Showing 15001 words to 18000 words out of 69765 words

Chapter 6 - MATAR AURE BOOK COMPLETE PDF.txt

gida saida ciki, shiyasa har'yau bantaba zuwa gidan muba,Kuma a yanzu naga ya hudo da wata hanya wacce bazan laminta ba,Zata iya sanadin zaman Auran mu koda kuwa hakan zai iya zama Abinda zanyi akarshen numfashi na .


Inna ta taɓa hannu tace" kai amma wallahi akwai butulu Wannan mutumin, haba inama amfani Rashin Halacci.


Kai HABIBIEEE kabata sha'wara mana yanda zata gyara Auranta yafi wannan lumshe idon da kake,Dan ni girki zan Ɗaura kamin mu zauna da ita takarasa tana mikewa ta fita ta barsu su kaɗai.


Ƙasa ya sakeyi da kanshi yanajin nawin zaman su waje daya,to shiminene zaice?.


"YAH SHEIKH Inna tace Kamin Nasiha, kabani shawara dan Allah, kafadamin mafita matsayinka na masani akan zamantakewar aure,Ina son in samu farin ciki kamar yanda natashi naga mahaifiyata nasamu daga Abbah nah..


Karamin bakinshi ya tsuke kana ya dago kanshi ,duk yanda sukaso su kaucema haduwar kwayar idonsu kasawa sukai,dan Dukkan su zaka'iya karanta abinda ke Tsatsafowa daga zukatan su,Yah Shekh zuciyar shi na cike da rauni gami da bege da kuma son samun abinda yafi karfinshi, wanda wannan alhakin zuciyarshi ne ta kaishi garin da bazaya dawo ba,Tana neman kaishi kan Tsaunin da bazai iya sakkowa ba,tana neman sashi ya halaka,tana neman Tusashi wajen da baidace dashiba, Tana neman sashi Dajin dake cike da kayoyi masu Tsananin suka . .


Husnah kam kyau da zatin da rabbi yamai gami da kamala take ganin,ga tsantsa addini da natsuwa,inama ace sadam nada natsuwar malamin ta da wallahi zata iya zama dashi koda zata mutu baice yana sonta ba.


"Husnah ki gyara auran ki,kiyi duk abinda zakiyi wajen jawo da hankalin mijinki akanki,zan iya cewa sakacinkine Ya jawo haka,taya kina gida kika bashi dama da wata kofar kula matan banza a waje, Akwai abinda kika rageshi da shine?.


Inaso kije kiyi nazari, Tin'daga tsaftar gidanki, gyaran muhallinki,kuma dashi kanshi mijin naki dole ki bincika kikuma gano gaskiya daga ina matsala take,Ai ba kanku aka fara Auran Haɗiba,Kuma kuma kiga An'zauna lfy,An'kuma samu Albarka Aure Ya karasa Cikin rawar murya yanajin zuciyarshi namai nawie da kalaman da yake furtawa.


YAH SHEIKH,Wallahi ina gyara muhallina,Abinci kam dama bayacin irin cimar da yake bani Tinda nayi wata ukku,nashi daban nawa daban,kanan dama ai baya cewa inje wajen sa.


Afusace har yanamata tsawa tsawace yace "to sai yace ne ke ba mace bane? Dan haushi yaji tanaso ta nunamai baya nemanta sai inshi yazo kenan.


Kanta ta langwaɓe tanayi Rau Rau da ido kamar zatai kuka ta kalleshi tana turo dan karamin bakinta tare da shegwaɓe fuska wacce ta kasa sanin yama akai ta iya hakan gaban shi.


Sosai kam yanda tayi ya daki zuciyarshi,Da sauri ya hade fararan hannuwansa yana mai jujjuya kai yace "Affuwan Affuwan Mamanah bazan sake ba kinji Yakarasa cikin wata murya mai sanyi da Tsayawa A rai.




Kai ta dagamai tare da faɗin" Nagode Yah Shekh.


Kai kawai ya jinjina mata ya fara kokarin mikewa dan ya fita shagonsa.


