Showing 99001 words to 102000 words out of 169868 words

Chapter 34 - MAR'ADAM'S BOOK 2 COMPLETE DOCUMENT by Aisha Bagudu .txt

06 Nov 2024

10885

da maza tashi ki sake shirya kanki kije ki kula da mijinki "km cire wannan tsoron nasa da nake hangowa acikin kwayar idanuki da kyar maryam ta samu ta mike tana may dagawa Mami kai alamun taji .”




Gaban mirrow dinta ta qarasa ta feshe ilahirin jikinta da turaruka masu sanyi kamshi sanna ta dauki hijab ta daura a saman rigar baccin dake jikinta ta fito zuwa dakinsa sai datayi addua sannna ta tura kofar dakin ta shiga ."acikin hasken da bai gama haskaka dakin ba ta hangosa kwance cikin bargo ahankali ta dinga daga kafafunta dan kar mostinta ya tayar dashi ta dan tsaya gabansa tana kallon kyakkwar fuskarsa ahankali yake sauke numfashi inda tasan mami zata bukaci tazo dakinsa data zuba masa magani acikin coffe ya sha ta samu natsuwar kwana tare dashi cikin salama ta zare hijab dinta ta ajiye bayansa ta zagayo ta hau saman gadon ta dan yaye bangon dake lullube dashi ta kwanta bayan ta cire hijab din jikinta bai motsa ba hakan yasa tayi tunanin baccinsa yayi nisa ta sake matsosa tana shakar kamshi jikinsa da kamshin turarensa. jikinta daya hadu danashi yaji kamar an ta’ba shi da wuta yayinda ita kuma sauyin yanayi taji a ilahirin jikinta kusan awa daya da wani abu suna kwance haka yadda bata runtsa ba haka shima bai runtsa ba .”




Zuciyarta ce ta bata kwarin gwiwar kai hannunta jikinsa ta soma shafasa tana aika masa wasanni stil bai motsa ba kuma bai ji komai ba sai tarin bakinciki mamaki da karfin halinta ya kamata shi Kmr ya tashi ya rufeta da duka amman ya kyaleta saboda darajan sweetheart dake gidan ganin bai motsa ba yasa maryam tayo kasa da hannunta daidai kasan marasa nan ne fa yaji bazai iya barin ta cigaba da iskancinta data tsiro dashi ba a yau ,zaraf ya damke tsintsiyar hannunta tare da jijiyo ya zabura ya mike zaune tamkar wani zaki mikewa tayi zaune Kmr yadda yake ,kallon da yake mata yasa qirjinta dokawa da sauri sauri saboda kallon ne mai tattare da tsana da gargadi ."a matuqar tsawace yace "uban wa yace ki shi go min daki ?kinga nayi kama da wanda zaki ta'ba? Ko jikina saanki ne ?yayi mata tmbyr ajere nan da nan yasa maryam ta gigice "tmbyarki naki "tayi shiru wallahi komai zaki min bazan ta'ba jin komai ba saboda bana kallonki amatsayin mace kmar yadda nasha fad’a miki idan kika sake gangancin kai hannunki jikina wallahi sai cakawa zuciyarki wuka .”kallonsa tayi da bayananen tsoro “wannan ya zama karo na qarshe da zaki shigo min daki domin har abada bazaki zamo abokiyar rayuwata ba jikina ma bazaki samu ba bare zuciyata fuskarsa babu annuri ya nuna mata kofar fita oya get out from this room kafin na miki mugun bugu cike da sanyi jiki ta rarumo hijab dinta ta soma qoqarin jirawa ajikinta sai dai ta kasa fita daga dakin tana tunanin me zata koma tacewa mami ganin taki fita ya sauko ya kamo hanuta bai tsaya wata wata ba ya soma janta ya bud'e kofar tare da hankadata waje da sauri ta tokare hannunta da bango batayi mamaki ba dan tasan zai iya aikata fiyye da haka ."




