Showing 60001 words to 63000 words out of 169868 words
Chapter 21 - MAR'ADAM'S BOOK 2 COMPLETE DOCUMENT by Aisha Bagudu .txt
kalli nana hauwa’u taga itama hawaye take ta kalli ata cikin sa’a idanunsu ya tsarke cikin juna tayi kamar zata girgiza masa kai amman wata katuwar hararar daya zabga mata mai had’e da kallon banza yasa ta d’auke idanunta akanshi ,tana mai share hawayenta da hannu ta qaraso kusa daita nana hauwa’u ta riko hannunta zuwa gefe “sister kinji hukunci yayanki dan allah karki yarda ya kashe miki aure saboda ya hisham mutumin kirki ne nuzla ce matsalarki .”
“bani da zabi sister bazan iya ce masa a’a ba duk abinda yake son ya zarta akaina na amince ni mai biyayya ce a garesa ,maryam ta rungumeta ajikinta “bakya son yaya hisham ne ?”to bazan ce bana jinsa araina ba , amman idan yayana yace na koma gidansa zanyi idan yace a’a babu inda zani “wallahi sister kina son mijinki “ta fad’a tana zare jikinta a nata ta tsura mata ido tana kallonta hawaye ne kawai yake fita daga cikin idanunta qirjinta har wani sama da kasa yake “ta riko hannunta tana cewa “ shi bai rike nashi auren ba zai kashe auren wasu muje ki fad’awa mami kina son mijinki nana hauwa’u taki binta ta zare hannunta ta rakube gefe tana share hawayenta dole tasa maryam ta dawo ta tsaya kusa daita tana share mata hawaye .”
mb ya kira layin hisham cikin kankanin lokaci sai gashi ya shigo yayi mamakin ganin mutane cike ya tsaya yana kallonsu d’aya bayan d’aya sai dai bai ga matarsa acikinsu ba , wani mugun kallo ata yayi masa sannan ya qaraso gabansa ya tsaya tare da jin kai ya zuba hannuwansa duka cikin aljihunsa “baka son auta shiyasa ka zabi ka dinga quntata mata ta wannan hanyar ko ?hisham yayi shiru yana mai sunkuyar da kanshi kasa dan jin kunya “kasani nasani kowa yasani ban bada goyon bayan auren nan ba dan har yanzu bana son aurenku daita “cool down ata mb ya fad’a yana dafashi ya buge masa hannu yana qoqarin cukumar wuyan hisham yaya ibrahim ya shiga tsakaninsu “dan girman allah ka matsa “ babu inda zani ka samu waje ka zauna ayi magana ta natsuwa “idan har kaga na zauna to ya miko min takardar sakinta dan bazata qara zaman aure daahi ba har abada ya saketa yaje ya auri wacce yake so .”
Mmn sudais
💗💗💗💗💗💗
MAR'ADAMS
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗
*AYSHA A BAGUDO*
WATTPAD @HAUESH
AREWABOOKS USERNAME
AYSHAABAGUDO
bismillahirrahmanirrahim
Wannan littafin na kudi ne mai bukatar karantashi byn na kammalashi zai biya 1000 ta wannan account number din 1438775094 Aishat abdullahi access idan an tura sai a turawa wannan 09136918331 alert domin tabbatar da an tura domin sauraron littafaina a tuntubi chaneel dina (Hausa bakwai ) a YouTube.
Page 12
Jin abinda ATA ya fad'a yasa maryam duk ta rud'e sai zufa take fitarwa hankalinta yayi matukar tashi gbdy ta nemi natsuwarta ta rasa domin tasan halinsa tunda ya furta zai raba auren lallai zai aikata hakan "ta fashe da wani irin kuka mai karfi , haka ma nana hauwa'u kuka take sosai , yadda maryam ta rud'e haka matan dake tsaye a wajen suka rud'e gashi babu damar yin magana .mazan kuwa sai faman bashi hakuri suke yana fixgewa mb ya fuskancesa sosai yana cewa "haba ATA ka kwantar da hankalinka abi komai ahankali "kasan allah muddin ina raye sai na kashe wannnan banzar auren ."
