Showing 66001 words to 69000 words out of 169868 words
Chapter 23 - MAR'ADAM'S BOOK 2 COMPLETE DOCUMENT by Aisha Bagudu .txt
take bani irin kulawar da take bawa yanuwanka da kowa naka ni mahaifiyarka ce na fi kowa sanin abinda ya dace da rayuwarka ka sake da maryam zata kula da rayuwarka dan dukkanin alamunta sun nuna tana sonka yanzu ,ganewa bakwa yi amman kun fi samun kwanciyar hankali a wajen matar dake sonku ,matan da kuke so kuma wahala suke baku ."shiru ATA yayi yana nazarin maganarta ."
" kasan me yasa na had'a aurenka da maryam ?ya girgiza mata kai yana daura kansa a saman cinyarta ya natsu sosai ya bata dukkanin natsuwarsa "na had'a aurenku ne saboda ko byn raina maryam zata maye maka gurbina zata baka kulawar da uwa ce kawai zata baka, zata jurewa duk wani shagwa'ba da jin kanka,uwa uba hakuri gareta ,zatayi hakuri da duk wani iskancinka dan haka ina mai umartarka ka dauketa a matsayin mata zakaji dadin rayuwar aure daita". ta qarasa maganar tana shafa sumar kansa ya dago a hankali ya sake zuba mata idanunshi kamar zatai kuka "please sweetheart karki min haka karki bani umarni ,zanyi kokari na koyawa zuciyata sonta ta yadda zata bata matsayin mata amman ki bani lokaci ."
ta numfasa taso ya fadi abinda yafi haka amman a hakan ma ta gode "na gode allah yayi maka albarka ta mike tsaye bari na turo maka maryam ta zuba maka abinci kasa ma cikinka ,kanshi kawai ya gyada mata tana barin d'akin ya sauke wani wahalallen numfashi yana tunanin maganganunta "ta ina zai fara bawa maryam matsayi mata ?"
"matsayin mata da take nufi fa tana nufin wani abu ya shiga tsakaninsu kenan ?ya mike tsaye cike da sanyi jiki "tabbas abinda take nufi kenan idan dai haka ne ta ina zai fara ?a hankali ya shiga zariya acikin dakin yana ciza lip's dinsa at the same time yana hura hancinsa ."
byn kmr minti biyar mami ta dawo d'akin hannunta rike da mrym tana bata umarni "maryam zuba masa abinci" ta fad'a tare da samun wuri ta zauna kusa dashi tana dubansu adamcy nah bari mrym ta zuba maka abinci kaci ka d'an kwanta ka huta kafin zuwa anjima ka d'auki matarka ku wuce gida kaji masoyina ."kallonta kawai yayi yana mai tausaya mata " maryam ta zuba masa abinci ta janyo qaramin table gabansa ta ajiye masa tana satar kallonsa aranta tace "rigimamme kawai da baya son zaman lafiya ."
yayi shiru kawai yana kallon abincin kafin ahankali ya fara tsakura babu laifi ya d'an ci kad'an ya ajiye spoon alamun ya koshi mami ta tsiyaya masa ruwa a glass cup ta bashi ya sha sannan ta mike idan ka tashi ka d'auki matarka ku wuce gida kanshi ya gyada mata batare da yace uffan ba , ta juya har tayi taku biyu taja ta tsaya "batun hisham kayi hakuri kabar auta ta koma d'akinta zai yi magana tace "alfamar na nemar masa a bashi dama ta biyu stil bai yi magana ba ta fito ta bar maryam tana tattara wajen ."da yamma mami ta kira hisham yazo ya d'auki matarsa bayan tayi masu nasiha mai ratsa jiki ." haka ma maryam tabi mijinta suka wuce. gidan ya saura daga mami sai yayanta wad'an da suke shirin tafiya ."