Makalewa tayi a bangon koridor hawaye masu dumi da ciwo suka zubo mata tasa bayan hannunta ta goge shi kuwa rufo kofarsa yayi ya murda key a galabaice ya fad'a bed dinsa ya runtse idanushi ya sake jan laulausar bargo ya lullube jikinsa maryam kuwa natsuwarta take qoqarin daidaitawa amman ta kasa dan hawayenta ya gagara tsayawa bata koma dakinta ba sai wajen karfe daya wanda a tunaninta zuwa wannna lokacin mami tayi bacci sannan ta nufi dakinta tana danne sheshekar kukanta Koda tashiga dakin mami na kwance , maryam ta haye saman gado ta kwanta lamo abayan mami tare da kamkame jikinta wani irin kewa da son mijinta ce ke damunta amman shi babu halittar daya tsana kamarta , kuka take son yi dan rage damuwarta amman bbu dama domin damuwarta zata iya haifawar da mami damuwa , a dalilinta mami zata iya muzgunawa yaya Adam , ita km abinda bazata so ba kenan, batason abinda zai sake hassalashi akanta
ta kai hannunta ta dafe daidai satin zuciyarta dake mata ciwo bayan Kmr minti goma mami ta tashi zaune ta dubeta tana mata kallon tsab batare da tayi magana ba sannna ta sauko ta shiga bayi ta dauro alwala ta fara gabatar da nafilflii .”




" juyi tayi tare da sake kamkame jikinta “yanzu ita yaya zatayi da rayuwarta ?”mayye zatayi ?”ga soyayyarsa ga tsananin sha,awarsa duk sun taru sun hade mata ,take zuciyarta ta bata amsa da kima kama kanki da rashin hakurinki dan muddin kikayi kuskure sake zuwa inda yake zai iya kasheki tunda har ya rantse “ya allah ka taimakeni kasa na samu ciki a karon mu na biyu dashi yanzu ta shiryawa kowani rigima zaiyi idan ciki ya bayyana ajikinta a boye take goge hawayen dake bin kuncinta ,har mami tagama tayi laziminta da sauran addu'o,inta
.bacci bai yi nasarar daukar maryam ba kuka take qasa qasa . Tana jin motsin mikewar mami ta shanye kukanta Tare da goge hawayen idanunta amman hakan bai hana mami gane wani abu ba ,daidai inda fuskarta take tazo ta zauna tare da kamo hannuta ,"me kike tunanin maryam ko kuma nace me ya dawo dake dakin nan har ya hanaki bacci ?




Kafin maryam tace wani abu mami ta km jiho mata wata tmbyr “sai ma naga kmr kuka kika yi ko?
Maryam ta Mike zaune suna fuskartan juna da mami ,yayinda hawayen dake makale a idanunta suka yi nasarar zubowa...."mayye km abin kuka tmbyrki kawai nayi fa? sai km ki kama min kuka.” wani abu adamcy yayi miki ?ahankali ta girgirwa mami kanta “ki fad’a min idan wani abu yayi miki da kyar maryam ta iya bude bakinta ..." ammi me yasa yaya Adam ya tsaneni haka ?kullum so nake naga na rayu dashi har qarshen rayuwa amman shi kullum burinsa ya ruguza rayuwar gidan aurenmu da ni kaina bansan yadda zanyi abubuwa su dawo min daidai tamkar kowasu maurata ".




“basan abinda na aikata masa ba da kullum yake son ganina cikin qaqa na kanyi .Ida abubuwa da yake min suka cigaba da faruwa bana tunanin zuciyar dake kirjina zata cigaba da bugawa , mami tambayar min shi laifin me nayi masa ?”wallahi ni ina qaunar zama dashi muddin raina .”mami ta rungumeta ajikinta tana mai tausaya mata "kukan ya isa haka babu abinda kika masa halinsa ne haka
halin bakar zuciya irin tasa yana damuna ni kaina na gaji da halinsa ,amman matsawar Ina raye ba zaki taba kasancewa cikin bakinciki ba , bugu da qari har yanzu kina da sauran damar rabuwa dashi dan bazan cigaba da baki hakuri ki cigaba da zama dashi ba dan duk wani abinda zaa masa anyi masa idan dai ba rayuwarmu yake nema ba .”