"YAH SHEIKH kabani book din kaga lokaci yakusa cewar Husnah.


Dawowa yayi byanta ya ɗauki jikkar da yake ajiye littafin sa ya zarosu duka ya bata.


Nawane?


Kallon kanwa yakemata,awani gefen kuma kallon uwa, saboda sunan ta,awani gefen kuma yana tsananin tausayinta Dan yarinyace mai kananun shekaru, Amma batai Sa'a mijin da zai lalashetaba ya tarairayeta .


"Ki barshi ki adana kudin kya sayi wani abu dashi, yafada yana mai kokarin fita.


Da sauri tasha gabansa kamar zatai kuka ta mikamai duka 5k din tace "Dan Allah da manzonsa ka karɓa,kaga saika sake siyo wasu,ni ina da kudi babu abinda zanyi dasu.


Jin yanda ta gamashi da Allah yasa ya karɓa yana mai zarar 2k yabata sauran.


Kai ta jinjinamai tana sakin wani murmushi dayasanya duka Dimple ɗinta guda biyu loɓawa.


Wani masifar burgeshi tayi kuma hakan ya karamata kyau sosai.


Baison sadda ya karɓaba yana fadin" Jazakillahu Hubbul jannah.




Ameen ya hayyu ya qayyum tace tana fita da sauri tayi wajen Innah dake girkin Taliya yar hausa.


Kayan Inna tashiga shanyawa bayan ta ajiye littafin abakin kofar Inna.


Duk yanda Inna taso ta ajiye kiyawa tayi saima kuka dataso samata dole ta kyaleta tacigaba da tsince waken ta .


Lafiyayya taliya da wake da manja sukaci Husnah sai zuba santi take , Dan waken kamar Hanta.


Husnahhh!Husnahhh!!


Taji kira daga waje wanda kuma nurya Shekh ne ya ratsa dodon kunnan ta,Tinda Allah yasa tayi wayo bata taɓajin mutumin daya iya kiran sunantaba Cikin sanyin lafazi Kamar Sheikh Habibbullahi B Adam.


Inna tace yana magana Allah yasa wata fatawar aka sake samu kamin inbaki nawa nima.


Hijjob dinta ta zura ta fita abakin kofarshi ta ganshi tsaye.


Batare daya kalleta ba yace" Ki kula da kanki da lafiyar ki,ki kula kisanya ido da wayanda yake kawomaku,Idan son samune kiyi yaki dashi yadaina kawowa baki ɗaya duk da abune mai wahala,amma in an jure za'acimma Sa'a,Idan kau ankiji baza'aki gani ba,Dan Kwaya ɗaya zata iya zama ukku ,yana fadin haka ya fita cikin kamala tabishi da kallo *miye" Kwaya ɗaya zata iya zama ukku*
Oho bata saniba,dole ta koma tayi alwallah kana tayi sallama da Inna ta shiga islamiya da niyyar in ta dawo zata biyo.


Koda ta shiga ajin Hafsah kawai ta iske cikin wayewa suka gaisa tana janta da fira, Kamin ta kalleta dakyau tace miya sameki k'awata ga Fuska?.


Dariya tayi tace bigewa nayi fa.


Ɗan murmushi tayi dan som bata yarda ba, ko mahaukacin yaga fuskar Husnah yasan Mahangulɓa tasha,Amma bazata takurata ba tinda sirrin tane.


Hafsah tace "Wai Nikam ina wayar ki,bakya bani Number ki,ko chart mudingayi inba islamiya tinda ba zuwa gidanki za'aiba , Ni inaso muyi zumunci sosai Wallahi.


Ido tadan waro tace "kiyi hakuri WALLAHI bana chart sai dai kisamun Number ki kawai, banma iya budeshiba dana fara,Nifa duk banma son kar wayan ba,kawai dai gatanan shekaran jiya aka kawoman ita.


