Showing 45001 words to 48000 words out of 169868 words
Chapter 16 - MAR'ADAM'S BOOK 2 COMPLETE DOCUMENT by Aisha Bagudu .txt
wani shawarar ya auri wannan yarinya,amman yanzu sai shukura itace zabina a halin yanzu ma na kagauta na d'auketa daga wannan gidan dan ta fi karfin zamansa ita din ta dabance acikin zuciyata Ina kallonta ina jin farinciki araina "
hawaye dake makale acikin idanunta maryama suka zubo akan kuncin tayi sauri tasa hannunta ta goge yayinda zuciyar shukura tayi mata sanyi ta qara tabbatarwa kanta aikinsu yayi tasiri akanshi ta d'auko ruwan lemu ta tsiyaya a cup ta mikawa yusif tana cewa "ungo sha kaji sanyi aranka "yasa hannu ya kar'ba yana sakar mata murmushi cikin tsananin tashin hankali kausar tace "karka sa'ba alkwarin daka d'auka ,da maryama kawai kafi dacewa ba da wata shukura ba ka bud'e idanunka da kyau please ."
cikin wata irin murya mai sanyi da tausasawa maryama tace "kausar karki d'aga hankalinki dan baya cikin hankalinsa da natsuwarsa hasalima bazai ta'ba fahimtarki ba a halin yanzu ,kiyiwa danuwanki addua dani da shukura duk abu d'aya ne bazan ta'ba bakinciki dan yusif ya canza ni da shukura ba fatana allah ya basu zaman lafiya tana cikin fad'ar haka taji an fasa kuka abayanta mai kukan tana fadin" lahaula wala kuwwata inna lillahi wa inna ilahi rajiun wannan wani irin massefa ne haka ?
Duk suka juya umma suka gani tsaye cikin matsanancin tashin hankali "Shukura me maryama tayi miki kike shiga rayuwarta ?amman Kisani allah baya bacci kuma zai saka mata da kyakkyawan sakayya Ke kuma zaki ga muguwar sakayya dake da uwarki "idanu kawai yusif ya zuba mata ya kasa cewa komai "kiyi mata na malam yahuza ta hakura ta bar miki shi yanzu kuma yusif din kike so ?".
"umma gashi nan ki tambayesa bani nace ina sonshi ba shine da kanshi ya canza dani " yi min shiru munafukar allah daga Ke har uwarki zaku girba abinda kuka shauka ,da izinin allah sai maryama ta samu wanda yafi yusif komai kausar ta bukaci umma tayi mata qarin bayani akan mlm yahuza batare da 'bata lokaci ba ta zayyane mata komai ."
"uhmm lallai maryam kina cikin tashin hankali allah ya fitar dake kawai zan iya cewa sannan ta cire wayarta daga cikin fost dinta ta kar6i mukullin mota daga hannun yusif ta fice waje tana neman layin mumy yusif ya cigaba da yin shiru maryama ta juya jiki a sanyaye ta bar d'akin tana goge hawaye haka zalika umma kasa cigaba da tsayuwa tayi zuciyarta na tafarfasa ta shige d'akanta tana kuka ."
yaya sadam dake tsaye yana waya ya hango fitowar maryama tana tafiya tana goge hawaye ya bita da kallo Kamar ya tsaidaita yaji damuwarta sai kuma ya rabu daita da zumar zai nemeta daga baya ya cigaba da wayar da yake cikin haka kiran umma ya shigo wayarsa daman what's app call yake ."ya katse kiran domin ya d'auki kiran ummah kiran ya katse ya lalubo qaramar wayarsa yayi mamakin ganin missed call dinta dayawa ashe a silet yake "
ya kirata dan baya son ya shiga sai ya gama wayar da yake ,tana d'auka yaji muryarta can qasa tana kiran sunansa ya amsa yana tambayarta "lafiya ummah naji muryarki haka ?tace sadam kana ina ne ?ina cikin gida " tace ka shigo yanzu yanzu "okay! kawai ya fad'a ya soma tafiya cikin sauri ya shigo d'akinta."ya garasa inda take zaune yana cewa "lafiya umma meke damunki kamar ma kinyi kuka ?."
