tasanya tayi wanka ita kuma ta hada breakfast din da sukayi a basket sukayi arranging din komi,cikin lokaci Sameer yazo Nan ya kwashesu suka nufi Asibiti.
Koda suka shiga har an fito da Shekh da aka samu numfashinsa ya daidaita bayan alluran dayasha, Ga Drif an samasa akayi ɗakin hutu dashi.
Da kallo duk sukabi gadon da ake turashi dashi gwanin tausayi, kamar ba shine jiya lafiyan sa kalau ba, wannan ma kadai ya isa bawa ishara.
Dr ya kira Daddy akan yana neman sa office dinsa, anan shima Daddy yaja Abba suka nufi office din tare,Daka gansu kaga dukkan su basa cikin natsuwar su.
Koda suka shiga suka zauna Anan ya fara masu bayani.
"Yallabai yaran ka na cikin matsala gaskiya,wacce na tabbata inba mai dauriya kamar saba tofa da wani ne da tini ya sama ma kansa mafita,Any way kawai dai maganin abin kayi gaggawar yimasa aure inda hali.
Kana abu na biyu ya samu ciwon zuciya a kiyayi abinda zai bata ransa Dan Allah, Duk abinda yakeso inda hali abasa, wannan shine babban magani daya kamata afara kulawa dashi dan samun damar magance abin.
Abbah da yake akwai tausayi da karyayya zuciya tini hawaye suka sakkomi ,to miyasama SHEKH ciwon zuciya.
Tashi yayi ya fita Daddy mah ya masa godiya ya fito jiki a sanyaye.
"Inna tace minene?..
Daddy zayyi magana Abba yace "zazzaɓine da ciwon ciki.
Anan yace dasu yana zuwa ya fita.
Koda ya fita a harabar Asibitin ya ɗan zauna na wani lokaci yana nazari kamin ya kira Sameer akan yazo zai kaishi wani wuri.
Fitowa Sameer yayi anan Abbah yaja Sameer wani katafaran campany inda yayi order kayan gidan sa.
Ba karya wajen ya haɗu iya haɗuwa,kayan dakine ya fara zaba na alfarma yan waje masu masifar kyau set biyu, Bayan ya gama yamasu Transfer kudin su suka fito Asibiti suka koma inda ya iske Ummy nata fama da Husnah akan tayi shuru tabar kuka takiya.
Daddy yashiga wajen babban Doctor yace matar shi zata iya ganin sa?.
Kai ya jinjina tare da fadin "zaku iya ganin sa amma akiyaye hayaniya, abar shi ya huta dan Allah.
Kai ya jinjina kana ya fita yace su shigo.
Da sauri Husnah ta mike ta fara shiga,kana suka fada dakin suduka suka matsa ga SHEKH da yini daya yayi wata irin rama kamar wanda ya shekara da ciwo.
Jikin nan nashi da kwantacciyar suma tama kawanya ya fito na sadaukan maza saboda ko riga babu jikin sa sakamkon na'urorin da suka sanya masa kota ina,Farar fatar shi murzaza ta ya'yan hutu har wani Yellow Yellow take ta larabawan asali.
Daddy yace Dasu muje ko.
Fita sukai suka bar Husnah ita daya.
Ƙasa tayi da kanta tanajin wani matsanancin tausyainsa.
Aysha ce ta dawo tace ki kula dashi sosai Husnah, ki tuna halaccin daya miki lokacin da kike tsammanin yin bankwana da Duniya,Kayan sa sune abar shimfida gareki dan kiji taushi,Ya soki lokacin da Akaso ɓata sunan ki a idon duniya,ki kula da Habib iya iyawarki Mijinkine baki da yashi .
Tana gama fada ta fita.
Wani irin kuka ya kwacema Husnah , Lokaci daya ta tusa Hijjob inta cikin baki dan karya tashi.
A'Hankali halaccinsa ya fara dawomata cikin kwalwa,Abinda tamai bak kamataba ,kilama hanashi abinda yakeso yasa yasashi wannan halin.
Hannushi mai lafiyar ta kama ta rike gam tasanya fuskarta cikin tafin hannu tafara huramai iskan bakinta mai ɗumi,cikin kuka tace.
" Nayi Alkawari bazan sake saɓamaba mijina, ina sonka,ina kaunarka,Ka taimakeni ka tashi,zanbaka duk abinda zai zamema farin ciki, Zan iya bayar da raina domin fansar naka.
Ta daɗe tana dumi amma ko motsi baiba saboda allura da akai mai.
