Showing 96001 words to 99000 words out of 169868 words
Chapter 33 - MAR'ADAM'S BOOK 2 COMPLETE DOCUMENT by Aisha Bagudu .txt
a yanzu ni kaina ina nadama had'a wannan auren, na d'auka komai zai samu sauyi a samu cigaba ashe damuwa akan damuwa kawai za'a haifar. murmushin 'bacin rai ya bayyana akan fuskar maryam kana ta girgiza kanta "please maryam Kiyi tunani mai kyau kamar yadda nayi bana son ki bata shekaru cikin wannan halin, still dai shiru maryam tayi wanda hakan yake nuna alamun shawarar mami bata mata dadi ba “maryam ba kya tausayawa kanki ?ki tausayawa kanki maryam nasan kina yin komai saboda ni ne na kuma gode da biyayyarki gareni allah yayi miki albarka ."
Zuciyar maryam wani irin zafi take mata da tuttukin bakinciki tana jin wata irin tsantsar soyayyarsa na sake ratsata baza ta'ba kuskuren rabuwa da yaya Adam tayiwa kanta wanan alqawarin suna tare mutuwa ce kawai zata rabusu ,koma yayi qoqarin rabuwa daita baza barshi ba tagumi ta zuba cikin zullumi da rashin sanin madafa dan bazata iya aikata abinda mami take buqata ba ,duk magiyar da mami take mata amman maryam taki bud'e baki tace zata rabu da ATA." sosai mami ta fahimci soyayyar adamcy din ce mai tsanani ta hana maryam bin umarninta jikin maryam a matuqar sanyaye ta mike batare data kalli fuskar mami ba tace "mami dan allah ki bar maganar rabuwar nan haka ,ni abinda nafi buqata daga gareki shine addua ko kad'an yaya Adam ya soni acikin zuciyarsa tana gama fad'ar tace "bari naje na kawo miki abun sha har tayi taku biyu ta taya "dan allah mami karki masa magana akaina tana gama fad'ar haka ta cigaba da d'aga qafafuwanta ."
Mami tabi bayanta da kallo duk ta zube ,duwawukan nan nata duk sun kusan qarewa, ramar da tayi tasa ta qara kankacewa ,ta fito daga kitchen rike da cup da jug ,kawai taga mutun tsaye kikam tamkar wani jami'in tsaro cikin wani had'ad'den suit ash colour haka ma takalman dake sanye a qafafuwansa ash ne sai sheki suke ,tsintsiyar hannunsa makale da agogon rolex ya zuba hannuwansa duka cikin aljihun wondonsa ga sihirtaccen kamshin turarensa mai tsananin kamshi ,nan da nan kamshi parlour'n ya canza zuwa na kamshinsa ."suka tsurawa juna ido shi yana kallonta cike da tsantsar tsana yayinda ita Ke kallonsa cike da tsantsar qauna satinta uku kenan bata sanya shi acikin kwayar idanunta ba
bata san tayi kewar ganin kyakkyawar fuskarsa ba sai a yanzu da take kallonsa tsaye agabanta ,kullum kamar qara masa kyau ake sam bazaka ce 40 garesa ba ,ga kamshin daddan turarensa duk inda ya shiga sai anji wannan mayataccen kamshin nashi mai tsayawa arai da dagula lissafi,taji kamar tayi wulli da cup din hannunta taje ta rungume shi ajikinta taji d'umin jikinsa ."
