Showing 69001 words to 72000 words out of 169868 words
Chapter 24 - MAR'ADAM'S BOOK 2 COMPLETE DOCUMENT by Aisha Bagudu .txt
sam bashi da alamun zai kalli inda take bare yace wani abu ,tunani rayuwarsa kawai yake ta ina zai cigaba da zama daita bai ta’ba jin komai akanta ba ,shikenan mafarkinsa ya kasance karya ne kamar yadda aka sha fad’a masa dan da gaskiya ne yadda yake qoqarin neman princess daya sameta “nasan na dameka da magana kayi hakuri sannan dan allah kaci abinci .”shiru ne stil ya biyo baya bata ji komai aranta ba dan wannan yana cikin halinsa rashin son magana ta numfasa tana cigaba da kallonsa idanunta cike da ruwan hawaye .“dan allah kayi hakuri kaci wani abu ,rashin cin abincinka zai iya haifar maka da mummunar damuwa kuma bashi bane mafuta agaremu dan allah kaci wani abu tayi mgnr muryarta can kasa sannan cike da rawa .”
sai lokacin ya cire hannuwansa dake sarke cikin juna ya d’an kalleta ,gabad’aya ta dawo kalar tausayi amman ko kad’an bai ji wannan tausayin ba acikin ransa .”har sanda ta cigaba da magana “nasan baka yarda da wannan aure ba ,sannan baka sona amman at least dan allah ka boye wannan rashin qaunar da kake min a idanun mutane, idan ya zama dole sai ka nuna ka nuna shi atsakaninmu ,saboda samun kwanciyar hankalin mami ,aunty shahida da sauran yan’uwana bana son na gansu cikin damu “.“I can’t do it and I can’t accept this marriage ban tsara rayuwata dake ba gbdy bakya cikin tsarin rayuwata.” ya katseta ta hanyar fad’ar haka “why sweetheart ?” me yasa kike son tursasa zuciyata?shiru tayi tare da runtse idanuwanta hawayen dake boye cikin kwarnin idanunta suka samu nasara zubowa,ba tayi yunkurin sake cewa komai ba ta bude kular abinci ta zuma masa wani ta mika masa “ya adam eat your food zan juri komai amman bazan iya jurar rashin cin abincinka ba .”
kin amsar plet din hannunta yayi dan baya ji zai sauko haka cikin sauki ya rungume aurenta never yatsan hannunsa ya kai ya nuna mata bakin kofar fita “please leave i don’t want to see your face “ya furta a tsawace “ya Allah ta furta a fili tana sauke naunayen ajiyar zuciya sannan ta cigaba da kallonsa fuskar nan nashi a d’aure kamar koda yaushe,”amman yaya ..”I said leave …”ya sake nuna mata hanyar fita daga d’akin maryam kam gbdy ta rikice ta rasa abinda zatai jiki a sanyaye ta mike har tayi taku biyu tajiyo sautin muryarsa a kasalance tankar bashi ya gama rashin mutun ci ba “ki d’auke wannan banzar abincin naki !” lumshe idanunta tayi tana mai had’eye kololun bakincikin daya tokare mata qirji ta dawo ta durkusa ta d’auki tray ta fito ta shiga d’akinta .”
A fusace ta dangwarar da tray a qasa ta d’auki wayarta ta soma neman layin mahaifiyarta kira d’aya ta d’auka “Umma akwai matsala fa, ta fad’awa mahaifiyarta haka cikin tashin hankali da kidema.” “Akwai matsala kamar ya“?”yaya Adam fa yau ma bai ci abincin ba ,coffe ma dana had’a masa ya kwa’be ban san me zan yi ba kuma “ta fad’a tana maida dubanta ga kofar shigowa d’akinta cikin alamun damuwa sakamakon jiyo motsi muryarsa can qasa tace “ummah ina zuwa naji kamar motsinsa ta bud’e kofa ta leko shi din ta hango yana taka step da kyar kamar mai tausayawa step , wani dogon ajiyar zuciya da numfashi ta sauke alokaci d’aya “shine ya fito”ta fad’a tana komawa cikin d’akin “okay karki damu kullum idan zaki masa tayin abinci ki tabbatar kin saka masa wannan magani ni dai burina yaci ko spoon d’aya ko ya sha acikin abun shansa ,wallahi maryam a yadda nake jin bakincikin abinda wannan mijin naki yake miki matsawar bai zama naki ba zan iya kawar dashi daga doron duniya cikin ruwan sanyi kowa yayi asara ,muddin bazaki mallakesa ba gara kowace mace ta rasashi .”