qanqame maryam nana hauwa'u tayi ajikinta suna mai fashewa da wani kuka cike da tashin hankali maryam ta soma magana muryarta na rawa "sister ke kad'ai ce zaki kawo karshen wannan matsalar "nana hauwa'u ta zare jikinta ta tsura mata ido ,idanunta na sake cika da ruwan hawaye . saboda babu mai fad'a ma yaya adam yaji sai ke a yanzu idan kika nuna masa kina matukar son mijinki shikenan magana ta qare dan dole zai hakura ya barku "nana hauwa'u ta girgiza mata kai "dan allah sister karki bari ya rabaku yaya hisham mutumin kirki ne ki tashi kiyi wani abu ta karashe mgnr tana kuka numfashi nana hauwa'u ta sauke tana share hawaye "bazan iya ba sister duk abinda yayana ya zaba min shine daidai ."haba sister haba sister !! karkice haka mana kiyi hakuri kiyi wani abu mana ta qarashe maganar tare da qoqarin mikar daita tsaye "
da kyar nana hauwa'u ta mike tsaye bisa kafafunta ta soma tafiya jikinta na rawa rawa taku biyar tayi ta tsaya cak ta kasa cigaba da tafiya hawaye na sake wanke fuskarta yayinda ata da hisham suka tsurawa juna ido kowannensu zuciyarsa na zafi cike da tashin ahankali ." hisham ya janye kwayar idanunshi cikin nashi ya tsurawa nana hauwa'u yana mai shafa kanshi abu d'aya zuwa biyu ne suka tsarga masa a tsayen da yake a gabansa ,abu na farko farinciki yadda Adam yaji zafi da ciwo acikin zuciyarsa ,abu na biyu kuma mahaukaciyar soyayyar nana hauwa'u da yaji yana bin jinin jikinsa tare da huda duk wani tsoka dake sansar jikinsa ,cikin wani irin sauri zuciyarsa ta dinga tsalle tana bugawa da matsanancin karfi kamar zata fito daga cikin qirjinsa hannuwansa duka ya miko mata alamun tazo garesa dan bazai iya rabuwa daita ba ."
ta kalli yayanta dake tsaye rike da kugunsa, ta waiga ta kalli yan'uwanta sannan ta kalli hisham da har lokacin yake miko mata hannunwansa gabad'aya nana hauwa'u ta nemi natsuwarta ta rasa ji take kamar zuciyarta zata buga sakamakon fad'uwar gaban data risketa ,haka ne ma yasa jikinta ya cigaba da rawa gashi yaya hisham yaki d'auke kwayar idanunshi akanta wanda yayi sanadiyyar da suka fad'a kogin tunani hankalinsu ya bar duniyar da suke ciki ya lula dasu can wata duniyar . "friend kayi hakuri ka kwantar da hankalinka hisham bazai ta'ba cutar da auta ba ,sannan hukuncin da d'auka akanshi daidai ne ko yanzu ka taka rawa aciki rayuwar aurensu wannan zai zama kashedi ne mai karfi kayiwa hisham".
"shi kansa bai san yana son matarsa ba sai yau haka zalika itama auta tana son mijinta ka duba ka gani yanayin da suke ciki na damuwa a yanzu "ATA ya sauke hannunsa dake rike da kungunsa ya juyo yana kallon mb a kallon da yake masa ya fahimci ransa ya kai kololuwar tashi da maganar da yayi masa ahankali ya kalli inda hisham yake tsaye yana mikowa nana hauwa'u hannu ranshi ya qara 'baci cikin tsananin fushi yace "wallahi wallahi idan kika kuskura kika isa garesa sai na balballa ki "Jin sautinn muryarsa yasa nana hauwa'u tai saurin dawowa haiyacinta tana mai sunkuyar da kanta kasa ."