Qaramin tsaki yaja ganin yadda take kallonsa kamar bata ta’ba ganinsa ba arayuwarsa baya son yawon kallo ya d'auke kwayar idanunshi ya qarasa shigowa sosai ya zauna kusa da mami ya baje akan kujera yana furta "wash allah nah na gaji “yayinda maryam ta qaraso tayi masa sannu da zuwa aciki ya amsa mata shima ganin mami zaune ne ,a natse maryam ta fara hidima da mami "sweetheart a she dana biya ta gida bazan sameki ba ?"tace uhm bazaka sameni ba amman nasan ko kwanaki nawa kayi zaka zo ka sameni zaman jiranka kallonta kawai yayi ya d'an ciza lip's dinsa yana d'aure fuskasa dan ya fahimci kamar akwai wata a qasa . mami ta kalli maryam dake zaune kusa daita taga ta girgiza mata kai alamun karta masa maganarta take ta fahimci abinda take nufi numfashi ta sauke inda ATA ya fara jan mami da hira maryam ta tashi ta dawo gabansa ta tsugunna yayi saurin janye qafafuwansa tmkr yaga mugun abu numfashi ta sauke ta sake matsowa ta kai hannuwanta ta janyo qafafunsa saurin runtse idanu yayi yana jin kamar da wuta ta ta’ba shi .”
Ahankali yaji ta soma kwance igiyan takalminsa d’aya kamar ya zare qafarsa ya buga mata takalmin a fuska amman ya share sakamakon darajan mami dake gurin ,tana gama cire masa takalman ya janye qafafuwansa ta kwashe takalman ta nufi hanyar step ."ya bud’e idanunshi ya cigaba da jan mami da magana acikin hirarsu da mami take fad'a masa kwanakin nan zuciyarta na mata nauyi "wallahi adamcy bana jin dadin zuciyata jiya fa da kyar na samu na runtsa numfashina kamar zai bar gangar jikina "haba sweetheart ya zaki min haka?ya kina jin ciwo ajikinki amman ki kasa fad'a min ko fad'awa aunty shahida "yaushe rabona da kai adamcy ?” duk ya’yana suna zuwa su duba lafiyar jikina ,amman kai yaushe rabon kazo wajena ?idan dai mai rabawa ta rabamu ai shikenan kowa ya huta ko da yake kai ne zaka huta idan na mutu amman sauran zasuji babu dadi "allah ba zai sa naga wannan ranar ba "kema kinsani sweetheart kina cikin raina da bamu raba gida ba ,babu abinda zai sa kiyi rashin ganina a duk lokacin da kika só ,dole duk tsananin aikin daya sakani gaba dole zan dawo gida na kwanta .”
“ wallahi yanayin aiki ne yanzu da kuma d’a nisan da mukayi amman da zaki min alfarmar rabuwa da auren nan da na huta domin zan dawo gidanki gbdy ta yadda zan dinga kula da duk wani motsinki "kaji dashi idan zaka kare kanka kayi amman babu ruwan aure da rashin zuwanka akai akai "to ma meye amfanin auren?me zanyi dashi tunda bana sauke nauyinsa dake kaina shiru mami tayi tana nazarin maganarsa "to ma meye amfanin auren?me zanyi dashi tunda bana sauke nauyinsa dake kaina ta sake maimaita abinda ya fad'a tayi wa maganar falla falla domin fad'a dashi dan ta fahimci abinda yake nufi idan dai ta fahimta bayan rashin kwanciyar hankalin da baya bawa maryam har da hakin aurenta baya saukewa kamar tace ya sauwake wa maryam din kowa ya huta amman maryam din take ji a halin yanzu ,domin dukkanin alamun sun gama nuna soyayyar adamcy tayi mata kamun kazar kuka "sweetheart Kiyi hakuri ki yafe min na kasa miki biyayya na kasa son abinda kike mutuwar so "wannan son ranka ne kake fad'a da nuna baa isa da kai ba "bai sake cewa uffan ba akan maganar da take sai ma canza magana da yayi zuwa ta lafiyarta "sweetheart ki shirya next week zamuje India a duba min lafiyarki "a'a ni bana buqatar zuwa koina anan ma ina samu kulawar shahida tana iyakar qaoqarinta akaina "dan sweetheart ki amince please ".
