Showing 66001 words to 69000 words out of 69765 words
daya ya hau hargitsa tinanin ta wanda hakan yasata kware baki ta hau ihu da neman ya kai ga in da take so.
Saida yakaita karshe yaga tana neman Sume mai kamin ya fara Addu'a ziyar tarta" *ALLAHUMMA JANNIB NA SHAIƊANA,WA JANNIBI SHAIƊANA MA RAZAQTANA.*(Addu'a kasancewa da iyali bafa sai daran farko ba, anso ko wane lokaci kanayinta saboda korar shaidan da kuma Fatan in'ganta rabon da zaku samu a wannan saduwa, fatan an gane yawwa,karkiyi balagwadai kinajin daɗi ko kina ihu , karkije ki samu yaro mai hayaniya bala'i dajawo maki magana😏)
Ɗuff Husnahhh ta dauke wuta yayin da tafarajin jarumin mijin nata,lokaci daya ta dawo hayyacinta tafara kokarin tureshi amma ina Sheikh Yakai geji kabbara kawai yake tare da azkhar ɗin yamma cikin halin kuka da rudewa gami da neman taimakon Allah kar numfashin sa yabar jikin sa, Dan wani fitinan nan daɗi yakeji , Ga korama tashi cunkus da ruwan ni'ima taban mamaki( wani aikin sai Masara )
Husnah kau abin ya girmi Tinanin ta tin tana sanya rai ga gamsuwar mijin nata har dai tayi likis , Daga karshe dole ta fashemai da kuka,tana kaimai duka da fadin"Ya barta..
Cak ! ya tsaya yana zubamata jajayen idanuwansa, kamin dakyal ya iya cewa.
" my Husnah kin gamsu?
Da sauri ta ɗagamai kai hakan yasa shi yin luff jikinta sai haɗa gumi suke.
Zuwa wani lokaci ya Murgina gefenta yana sauke numfashi tare da jawota jikin shi ya hau samata Albarka.
Husnah kau cikin lokaci wani wahalallan bacci ya ɗauketa.
Yah shekh kau mikewa yayi ya shiga toilet ya tsarkake jikincshi yanjin shi wani sawat, bazai taba manta wannan garin ba mai Ɗumbin tarihi a rayuwar saba,wani matsayi da Babban gurbi Husnah ta sake samu a zuciyar shi,yanaji inama yamayar da ita cikin sa,ba karamin farin ciki yasamu da gamsuwa da iyalin nasa ba .
Yana fitowa ya zura jallabiyar shi milk yayi zaune kana bedsit yana kallon kyakywar fuskar Tata da duk tayi sayun hawaye.
A'Hankali yasa sassanya hannusa mai masifar taushi ya fara shafa fuskar nata yana wani jujjuya yatsan sa a kunnan ta.
Lokaci daya ta fara bude idonta har ta suakesu fess akan shi na dan lokaci,da sauri kuma ta mayar ta rufe tanajin wani fitinannan kunya duk abinda ta dingayi yana dawomata a kwalwa.
Hancinta yaja yana fadin "Daina kunyar mijinki kinji,abin da kikaiman ya faranta raina sosai,kuma hakan shine fatana,Allah yayima rayuwarki albarka data abinda zaki Haifamun,tashi muje namiki wanka kizo kichi abinci nason cikin nan babu komi gashi time din sallah yanata gabatowa.
Ƙin motsawa tayi hakan yasa shi faramata cakulkulo dole ta wartsake tana zillewa tana masa dariya.
Shikau sama yayi da ita har Toilet ya gasa jikinta sosai kana ya fito yabarta tayi wanka Tsarki ta fito tana sinne kai.
Da saurin sa ya tashi ya iso inda take ya kama hannuta ya zaunar akan gado tare da ɗaukar mai mai kamshi ya hau murza fatar jikinta yana sakarmata kalamai masu dadi da sanya natsuwa gami da faɗama ta halin farin cikin daya jefata.
Wannan rana Husnah taga tattali taga soyayya da babu algus a cikinta,Ashe duk lokacin da mijinka ya kusan ceka kara samun gurbi kake a zuciyar shi tama kanta wannan tanbayar.
Ya zama dole ta dage dan faranta ranshi.
Hakan ya sata kama hannunsa tace "kayi hakuri da duk abinda ya faru nayi tinanin xanji kamar na wancen time ɗin ne kaji?.
Sassanyar murmushi ya saki yace" ki ɗauka ba ayi komiba ya wuce kuma ni ban rikekiba,Gashi yau kin shayar dani madarar dana daɗe ina fatan sake samu A rayuwa,A tarihin rayuwata Husnah banaji akwai kamar ki,komi naki mai kyau mai daɗi,sunan ki,halittar ki,koramar ki,komi ya dace dake.
