Showing 30001 words to 33000 words out of 169868 words

Chapter 11 - MAR'ADAM'S BOOK 2 COMPLETE DOCUMENT by Aisha Bagudu .txt

06 Nov 2024

10857

tayi kmr bata fahimcesa ba har tayi taku biyu taji Kmr ya mike ai da mugun gudu tayi Kan step, bata tsaya akoina ba sai a dakinta har da rufe kofar ta tsaya tana haki da maida numfashi "bayan ta samu natsuwa kwalla ta zubo mata "bata san tana tsananin tsoronsa ba sai yanzu yaya adam baya sona gashi ni kuma ina sonshi ta fad'a a fili cike da sanyin jiki ta zauna jugun tare da dafe kuncinta ."




kusan awa daya taji motsin fitar motocinsa ta sauko da sauri sai dai hawaye ne ya zubo daga idanunta
Sakamakon ganin ya rufe kitchen din duk inda ta kalla acikin parlour'n babu wani abu da zata iya sakawa cikinta dole taja jikinta ta dawo daki bayi ta shiga ta dauro alwala ta gabatar da sallar laasar ta kwanta lamo a saman abun sallah yunwa na nukur kusanta sai tayi kamar ta kira mami akawo mata abinci sai tayiwa kanta fad'a ta maida wayar ta ajiye ."




wasa wasa awanni suka dinga wucewa duhu ya fara sako kai lokacin magariba yayi a daddafe ta tashi tayi sallahr magariba ta dawo ta kwanta a haka ishai tayi wanda zuwa wannan lokacin ta fara raina kanta tuni hawaye ya fara fareti akan kuncinta tasan mugunta da kuma hukuntata yasa yayi haka tana daga kwance amman jiri take gani saboda tsananin yunwa tuni idanunta suka canza kala saboda kukan yunwa da take bata san yunwa bata da hakuri ba sai yau hatta test din miyon bakinta ya canza ."




Ata kuwa tunda ya fita yana wajen wani abokin kasuwancinsa daya sauka a kasar yau din nan sun jima suna tautaunawa akan kasuwanci shi kanshi banda coffee babu abinda yasanyawa cikinsa karfe bakwai daidai a haraban family house dinsu tayi masa, yana qoqarin fitowa daga mota yaga direban mami na fitowa daga gidanta hannuwansa duka rike da wasu hadaddun kuloli “ aransa yace “shegiyar yarinya sarkin rashi hakuri har ta kira akawo mata abincin ,ai da baki kira ba yau haka zaki kwana da yunwa nonsense girl kawai .”




massalaci dake cikin esate din ya shiga yayi sallah bai fito ba har sai daaka idar da sallah ishai ya zauna yana azkar yana nadamar abinda ya fadawa mahaifiyarsa wanda yayi haka ne cikin zafin zuciya gashi yanzu yana dayasani ."ahankali ya dinga jin rashin kyautatawar da yayi mata , nan da nan kyakkyawar zuciyarsa ta dinga umartanshi da yaje ya bawa mahaifiyarsa hakuri ya nemi tafiyarta yayinda bakar zuciyarsa ke gargadinsa har ma da bashi karfin zuciyar nisanta kanshi daita .”




wayarsa dake ringing ya katse masa tunanin da yake ya ciro yana duba wayar sunan ammar ya gani ya dauka yana cewa "yaakayi ammar ?eh mun gama magana dashi yanzu haka ina family hausa ,ok bani minti biyar yanzu zaka ganin a gaugauce ya fito ."
Kai tsaye rufar da yake zama da bakinsa ya nufa inda ya iske ammar yana ganinsa ya washe baki yana cewa ango !ango !! angaishe da ango kasha kamshi"
"A ina kenan na sha ? A wajen ama... "kaga dan Allah malam ka barni naji da abinda ke damuna dan ni babu wani kamshi dana sha kuma bana saka rai zan sha shi har abada ".