da tarin mamaki maryam ke sauraron mahaifiyarta bakinta na rawa tace “a’a ummah banason!banason na rasa shi “tô meye amfanin ke baki samesa ba wata can tazo daga sama ,bari na fad’a miki abinda baki san na sani ba na samun labarin yadda yake son yarinyar mafarkinsa kuma kullum burinsa da adduarsa akanta ne .”ummah ta d’an yi shiru yayinda maryam cike da mamaki tace”wa ya fad’a miki haka ?”bangane waya fad’a min ba maganar duniya yana boyuwa né ko kin d’auka duk abinda ke faru bani da masaniya né ?tun daga lokacin da kka furta min kina son adam na maida hankalina kacokan akan sanin halin da Kike ciki dashi karon kanshi adam din ,dan haka idan bakya son ki rasashi kiyi duk dabarar da zakiyi yaci maganin nan ya zamo naki ke kad’ai ,ina son ki juya adam ,ina son ki saukewa adam jin kanshi ina son duk sanda zan shigo lagos jiniyar motocinsa né zasu tarbeni ,ke ina son na shigo gidansa cikin nuna isar ni uwar matarsa ce “.sun d’an jima suna tautaunawa umma na koyar daita hanyoyi da dabaru tare da yadda zata kwantar da kai ta samu yaci abincinta .”
Kwanaki biyu kenan aunty ta rasa gane kan maryama haka umma da habib har ma da sadam sosai suka d’aga hankalinsu dan haka ranar monday tun da safe umma ta shigo bangarensu tace ta shirya suje asibiti maryam ta kalleta a marairaice tace “lafiyarta kalau fa !umma tace “ke dai ki shirya muje a duba min lafiyarki hankalina yaki kwanciya, dan wannan rashin lafiyar bata rashin samun aiki bane kawai akwai abinda ke damunki “.maryama ta mike da kyar ta shirya cikin doguwar riga milk colour tayi Roling din kanta da mayafin doguwar rigar ta sanyawa qafafunta takalmi flat.” ita dai aunty idanu ta zuba masu har suka fice maryama naja qafafuwa umma da yaya sadam da habib na biye daita har bakin titi suka rakosu sai da suka shigarsu mota sannan suka dawo gida zaman jiransu ”.
Kai tsaye asibitin mayfear dake oke koto suka nufa umma tayiwa likita bayani yadda maryama take ji sannan likita ya bukaci ta basu guri fitar ummah yasa likita tambayarta yadda take ji “kasala nake ji sai qirjina dake min nauyi ga ciwon kai mai tsatsanani sannan zuciyata na min ciwo likita ya gwaggwadata sannan yace “kina yawon tunani ko ?tayi shiru tana nazarin maganarsa can tace “eh to bazaa rasa ba “.tunanin me kikeyi da qarancin shekarunki haka ?muryarta a raunane tace “ba komai ! ya kalleta na second biyu sannan ya d’auke kanshi yana rubuce rubuce tare da cewa “karya ne kina tunani domin tunani ne ke kawo duk abinda kika lissafa” shiru tayi ta rasa mai za tace likita ya dage lallai sai yaji damuwarta .”
numfashi ta sauke mai karfi tace “kawai d’an damuwar rashin samun aiki ne nan tayi masa bayani kad’an acikin damuwarta likita yace “to shikenan ki daina yawon tunani kisa allah a gaba ya rubuta mata magunguna suka koma gida da addua da rarrashin ummah da aunty tare da yaya sadam dan yanzu kullum yana tare daita yana bata kulawa har mamakinsa take kafin ya fita office zai shigo ya dubata haka idan ya dawo zai shigo daga shi har mahaifiyarsa suna bata kulawa wanda hakan yasa maryama ta dawo daidai ta cire zance samun aikinta aranta ta maida hankalinta akan zane .”ranar wata lahadi tana zaune a bangaren ummah suna hira suka jiyo sallamar subai’a ahankali ta d’ago idanuwanta ta saukesu akan kofar shigowa tana kallon subai’a tsaye, sanye cikin wasu hadaddun kaya riga da siket tayi rolling kanta da mayafi baki kafafunta sanye cikin baby shoe masu shegen kyau hannunta rike da leda kana kallonta zaka fahimci rayuwa ya sauya mata daman kuma idan Z&A suka d’aukeka aiki suna baka kudi masu yawa ka fara kimtsa kanka bare ita matsayin da take tasan zata samu da d’an yauwa .”