Kana da gaske bakiji na wancen karan ba to mikikaji yau ? Yakarasa yana kashe mata ido ɗaya.
"Daɗiii" tace tana fadawa jikinshi ya rungumeta suka hau dariya yana kwaikwayonta da fadin.
" *kai nikeso dan Allah Habib, kayi hakuri komi ya wuce wallahi bazan sakeba ina so yanzu*..
Innalillahi ! kunya duniya rufe Husnah tayi hakan yasa takasa ɗagowa shikam dariya yake cikin Happy.
Wayar shi ce ta hau Ring yana dubawa yaga Ahmad ne
Bayan ya ɗauka yace'' yane Yah Ahmad.
Shewa Ahmad ya saki yana faɗin yau harda ya'ya na samu , to ustaz a fito muje sallah kaji.
Ok yace yana ajiye wayar ya sumbaci goshinta yace zan fita inyi sallah,bakyajin dai yunwa har na dawo?
Kai ta ɗagamai yace ok bye.
Yana fita ta mike ta daka tsalle tare da rarumo wayarta ta fara neman Aunty Aysha.
Bayan ta ɗauka Husna ta saki ihu tace" Aunty munshiryaaa.
Dariya suka fashe dashi cikin raɗa Aysha tace" yana nan ko tare suka tafi Sallah?
Husnh tace eh bayanan .
Ok tace tare da faɗin buɗe kofa.
Da sauri Husnah ta kashe wayar ta zira rigarta sai murmushi take ta fita ta buɗe.
Gabaki ɗaya suka rungume juna Aysha tace" Ai maganin ki nayi,wato da ban baki ( Babban sirri) ba da yanzu yana nan a gantale kina jamai aji da makaranta boko.
Cikin mamaki Husnah tace wai kina nufin wannan yar abar mai kamar masara itace tasani jin wannan masifa.
Gabali daya suka fashe da dariya,Meenah tace raina kama kaga gayya kenan .
Kai ta jinjina tace nagani kam.
Sallah sukayi Aysha ta fiddomusu cake da lemo suka sha suka hau fira har saida Shekh ya shigo suka mike suka fita sai godiya yake masu.
Suna fita ya rungume abarsa tare da furta ina sonki.
Cikin fari da ido tace nima ina so ka.
Ahaka suka fara sabuwar rayuwa cike da farin ciki, Ɗan zaman da sukayi Husnah ta zama yar hannu ta koyi darasi kala kala a wajen shehin malamin nata, taga soyayya Ustazai mai sanyi da natsuwa,ya sabamata da komi nashi.
Gashi shekh bashi da fitina kana yana amfani da yanda ya fahimci yanayinta kan ya dosheta da buƙatar sa.
Misali! in sun fita sun dan yawata in sundawo zai rungumeta suyi bacci kawai ba ruwanshi da matsamata hakan kuma na mata dadi,In kau ya dafe ta sai Tayi dakyal yake barin ta.
A haka suka kwashe wata daya gabaki dayan su sun sake kyau sunyi sharr abinsu masha Allah Dubai ta karɓesu sana sun kafa babban tarihi a wannan kasa da bazai taɓa goguwa ba.
Daran da zasu taho suka shiga kasuwa sukai sayayya taban mamaki, amma sayayyar da Shekh keyi tafi basu mamaki dan kaya yake saye masu tsananin kyau da tsada na Baby.
Husnah kau kasa hakuri tayi tace'' Hubby waya haihu da kake sayen kaya?.
Gira daya ya dagamata tare da fadin kece zaki haihu man.
Ido ta zaro sai kuma tayi dariya tana rungumeshi tace "Allah yasa wallahi ina so Baby nima amma shuru .
Murmushi kawai ya mata baice komi ba.
Bayan sun gama suka fito suka tsaya sukaci abinci suka koma gida duk agajiye suke .
Husnah kau sai turo baki take tana sake shishhigema Sheikh.
"Yadai Madam" yace cikin sanyi yana huramata iskan bakin shi da shafa gashin goshin ta da yanemi hadewa da girar ta.
Cikin shagwaɓa tace kaine.
Ok ok yace da sauri tare da ɗaukar ta sukayi wanka bayan sun fito suka raya sunna har mamakin jaraba datake da ita yanzu yake ,amma ba mamaki duba da karamin cikin jikinta watakil shine ya samata hakan wanda ko ita batason da shiba,Dan duk sadda zasu fita hutu suke amma yanzu bata son wannan ba.