Akan hanyar su nana hauwa'u ta koma gida tafiya ce sukai tamkar kurame hassalima bata kalli inda yaya hisham yake ba ta juyar da kanta gefe tana kallon tsirarrun motoci dake wucewa akan titi saukar hannunsa taji akan nata wani irin yarrrr taji a gbdy ilahirin jikinta, sai dai bata juyo ta kallesa ba ta cigaba da kallon titi "auta !" ya kira sunanta yaushe rabon da ya kirata da wannan sunan ?sai daya sake kiranta sannan ta juyo da kyar ta zuba masa idanunta ya kwantar da murya sosai "kiyi hakuri da abubuwan da suka faru a tsakaninmu shiru tayi Kmr bazata yi magana ba sannan ta motsa labbanta tace "babu komai ,komai ya wuce ,"Kinsan ko wanene ba haka halina yake ba ."
"Nasani shiyasa nayita mamaki wai yaya hisham mai tausayi da kulawa ne nake rayuwa dashi cikin fargaba da nadamar da tsoron kasancewata dashi yadda baka son auren nan haka nana hauwa'u bata só ,alfarma tayi ta sadaukar da farincikinta, na dauka yadda nayi zai sa na kasance masoyiyarka tare da tunanin zaka fi kowa jin dadi da sona amman sai naga sa'banin haka wallahi nayi mamaki yaya hisham ban ta'ba tunanin haka daga gareka ba". ta qarasa mgnr cikin rawar murya ya kamo hannunta ya tsarke cikin nashi" yana murzawa ahankali yana jin canjin yanayi a sansar jikinsa ,yayinda soyayyarta ke sake huda zuciyarsa "kiyi hakuri hisham zai dawo miki fiyye da yadda kika san shi a baya ,bazan sake yunkurin cutar dake ba ."wani sanyi dadi taji yana bin jinin jikinta ahankali ta dinga jin gurbin daya fara samu a zuciyarta yana qaruwa ."
Washegari ATA na barin gida aka kira maryam sakonta ya iso take ta shirya ta fita batare da neman izininsa ba ta karbo magani cike da farinciki ta dawo gida ta kira mahaifiyarta ta sheida mata ta kar'bi sakon ,yini ranar cikin farinciki da murna maryam tayisa da yamma ATA ya dawo gida cike da kulawa ta tarbesa da abinci ,bai kalli inda ita da abincinta yake ba ya haye samansa wanka yayi ya sauya kaya ya bar gidan gbdy .hankalinta a tashe ta kira mahaifiyarta tayi mata bayani "umma ki tambaya ko zan iya zuba masa cikin abun shansa dan baya cin abinci sai coffe da ruwan gidan kawai yake sha?to shikenan sai najiki ."
*****
Bangaren maryama kuwa zaman gida ya soma damunta yayinda subai'a tuni ta fara aiki da kamfanin Z&A dan haka ta fara neman aiki sai dai duk inda taje ba'a daukarta aiki tun abun baya damunta yazo ya fara damunta tayi tunanin tayi chart din ammar ko zai taimaka mata dan haka ta shiga what's app dinta tayi masa sallama ya bude amman bai bata amsa ba. ta sake aika masa still ya bude amman babu amsa dan haka tayi tunanin kiransa WhatsApp call bai dauka ba sai ma sakonsa ta gani "lafiya !?kiran me kike min ?"Jikina na rawa ta soma typing "dan allah oga ammar kayi hakuri akan abinda nayi, yanzu nasan nayi kuskure mai girma "ta tura masa."
jin kad'an sai ga amsarsa ta shigo " bakiyi kuskure ba tukun sai anan gaba karki manta don't ever call me again or chart me "inna lillahi wa innna ilahi rajiun allah ka gani taimako nayi allah karka barni da iyawata kabi bayana akan dukkanin lamurana ."
tun daga wannan rana maryam bata kuma wani sukuni ko walwala ba ,har mamakin kanta takeyi dan bata d'auka abun zai dawo ya dameta ba kullum cikin damuwa take da neman aiki bata wani cin abincin kirki gashi kowa ya gane halin da take ciki a gida sai dai kowa ya tambayeta sai tace bata da lfy ne aunty salma kam kirikiri take mata dariya tare da cewa "an gama boko anyi bautar qasa babu riba dole a zaman gida tare damu ."
azumi da nafilflii kullum cikinsu take domin allah ya kawo mata mafuta da samu aikin, abun duniya ya ishi Aunty dan yar magana da take ma yanzu ta rage Ta sake dawowa shiru shiru ga rashin aiki ga aurenta da yaya sadam na matsowa ranar monday ta shirya zata neman aiki aunty tace kar taje koina "me yasa Aunty ?"bazan iya kije ki dawo baki samu ba ki kwanta rashin lafiya nafi bukatar lafiyarki akan aiki ida ma zaki iya muje Asibiti a duba min lafiyarki dan wannna ramar ta isheni" muryarta a sanyaye tace "nifa lfy ta kalau "ina wani lafiya ana ?Kiyi hakuri aunty ki barni naje ."