A rud'e maryam tace "me yasa yaya adam "! ta matso gabansa ta tsaya tana dubansa hawaye na sauka daga idanunta "me yasa zaka kashe mata aure alhalin tana son mijinta ?ya kamata kayi masa uzuri saboda kai kanka kasan yaya hisham mutumin kirki ne wallahi bazai ta'ba cutar da sister ba duk duniya a halin yanzu sister bata da kamarsa idan ka tsaya domin kwatar mata 'yancinta nifa ?"nida kake min fiyye da abinda yake mata fa"? sai da gaban kowa dake wajen ya bada wani sauti bugu mai karfi
Wani mugun kallo yayi mata da tsumammun idanunshi yana nuna da yatsan hannunsa "wacece ke da ina magana zaki saka min baki ?ya fad'a tare da d'auketa da wani gigitaccen mari yana sake nuna ta how dare you ?".
" duk nan babu wanda ya isa bare ke din banza da ko kwatan matsayi kowa anan baki kai ba ." abinda nake miki ina yi ne dan bana sonki ,suma kuma da kika ga zan rabasu dan nasan basa son juna sukai aure, bana goyon bayan auren da ba'a so, dan bana son a aura min matar da bana só kamar yadda adabaibayeni dake "yayi maganar da karfi jikin maryam yana rawa ta fad'a jikin aunty shahida tana wani irin kuka mai ta'ba zuciya ."gabad'aya parlour'n yayi shiru tamkar babu wasu halittu acikinsa, babu wanda bai tausayawa maryam ba illa aunty abida wacce taji dadi aranta kuma hankalinta ya kwanta ta qara tabbatarwa kanta sultana ce macen da zatai wining din heart dinsa dan haka ta washe baki cikin jin dadi tace tana ".
"kema maryam da karanbani kike keda kika san matar cushe bata daraja ,me ya kaiki saka masa baki a maganarsa ?."you're very stupid kema nace ki saka min baki a maganata ne ?"ko ina ruwanki ? kai tsayuwar me ma kikewa mutane anan ?da mijinki nake da issue ba dake ba oya leave "ya nuna mata kofar fita cikin kuka tace "ah ah ni ai yar'uwarka ce dole ina da ikon da zanyi magana kuma ma ai anan ka sameni ba daga sama na shigo ba ,magana kuma dole nayi wallahi wannan kam ba irin matarka bace sam baku dace ba ka jira matarka na nan zuwa amman kam sam ba mata bace " abida i saiid out of this hall kuma ko da wasa karki sake shiga hurumina idan ba haka ba zan baki mamaki .yaya ibrahim ya kama hannun matarsa yayi hanyar waje daita amman aunty abida ta turje tana cewa "ka sakar min hannu babu inda zani da kyar ya samu ya fitar daita ya dawo ."
"Me ye laifinta adamcy ai gsky maryam ta fad'a maka "wato laifi tudu ka take naka ka hango na wani ya kalli Aunty shahida da kyau yace "ina mata abinda nake mata ne saboda bana sonta kuma da ina da dama zan iya rabuwa daita har abada ,haka zalika shine dalilin da yasa zan kashe auren auta domin zukatan kowa ya huta, yaje ya auri wacce yake so itama ta samu wanda take so yake sonta ya qarasa mgnr gumi na karyo masa sannan ya kalli nana hauwa'u "Ke maza ki koma d'aki "da mugun sauri ta juya tayi hanyar d'akin tana jin wani irin fad'uwar gaba mai tsanani hisham ya kallesa kawai batare da yayi magana ba duk da maganar yake son yi amman idan yace zai yi komai zai qara rikicewa ne shurunsa ne yafi zama alkhairi ."
A rikice mami ta fito alamun tashin hankali aunty khadija na biye daita ."ta tsaida nana hauwa'u aunty khadija ce taje ta fad'a mata abinda yayiwa maryam tana gama qarasowa ta dakawa ata tsawa tace "me maryam tayi maka ka mareta "?yayi shiru yana sake tamke fuska sosai "adamcy kaji tsoron allah, kaji tsoron ranar da hakin maryam zai kamaka idan baka sota ba'ace ka qaunaceta ba amman me yasa zaka dinga tozarta min ita agaban mutane wallahi duk namiji mai wulakanta matarsa agaban mutane yayi asarar rayuwa dan haka ka bata hakuri yanzu yanzu ."