hakan nan taji wani abu ya tsarga mata da sauri tayi qoqarin kawar dashi acikin zuciyarta dake bugawa da karfi ta sakar mata murmushi wanda suka bayyana wushiyarta sama da qasa .”ummah ma ta saki fuska tana “cewa subai ce a gidanmu yau .”?marhabun lale da zuwa “cike da farinciki subai’a ta qaraso ciki ta durkusa har kasa gaban ummah tana cewa “nice ummah ina yini ?lafiya kalau subai ya mamanki da kannenki ya aiki kuma ?alhamdullahi mun godewa ta mike tsaye ta zauna kusa da maryama da idanunta ke kanta har lokacin ga wani murmushi da yaki daukewa akan fuskarta .subai ta kamo hannunta cikin nata “daga wajen aunty nake tace kina nan ya kike ya kwana biyu ?lafiya qalau subai’a nayi kewarki sosai ,wallahi nima kina raina kullum da tunaninki nake kwana nake tashi amman yanayin aikin dana iske a office babu sauki .”
maryama tayi murmushi tana cewa “wallahi subai’a idan na ganki cikin farinciki sai naji dadi a raina ”na gode kawata ina alfahari dake ta kalli ummah “umma ki tayani godiya a wajen kawata ta sadaukar min da aikinta “allah ya taimaka ai yiwa kai ne subai’a allah ya bata wanda yafi wannan amman maryamah ta nunawa duniya cewa ita mai qaunarki ce ummah ta furta tana dubanta .”Sosai kuwa ai bazan ta’ba mantawa daita arayuwata ba allah ya bar mana zumunci mu har ya’ya na haifi mace ta haifi nmj mu had’asu aure ummah tai murmushi “to allah yasa muna da rai da lafiya maryama ta mintsine cinyar subai’a tana cewa “dan son kai kece zaki haifi nmj ni kuma mace salon ki dinga kwacewa d’ana yan kudadensa subai’a ta sosa inda maryama ta mintsineta tana dariya “to shikenan ni na yarda zan haifi nmj ai duk ya’yana né atare suka rungume juna cike da farinciki .”
bayan su natsa maryama ta mike ta kawo mata ruwa da abinci tare da janyo ledar data shigo dashi tana cewa “kawata me kika kawo min né ?subai’a tace “bud’e kigani” ta bud’e mayuka ne set da turaruka masu yawa har da pad aciki ta saki murmushin jin dadi“tun kafin maryama tayi mgn tace” duk naki ne kawata .maryama ta dan zaro ido “kai subai’a na kuwa go ..”no maryama kin wuce haka a wajena me ma nayi miki da zaki gode min ?maryama ta mikawa umma ledar ta duba itama godiya tayi kuma yabawa subai’a sosai .”ahankali subai’a take cin abinci suna hira da maryama a qalla sun d’auki minti talatin zaune cikin parlour’n umma sannan subai’a ta kalli maryama a karo na sau babu adadi “kawata kinsan karfin zuwanah yau din nan kuwa ?maryama ta girgiza mata kai alamun a’a.”
“mr ATA mai kamfaninmu yana buqatar kwararrun masu zane a kamfaninsa na AGC shine nace nazo na fad’a miki ko zaki shiga tsawu masu neman aiki akarkashinsa?”why not ?me nake jira ?to ai kuwa sai shirya zuwa da samfurin zanenki kiyi sumit ta haka ne zaa tantance sosai tayi mata qarin bayanin yadda tsarin yake “kai gsky kawata naji dadin wannan labarin da kika zo min dashi na gode sosai,dan allah ki daina ai babu wannan tsakaninmu “na ma yi tunanin ko mr ammar ya fad’a miki ,wallahi ko d’aya bai fad’a min ba ai fushi yake dani .”fushi kuma ?”akan me zai yi fushi da yar gaban goshinsa ?