wani sabon kukan ta fashe masa dashi tana zayyane masa abinda ya faru yace "ikon allah anya kuwa lafiya ?ina fa lafiya sadam kai ma kasan ba lafiya ba ,"yanzu dai sai a kira abba aji me zai ce ,ai wad'an nan mutanen abun nasu babu imani ai bazasu bar iyayensa ma haka ba duk abinda zasuyi dan su juyar da hankularsu zasuyi ."
jikin yaya sadam yayi sanyi ya kasa cigaba da magana "wallahi da ina da inda zan kai maryama ta cigaba da rayuwarta da nayi dan ina son taji dadi, maryama tasha wahala a hannun mutanen gidan nan sam sam basa son ganin cigabanta .""Kiyi hakuri umma komai zai wace babu abinda yafi karfin addua maryama malama ce nasan zatayi addua ."ban ta'ba shiga tashin hankali irin na yau ba domin har ga allah naso auren maryama da yusif amman da izinin allah bazasu ci bulus ba duk abinda sukai mata bazai tafi a banza ba sai allah yayi mana maganinsa ."
bayan fitarsu maryama yusif ya tattara hankalinsa kacokan akan shukura ita kuma sai faman zuba masa surutu take ,acikin zuciyarsa baya jin dadin hirarta amman kuma zahiri abun ba haka bane murmushi kawai yake sakar mata yana biye mata ."karfe biyu daidai suka fito tare da shukura sai ga baba gali ya shigo ."yana ganin yusif tare da shukura ya washe hakora yana cewa "a'a yusif ashe dai kazo?yusif ya gaishesa , baba gali ya amsa yana tmbyrsa "ina ita maryama take dana ganka da shukura ?yusif ya d'an tsotsa keyarsa yace "yanzu ta wuce tana kuka wai dan nace shukurace zabina ita zan aura "shukura kuma yusif ?yayi mgnr Kmr bai san komai ba "kwarai kuwa baba ita zan aura dan haka da zarar na koma gida zan sheidawa dady da mumy agaugauta azo a nemar min aurenta ta zama mallakina ".
"Ikon Allah haka kuma abun ya kasance ?kai kuwa yusif me yasa zakayi haka?" idan wani abu tayi maka sai ka sanar ayi mata magana bawai ka canzata da shukura ba ya fad'a haka a fili amman a bad'ani murna yayi yace abu yayi kyau aikin salama yayi tasiri daman yasan zata iya fiyye da hakan muddin akan biyan buqatarta ne "babu laifin da ta min kawai dai bana sonta ne yanzu shukura zan aura "to to shikenan allah yayi maka albarka Allah yasa ayi damu ."
Yasuf ya amsa da "ameen !ya tura hannunsa cikin aljihu ya ciro bandir din yan dubu ya mika wa baba gali "ga wannan baba "kai yusif har da wata hidima ai da ka barshi ni murnar auren shukura ma da zakayi ya wadatar dani sukai sallama da baba gali ya wucesu yana murna yasuf ya kira kausar tana dauka yace "Ke kina ina ne ?ina tare da maryama ne " ta bashi amsa da haka "to ni zan wuce idan kin shirya ki fito mu wuce idan kuma na wuce ne na barki to ?ok minti biyu kawai na baki tare da maryama suka fito tana kwantar mata da hankali "
kausar kenan karki wani damu dani fa idan da sabo maryama ta rigada ta saba kawai Kiyi wa dan'uwanki addua in sha allahu nima zan tayaku yi masa addua ki gaishe min da mum kice ina matukar qaunarta "tana gama fad'ar haka ta juya ta soma taku a natse kausar ta bita da kallo hawaye na zubo mata ."tunda maryama ta juya hawaye ke turereniyar zubo mata qirjinta banda bugawa babu abinda yake ta kasa shiga bangarensu ta wuce bayan d'akinsu tana kuka tun daga kasan zuciyarta " ko kallon shukura kausar batayi ba ta fice daga gidan cike da tausayin maryama suka wuce ."