“na yafe adamcy abarni anan idan ma mutuwarce na mutu acikin ahlina allah dai ya bamu saar tafiya tunda yaji inda mami ta dosa ya lalubo wayarsa ya kira musa yana bashi umarnin yayi order abincin mutun biyu "mami ta kallesa a tsanake tare da katse masa hanzari ta hanyar cewa "mai yasa za'ayi order abinci bayan ga matarka a gida ?"shiru yayi yana karkad'a qafa "me ye amfanin haka adamcy ?"allah ya rufa maka asiri ka nemi ka tonawa kanka "sweetheart ya kike magana haka kamar baki san shirmen yarinyar nan ba ?"ai cin abincin wannan sakar yarinyar daidai yake da cin guba ai sai ta kashe mutun da yaji da maggie "yayi mgnr a matuqar fusace yana jan tsaki kana ya cigaba da bawa musa umarni yana gama wayar ya mike da kyar ya hau sama ,a bakin kofar d'akinsa yaga ta ajiye masa takalmansa ,ya bud'e dakin sannan yasa hannu ya kwashe takalman ya shige dakin,wanka ya shiga bai wani d'auki lokaci ba ya fito bayan ya shirya kansa cikin kananan kaya ya sauko ya zauna alokacin maryam tana tare da mami tana tmbayarta abinda zata girka mata "ki girka min duk abinda kike dashi maryam zanci “ata ya zauna adaidai lokacin da maryam ta mike zata nufi kitchen muryarsa can qasan makoshi yace "ke.."!
Ta tsaya cak a natse tare da juyowa ta fuskancesa "karki dafa mata wannna banzan abincin naki “
mami na qoqarin bud'e baki musa yayi knocking ya bashi izinin shigowa musa ya turo kofar parlour'n ya shigo cike da girmama ya gaishe da mami sannan ya rusuna ya gaishe da ATA ya ajiye ledodin hannunsa ya juya da sauri ya fice ."ATA ya janyo ledar farko dake gabansa ya bud'e kamshi kifi tilafia ya doki hancin maryam wanda yaji kayan hadi da arish had'in kabej da sauri ta had'eyi miyo , ya tura takeaway gaban mami yana cewa "sweetheart bismillah shiru mami tayi taki ci "tana son yi masa maganar abincin da ya hana maryam girka mata da kuma abincin da babu a gidan amman tana jiwa maryam tsoron bala'insa dan haka dole itace zata kawo mata komai na bukata ta ajiye mata batare da saninsa ba "sweetheart eat !ni babu abinda zanci gida ma zan wuce mami ta fad'a tana haramar mikewa nan take ATA yace"a'a sweetheart kiyi zamanki babu inda zaki "bangane babu inda zani ba ?"haba sweetheart ya kike magana hk kamar kina jin haushina ?saboda ke nasa akayi order abincin nan amman duk kinki ci komai ,nifa ban gane miki ba “idanu ta zuba masa tana kallonsa ta rasa wani irin mutun ne shi ,babu yadda zatayi magana bai canza mata magana ba dan haushinsa tana ji amman meye na fitowa ya fad'a mata ?"dan Allah sweetheart kici komai da nayi miki order "tunda kake dani ka ta'ba ganin naci abinci order ?"yayi shiru yana furzar iska “da kayi order dan ni nace mka zanci ne ?"kai kafi kowa sani bana cin abinci waje kuma kai ma akan haka na raineka ina da tabbacin ko kana cin abincin order sai dai idan baka qasar nan kai ya langwabar yana dubanta dan gskiya ta fad’a.”
“dan haka kafi kowa sanin bana cin abinci waje kuma kaima haka duk abinda nake so ina yi da kaina ko nasa kuku su dafa min amman dan ka wulakanta matarka kake wani aikawa a siyo maka abinci daga waje idan ma nata ne baka buqata ai zaka iya daukar mata kuku ko wane su girka maka acikin gidanka
Mami na fadar haka gaban maryam ya bada rasss "kuku a gidanta a'a ?ina bazai yuwu ba bata son kowa atsakaninta da mijinta tafi bukata ganin gidanta daga ita sai mijinta gabanta na fad'a uwa ta zubawa ATA idanunta taji abinda zai fad'a."ba d'aukar kuka bane matslata sweetheart" meye matsalarka adamcy fad'a min meye matsalarka?"ko kuku nawa zan d'auka basu ta'ba min abinda sweetheart dina zata min ba"wani boyayyen ajiyar zuciya maryam ta sauke "haka mami yadda yayi maganar sai kuma taji tausayinsa ya lullubeta “duk abinci nan da nake order nake ci wallahi ina dai turawa cikina ne kawai amman maganr gsky ni abincinki nafi bukata fiye da kowani abinci a duniya, idan kina son na daina order abinci sai dai idan zaki dinga mana kina aiko mana amman sai ta qara hade rai tana zabga masa harara ".