"Ni baki min laifin komai ba "to amman ai fushi kike dani Kiyi min addua ko zan samu aiki "kullum ina miki addaua amman dai yanzu kinsan kiyi wasa da damarki ta barwa subai'a aikinki ?nasani Kiyi min addua allah ya sake aramin wata damar "allah yasa a dace sai kin dawo allah ya tsare" jiki a sanyaye tace "ameen!"sannan ta fita yau din ma dai kamar ko yaushe bata samu tayi kukanta har idanunta suka kunbura damuwarta ta qaru wunin ranar cikin tsananin damuwa tayisa . yadda take cikin damuwa haka zuciyar ATA ta kasa samun sukuni duk inda ya motsa sai yaji zuciyarsa na luguden bugu da tunaninta duk inda ya motsa yana jinta a jikinsa da zuciyarsa ,wunin yau din wutar soyayyarta sai qaru yake a cikin zuciyarsa ya sauke naunayen ajiyar zuciya ya yunkura ya mike tsaye daga zaunen da yake yana gyara zaman yar saman suit dinsa ."
Dakin dake manne acikin office dinsa ya shiga ya tsaya hannunsa d'aya rike da kugunsa yana qarewa makeken zanenta kallo "to ban zata daidai bane ko ya ?ya tambayi kansa yana zurfafa tunaninsa "amman kuma wannan fuskar nake gani acikin mafarkina "me zai hana kasa a nemo maka kwararrun masu zane su zana maka ita kaga nasu kwarewar ko akwai abinda zai bambamta da naka ?nan take ya amince da shawarar zuciyarsa ya fito yana kiran yaronsa seun cikin kankani lokaci ya shigo cike da girmamawa "yayi masa bayanin abinda yake bukata "amman sir me zai hana ka gwada masu zanen kamfaninka AGC mana "nasan dasu na buqaci wasu dabam ,kaje kayi abinda nasaka "okay sir ya juya da sauri ."yadda yake cikin damuwar rashinta haka itama ta kasance cikin damuwar maseefar rashin aikinta dake bibiyar rayuwata kukan data yini yi ne yasa kafin shida na yamman ranar jikinta yayi zafi tamkar garwashin wuta aunty ce tsaye akanta tana shafe jikinta da jikakke
towel byn ta bata magani tasha ."
Mmn sudais
💗💗💗💗💗💗
MAR'ADAMS
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗
*AYSHA A BAGUDO*
WATTPAD @HAUESH
AREWABOOKS USERNAME
AYSHAABAGUDO
bismillahirrahmanirrahim
Wannan littafin na kudi ne mai bukatar karantashi byn na kammalashi zai biya 1000 ta wannan account number din 1438775094 Aishat abdullahi access idan an tura sai a turawa wannan 09136918331 alert domin tabbatar da an tura domin sauraron littafaina a tuntubi chaneel dina (Hausa bakwai ) a YouTube.
Page 13
amatukar galabaice ATA ya qaraso gida zuciyarsa na hasko masa fuskar zanen mafarkinsa " mai yasa na qasa mantawa dake ?yayiwa kansa tmbyr yana shafa sumar kansa, gbdy yau din tunaninta ya hanani sukuni ya fad’a a fili yana fesar da numfashi mai zafi daga bakinsa ,qirjinsa kuwa banda bugawa da karfi babu abinda yake, ahankali ya shiga zagaye d’akin hankalinsa na sake tashi ,a tsakiyar d’akin ya tsaya rike da kugunsa yana ciza lip’s dinsa na qasa “mai yasa bazan manta daita na cigaba da rayuwata ba ?”ya wurgawa 'kwal'kwaluwarsa tmby " ban san me yasa nake ji araina kina cikin wannan duniyar ba yaja qaramin tsaki “what's wrong with my brain ?I have to stop all this nonsense.”ya fad’a yana cigaba da d’aga kafafuwansa. bayan kamar minti biyar ya tsaya cak yana sake kamo lips dinshi na kasa yana cizawa ahankali ahankali ya d’auki lokaci mai tsawo yana shawagi acikin d’akin sannan ya cire kayan jikinsa ya shiga wanka ya fito ya sanya kayan marasa nauyi riga yellow mai hannun hamles da farin wondo iya gwiwa , ya samu waje ya zauna a bakin gado zuciyarsa na sake hasko masa fuskar zanensa.”