“kai dai anyi mai cutar kanshi kai muguntar ma har da kanka zakayi wa ?"har kuwa karshen rayuwata zan cigaba da zama haka ban sha wannan kamshin ba ya fad'a yana zama acikin daya daga cikin kujerun dake ajiye agurin ."ai ni an gama da rayuwata an cuceni wallahi amman I think kawai zan samu wata in aura dan bazan iya rayuwar aure da wannan yarinyar ba dan sam sam attitude dinta is something else..." ya fadawa ammar yana jan dogon tsaki .”




"hmmm amman da kayi hakuri ka d'an sake daita kad'an kagani ko tafiyarku zatai daidai "no it can be possible ammar "okay idan haka ne na hadaka da wata sabuwar mai bautar qasa dake karkashin kamfaninmu yarinyar tana da kirki sosai , koni bancin bani da wata matsala da salima dana shiga sawun masu nemar aurenta dan yarinyar akwai natsuwa da kirki ga kamun kai .”




shuru ata yayi without saying a word."Ko baka sonta ?.."ammar ya tambayesa, ahankali yace
" ammar I don't really know tunda banganta ba amman bani da zabi tunda na rasa princess zan iya manage da wata "ya qarasa mgnr yana duban fuskar ammar" to kayi hakuri da mrym din kawai madadin ka qara da wata tunda itama wacce zaka aura din ba sonta zakayi ba manage ne ai kaga gara kawai ka dinga rage zafi da mrym kawai zai fi ga tarin ladan aure gana biyayyar mahaifiya" over my dead body ni fa I can't let the woman I hate touch my fingers balle hannuna har azo ga jikina gaskiya ammar bazan ta'ba Iyawa ba ."




“Bama zan barta ta ta’ba ni ba bare ni na kai kaina dan rage zafi tayi zamanta haka nima nayi rayuwata haka amman batun rage zafi ma duk bai taso ba “
ATA sai hakuri fa kuma wallahi irin wannan auren ma ya fi dadi gashi da alamun mrym din ma tana sonka zakayi yadda kakeso daita har Allah yasa ka fara sonta “ammar ya fada yana dariya, da sauri ATA ya daga Kai yana cewa "me yasa kace tana sona ?ai mace idan bata son mutun da wahala ta yarda a daura aure ka duba nuzla misali ce guduwa tayi har sai byn daaka daura auren hisham da nana hauwa'u ".




“wannan ba gskiya bane , nana hauwa'u ta auri hisham ne ba dan tana son shi ba hakazalika nima na auri yarinyar nan ba dan ina sonta ba "anya kuwa wata killa fa nana hauwa’u tana son shi ta boye ne kawai dan bata damar samunsa a wannan lokacin dan hk kawai ka rike marym dinka kamar yadda hisham ya hakura da nana hauwa’u ."I can't" ya fada atakaice, dariya ammar yayi yana cewa "Ka bani dariya,irin ku né da anyi mistake kun kusanci matan da baku so sai ciki."duk fa zaka gama cika bakin kiyayyar ne ka gama zaka zo ka nemi hakinka ".




“Allah ya tsareni da ganin wannan bakar ranar "kai dai sai idan babu rabo a tsananinka daita amma wallahi in da rabo komin kiyayyar dake tsakaninku sai kun jone anyi ciki " ammar ya fada masa hk cike da zolaya ."yanzu ya batun yarinyar da nayi maka maganarta yanzu zaka aureta na hadaku dan gsky idan dai da gaske aure zaka qara gara wannan yarinyar ?” wallahi kawai sweetheart nake tunani nasan ma da wahala ta barni “bayan ta matsa maka ka auri zabinta sai kuma ta hanakali qarawa gsky ta barka ka qara tunda kana so .”




“Kai dai bari kawai ammar abinda nasani ko banyi acikin lokacin nan ba zanyi a gaba ko nan da shekara goma ne sai na qara aure "Gsky abun naka na gaske ne "kai dai ka tayani addua Allah ya bani wata mai kyau kamar irin mace da nike so “da gudu ma kuwa zaka sameta dan wannna yarinyar da nake maka mgn akanta ta had’u sosai” ata ya girgiza kai "da wahala haduwarta ta burgeni nifa ina da test "okay kenan ya kamata ka hakura ka rungume matarka amman kuma wallahi maryama ta had’u matar manya irinku ce ".