"What !?
ya furta a razane zai sake bud'e bakinsa yaji mami ta d'aukesa da mari "you're very stupid too hakurin ne bazaka bata ba "sweetheart marina kikayi akan wannna yarinyar ?na mareka kai ma baka duba darajata ba bare hisham ya duba darajata har ya ragawa diyar cikina "hisham ya sunkuyar da kanshi kasa yana mai tsananin jin kunyarta "yanzu sweetheart akan na mari wannan duwaf din yasa kika mareni?"eh akanta na mareka idan ka sake ce mata duwaf zan maka double dinsa idan bakaji kunyata ba bazan ji kunyarka ba bare na raga maka maryam ta rike hannu mami dan ta fahimci qara masa wani marin zatayi "dan allah mami ki rufa min asiri kiyi hakuri karki masa komai ."
a fusace yake kallon maryam fuskarsa a tsuke itama din shi take kallo nan da nan jikinta ya dauki rawa ."ido cikin ido suke kallon juna a karo na farko kenan a rayuwarsu duk da suna kallon juna amman ba kamar haka ba kallon nadama take masa yayinda shi kuma yake mata kallon zaki gane kurenki da sauri ta janye kwayar idanunta saboda wani irin mugun kallon da taga yanayi mata yana fesar da iska mai zafi daga bakinsa."hisham !"mami ta kira sunansa ya d'ago a natse yana dubanta cike da girmamawa "ban hanaka qara auren duk wacce kake so ba amman bazan d'auki tozarci da wulakanci ba karka wulakanta min yarinya idan kasan wulakanta min yarinya zakayi na had'aka da allah ka sauwake mata kamar yadda d'anuwanta ya bukata ".
"kiyi hakuri Mami "ba maganar hakuri bane hisham bazan yarda yarinyata tayi zaman rashin yanci a gidan aurenta ba" hisham ya sauke boyayyen ajiyar zuciya domin gani yayi kamar son kai garesu menene ata baya yiwa maryam? irin cin kashin da yake mata shi ko kwatansa ba yayiwa nana hauwa'u amman shine dan son kai irin nasu zasuji haushi har su buqaci raba auresu "idan kasan baka bukatarta arayuwarka kaje ka aiko min da takardarta "muryarsa a sanyaye sannan cike da girmamawa yace "mami Kiyi hakuri ina son aurena ! "to kayi magana da yayanta tana gama fad'ar haka ta juya ta zata koma d'akinta." taji qara fashewar glas tass !
Ta tsaya cak tare da juyowa ata ta gani tsaye jini na bin hannunsa ,ya rasa meke masa dadi bakinciki goma da ashirin ga marin da mami tayi masa ga damar da ta bawa hisham yasa zuciya ta dibesa ya bugi show glass din dake gefensa shine nan take jini ya soma bin hannunsa aiko maryam ta rikice "na shiga uku mami yajiwa kanshi ciwo ita kanta mami cikin tashin hankali da kidema take kallonsa ranta ya baci matuka da abinda yayiwa kanshi amman ta danne zuciyarta daga taimaka masa ta maida idanunta ga maryam dake kyarma cikin alamun rashin damuwa tace "meye damuwarki dashi ?cikin yin qasa da murya maryam ta kalleta "jini ne fa mami ."ina ruwanki oya wuce muje d'aki taja hannunta suna tafiya maryam na kallon bayanta ."
Shi kuwa ATA zuciyarsa banda tuttukin bakinciki babu abinda take Mb ,yaya ibrahim yan'uwasa har ma da hisham hakuri suke bashi ganin yadda jinin ke tsiyayya a sakamakon jininsa dake gudu fiyye da kaida amman ko motsi bai yi ba ,da kyar suka kamoshi suka zaunar dashi akan kujerar dinnig d'aya byn d'aya mutanen dake tsaye suka fita a parlour'n ya saura iyasu kawai nana hauwa'u ta yage bakin mayafinta ta durkusa gabansa idanunta cike da kwalla bai d'ago ya kalleta ba ,tana qoqarin kamo hannunsa cikin zarewar ido da maseefa ya janye hannunsa ." cikin tsarkewar murya tace "please yaya karka ce a'a wallahi zan iya had'iyar zuciya na mutu idan wani abu ya sameka bazamu iya jurar rashinka ba muna sonka fiyye da tunaninka ,bazamu so mu rasa d'an'uwa kamarka ba ."