Washe gari tinda Asuba sukayi Airport.
Suna zama a inda aka tanada dan zaman fasinjoji suka farajin wani fitinanna wari.
Gabaki ɗaya su kalle kalle suke dan wajen dama su ka ɗaine kowa ya koma baya sosai,sai wani mutum da yayi kasa da kanshi yana sanye da face maks .
Iya Dauriya sunyi daga karshe dole Husnah ta mike ta fara kelaya amai tana kuka da faɗin Hubby mubar nan wallahi mutuwa zanyi.
A rikice Sheikh ke shafa bayan ta da faɗin sannu sannu nima banson mine ke wannan warin ba ya fada yana jujjuya kai tare da zubama wannan mutumin ido da har lokacin bai ɗago kaiba.
Husnah ta fara kalle kalle cikin ihu tace.
" Ga wanda ke warin cen , Dan iskanci sai yamana kashi a wando ina dangin sa?
A zabure mutumin ya dago kai lokaci daya kuma ya zare maks ɗin fuskar sa ya fara kokarin tashi bakin sa na rawa yake nunasu da yatsa yace.
" Husnah.
Wani irin kallo takemai irin na ina na sanka shekh kau kama jikin sa yayi ya ɗaure fuska tamau yana rungumota jikin shi tare da fadin.
" malam ka tsaya a matsayinka banso ina jin sunan matata a kazamin bakin ka,waye kai,A ina ka son mu..
Kuka sosai mutumin yasa yace Husnah kina nufin baki ganeni ba, Husnah sadam ne fa Yaƴan ki ɗan uwanki
Tsawa Ahmad ya dakamai yace to miye namu,ina ruwan mu,baka da kudi ko kana dasu babu wanda ya shama kai,kaje Rayuwa ce ta isheka riga da wando,kuma dama karshen alewa kasa.
Sadam ya share hawaye yace.
" Husnah daga ranar da Aka daura auran ki na rasa duk wani farin cikina .
Kwana biyu tsakani na siyar da gidana dan in kauracema ƙaidar da uban mijinki yabani, in bar unguwar in koma wani wuri inda babu sanya ido, aka bani kudina cass tare da notice na sati ɗaya.
Da Daddare ina kwance aka zo aka ɓalle gidan tare da kwashe kudin aka tafi dani wani kungurmin daji akaita ganaman azaba daga baya na fahimci Zuma ce tasani wannan bala'in.
Mutanan dake tsarona haka sukaita fasikanci dani na zalinci tare da wasu siddabaru ina fidda masu manyan kudi.
Na dade wajen su kamin suka sakoni da saman dokar in nakara zuwa katsina sai sun lahantani hakan yasa dole na ari waya nama Hajj cakwai magana ya turomun kudi na yanki visa nazo nan wajen sa Dubai, anan ya hadani da turawa makiya Allah masu samun kwaya wata daya kenan takashina ta lalace bana iya control in bahaya zaizomun ne kara zube ina tafi ko zaune ko kwance,ga tsutsoci dake zuba hakan da suka gani suka koroni da bani kudin jirgi in barmasu waje,ko Asibiti basujin zasu iya kaini saboda yanzu bani da rana gare su,Husna naga ishara naga butulci ga wayanda na yarda dasu ki yafemun..
Shekh yace yayi Habibty ta yafe maka Allah ya shiryaka in da rabo.
Ameen yace tare da fadin nama shiryu inba damuwa dan Allah kuzama Abokai nah.
Gabaki ɗaya suka gwalo ido suna masa kallon mahaukaci...
UMSAD MAKENTOSH
*Makentosh*
*Makentosh*
*Makentosh*
Ina macen da ta isa takejin takai Hajiyar gayu.
*HMMM DA SAURANKI HAJIYATA INDAI BAKYA AMFANI DA MAKENTOSH*
Matso kiji hajiyata
Kamar yanda kuka sani UMSAD INCENSE ta sake zomuki da wani sabo sahihi mai suna MAKENTOSH
MAKENTOSH wani sirrine nasu na mutan Maiduguri,yana da masifar kyau yana hade mace gam koda haihuwa goma tayi,ina uwargida ina amarya ina budurwa ina zawara duka dai gudun'muwace daga mai kishinku har kullum UMSAD INCENSE.
Ina baku shawara da ku nemeta dan magance matsalolin da suke faruwa damu tsakaninmu da mazajenmu dan gyara shinfiɗarmu kai tsaye.
Ni Ummy Aysha shiyasa na kasance shalele awajen mai gidana saboda gabaki ɗaya sirrin gyaran jikina yana Tattare da gudun muwar UMSAD INCENSE shiyasa koda yaushe muke cikin walwala da farin ciki da mai gidana🥰.