A ɓangaran su Daddy kuwa suna fita Abba yace da Sameer ya mayar dasu gida suyi girki in sungama sundawo.
To yace suka tafi su kuma suka shiga motar da Abbah yazo da ita suka zauna.
Abba ya kalli Daddy yace.
" Dan uwa wannan bikin na dawo dashi sati daya,Nafison farin cikin yarona akan komi,ita mace dakake ganin tana maganin wani damuwar,dan haka,sati mai zuwa in sha Allah za'akawoma habib matar sa.
Sai kafadaman inda za'aje asamata kayan ta.
Baki Daddy ya kama yana juya kai yace" A'a Aboki, kar amata haka, kason mace akwai son nazari da gyara gyare abarta dan Allah, zayyi hakurin wata ɗaya, ba gashiba anci kwana daya?.
Fuska Abbah ya ɓata yace "sai kace kai din zaka iya wannan hakurin dan Allah malam ina zaya zauna kaji.
Dariya sosai Daddy yayi yace harda Gori Aboki, To anan kusa damu yake,Nan ne bayan gidan mu , Akwai kofar dana fitar ta bayan lambuna to nan ma inka fada cikin lambun gidan sune,Su na ginawama dan inason hada kan family nah waje ɗaya.
Kai Abbah ya gilgiza yace hakan ma Dubarane.
Key din gidan ya karba tare da cewa muje ka kaini.
Kai tsaye Unguwar su suka nufa sukai parking bayan gidan su,Anan suka nufi inda sukaga wani tafkeken get Wani buzu na tsaron shi,Katoton gidane na gaske kamar wata ma'aikata, part ukku ne lafiyayyu masu shegen kyau, ko wane yana ɗauke da benan sa.
Tsakanin wannan da wannan ma wani tazara ne mai zaman kan sa.
Daddy yagwadama Abbah na tsakiyar dayafi fitowa sosai yace.
Wannan shine na Habib, sukuma kowanne zai ɗauki ɗaya.
Sosai Abbah ya yaba da tsarin gidan, Dan an'kashe hamshakan kuɗaɗe bana wasaba wajen yinsa,Babu inda basu shigaba iya kyau da tsaruwa Dakunan sunyi.
Koda suka tashi ta ƙaramar kofar suka fito suka faddo lambun gidan Daddy.
Part din Daddy suka shiga suka sake tsara yanda abin zai tafi kamin ya shiga gidan sa dan sanar da Umma.
Anan shima Daddy ya kira UMMY yake faɗamata ciwon Habib da kuma shawarar da Abbah ya bada.
Sosai ta shiga Damuwa,Amma tanajin abinda Abba yace yasa ta hau murna da farama yan gidan su waya da ta tsayar da zuwansu akan zasuzo yima su Inna sannu da zuwa, tace suyi shiri suzo biki, Anan ta fara sanar da mahaifiyarta irin abubuwan da takeso a hadoma Husnah na gyaran jiki matsayinta na mahaifiya zata badasu gudunmuwa.
Dariya Daddy yayi yajawota jikinshi yace mai kuka tana dariya,Wato zaki gyarama yaronki kenan yaji zanzan kamar yanda Daddyn sa keji ko.
Kashe wayar tayi jin zai bata kunya kana tace.
" Ai duk kai kajama yaran nan Daddy, sunbiyoka wallahi, gashi yarona yaga yar kyakyawar yata ya rude ya kasa natsuwa, yanzu yamaganar kawo lefe?.
Daddy yace bari in'baki kudi ki turama Haj Halima ta haɗomuna,, sai su wuto dashi baki daya,kinson Bazan iya hakurin zuwanki Dubai ba ki barni.
Baki ta turo tace" kullum haka kake cewa ka tsufa amma baka hakuri.
Hancinta yaja yace wallahi bakicemun tsoho ko jiya bari in fadamiki abinda kika dinga cewa ban mantaba..
Da sauri tamike tana dariya tace Allah ya shiryaman kai Daddy tayi waje.
Murmushi yayi yace matsoraciya.
A bangaran Husnah kau saida ta koshi da kukan kana ta aza kanta agefen gadon, take bacci yayi gaba da ita.
Karfe biyu saura ya fara bude idonsa da sukaimai nawie..
Akan kyakyawar fuskarta da keda shatin hawaye ya sauke gajiyayyun idonshi.
Ɗakin ya kallah da jikinshi dayake jinshi a tamke ko ina da na'urori.
Maida kanshi yayi ya lumshe kamin ya sake budesu ya dire akanta.