“manta dashi kedai thank you so much I really appreciate “ko akan kin bar min aiki ?kai nasan ma saboda shine yake fushi dake ,”nace ki manta dashi muyi wata hirar yadda maryama ta tsinci kanta cikin farinciki haka ma ummah har murnata taso tafi ta maryama sosai ta sake sakankancewa da subai’a lallai itama kawar arziki ce daman sai hali yazo d’aya ake kawance ummah ta tashi ta shiga ciki domin ta basu waje .”hira ce ta barke sosai atsakaninsu sosai maryama taji dadin zuwan subai’a sunyi hira mai mahimanci da subai’a dan bata boye mata komai ba akan aurenta da yaya sadam aiko tayi murna tare da mata fatan alkhairi” sai laasar sannan subai’a ta mike tayi masu sallama ta kama hanyar zuwa gida.”
Zaune maryama take a d’akinta tayi nisa a zanen samfurin da zata gabatar a A.G.C ta jiyo sautin muryar aunty tana kiran sunanta “Ina zuwa aunty “ sai dai shiru bata mike ba ta cigaba da zanenta aunty ta shigo d’aki ta mika mata cup din tea” na gode my world best kamr Kinsan ina bukata “ don’t worry my life is for my princess. aunty ban san irin son da nake miki ba wallahi ina jin kamar na fasa auren nan na cigaba da zama dake .”thank you so much my princess nima zanyi kewarki sukai shiru na wani lokaci yayinda maryama ta cigaba da zane .”
“ maryama !”
da sauri ta d’ago daga abinda take ta tattara hankalinta dan duk sanda mahaifiyarta ta kirata da wannan sunan abu ne mai mahimanci zata fad’a mata “nan kusa zakiyi aure my princess Kinsan rayuwar gidan aure ba kamar rayuwar gidan iyaye bane ina son ki sawa ranki cewar lallai sai sadam ya yarda zakiyi aiki sannan ki amince da aurensa da zuciya d’aya sannan ki sonshi har cikin zuciyarki .”
Maryama tayi shiru tana cigaba da kallon mahaifiyarta .”me zai hana ki hakura ki ajiye aikin ki rungume rayuwar aurenki “wani dogon naunayen ajiyar zuciya ta sauke “aunty kina son aurena da yaya sadam kusan duk kinfi sonshi akan sauran wad’an da suka nemi aurena a baya ?”sosai kuwa my princess ina son ki auresa , mahaifiyarsa ta taimaka min arayuwa ,mahaifiyarsa mutunce da kirkinta ya wuce misali ,bancin allah da ita da yanzu ban san makotana acikin gidan ba ,ta tsaya min ta tsayawa ya’yana ta yanto min ya’yana daga bauta nasan bakisan dalilin da yasa aunty salma da hassana suka daina bautar dake ba ?itace silar wannan ta kwatar min ‘yancinki wallahi ko yanzu na mutu nasan ruhina zai samu salama tunda gabadaya kulawarki zata koma qarqashinta .” ta qarasa maganar hawaye na cika idanunta .”
shiru sukai gbdy babu wanda yace uffan daga aunty har marayama kafin daga bisani maryama tace “ amman aunty taya zan bar aikina dana rayu dashi idan ma na hakura da aikin office aikin zane fa ?ban san ya zanyi ba bayan rayuwar nan babu tabbas “ amman shikenan aunty karki damu zanyi komai akanki haka qaddara rayuwata tazo yaya sadam yazo cikin rayuwata ba dan ina sonshi ba na sasadaukar da rayuwata zan auresa yanzu kuma ya zo ya rusa min komai nawa ,gbdy yayi distroyen rayuwata matukar bai barni nayi aikina ba “ta ajiye pencil din zanenta tasa hannunta tai tagumi tana kuka.”kuka take sosai har da sheshekan nan da nan hankalin aunty ya tashi “ki daina kuka please!” me zanyi aunty ?”me zanyi daya wuce kuka tund bazan iya ja da dukkanin umarninki ba “.