Dan neman farin ciki akoda yaushe tsakanin ki da mijinki ki tuntuɓeta a wannan layin
Sayen nagari maida kudi
UMSAD INCENSE 080 288 27241
5️⃣9️⃣&6️⃣0️⃣
A zafafe Umar yace.
* Lallai ka samu taɓin hankali,da ƴaƴan sunnah kakeson haɗa Alaƙa,to bari kaji wallahi billahi tafiyar nan dakai bazai yiyuba,saidai su son yanda zasuyi dakai , Amma babu gidan ubanda zamu iya zama dakai ahaka ka kumburamuna ciki.
Abinka ga Babba nan yayi ya shiga ya fita dole aka dakatar da tashin Sadam gudun karya cutar da mutane , Wasu suka bashi sadaka dan ya fara zuwa Asibiti a ɗan magance mishi wani abu kamin yatafi .
Korashi akai daga wajen yatafi yana kuka da dana sani Yau yaga sharrin ruɗun duniya.
Sai lokacin Husnah ta sauke Ajiyar zuciya tana jin yanda zuciyarta ke ta tashi.
Ahaka suka hau jirgin tanata kwara amai Gabaki ɗaya ta galabaita,Haka suma gabaki dayan su a rude suke ba kamar Yah Sheikh.
Suna dawowa kano suka sauka, basuyo Gidaba suka zarce Asibiti, Anan aka bata gado tare da mata gwaje gwaje inda aka gano ciki dan sati bakwai a jikinta .
Gabaki ɗaya bakin cikin su ya koma farin ciki, SHEKH kau dama yana wannan hasashen, gashi yanzu an ida tabbar mai har sujjada yayi dan nuna godiyar sa ga Allah.
Shata mota sukai sai gasu katsina gab da mangariba cikin ikon Allah, gabaki daya su ummy sun rikice da ganin yaran nasu sai hidima ake masu ta ban mamaki.
Su Abbah kau fara'a tamkar mi mussamman dayaji ance Husnaty sa nada juna biyu.
A takaice dai wannan rana sunga gata .
Abbah yaba su Umar wani katon gida daya saya kusa dasu yace.
" gashi kuma yara nane na siyamaku wannan gidan ne dan banaso kuyi nisa dani , Umar, Ahmad, Saleem, gashinan halak malak na mallaka maku
Rungume Abbah sukai dan sunma rasa wane iirin murna zasuyi,samun siriki kamar Abba a wannaj zamanin akwai wahala,Baya jira amai a matsayin sa na dattijo kawai yana masu abinda ya dace kamar yanda zaiwa yaran sa.
A haka Rayuwar taita tafiya ,In da Shekh ya faɗa harkar kasuwanci gadan gadan kuma Allah yasama abun Albarka,Dan sosai campany Daddy ya tashi aka fara samun Alkhairi cikin wata kaɗan aka mayar da asara da akayi.
Ta ɓangaran Abbah ma sun haɗa wani kasuwancin shida Daddy Shima ba karamin riba suke samuba dan danan dukiya ta sake zamar musu babu abinda suka nema suka rasa,Babu wanda zaice ba jini daya sukeba duk inda zakaga Abba zakaga Daddy,Ga taimako sadaka yi suke sosai,sun fidda duk jama'ar karshe wata sukanje Asibiti su bada taimako sosai na marasa lfy manukata wayanda za'aima aiki basu da hali ko magani duk sukan biya,Wannan ma ya kara masu girma da daraja ga idon bayin Allah.
Bayan wata bakwai.
Husnah ce na hango zaune da wani zabgegen ciki jikinta ta koma katuwar gaske gabaki ɗaya ta kumbura.
Sheikh na zaune kasa hannunsa rike da towel yana tsomawa a ruwan zafi yana h
Gogemata kumburin da kafar tayi.
Cikin halin jin jiki tace..
Hubby anya ba mutuwa zanba, ina zan iya haife wannan cikin?Yamun kato Wlh takarasa cikin kuka.
Cikin tausayinta yace'' in sha Allah Habibty zaki haihu lafiya kinji karki damu.
Kai ta jinjinamai tana cije lips dan tin asuba mararta ke mata wani fitinan nan ciwo.
Ganin yanda taketayi yasashi cewa yakamata muje Asibiti Habibty.
Kai ta gilgizamai tace" A'a ba yanzuba sai next month zan haihu, ko munje babu abinda zasuman .
Hajjah ce ta fito daga Ɗaki dan dole ta dawo gidan saboda haihuwar Husha.