"Maryama !"?ya furta sunan a tsanake yana duban ammar yana jin sunan na ta'ba ranshi wanda bai kamata yaji hkn akan kowa ba sai akan princess dinsa ,muryarsa a kasalance yace "sunansu daya da wannnan dolen dolalon yarinyar "wacce kuma haka ? wannan yarinyar daaka aura min mana“yayi mgnr yana jan tsaki ammar yayi murmushi yace” eh sunansu daya ko bazaka aureta bane sbd sunansu daya ?kai ban son iskanci ya kake wani tursasa ni kamar dole to bazaa aureta ba muyi abinda ya kawoka nan da nan yayi qoqarin canza mgn zuwa ta business dinsu.”




Ammar kuwa sai faman dariya yake “wallahi ata kabani dariya ” wai dolen dolalo kai ata wallahi baka da kirki nifa ina jiye maka tsoron ruftawa karkazo kana rokonmu muje maka rarrashin dolen dolalo tace sam bata san da wannan ba “wani tsaki yaja yana maka masa harara .”bai sake cewa komai ba ya mike tsaye yana cewa “ina ganin baka shiryawa kasuwanci ba “ko kafin ammar yayi magana tuni ata ya soma taku “ata tsaya mana dan allah ka dawo muyi mgn tsaki yaja ya shiga bayan mota dan tuni masu tsaranshi sun bude masa gidan baya .”






Mmn sudais


💗💗💗💗💗💗
MAR'ADAMS
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗




*AYSHA A BAGUDO*


WATTPAD @HAUESH
AREWABOOKS USERNAME
AYSHAABAGUDO
bismillahirrahmanirrahim


Wannan littafin na kudi ne mai bukatar karantashi byn na kammalashi zai biya 1000 ta wannan account number din 1438775094 Aishat abdullahi access idan an tura sai a turawa wannan 09136918331 alert domin tabbatar da an tura domin sauraron littafaina a tuntubi chaneel dina (Hausa bakwai ) a YouTube.




Page 7


Ahankali motocinsa suka fice daga cikin abdullahi estate ,mr ATA zaune a bayan mota yayi shiru yana sake tariyo tautaunawarsu da ammar shi dai baya jin zai auri mai kamanceceniya da harafin sunan maryam ma bare mai sunanta, sai kace babu mata a duniya masu sunan arziki sai nata , tabbas shi yasan dan dole ya qara aure kuma acikin tsakankanin wannan lolacin amman kuma ba mai irin sunan yarinyar ba .”wani dogon tsaki yaja sanda ya tuna dole zai koma ya kwana gida d’aya da yarinyar da yafi tsana .”




Qarfe goma daidai suka qaraso bakin get din gidansa wanda sai alokacin ya tuna daya sallami masu tsaron get din gidan, hakan yasa ya lalubo wayarsa ya kirasu su dawo bakin aiki kuma alokacin wanda zuwa wannan lokacin motocinsa sun kutsa zuwa cikin haraban gidan kai tsaye parking space suka nufa .”sukai parking suka firfito da sauri ata na qoqarin bud’e murfin kofar motar mutun d’aya acikinsu ya bud’e masa cike da girmamawa . “




cike da natsuwa ya fito daga cikin motar ya tsaya yana magana can kasan makoshi “gobe da wuri zan bar gida “ ya fad’a atakaice “okay sir duk suka had’a baki gurin fad’ar haka, daga haka bai sake cewa komai ba ya soma takawa .”maryam dake zaune tana cin abinci tana kallon series na turanci my husband my destiny ,title din series din ne ya d’auki hankalinta har ma yasa ta cigaba da kallo, ahankali taji ana qoqarin bud’e kofar parlour’n,zumbur ta mike tsaye tabar cin abinci da kallon da take sbd jin motsin shigowarsa .”