“ idan tunaninta ya sakashi gaba jin zuciyarsa yake kamar zata buga hakan yasa yaki sauka parlour ‘n gidan kamar yadda ya saba a duk sanda ya dawo .”tsaki yaketa já yana qarawa domin tunaninta na damun kwakwaluwarsa,idan a son ranshi ne baya son yana damun zuciyarsa da kowa i irin tunani yana nan zaune a bakin gado yayinda kafarsa daya ke kasan tayis d’ayan kuma ya tankwashe tare da dafe gaban goshinsa dake sara masa kad’an kad’an gefe guda kuma yana jin damuwar da ciwon abinda dakikiyar yarinyar nan tayi ,shi tunda yake babu wanda ya samu aiki da kamfaninsa yayi rejecting dinsa sai ita ,ai kuwa zata ga wahala ganin idanunta yana zaune maryam ta turo kofar d’akin ahankali ta shigo bakinta d’auke da sallama bai amsa mata ba haka zalika bai d’ago ya kalli inda take ba .”
kusan minti biyar tana tsaye tana qare masa kallo sannan yaji sautin muryarta a sanyaye “baby sannu da zuwa !”ta fad’a ahankali tamkar wacce mako shinta Ke ciwo “ya d’ago a natse ya kalleta sanye take cikin kananan kaya wondo da riga maron colour mai ratsen fari ajiki yayinda jikinta ke fitar da kamshi hannunta rike da wani had’ad’den tray. bai amsa mata ba ,ya d’auke kwayar idanunshi akanta zuwa wani bangaren yana jan tsaki dan ya tsani sunan baby din da take kiransa dashi ,bugu da qari bazai iya jurar cigaba da kallonta ba, dan babu macen data isa ya tsaya yana kallonta .” sa’banin ita daya rigada ya saba da kallo irin nata indai tana kusa dashi to fa dukkanin idanunta da natsuwarta suna kanshi ne “ bata damuwa da duk irin wulakancin da yake mata hassalima ya fahimci dadin kallonsa take ji dan ya santa farin sani babu yadda zaayi tana tsaye haka agabansa idanuwanta ba akanshi suke ba .”
daga sannu da zuwan da tai masa bata sake ce masa uffan ba ta ajiye tray hannunta ta soma hidimar zuba masa abinci bayan ta gama zuba masa ta sake motsa bakinta “baby ga abinci “!still bai ce mata komai ba sai ma haushi da ta sake bashi ta cigaba da kallonsa dan kallonsa ba qaramin jefata cikin nishadi yake ba ,kamar ta bud’e baki ta tambayesa meke damunsa dan ta fahimci yanayinsa na yau ya canza fiyye da sauran lokutan daya saba kasancewa cikin miskilanci amman ta qasa tmbyrsa sbd gudun abinda zai je yazo .taga ya sake kallonta amman sai ta qasa d’auke idanuwanta akanshi duk da ta fahimci shi hakan yake buqata daga gareta .”madadin ta d’auke kwayar idanunta kamar yadda yake buqata sai ta durkusa gabansa ta d’auki glass cup ta had’a masa coffe ta mika masa “baby ga coffe ka sha nasan zaka fi buqatarsa “.