Mamaki sosai yakama Hafsah, Nan ta karɓa ta shiga budemata Whatsapp,ta samata WPS Office,Kana ta samata Hausa novel masu daɗi, Dan ɗebe mata kewa ,Daganan tasa number ta da ta wasu yan ajin kana ta turamata app na karatutuka sosai dan duk ta karu.


Wani irin runguma tayima Hafsah lokacin datake gwadamata abinda ta samata.


Murmushi tayi tace" Yiwa kaine yar uwa ,zanma sa asaki group group zaki karu.


To tace daganan malam Abdallah ya shigo dan gabaki ɗaya Sun rasa gane kan Yah Sheikh,Dan ko kaɗan bashi da natsuwa indai zai ganshi gashi gata,akwana ɗaya ta hargitsa tinanin shi wanda har tsoron tabbatar da abinda ke shirin faruwa dashi yake shiyasa yama kanshi faɗa akan son rage samun kusanci da ita..


Bayan ya gama yafita suka zauna shuru baizoba sukayo murajia suka tashi .


Husnah a tsaitsaye tashiga gidan Inna tana sauri tace" Inna zan koma kamin yadawo.


Tace shikenan Husnah ki kara hakuri, Amma wallahi sai kin kiyaye , Dan Cututtuka sunyi yawa,kibashi lokaci Allah ma yaga zuciyarki akan kaurace masa ,zakiyi ne dan kare kanki da lafiyar ki daga cututtukan zamani,karki yarda ya dinga kusantar ki wallahi inamaki dallah dallah har sai an tabbatar da lafiyar sa,kinji ko,Kuma wallahi , Billahillazi duk sadda ya sake dukanki sai kinbar masa gidansa barazanar sa ta banza, kidawo gabana ki zauna sai inma iyayenki waya suzo su ganema idonsu kinji ko?.


Kai ta jinjina tana faɗin" Nagode Inna, Allah yakara girma kana tamata sallama ta fita.


A tsorace ta shiga gidan inda ta samu tabbaci daga mai gadin gidan cewa Sadam bai dawoba kana ta shiga .


Agulguje ta hayda duk abinda zata hada da zata bukata dan bama yunwa takejiba tayi sama, Kana tasama
Ɗakin ta key tabarshi jiki tayi Sallah, Tayi azkar, Tana zaune har akayi isha amma sadam bai dawoba .


Sadam


Tinda yabar gidan yaji ranshi bace miyasama tini bai haƙema yarinya nan ba, miyasa ya tausayamata,indai har zayyi mu'amullah da wasu ai yakamata ya hada da ita, amma wani tinaninsa na banxa yasashi kasa cimma burunsa.


Ahaka ya isa office dinsa sai dai zaman ya isheshi,duk yanda yaso ya daure kasawa yayi, dan yana da fitinanniyar sha'awa baida jimirin zama ba mace kusa dashi ko kaɗan ,Tin Gana ya riga yasaba mu'amullah da mata ,Gashi yanajin zafi akan Hajiyar sa Dole yasamu Yayi abinda zai maidomai da kuzarinsa baki ɗaya .


Ganin bashi da mafita yasahi kiran Amira amma wayar kashe , Dole ya hakura amma zuwa azahar mararshi ta cika ta kulle dole yasashi tashi ya fara zaga gari amma baiga wadda Tayi kama da Karuwai ba, Duk mutanan kirki ne masu dogon Hijjob .




Mai gidanshi ya kirashi akan yana son ganin sa anan gidan sa dake cikin Goruba , dole ya katse komi ya tafi bai samu fitowaba sai yamma, Anan ma ya nema shuru dakyal ya iya jan Motar sa yaje bakin Katsina motel inda yataɓa ganin zuma.


Yadade wajen kana wata tayo wajenshi tana kwarkwasa da hura hanci.


Dakyal ya tsaidata yace" kinson wata mai suna zuma anan kuwa?


Eh batajin dadi tana Ɗakinta sabon layi, a kwance batasami fitowa ba.


Ok ɗan bani address nata zanje indubata yafada.