“Ai ba sakar uwa bace ni ,kayi aure yanzu dole ka canza adamcy ka koma kamar tsarin kowani ma gidanci “kai sweetheart ki ajiye wannan batun magidanci ko menene ni har yanzu empty nake jina “kai fa sam bakasan mutunci ba bakasan rarrashi ba bakasan meye hakin aure akanka ba allah ya gani nida mahaifinka muyi Iya qoqarin mu akanka mahaifinka mutumin kirki daya san darajan iyali kafi kowa sanin kirkinsa akan iyalinsa kai ne dai bamu san a inda kaje ka kwaso wannan halin ba tana kaiwa nan a zafafe ta mike saurin riko hannunta yayi cikin nashi "haba sweetheart wai laifin me nayi miki haka ?Kallonsa tayi ta tabe baninta "bazata lamunce wannan iskancin ba ko ya bari matarsa ta dinga girka masa ko kuma ya dauko mata masu aiki cikin biyu yayi d’aya “kiyi hakuri sweetheart idan wani laifi nayi miki am very sorry ma zan d'auki masu aiki shikenan ki zauan kici wani abu sannan Kiyi zamanki kiyi mana kwana biyu ya zaunar daita kusa dashi mami yana shagwabe mata kamar wani qaramin yaro tace "aa banzo da niyyar kwana ba koma zan kwana ban zo da magungunan ba "wannan ai mai sauki ne ai sai naje na dauko miki ."
Yadda ya kwantar da kai yau yasa zuciyar mami ta sauko ta sausauta masa daman kuma tsakanin da d’a uwa d’an ma gilashi,ta sauke numfashi tace "karka damu zan dawo nayi maku kwana biyu in sha allahu amman yanzu gida zani "No sweetheart babu inda zaki kin ma dawo nan kenan ko kuma mu tattara kawai mu koma gidanki gabad'aya "dan murmushi tayi kamar ba ita tagama daukar zafi ba "kai adamcy ba dai rigima ba shikenan naji zan kwana dan tunda ka nace sai dai a sallama maka amman gobe goben nan zan kama gabana maryam tayi murmushi har ta qasa boye farincikinta dan jin mami zata kwana suka cigaba da hira mami ta jawo ledar gaban maryam ta bud'e mata "maza só ma ci duk an ramar dake abanza ATA ya saci kallon mami da alamun akwai magana abakinta “ aiko maryam kamar jira take ta soma cin abincinta hankali kwance tana cewa "kai gsky mami kici ko kad’an ne abincin yayi dadi sosai " ATA yaja tsaki "nonsense kawai kin iya cin na wasu kice yayi dadi amman idan cewa akayi Kiyi bazaki iya kamarsa ba sai dai ki kashe mutane da .."ya isa ya isa !! dan allah maryam tashi muje dakin ki kar a kashemu da gori suka mike suka soma qoqarin barin parlour’n.”