alhamdulillah aunty salma ta furta cike da yalwataccen farinciki wannan magana itace mafi dadi acikin zuciyata "wallahi mama kin gama min komai arayuwata kinga yadda ya rikice yace ma nan kusa zaa daura auren "haba wa ai ni din bata wasa bace ai muddin baku auru ba to wallahi babu mai zuwa ya kwashe wannan banzar yarinyar.""baba gali yace "ai baki ta'ba faranta min rai ba kamar yau na dauka fa abun bazai yuwu ba ashe shi yafi komai sauki a wajenki dan allah kisa ayi aikin da zaayi auren kamar yadda ya fad'a "kai dai ka zuba ido kawai kayi kallo wannan auren kamar anyi an gama ."
"Kinga bari na kira fati na sheida mata ta soma shirinta "ya fad'a yana lalubo wayarsa "wani shiri kuma gareta ?aunty salma ta tambayesa "ai muktar dinta ke mutuwar son maryama tun kwanaki dana je gidanta take sheida min nace ta d'an jinkirta muga me zai faru kinga yanzu dama ta samu",lallai kam dama ta samu daman shine daidai da aurenta" aunty salma ta fad'a tana kwashewa da wata mahaukaciyar dariya zaa qare auren dan giya " kai salama baki da dad'i wallahi bakaji dadin da naji ba ai nan duniya bana qaunar maryama yarinyar kamar aljana ga kyau ga shiga rai suje su karata da muktar, shi din ma bazata auresa ba sai ya'yana sun bar gidan nan ."
Cike da murna da farinciki baba gali ya kira aunty fati ya sheida mata komai ai kuwa tayi murna dan muktar din ma ya dameta kullum bashi da magana sai na maryama hatta shaye shayen da yake yace zai daina muddin zaa bashi aurenta" da kyar maryama taja kafafunta ta shigo parlour'nsu tana mai danne damuwarta sai dai kallo daya zaka mata ka fahimci tana d'an cikin damuwa aunty ta dubeta tace "Kuna fita aunty fati ta kira waya wai kizo gobe da safe tana son ganinki "to !kawai maryama ta fad'a ta shige d'akinta dan bata son tayi doguwar hirar da har zai sã mahaifiyarta ta fahimci wani abu duk da tasan dan dole tasani amman ba da wuri haka ba "safa da marwa ta shiga yi acikin d'akin tare da cure hannuwanta waje d'aya" tsawon shekaru aunty salma na bibiyar rayuwarta ."
"laifin me tayi mata ? me ta tare mata? idan wani laifi tayi mata ta fad'a mata ta nemi yafiyarta ta barta ta huta "? wasu hawaye masu ciwo suka gangaro mata a yanzu ba kanta kad'ai take tausayawa ba har da mahaifiyar yusif da yaruwarsa dan ita tsakaninsu dasu aunty salma da baba gali da ya'yanta allah ya isa ne bazata ta'ba yafe masu ba ,domin cirewa kanta damuwa Kan kujerar zanenta ta nufa ta zauna ta zaro farar takarda ta ajiye agabanta ta d'auki pencil ta tura cikin bakinta ta fara tunanin me zata zana ?".
Babu abinda yazo cikin kwakwaluwarta sai fuskar kausar murmushi mai hade da damuwa ya bayyana akan fuskarta "kausar zan zana domin dai nasan shikenan ni da ita kuma sai wani ikon allah ."ahankali ta soma bada shape din fuskarta tunda ta zauna bata tashi ba sallah laasar né kawa ya tashita koda ta idar ma Kan aikinta ta koma ta cigaba ranar a d'akin maryama ta qarasa niyyinta da misalin karfe bakwai aunty ta shigo d'akin ta isketa tana gabatar da sallar magrib ."