hawaye ya zubo ma aunty ,lokaci daya ta tuno mahaifinta da mahaifiyarta irin gwagwarmayar da suka sha akan karta auri mahaifinsu amman taki masu biyayya ita kuwa wani aikin alkhairi ta ta’ba yi arayuwarta da allah ya bata ya’ya kimtsasu masu gudun ‘bacin ranta ?tayiwa kanta tambaya tana mai fashewa da kuka” nan kuma hankalin maryama ya qara tashi ta kai hannu tana goge mata hawaye “please aunty ki daina kuka akaina wallahi duk abinda kike so shi zanyi bazan ta’ba bata miki rai ba “ zan miki biyayya amman ina neman alfarmar agurinki ?aunty ta kamo hannunta ta rike gam cikin nata “komai kike so my princess zanyi miki shi “ki kai mu wurin danginki ina son naga family’s dinki ki amince aunty dan allah ko sau d’aya ne mu sansu .”numfashi aunty ta fesar kawai tana runtse idanunta “ bilkisu rayuwa babu tabbas ki koma ga iyayenki ki rungume iyayenki da qaddararki bawa baya wuce qaddarasa na ari bakin gbdynmu ki yafemu bilkisu muma bamusan qaddararki bace auren hussein ,da dukkaninmu muyi biyayya ga allah ,da bamu jayayya ba hukuncin allah ba, ina mai baki hakuri kiyi hakuri ki dawo garemu allah kuma ya baki ikon cinye jarabawarki maganar babbar yayarsu kenan wacce suke uba d’aya alokacin da take chart din zuciyarta a bushe take bata jin zata koma garesu amman yanzu ita kanta tana kewarsu .” tana son zuwa garesu amman bata san me zata tarar daga iyayenta ba ,”aunty kin min alkwarin zamuje kafin bikina ?ta gyada mata kai tana dubanta ,maryama ta matso kusa da mahaifiyarta tana goge mata hawaye” ina sonki mamana “nima ina sonki sarauniyata “ta fad’a tana shafa sumar kanta da suka zubo zuwa gadon bayanta .”
******
Zaune ATA yake a parlour’nsa tare da abokansa kuma yan’uwansa shawul,mb da salim hira suke amman shi jifa jifa yake sanya masu baki “qarar takun takalmin maryam ne ya janyo hankalinsu wani hill ne mai shegen tsini tasa wanda ya qara mata tsawo daman kuma haka gabad’aya takalmanta suke bata da silipas sai na yawo acikin gida da bayi sarai ATA yaga tahowarta ta qasan idanunshi itama ta lura da hakan amman kuma sai take ganin kamar ba gaske bane , dan yadda yayi din bazaka ta’ba cewa ya kalleta ba .a natse ta qarasa saukowa fuskarta a sake ta gaishe dasu “sannuku da zuwa ina yininku ko ina kwana zance dan ban duba lokaci ba na sauko ?lallai yar mami kinji dadin aure to ina yini muke “inji cewar mb shawul yace “wannan mijin naki ne zai yarda azo masa gida da safe ai wallahi da sai ya tafattakemu.” gabad’ayasu suka dariya ta d’an saci kallonsa taga ko kallonsu bai yi ba danne danne kawai yake a wayarsa tace “a’a karku yiwa mijina sharri babu wani fatattakarku da zai yi ta fad’a sannan ta samu waje ta zauna kusa dashi sukayi mugun daf da juna da zata qara taku guda zata iya masauki a faffad’an qirjinsa shawul ya kalli salim yace “lallai yarinyar nan wuyanki yayi kauri har kin soma shigar masa ?.”
“ba dole ba miji ai ba wasa ba” zaro idanu sukai duk hirar da suke ATA yana jinsu amman bai ce uhm ba bare uhm uhm sai ma wani kololon bakinciki daya tokare qirjinsa yadda ta wani saki baki “yaya bello bari naje na shirya maku dining na dawo “ta yunkura ta mike ta soma taku su kuma suka cigaba da kallon ATA mb yace “dan allah dan annabi abokina ka sausautawa yarinyar nan haka “me nayi mata ?ya tamnayesa batare daya kallesa ba