Murmushi ta saki kana ta bashi ta wuce, Tana matsawa ta kwashe da wata kafurar dariya tana fadin komi zai tafi dai-dai .


"Zuma"


Tinda tabar gidan cikin bacin rai taje tasamu aka dan Wanwankemata raunin dayamata, Tare da bata magani kata ta wuce Sabon layi, Anan tabama Magajiya labarin abinda ya faru, Tare da rantsuwar baza'a kwana ba saita rama , Saboda tason ta lasamai zumar da sai ya nemeta da kansa,Har kudi ta ɗorama magajiya akan in'baizo nemanta ba zata bata.


Hakan yasa Suka tsara yanda abun zai kasance, Yini guda Magajiya tayishi awajen har sadda Sadam yazo kana taji daɗi ta turama Zuma text message akan yana hanya.


Duk Adress ɗin da aka bashi yabishi har kofar gidan su,Sanin ko ina ne yazo yasashi shiga kai tsaye ba tare da neman iziniba,A tsakar gidan yayi tsaye yana karemai kallo.


Madaidai cine mai ɗauke da Ɗakuna shidda sai bayi guda biyu.


"Mtsss Ashema matsiyaciyar anan take amma take nuna ita mai tsadace,Yau zanmaki kaca kaca in tsallakeki inbarki shegiya yafada yana lalleka dakuna har yazo daki na hudu.


Ganin manyan photina ya tabbatar mai da nata ne.


Hakan yasashi shiga yana karema Dakin kallo.


Katuwar katiface a ciki mai tudu,sai ko kayan kallo da sauran kayan buƙata.


Bakin shi Ya taɓe kana yace Karamar Yar iska,jibi Ɗakin kamar na agwagi.


Yaakai na uwar kane ɗan samari?


Yaji wata basamudiyar muryar ɗan Daba na fadi.


Da sauri ya juyo anan yaga katti sunkai su goma sai Zuma a gefen su tana sakin Murmushi.


Tare da faɗin"Kuyi abinda ya kawo ku *MAKASHI*


UMSAD MAKENTOSH


*Makentosh*
*Makentosh*
*Makentosh*


Ina macen da ta isa takejin takai Hajiyar gayu.


*HMMM DA SAURANKI HAJIYATA INDAI BAKYA AMFANI DA MAKENTOSH*


Matso kiji hajiyata


Kamar yanda kuka sani UMSAD INCENSE ta sake zomuki da wani sabo sahihi mai suna MAKENTOSH


MAKENTOSH wani sirrine nasu na mutan Maiduguri,yana da masifar kyau yana hade mace gam koda haihuwa goma tayi,ina uwargida ina amarya ina budurwa ina zawara duka dai gudun'muwace daga mai kishinku har kullum UMSAD INCENSE.


Ina baku shawara da ku nemeta dan magance matsalolin da suke faruwa damu tsakaninmu da mazajenmu dan gyara shinfiɗarmu kai tsaye.


Ni Ummy Aysha shiyasa na kasance shalele awajen mai gidana saboda gabaki ɗaya sirrin gyaran jikina yana Tattare da gudun muwar UMSAD INCENSE shiyasa koda yaushe muke cikin walwala da farin ciki da mai gidana🥰.




Dan neman farin ciki akoda yaushe tsakanin ki da mijinki ki tuntuɓeta a wannan layin






Sayen nagari maida kudi


UMSAD INCENSE 080 288 27241




Data service available
1gb 250
2gb 500
3gb 750
4gb 1000
6gb 1500
8gb 2000
Account number 1479603206
BANK name ......
BANK account jaiz bank
Phone number 09064260199


❤️ *MATAR AURE*❤️


*NA*
❤️ *UMMY AYSHA*❤️
1️⃣5️⃣&1️⃣6️⃣


"*Cikin mamaki da jarumta yace "mikike nufi,kamarya suyi abinda ya kawosu,kardai ace wayan'nan Yan kwarin ni kika kawomasu,wai kina nufin dukana zasuyi shiyasa kowa da makami a hannunasa? Hahahahaha ya kwashe da dariya tare da fadin " Yaro baison wutaba saiya taka,to mazaje Bissimillah, ku daki sadam,yau iyayen ku da sai dai su haifi wasu wallahi,Banzaye ƙazamau yayi tsaki zai fita cikin isa yake tafiya.