Ta qarasa gaban table din kayan zanenta nan idanunta yaci karo da hoton kausar har da kalar kayan data zo dashi yau din nan aunty ta saki murmushin jin dadi tare da cewa "lallai princess an fad'a soyayya ko da yake yarinyar tana qaunarki ta qarasa mgnr adaidai lokacin da maryama ta sallame ta mike jiki a sanyaye take kallon aunty dan wallahi sai take jin kamar bata kyauta mata ba tunda ta tabbatar kota fada mata kuka kawai zatayi tayi hakuri sannan ta kwantar mata da hankali "
"kinyi shiru kina kallo meke damunki ?girgiza mata kai tayi alamun babu komai "amman tun bayan tafiyarsu kausar na lura kike cikin damuwa idan wani abu ne ki sheida min mana ?ajiyar zuciya ta sauke da karfi tace "babu komai "to muje kici abinci ta kamo hannunta suka fito tana cewa "gsky zanen kausar yayi kyau idan tagani zataji dadi sosai tare da aunty suka ci abinci bata wani ci abincin kirki ba tace ta koshi ta sha ruwa ta mike ta shiga bayi ta dauro alwala ta koma d'akinta sallar ishai ta gabatar byn ta idar ta mike tana nade daddumar sallah ."
Ta ajiye a inda yake ta tsaya shiru acikin d'akinta tana jin wani irin faduwar gaba ta qarasa ta kakkabe wajen kwanciyarta sannan ta kwanta rigingine ta hade hannuwanta duka a qirji tana tunanin rayuwa ganin zata damu zuciyarta ne kawai a banza ta sauke ajiyar zuciya ta soma karanta suratul mulk ahankali bayan ta gama karantawa ta shafe jikinta da addua ta kwanta, ahankali bacci ya dauketa cikin baccinta tayi mafarkin umma tace a daura aurenta da yaya sadam har ma ya amince da auren kiran sallah asuba ne ya tasheta daga mafarkinta ta mike ahankali ta zauna ta zuro kafafunta kasa tare da dafe goshinsa ."
Tayi shiru tana tunanin mafarkinta addua tayi Allah ya zaba mata abinda yafi zama alkhairi arayuwarta da kyar ta yunkura ta mike tsaye ta fito ta shiga bayi ta dauro alwala ta dawo daki tayi sallar asuba duk ta rasa meke mata dadi duk da tasan mafarki ne amman sai taji abun ya tsaya mata arai cike da raunin zuciyata ta koma ta kwanta ahankali bacci ya kwasheta aunty ce ta shigo ta tasheta tana cewa "bazaki gidan aunty fati bane kinfa san halinta babu hakuri sai ta d'auki abun wani iri azo ana damun rayuwarki “ numfashi ta sauke kawai tare da mikewa zaune tana dafe goshinta "ko baki jin dadi ne dan tunda kika koma kika kwanta bacci bayan sallahr asuba to baki da lafiya tayi mika tace "kaina ke d'an min ciwo sai dai kuma .."sai tayi shiru ta kasa mgn "sai dai kuma me ?"
"Wallahi umma mafarki nayi wai umma tace a daura aurena da yaya sadam kuma har ya amince ?aunty tayi dariya tana cewa "kai princess wani irin aure kuma bayan ga maganar yusif ? ta kalli aunty tana jin fad’uwar gaba mai tsanani tace “aunty ki bar maganar yusif muyi maganar mafarkina gsky banji dadin mafarkin nan ba " to ai mafarki ne mafi yawon lokuta mafarki baya zama gasky tashi ki sha magani kije tun karfe tara aunty fati take kiran waya "to ni me zan mata ne ?tayi magana Kmr zatayi kuka "ni wallahi bana son zuwa koina idan kaga sun nemeka to aikin wahala ne ga wannan d’an nata mai shegen maseefar kallon tsiya kamar zai cinye mutun ".