Itace tace A'a Husnah ba awasa da lfy muje Allah ya rabaki da wayan nan yaran lfy.
Ido ta zaro tace yara kuma?
Hajja tace ke ina nufin yaron cikin ki.
Ajiyar zuciya ta sauke lokaci daya kuma ta zabura tana sakin salati da shako Wuyan Yah Sheikh jikinta ya fara rawa Sosai.
Gabaki ɗaya suka rude cikin jarumta Sheikh ya sungumeta yayi waje da ita aguje yasa mota Hajja ta biyosu da Hijjob dinta Hankali tashe.
Asibiti datake awo suka nufa bayan sunje aka dubata aka ga haihuwa ce amma kwanciyar yaran ba daidai takeba akwai bukatar ya sanya hannu a mata aiki.
Cikin tashin hankali ya sanya hannusa cikin kankanan lokaci aka shiga da Husnah Theater room.
Anyi aiki cikin nasara aka fiddo mata kyawawan yaranta huda biyu duka mata masu tsananin kama da shekh kamarma har ta ɓaci .
Ana kawosu ko kallon su baiba ya fara tambayar lfyr matar sa.
Saida suka bashi waje ya shiga ya ganta kana ya samu natsuwa ya hau yimata Addu'a cikin tausayi.
Yana kallon yanda ake dinke Fatar cikinta kamar kwarya, wani irin rauni da kuka ne ya kufcemai,lokaci daya ya kara bata matsayi mai girma a cikin rayuwar shi,lallai ba mai wulakanta mace sai wulakantacce,mata ba abar cima mutunci bane,mata abar lallashine,irin wannan wahala da sukesha kadai abar a tausayamasu ce,yana Addu'a Allah kar ya gwadamai ranar da zai wulakanta Husnah, dan tayi mai rana arayuwa,ta sadaukar da rayuwarta akan farin cikin shi da nata, Yanzu nan zata iya rasa rantafa wajen kawo yaran shi duniya, Yah Allah yace yana shafa fuskarta da tofamata Addu'a har sadda aka gama aka kimtsa ta .
Da kanshi yake turo gadon datake kwance kamar gawa idon shi na fitar da kwallah.
Tinda ya zauna akan kujera kusa da ita bai sake motsiba sallah kawai ke tadashi amma har lokacin baiga fuskar yaran ba dake hannu su Hajja, Dan kamarma fushi yake da kowa ta matar sa kawai yake,Fatan shi yaga tashin ta cikin koshin lfy.
Hankalin shi bai dawo jikin shi ba saida yaga Husnah ta fara motsawa, tana fadin Ruwa! Ruwa!! Hubby!..
Da sauri ya fita ya kira likitocin sukazo suka dubata ,ba wani matsala aka tadata ya wanke mata baki ya bata tea tasha yamata sannu.
Murmushi tayi tace Hubby ina jaririn dana haifa?.Ina fatan dakai yake kama..
Sai lokacin ya saki murmushi yace.
" Sannu da ƙoƙari Baby yara biyu kika bamu.
Ido ta zaro tace dan Allah fa?.
Kai ya jinjinamata cikin tabbatar wa yana Mikewa ya fita yazo wajen su Hajja yana faman Murmushi.
Gabaki ɗayan su suka ɗaure Fuska kamar hadi baki suma adole sunyi fushi tinda tin ɗazu sukemai magana ya kyalesu.
Ummy ya kallah da taci kuka ta gode Allah, dan Ummy akwai tausayi,Tinda Aka cemata Cs za'ama Husnah take kuka umma kau addu'a kawai tayi cikin Dauriya .
Hannusa ya hade yace Affuwan Ummy.
Inna tace Dan wulakanci munatama magana ka kyalemu sai yanzu to baza'abada yaran ba .
Murmushi yayi yace sorry Albishir mai dadi Habibty ta tashi zaku iya shiga ku ganta.
Gabaki daya kau suka mike kowa farin ciki ga fuskarshi sukayi ɗakin da Husnah take.
Dakin suka fada suka hau yima Husnah sannu da jiki tana kallonsu da murmushi murya kasa take amsawa.
Daganan ya kwashi yaran ya tsura masu ido yana kallo wata soyayyar Ɗa da mahaifi yakeji yana shiga zuciyar shi,take ya masu Huɗuba ya raɗa masu suna ɗaya Husnah daya kuma maryam wato sunan Inna Dana Husnah..
Nanfa aka cika da murna da fatan Allah ya rayasu.
Ameen yace yana gwadama Husnah yaran ta kawar da kai tanajin kunya.
Hakan