Tass tass!! yaji wani bahagon mari hagu da dama .


Cikin tashin hankali ya ɗago fuskar shi sukayi ido hudu da Zuma dake huci, Tace'' kai Harka isa kaci banza ,kana nufin duk dukan dakaman yatashi abanza,badai takamarka duka ba kaiga babban kwaro,mazaje ku daki shege kota ina tafada tana Tillamasu rafar kudi yan 200 .


Caaa sukai kanshi suka fara duka kamar zasu kashe shi.


Tin yana ƙoƙarin kare kanshi har ya gaza dole ya durkushe yana kuka.


Saida sukaimai jina jina kana suka fita dashi suka sanya a mota Zuma ta taja motar har kofar gidanshi kana ta fita suka hau napep da samarin nan ta koma gidan su, Suma suka shiga ɗakin data kama masu na tsawon wata biyar saboda tsaro .


Mai gadin Sadam ne yaga message ya shigo wayar shi hakan yasashi bude gida ya fito da sauri,,jikinshi har rawa yake ya wangale get amma shuru Sadam bai shigo ba.


Hakan yasashi Matsawa jikin motar yace" kayi Hakuri Yallabai banji hon dinka ba,jin'shuru kimanin mintina yasashi bude motar, acen baya yaga Sadam kwance jikinshi duk ya ɓaci da jini sai nishi yake sama sama.


Ido ya zaro kamin ya bude yama sauran security magana suka fiddoshi Yanata nishin wahala, Nan yan unguwa sukayi dafifi wajen amma duk kan wanda zai bude baki baya cewa Allah yasawaka sai dai allayh yakara..


Cikin galabaita yace ku ajiyeni palo.


A palon suka ajiyeshi .


Mai gadin yace yallabai akaika asibiti mana jibi jinin daka zubar.


Aa barshi yafada yana sakin nishin wahala dan bayaso kowa yason abinda ya samai.


Fita sukai suka kyaleshi shikuma ya kwanta yana kiran Husnah ciki ciki.


Husnah kam tinda tagama komi ta haye gadi tafar chart dayan gidan su Da Hafsah,bata sake motsiba har sai karfe 10 kana bacci ya kwasheta mai dadi .


Yah Sheikh


Rayuwa tamai zafi kunci yakaimai ziyara , Yana cikin wani mawuyacin yanayi wanda ke bukatar ɗauki,Saidai ko mahaukacine shi baidace ya tinkari kowa da wannan maganaba balle abashi shawara,A kullum zuciyarshi kara azalzalashi take ga kusanta kanshi ga rayuwar Husnah,to amma taya,bayan ita din MATAR AURE ce.


Karfe 2 na dare yana juyi gabaki daya bacci ya kauracema idonsa, Duk yinin ranar Kokon safe ne kawai acikinsa, Gabaki daya bayakin dadi,daga lokacin dayaji yanda take zama agidan mijinta yafarajin yanajin wani masifaffan nawie a Zuciyar shi,"Dan Allah karka cutarmun da uwa" yafada abayyane cikin rawar murya,Shi ba yaro bane kana yakaranta yasani,duk wani nauin so ya sonshi,Dab ana masa shine dai baitaba furta yana son wani ba,amma ko Ɗalibbanshi sunsha kawomai hari , Saidai ya kori yarinya, Amma yanzu shine yakejin SO da kaunar MATAR AURE mai tsananin na ratsa lungu da sako na jikinshi.


Ya daɗe yana saka da warwa kamin A'hankali bacci mai daɗi yayi nasara cafke shi.


Sadam kau ganin Husnah ba sakkowa zataiba yasashi Lallaɓawa dakyal yashiga dakin dake kasa ya kwanta yana nishi sama sama, Idon shi na tsiyayar da hawaye inda suka daka sosai,Babban tashin hankalin shi ko gani dashi bayayi sosai.