runtse idanu shi yayi kawai jikinta na rawa ta sake riko hannunsa dake tsiyayar jini wannan karon bai dakatar daita ba ta daure tana cewa "bari a kira doctor" still bai ce uhm bare uhm ba sai dai wata irin zufa ke tsatsafo masa akan goshinsa da ilahirin jikinsa ya kamo lip's dinsa na qasa yana cizawa da karfi ya bud'e tsumammun idanunshi da suka gama canza kala tsabar zuciya ,hanunsa dake daure ya tsurawa ido suka dan ja baya kad'an dan ya samu dasataccen iska ." yana zaune yana cikin tsananin damuwa maryam ta fito da sanyi jiki ta kallesa zaune shiru har tsawon minti uku kafin ahankali ta dinga takowa har ta qaraso garesa ta tsaya taga alamun an daure masa hannu ."
ajiyar zuciya ta sauke kana ta daura tafin hannunta akan goshinsa tare da goge masa zufar dake tsatsafo masa duk da sanyin ac dake ratsa parlour'n idanunshi ya sake runtse wa yana jin qarin ciwo akan wanda yake ji cikin kulawa tace "sannu yaya bai amsa ba sai ji da yayi kamar ya tashi ya rufeta da matseyacin duka, ganin bai ce komai ba ta juya da sauri ta nufi dining area ta zuba ruwa a glass cup ta nufo inda yake zaune yana huci tamkar zaki da sauri aunty shahida ta rikota tana girgiza mata kai alamun ta barshi hakan sai dai itama kanta ta girgiza mata tana kokarin fixgewa daga rikon datai mata ta qaraso inda yake jikinta na kyarma ta mika masa cup din ruwa cikin tsanani tashin hankali ta furta" ruwa ..! "
ya dago fuskarsa a hade cike da fushi da zafin zuciya ya amshi glass cup din hannunta ya buga akan tayis yana huci tare da cewa "Congratulations maryam kinyi nasarar kinyi nasarar !! sace min zuciyar mahaifiyata ba? Cike da tsoro ta qame a gabansa hawaye na turereniyar zuba daga idanunta tana girgiza masa kai ya mike tsaye yana nuna ta "wannan kad'ai Ya sake ninka wutar kiyayyarki acikin zuciyata , bana sonki kuma bazan ta'ba sonki a matsayin mata acikin gidan nan ,bazaki ta'ba zama suruka acikin gidan ba dan ban amince dake a matsayin matata ba "yana gama fadar haka ya ciro waya daga cikin aljihun wandonsa ya soma kira wata number yana tafiya yana waya "kuna da daki a girls house dinku okay ka duba min ina bukatar d'aki ganin nan zuwa ".
Yana tafiya suna biye dashi babu irin kiran da Aunty shahida batayi masa da yaya Ibrhim mb har da hisham ba amman ina ATA bai waigo ba ya ma dade da yin nisa dan tuni ya shiga motarsa atare gbdynsu suka sauke ajiyar zuciya suna sauke numfashi su aunty shahida suka riko hannun maryam suka shigo parlour'n suka bar su yaya ibrahim tsaye a waje suna tautaunawa ."suka zaunar da maryam wacce ta gama rikicewa tare da zuba masa ido "dan girman allah waye ya fadawa mami ya mareni ?sukai shiru "wallahi ko waye bai kyauta min ba saboda kunga abinda aka jawo min, kunga bala'i da aka had'a min allah ne kadai zai kwace a hannunsa ta qarashe mgnr tana zubar da hawaye."
"kiyi hakuri maryam na d'auka hakan da mami tayi zai kawo miki mafuta né arayuwarki " maryam ta matso ruwan hawaye tace "dan allah karku bari mami tasan ya tafi guest house dan damuwar zata sake mata yawa mu bar shi a tsakanin mu ta qarasa mgnr tana sheshekar kuka dan tasan yau allah ne kawai zai kiyayesa daga koma wa shan giya sigari kam ma baa magana tasan dole sai ya sha aiyar zuciya suka sauke gabad'ayasu babu wanda zai fad'a basu sani ba bayan shigar mami ta dawo parlour'n kuma taji duk abinda