Mmn sudais


💗💗💗💗💗💗
MAR'ADAMS
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗




*AYSHA A BAGUDO*


WATTPAD @HAUESH
AREWABOOKS USERNAME
AYSHAABAGUDO
bismillahirrahmanirrahim


Wannan littafin na kudi ne mai bukatar karantashi byn na kammalashi zai biya 1000 ta wannan account number din 1438775094 Aishat abdullahi access idan an tura sai a turawa wannan 09136918331 alert domin tabbatar da an tura domin sauraron littafaina a tuntubi chaneel dina (Hausa bakwai ) a YouTube.




Page 19


Sosai mami ta dinga rarrashin maryam tana masu addua “allah ya daidaita tsakaninku ,Allah ya saka tausayinki acikin zuciyar adamcy ,allah ya kawo zaman lafiya a tsakaninku har qarshen rayuwarku “ahankali maryam Ke amsawa da “Ameen mami ,sai abu na gaba maryam na fahimci kina sakaci da addua ,Ina son kinsan wani abu ba’a nasara sai an rike Allah,idan ka rike Allah,Allah ta’ala zai taimakeka ki jajurce da adduoi maryam “ki rage wasu abubuwa ki maida lamarinki zuwa ga Allah maryam ta gyad’a mata kai alamun taji ,tana nan kwance ajikin mami har ta fara gyangyad’i alamun bacci .ahankali mami ta d’an buga bayanta tana cewa “maryam kwanta kiyi bacci da sannu allah zai kawo mana saukin wannan tashin hankali sannan ya kawo fahimtar juna a tsakaninki da mijinki .“maryam ta tashi daga jikin mami tana shafa idanunta sannan ta zame ta kwanta zuciyarta cike da soyayyar mijinta mami ta mike itama ta samu gurin nan kusa da maryam ta kwanta sai dai ita sam bacci yaki d’aukarta, kwakwaluwarta ne ya shiga cajin tunani
dan dole tasan abun yi tun kafin adamcy ya kashe maryam da bakincikinsa dan zuwa yanzu hakurinta ya fara qarewa akanshi .”






Juyi kawai mami take akan katifa kafin ahankali ta taashi ta sauko daga saman katifa ta tsaya gaban maryam tana kallon fuskarta bacci take, sai dai kana kallonta zaka san a matuqar wahale take baccin dan kana kallon yadda take sauke numfashi da ajiyar zuciya da karfi .”d’auke kwayar idanunta mami tayi ta fara zagaye d’akin kafin ta fara zance zuci ita kad’ai “dan dole zulai kiyi wani abu akan zaman ya’yanki “ to mai zanyi ?mai zanyi ? ta tambayi kanta har sau biyu tana cure hannuwanta waje d’aya “Kiyi qoqari adamcy ya kusanci maryam ko Allah zai basu rabo wata killa sanadiyyar hakan ya sauko ya sausauta mata ya rungume aurensu. “tabbas haka zakiyi zuciyarta ta bata wannan shawarar “to ta yaya zan masa magana ya fahimci abinda nake nufi ?”ta sake jefawa kwakwaluwarta tambaya shiru tayi yayinda ta koma ta kwanta akan katifa tana sauke numfashi tana mai sake had’e hannuwanta guri d’aya kafin ahankali ta soma sakin wani irin murmushi sakamakon abinda zuciyarta ta shirya mata wanda zai kawo mata saukin al’amuran ta, alokaci d’aya ta sauke wani naunayen ajiyar zuciya “dole dai kina bukatar shawarar shahida kafin ki aikata komai .”