tsumammun idanunshi ya zuba mata masu matukar firgitarwa cikin salo na harara , gabad’aya maryam ta gigice da sauri ta d’auki remut din tv ta rage volume ,shi kuwa wani kallon tsana ya cigaba da binta dashi tun daga sama har kasa “tabbas zaton shi ya tabba manu direban mami ita zai kawowa abinci .”yadda yake kallonta yayi mugun d’aga mata hankali dan bata san abinda zai biyo baya ba , jikinta ya saki sosai yayinda qirjinta ke wani irin bugawa da karfin gaske a sanda ya qara taku biyu ya qaraso tsakiyar parlour’n ya tsaya still kwayar idanunshi yana yawo ajikinta .”




“tsoro da matsanancin firgici ne duka suka kamata alokaci d’aya zuciyarta ta cigaba da bugawa da karfin gaske,yayinda gefe gudu kuma sanyayyen kamshin turarensa ke neman buwayar hancinta ,nan da nan hankalinta ya sake tashi jikinta ya kama rawa rawa “wayyo allah nah me yasa na zauna a parlour’n ban koma d’akina naci abinci ba gashi zan jawa kaina maseefa da tashin hankali?” ta fad’a tana dungurin kanta .”da kyar ta sanyawa jikinta jarumta tace “san ..sannu da zuwa “.ya jita sarai amman yayi tamkar bai ji ba .”




a kallon da yake mata yana iya ganin yadda qirjinta ke bugawa da sauri wanda hakan ke tabbatar masa da tsananin tsoronsa da take ji ne ,wannan ne kawai abinda yake d’an so daga gareta bayan shi babu komai ,ta koina bai ga ta yadda zai sota ba bare har suyi rayuwar aure daita .”tsaki yaja tare da d’auke kanshi yana cewa “minti d’aya!minti d’aya kawai na baki ki tattara ki bar nan kuma daga yau karki sake na shigo parlour’n nan na d’aura kwayar idanuna akanki dan bana son ganinki “me nace ?ya tmbyeta yana watsa mata harara “.




“kar na sake ka shigo parlour’n nan ka d’aura kwayar idanunka akaina dan baka son ganina “ta fad’a idanunta na cikowa da ruwa hawayen tausayin kanta “good idan kuma kin isa ki fad’a ki janyo wa kanki massefa dan wallahi matsawar sweetheart ta sake zuwa gidan nan da wata matsala na rantse da girman allah sai na kawo karshen auren nan bayan na gana miki azaba mai rad’ad’in “.ya fad’a cikin zafin rai.”
“bazan ..”! shut up nonsense girl kawai bar nan yanzu kafin na sauya miki kamani guntuwa kawai mara fasali ina magana kina magana sa’anki ne ?.”




da sauri ta d’auki basket din da babbar kula da qarami yake ciki ta nufi hanyar kitchen ,ajiyar zuciya ta sauke bayan ta shiga kitchen din tasa hannu ta share hawayenta “wani irin mutun né shi da bai da imani haka ?”sam sam zuciyarsa bata gajiya da fad’ar bakaken maganganu , gabad’aya ko cikaken minti biyar bai yi da shigowa gidan ba har ya hargitsa mata lissafi .“Oh ni maryam ta yaya zan iya shawo Kan mutumin nan bare na samu kulawar sa ?ya Allah kasan yadda ka jarabeni da soyayyarsa ya allah shima ka jarabesa da soyayyata ko dan yaji yadda nake ji akanshi “ta fad’a a fili tana neman inda zata juye abinci “.