a matukar zuciye ya kar’bi cup din hannunta ya saita ta dashi zai kwata mata ruwan zafi tayi saurin zaro ido tare da yin gefe ,glass cup din ya samu bangon d’akin, nan take ya tarwatse a qasa , ya mike a fusace sauran kad’an ya taka wani bangaren na glass cup din dan har kafarsa ta sauka akan kwalba maryam ta saki qara mai sauti dole ya d’aga kafarsa Ya koma ya zauna tana dafe goshinsa .ahankali ta juya ta fita da sauri bata jima ba ta dawo ta durkusa ta tattara dukkan wajen ta mike tana dubansa “dan girman allah ka dinga bin komai ahankali kada kajiwa kanka ciwo “ ta furta cikin wata irin murya mai sanyi da tausasawa “muga kafarka allah yasa bakaji ciwo ba yaji tana fad’a “ya salam wannan wata irin mayya yarinya ce haka? ita sam bata damuwa da wulakancinsa ,har sai zuwa yaushe ne wuya zai sa ta gudu ta fita cikin rayuwarsa?”yana son ta gaji dan kanta ,yana son hakurinta ya qare ta gudu da kafafunta ba sai ya sallameta ba amman da alamun shine zai gudu ya barta .”
“bai ankara ba yaji ta kamo qafarsa data fi tunanin ita ce ta kusan taka kwalba ta sanya tafin hannunta karkashin tafin qafarsa ta soma murzawa ahankali “Alhamdulillah babu abinda ya sameka kamar wanda ya farka daga wani mummunar mafarki ya fixge qafarsa da mugun sauri yana huci. numfashi ta sauke ta mike tsaye idanunta na kanshi miniti biyu tsakani ta juya adaidai lokacin da wayarsa ta soma ringing ta d’an rage tafiyarta ya kai hannu ya d’auka ya manna a kunnensa “yaakayi ammar ?ya fad’a yana furzar da numfashi ,dan girman allah bana ce ka rabani da maganar yarinyar nan ba? na rantse da girman allah zamu samu matsala da kai mutuqar baka rabu dani ba ,makaho ne ko me ?maryam ta kasa cigaba da tafiya ta tsaya cak zuciyarta na karkarwa “eh haka né nasa a nemo min kwararun masu zane “ban gane na fara ganinta kafin na anemo masu zane ba ?”dan allah share yarinyar nan kwata kwata banason ganinta “wace yarinya ce wannan da yaya ammar ya damesa daita ?tayiwa kanta tmbyr yanayinta na canzawa lallai akwai buqatar taga wannan yarinyar .”
ahankali suka cigaba da tautauna can yace “dolen dolalo muna nan a yadda muke taki zuciya ta gudu ,wallahi ban soma jin komai akanta ba kuma bana fatan na so wannan yarinyar “ wannan magar da yayi ce tayi sauri dawo daita daga d’an tunanin da kwakwaluwarta ta tafi na wuncin gadi .jiki a sanyaye ta cigaba da sauraronsa “kai fa na fahimci baka son kaga ina cikin kwanciyar hankali ,wannan ba matsalata bace dan ni har yanzu ban maidaita matsayin mata ba ita ..”tun kafin ya qarasa ta fice da sauri idanunta na kawo ruwan hawaye bata san me suka cigaba da tautauna ba “amman kalma d’aya zuwa biyu suka fi tsaya mata a kahon zuciya “bai sonta da kuma tayin auren da yaya ammar yake masa “anya kuwa bazata kai qarar yaya ammar wajen mami ba ta taka masa burki ?akan wani dalili zai dinga tursasa mata miji alhalin tana iyakar qoqarin taga ta shawo kansa sun zauna lfy?amman kuma da tayi tunanin hakan zai iya janyo mata gagarumin matsala da shi ta fasa gara ta nemi yaya ammar din tayi magana dashi .”
Bayan awa d’aya da wasu mintuna ta sake dawo d’akin ahankali ta qaraso ta tsaya nesa kad’an dashi ta d’auki kallonsa gabad’aya yanayinsa ya koma na damuwa ,ta kalli abinci data kawo masa ga dukkanin alamun bai ci ba ,amman dai ta bud’e taga bai ci din ba kamar yadda tayi zato har yayi sanyi “me yasa bazaka barwa allah komai ba ?ka sani duk duniya nan idan suna son zamammu ma’aurata ida allah bai hukunto hakan a tsakaninmu ba bazai kasance ba ,haka duk kinka da auren nan idan allah yaso mutuwa ce zata raba mu .idan kuma allah yayi iya rabon zama ne atsakaninmu dole za rabamu karka manta yadda baka son auren nan amman allah ya qaddara sai da akayi .”
Tai shiru tana dubansa