"To ko na fad'a mata bakijin dadi bazaki samu damar zuwa ba ta kira kaulat ko Islam suje idan wani aiki zaa mata sai suyi mata ?maryama tayi shiru can tace "yanzu rashin zuwan nawa zai zama tashin hankali azo ayita kananan magana "shiyasa nake son kije idan ma aiki ne kika ga zai miki yawa Kiyi iya wanda zaki iya ki dawo ,nifa ba aikin bane damuwata kamar matsefaffen kallon da yaya muktar yakewa mutane ".
"Babu ruwanki da kallonsa kiyi abinda ya kaiki maza tashi ki tafi dan ki samu ki dawo da wuri “numfashi ta sauke” gsky aunty bazanje yanzu ba “ya fad’a tana wasa da yatsun hannunta “sai yaushe zaki?maryama tayi shiru ta kasa mgn “da dai kin daure tunda kinga baki da lokaci sai asabar da ladidi tsaki maryama taja kana tace “wallahi ban san dalili ba hakan nan najin fad’uwar gaba kuma dai yau bana son zuwa koina “aunty ta numfasa tace “to shikenan Kiyi zamanki muje kiyi wanka ki karya ki sha maganin ciwon kai ta mike ta fito wanka tayi ta shirya ta karya aunty ta bata magani ta sha tayi kwanciyarta akan kujera .”
Ahankali ta rufe idanunta lokaci d’aya kwakwalu warta ta bud’e tunani ya kusantota yaki barinta ta huta duk da bata son tayi tunani akan matsalarta amman haka tunani ya mamayeta , ahankali ta dinga tunanin maganganun yusif ,me yasa zaki damu kanki maryama already kin rigada kin yarda kin rasa yusif har abada kamata yayi kin haka rami ki binne komai ya zama tahiri arayuwarki” zanyi haka zan cire komai araina kuma zan dage da addua har na samu nasara arayuwata ahankali tabi shawarar zuciyarta ta haka rami mai zurfi aciki zuciyarta ta binne duk wata matsalarta .”
tun daga wannan ranar maryama ta cire tunani da damuwar komai acikin ranta ta toshe kunnenta duk abinda ke faruwa aciki gidan tana ji kuma tana gani amman ta share sannna taki bari mahaifiyarta tasan halin da’ake ciki yayinda kullum sai aunty ta sheida mata sakon kiran aunty fati har sanda sati ta cika aunty ta matsa mata lallai taje taji dalilin kiran da take mata “Allah aunty bana son zuwa duk sanda kika fad’a min sakonta gabana faduwa yake “kiyi hakuri ki daure kije bana son tazo gidan nan “ta fad’a muryarta a raunane ganin yanayin aunty yasa ta riko hannunta “shikenan aunty zani bari na sauya kaya naje yanzu na dawo .”
“Yauwa princess maza tashi kije Allah ya tsare min Ke “Ameen !ta furta a tsanake ta fito ahankali take taku har fito titin unguwarsu ta mike zuwa captor road tana gama garasawa bakin titi ta samu adaidai mai zuwa unguwarsu aunty fati tafiya kad'an suka yi ta sauka pencilima ta mikawa mai adaidaita kudi ta ta tsallako hannunta na hagu inda zai shigar daita amawo ."a natse ta shiga gidan kai tsaye bangaren aunty fati ta nufa bakinta dauke da sallama ta shiga parlour'n inda ta iske muktar da aunty fati zaune ."
Rike da remut tana qoqarin canza tasha a tare suka kallo kofar tare da amsa sallama .”
tun daga kasa muktar ya dauki kallon maryama ransa nayi masa dadi wani irin yanayi ya tsinci kanshi ciki mai wuyar misaltuwa yana jin yadda soyayyarta ke fixgarsa yayinda maryama ta had'e fuska sosai tmkr taga wani mugun abu ta qarasa ta tsugunna har kasa ta gaishe da aunty fati ,aunty fati ta amsa mata fuskarta a d'an sake wanda hakan ya dan bawa maryama mamaki domin tunda suke daita kyara da hantara tattare da zagi né a tsakaninsu ."
Maryama ta dauke kanta tare da