“zaman uban me kike yi aciki ?”ammmm uhmm gani nan fitowa ,ta samu wani kwanon silver ta juye abincin haka ma stew din ta bud’e fridge ta saka bata tsaya wanke kulalin ba ta fito da sauri ta d’auki plet din abinci data fara ci tayi d’akinta tana sauke numfashi .”a natse ya haura sama ya shiga d’akinshi bathroom ya shiga ya sakarwa kanshi ruwa ya jima ruwa na sauka akanshi sannan ya fito yazo ya sauya kaya marasa nauyi ya dawo parlour’n kasa ya zauna tare da d’aukar remut ya canza channel zuwa na labarai yana cewa “useless girl kawai babu abinda tasani sani sai kallon abinda bazata samu ba .”




bayan kamar minti goma yaji cikinsa ya fara masa zafi alamun yana bukatar ya saka masa wani abu .”
Wayarsa ya d’auka ya kira d’aya daga cikin masu tsaronsa a gaugauce sale adamu ya qaraso bakin kofar shigowa ya tsaya yana neman izini shigowa “may i coming sir”coming! ya fad’a batare da ya kalli kofar ba sale adamu ya shigo bakinsa d’auke da sallama kasancewarsa muslim ne “ina bukatar abinci da sigari “okay sir” ya fad’a masa inda yake bukatar yayi masa order din abinci sannan ya mike ya sake komawa d’akinsa bai jima ba ya sauko ya zauna ya mika masa kudi yana fad’a masa irin abinci da yake bukata “cike da girmamawa sale adamu ya amsa ya juya ya fice daga parlour’n .”




Tsakanin gidan da wajen siyar da abinci babu wani nisa shiyasa bai wani jima ba ya dawo a natse ya turo kofar ya shigo dan yasan halin mai gidansa baya son yawon kwaramniyya ,ahankali ya maida kofar ya rufe , wanda tuni shi ata idanunshi a runtse suke yana tunanin mami yana sake jin aransa kamar bai kyauta mata ba ,ko zata iya runtsawa yau “?shi kanshi idan ya tuna furucinsa gareta yana jin fad’uwar gaba mai tsanani , yana jin ciwo sosai aransa, idan d’an daya haifa ne yayi masa abinda yayiwa mahaifiyarsa yau ya zai ji ?ya tmbyi kanshi .




Cike da girmamawa sale adamu ya ajiye ledodin daya shigo dashi akan dogon kujerar din dake gabansa yana cewa “sir gashi na siyo duk abinda ka bukata” kanshi kawai ya iya gyada masa ,sale adamu ya juya ya fice ATA ya sauke idanushi akan ledodi kafin ahankali ya janyo ya fara bud’ewa “yaushe rabonsa yaci abinci daga waje ?”matsawar yana qasar abincin mahaifiyarsa yake ci amman gashi yau sanadiyyar auren maryam zai koma cin abinci daga waje.”tsaki ya ja sannan ya bud’e robar abinci inda idanunshi ya soma cin karo da shimkafa ‘yar waje da gasashiyar kaza ya fito da robar fresh milk dana ruwan tataccen inibi .




a natse ya soma ci yana korawa da ruwan inibi kusan kazar kawai ya iya ci da ruwan ininbi da fresh milk bayan ya gama ya kunna sigari ya sha iya shansa ya mike ya rufe koina ya haye sama .”yana shiga d’akin ya cire kayan jikinsa ya saura daga shi sai qaramin plan pant ya kwanta flat akan katifa yana kallon saman d’akin yana shafa kwantaccen gargasar gashin qirjinsa dake kwance luf luf ,lokacin da zuciyarsa take son hasko masa fuskar mafarkinsa yayi saurin kawar da hakan ya sako tunanin mahaifiyarsa ,cikin haka wayarsa ta soma ringing bai mike ba har sai data katse aka sake kira sannan ya yunkura ya tashi ya d’auka yana duba screen din wayar sunan mb ya gani yana yawo ya d’auka ya koma ya kwanta .”




Acikin wayarsu da mb ne yake koro masa yadda sukai da mami shima dai fad’a yayi masa sosai tare da nuna masa mahimmancinta arayuwarsa, yayi qoqarin tun abun bai yi tsawo ba yaje ya bata hakuri ya nemi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login