D’akin qasa suka shige suka barshi zaune ."basu jima da barin parlour’n ba ya fita ya bar gidan gabad’aya sosai maryam ta kasance cikin farinciki tare da mami basu bar farincikin iyasu kadai ba sai da suka rabashi dasu aunty shahida yayinda jifa jifa umma take kiran wayar maryam sai dai da zarar ta duba taga itace sai taki dauka dan bata son mami ta fahimci wani abu sallah ne kawai yake tashinsu daga hirar da suke . karfe bakwai ATA ya dawo har lokacin suna a d’akin ya shiga ya ajiyewa mami qaramar jaka da wasu ledodi wanda ko baa fad’a nama rago ne aciki dan tuni kamshinsa ya bayyana “ sweetheart ga magungunanki har da kayanki na hado miki dashi da naman rago “lallai adamcy yau abun ya motsa bai ce komai ba yasa kai zai fice daga d’akin tace “na gode allah yayi albarka .”yana zaune a falo yana kallon labarai suka fito tare da maryam suka hau sama har kusan karfe shadaya saura suna hira .”
cikin wani irin yanayi ATA ya shigo d'akin maryam wanda ranar ne karo na biyu daya shiga dakin ya tsaya yana kallon mami wacce fuskata ke kwance da annurin farinciki tamkar mai koyan magana ya bude bakinsa yana wa mami sallama "Sweetheart ni zan shiga na kwanta sai da safe ya soma taku cikin isa da kasaita don barin dakin, cikin sanyi murya mami ta kira sunanshi adamcy !d'an tsayawa yayi tare da juyowa suna fuskarta juna da mami idanunta ta xuba mishi kawai Tana kallonsa tare nazarinsa ganin yadda gabadaya yanayinsa ya sake sauyawa cikin dan kankanin lokaci meke damunka naga yanayinka haka ?"babu komai sweetheart "hakika mami tafi kowa sanin koshi waye ta fannin halayyarsa da abinda ke tattare dashi bata rai mami tayi tare da ajiye wayar hannunta "meke damunka ?dan qaramin tsaki yaja "kaina Ke dan min ciwo shiyasa nake son na kwanta da wuri tunda taji haka bata sake cewa komai ba dai ina da sabo ta rigada tasa ba da rashin son hayaniyarsa daman shi mutun ne ba mai san hayaniya ba ballanantana gashi yau tasashi magana "allah ya tashemu lafiya ta fad'a adaidai lokacin daya kusan fita daga dakin "kai tsaye bedroom dinsa ya wuce ,yasoma cire kayan jikinsa yaja towel ya daura Tare da shigewa bathroom ya sakarwa jikinsa shower byn ya gama wanka ya dauro alwala yana fitowa bai wani tsaya shafa mai ba ya bude wordrob dinsa sai kamshi turaren ne ke tashi a gurin , ahankali yasa hannu ya zaro jallabiya milk colour ya zira a jikinsa ba qaramin kyau ta maisa ba ya qarasa inda daddumar salla take ya dauka ya shimfida shafi’I da wutiri ya gabatar sannan yayi addua ya mike batare daya nade daddumar ba ya zare Jallabiyar jikinsa yayi fillinging daita ya sanya vest da boxcer ya canza wutar dakin zuwa mara haske ya d’auki remut ya qara karfin ac sannan ya fad'a Kan bed dinsa ya lullube jikinsa da bargo mai taushi ."
Bangaren mami kuwa har karfe shabiyu ta buga suna tare da maryam wacce bacci ya soma daukarta kasa kasa ta soma kiran sunanta "maryam ki tashi kije dakin mijinki mana kema fa na fahimci baki kulawa dashi kamar yadda nake zato maryam ta mike ta zauna tana duban mami da fuskarta da d’an mamaki ,sosai mami ta shiga mata fada tare da bata shawarar hanyoyin da zatabi gurin shawo kan mijinta cikin sauki , sosai jikin maryam yayi sanyi likis ita kanta tasan" inda mami bata kasance yar,uwa,ce ga mahaifinta ba ,hakika bazata dinga damuwa akan damuwarta ba kullum burinta ta gansu suna zaman lafiya tare da nusar daita yadda zata sake mallakarsa a tafin hannuta cikin ruwan sanyi batare da biye biye ko wani abu ba, hakika mami dabance acikin mutane km zuciyarta may kyau ce ba kmr irin ta mahaifiyarta ba km gashi Allah yayi ta may tsananin zumunci ce mami takarasa zanceta "