Washegari da misalin karfe tara na safe maryam tana zaune akan kujerar sofa tana danna waya yayinda mami ke zaune akan salayya tana lazimi ATA ya shigo bakinsa d’auke da sallama sallamarsa kawai maryam ta amsa batare da ta kallesa ba ta cigaba da daddanna wayarta shima ko kallonta bai yi ba ya cigaba da tsayuwa mami ta d’an kallesa yana sanye da jallabiya yayi mata kyau sosai sai dai bata jin dadin ganin yadda ko yaushe fuskar nan tashi take a had’e’ ,sannan bata jin dadin ganin shi da maryam haka zaman su sam babu sha’awa kana ganin yanayinsu kasan gabad’aya zukatansu basa cikin walwala da jin dadi most especially adamcy wanda zaka fahimci baya son ko bisa kuskure ya kasance a duk inda maryam take .yayinda ita kuma tafi qaunar su kasance tare akoda yaushe ya rungumeta babu kyama ,mami na kallonsa ya juya cikin takun isa ya fita daga d’akin ganin tana lazimi ,bayansa mrym tabi da kallo har ya fice gabad’aya tasa hannu d’aya ta dafe goshinta tana jin wani tuttukin bakinciki tana jin zafi da ciwon abinda yake mata na kyarma da rashin son kallonta inda take ,amman ita ta rasa dalilin da yasa zuciyarta kullum take sake macewa akanshi ,a kullum zata d’aura kwayar idanunta akanshi to wallahi son shi da qaunarsa ne Ke sake huda zuciyarta da gangar jikinta” zata so ta mallakesa kamar yadda mahaifiyarta take buri amman hakan taki samuwa kullum babu abinda take hangowa attare dashi sai zallar qiyayyarta sam komai nata baya burgesa ita kuwa kwarjininsa kesa bata iya d’aukarwa kanta mataki ,bata iya tunkurarsa da komai tana matuqar jin tsoronsa aranta “da sanyi jiki mami ta qaraso inda take zaune ta kai hannunta ta dafata, ta d’ago tana duban mami da idanunta dake cike da ruwan hawaye mami tasa gefen hijab dinta ta goge mata hawayen da suka zubo mata batare da saninta ba wani wahallen ajiyar zuciya ta sauke tana kawar da fuskarta gefe“


“maryam !”


Mami ta kira sunanta ahankali maryam ta waigo inda mami take ta sake zuba mata idanunta tana kallonta fuskarta da tsananin damuwa ahankali ta sauke idanunta “ki daina damun kanki akan adamcy idan ba haka ba zaki rasa lafiyarki idan hakan kuma ta kasance babu ruwansa hasalima bazai ta’ba zama damuwarsa ba sai dai ta zama damuwarmu “kiyi hakuri ki dinga kawar da damuwar nan aranki sannan ki dinga kaiwa allah kukanki ,nasani maryam kina hakurin zama da adamcy ne saboda Kina matuqar ganin girmana da mutuntani da kuma qaunar da Kike masa nima kuma haka ne acikin zuciyata maryam ina qaunarki ina qaunar ku kasance a inuwa d’aya dashi .”numfashi ta sauke da karfi tana kallon mami “eh shine ma dalilin da yasa bakya son na rabaku maryam .