Wallahi saina kulleki yafada dakyal bacci na kwasheshi.


Washe gari takama Asabar, Husnah makaranta safe takeyi bata yamma ba ,Karfe takwas ta kammala shirints ta buɗe jikkar kuɗinta ta kwashi 10k da wayar ta, ta sakko cikin sanda aguje tabar gidan.


Sadam kau daya tashi dakyal ya iya bude ido duk yayi ruwa yayi kwantsa saboda ciwon da suka jimai,dakyal ya lallaba ya shiga toilet yayi fitsarin sa daga tsaye bai tsaya koyin tsarkiba balle Alwallah ba ya fito ya fada akan gado yana tsinema Husnah, Tare da tinanin irin dukan da zaimata,ace suna gida daya amma takasa zuwa duba lafiyar sa bayan tin jiya bata sakko ba.


Ga jikin shi wani irin tsami yakemai kota ina ciwo yakemai,yason in yace ya sanya ruwa sai ya kusa mutuwa shiyasa ko alwallah yakasayi(Dama bata shama kaiba Ɗan hegiya)


Wayarshi ya zaro ya kira Mai gadinshi akan yasa Dumba ya siyomai abinci.


To yace kana ya fadama Dumba,zuwa Yayi ya siyo ya dawo yace su kawomai daki.


Da sallama Dumba ya shigo dakin yana neman inda yake.


Dumba ganinan yafada dan yaji lokacin da aka turo.


Bin Ɗakin dayaji muryarshi yayi da ido kamin ya kutsa kai yana wani Bubbuɗawa yaja yayi tsaye ba sannu ba komi sai hura hanci yake .


A fusace Sadam yace "Taimakeni intashi kaji katon banza,Haba sai cika kake kana batsewa saikace bani na ajiyeka ba .


Wai oga wane dan yarinya ne ya taboka haka,wannan dagani majaujawa akai tayi dakai cewar Dumba yana murmushi.


Tsaki yayi yace" Ni har akwai wani shegen da ya isa ya dakeni a garin nan, Babu shi wallahi,kai ko kai da kake ganin ka kato wallahi baka isa ka kara dani ba,tashi kabani wuri sai tsami kake kamar Arne.


Murmushi yayi yana hada hannuwanshi yace" sai oga,kai dai kawai arzikin ka ɗaya, Da kake bamu na abinci amma wallahi ni har wanda yafika ina iya karawa dashi ,kuma wallahi saidai akwashi mutum.


Tass! sadam ya ɗauke ƙatuwar fuska Dumba da mari mai shegen zafi .


"Kutumar jar bura'uba,Mene? nika mara ,aiko zaka gane banyi lalacewar da zaka iya dukana ba wallahi in kyaleka, Nan ya Nannaɗe Sadam waje daya kamar kayan wanki, Ya hayemai ruwan ciki tare da turamai wani karamin towel a bakinshi yashiga duka kamar an aiko shi.


Saida yamai ligif baya ko motsi kana ya watsar dashi tare da tashi cikin bacin rai ya haye sama inda ɗakin Sadam ɗin yake,saida ya bincika komi ya watso komi ya kwashi tass kuɗaɗen dake cikin wadrop yasa a jikka, Tare da sakkowa yana mazurai ya ɗauki key din motar sa dake kasa yace "Gida da mota saina kwasheka tass, gobe ma in halinka ne ka sake Dukan wanda bakason ko waye ba Matsiyaci.


Motar sadam ya bude ya shiga neme neme amma bai samu kudi ba, sai wani akwati babba wanda yake da tabbacin kayane.


Har yayi tsaki zai juya yace" Ai kwara ko kayan ne in ɗauka in siyar, Raba mugu da makami ibadane, Ya sunkuci akwatin yayi waje yana tillamai mai gadi key ɗin motar akan ya ajiyema Sadam.


Mai gadi na faɗin" Ina zaya?


Yace" aikenshi yayi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login