Lafiyayyan hannusa mai taushi da yayi sanyi yasanya akan fuskarta ya dan shafa kaɗan yana murzawa.
Wani irin lumshe ido yayi yanajin wani sanyi kota ina yana ratsashi...
UMSAD MAKENTOSH
*Makentosh*
*Makentosh*
*Makentosh*
Ina macen da ta isa takejin takai Hajiyar gayu.
*HMMM DA SAURANKI HAJIYATA INDAI BAKYA AMFANI DA MAKENTOSH*
Matso kiji hajiyata
Kamar yanda kuka sani UMSAD INCENSE ta sake zomuki da wani sabo sahihi mai suna MAKENTOSH
MAKENTOSH wani sirrine nasu na mutan Maiduguri,yana da masifar kyau yana hade mace gam koda haihuwa goma tayi,ina uwargida ina amarya ina budurwa ina zawara duka dai gudun'muwace daga mai kishinku har kullum UMSAD INCENSE.
Ina baku shawara da ku nemeta dan magance matsalolin da suke faruwa damu tsakaninmu da mazajenmu dan gyara shinfiɗarmu kai tsaye.
Ni Ummy Aysha shiyasa na kasance shalele awajen mai gidana saboda gabaki ɗaya sirrin gyaran jikina yana Tattare da gudun muwar UMSAD INCENSE shiyasa koda yaushe muke cikin walwala da farin ciki da mai gidana🥰.
Dan neman farin ciki akoda yaushe tsakanin ki da mijinki ki tuntuɓeta a wannan layin
Sayen nagari maida kudi
UMSAD INCENSE 080 288 27241
4️⃣1️⃣&4️⃣2️⃣
""Cikin natsuwa ta ɗan fara bude idonta A'hankali har ta saukesu fess akan shi , Da sauri kuma ta ida warewa tana mikewa tsaye a rikice idonta har ya kawo ruwa tace.
"Yah shekh ka tashi? sannu nice ko? bazan sakeba , Dan Allah karka sake kwanciya ka barni kaji?
Ido ya ɗan lumshe mata yana murmushi batare da yace komi ba.
Cikin sanyi sosai na mai jinya yace.
" Taimakeni ki tayar dani ki kaini Toilet,Ina so inyi wanka inyi Alwallah karfe ɗaya ta wuce ko.
Ido ta zaro tace.
" Kamin kato da yawa bazan iya ɗaukar ka ba, Bari in'kira Doctor ya fara dubaka kana sai ya kaika ni ina zan iya dakai jibekafa kar ka karyani.
Sosai tabashi dariya amma baiba,wai bazata iya ɗaukar saba , Hmm duk wayon amarya...
Kai kawai ya ɗagamata batare da yace komi ba
Ta bude kofa zata fita Doctor ya shigo, Baya taja ta bashi hanya ya shigo,wani irin kallo yake mata wanda yasanya Shekh daya tsare shi da ido gyaran Murya da yasa shi juyowa aiko ya watsamai harara.
Kanshi ya sosa yace.
" Affuwan Yallaɓai wannan wacec...
"Afusace yace Matata ce".
Yawu ya haɗiye tare da ƙarasawa wajen yamasa yan tambayoyi a dakile yake bashi amsa.
"Shekh yace "Ka ciren abubuwan nan ni nasamu sauki, zanyi wanka inyi sallah.
Ciremasa yayi dan yaga alama azafafe yake.
"Zan taimakama Yallaɓai ka samu ka shirya jikin ka babu kwari cewar Doctor..
Kai ya gilgizamai alamar A'a, Tare da fadin" ga matana cen zatana taimakamun.
Mamaki yake ba Doctor sosai duk sadda yace Husnah matar sace,to yaza'ayi yana da mata kuma yake da wannan ciwon?
Wani kallo shwkh ya watsamai hakan yasashi fita da sauri yana jan kofar.
Da ido ya tsareta kamin kuma ya koma ya kishingida yayi shuru yanajin haushin likitan dara tsareta da ido .
Husnah kuwa Matsowa tayi kusa dashi tare da zama gefenshi tace.
" Sannu *M.L*.
Da sauri ya kalleta ita kuma ta zaro mai ido kamar wacce taji tsoron abinda ta furta, kamin cikin in ina da bata da ita tace'' Sannu Yaa Sheikh, mikake buƙata?.
Kai ya gilgizamata yana lumshe ido, Allah yasa ba kunnan sa gizo yamai ba,yaso ace ta furta dan sake tabbatar ma da kunnuwan sa abinda yake hasashe