Maryam ta tsurawa mami idanunta “ko karya ne bakya sonsa ?zazzafan numfashi maryam ta sauke ta kasa cewa komai dan tasan gsky mami ta fad’a “kina dai danne sonshi ne saboda rashin qaunar da yake nuna miki amman ni naji ajikina kina qaunar adamcy ,maryam taji dadin yadda mami ta fahimci hakan sai dai kuma zuciyarta tayi rauni wasu sabbin hawaye suka zubo mata mami ta sake share mata “kuka bayayi miki kyau maryam hakan ya sake karya wa maryam gwaiwa ta fashe da wani kuka sosai .“wallahi mami ban san lokacin da son shi ya shigeni ba “nice silarsa maryam kuma nayi danasani had’aku aure ,mami ta fad’a da matsanancin tausayinta ,duk yadda mami take jin qaunar adamcy ji take tafita qaunarsa maryam ta tsananta kuka tana tuna tun lokacin data fara jin qaunar yaya Adam din acikin ranta rungumeta mami tayi tsam tana rarrashi alokacin wayar maryam ta soma ringing mami ta zare jikinta tana kallon maryam itama d’agowa tayi ta kalli mami sannan ta kalli screen din wayarta bata dauka ba ta cigaba da goge hawayenta yayinda kiran ya cigaba da shigowa still maryam bata d’aga ba .”




mami ta d’an yi gyaran murya “wake kiranki ne tun d’azu ?ummah ce !ta bata amsa atakaice idanunta na cigaba da zubar da hawaye “me yasa bazaki d’auka ba kika sani ko kiran mai mahimanci ne ?shiru maryam tayi ta kasa cewa komai dan tasan kiran me take mata, ita kuma ta gaji da abubuwan mahaifi yarta ,kullum abu d’aya kuma babu wani biyan buqata “ki d’auki kiranta kar rashin d’aukar kiran yasa hankalinta ya tashi tayi tunanin ko wani abu ne“.ahankali maryam ta gyad’a mata kai tana “cewa mami bari naje na dafa miki ruwan zafi “to shikenan maryam amman ki hada min da abinci “bamu da komai fa mami ,karki damu ki dafa min abinda kuke dashi . Mrym ta mike tsaye ta fito tana qoqarin d’aukar kiran mahaifiyarta daya sake shigowa ta sauko kunnenta manne da waya “umma dan allah ki daina kirana na tura miki sako mami tana gidan nan bana son taji komai “ amman me yasa zaki fad’i haka ummah?” kema Kinsan mami tana matuqar qaunata “a’a umma nifa gsky na gaji kawai abarshi na hakura bazan iya ba dan duk abinda zaa zuba cikin abinci bazai ci ba tunda baya cin girkina ,shiru maryam tayi tana jin yadda mahaifiyarta ta balbaleta da bala’i ta inda take shiga bata nan take fita ba.”




“kiyi hakuri ummah ba wai bana ganin qoqarinki bane saboda mami idan ta fahimci akwai abinda muke shiryawa d’anta zata ji babu dadi to shikenan gara ma wannan zamu iya sake gwadawa ko za’a samu ya kwanta akai ,to shikenan amman dan allah ummah karki kirani kiyi chart dina muyi komai ta chart ta qarasa mgnr tare da shiga kitchen ta soma qoqarin d’aurawa mami abinda zatayi breakfast dashi cikin kankani lokaci ta gama dafa ruwan zafi ta zuba cikin flaks sannan ta dafa shinkafa da miya ta fito tana qoqarin qarasawa dining mami ta sauko tana cewa “sannu da aiki maryam ?murmushi ta saki tana cewa “kai mami wani aiki kuma byn shinkafa da miya ce kawai na dafa miki. murmushi mami tayi tana cewa “kawo min nan diyata ta qarasa inda kujeru suke ta zauna maryam ta biyo bayanta ta ajiye kular abinci akan center table maryam tace “nasan idan kowa yaci abincina yace babu dadi mamina bazatace babu dadi ba ?”ina sam bazan fad’a haka ba zuba min na matsu banji dandanon abincin my daughter ba “abincin dai mami sai dai kiyi hakuri babu komai aciki ta qarasa mgnr muryata a sanyaye “karki damu maryam fara had’a min shayi cike da kulawa maryam take hidima da mami yayinda mami ke nuna mata farincikinki a zahiri amman a bad’ani bakinciki ne cunkushe acikin zuciyarta suna zaune ata ya fito yana taku a natse akan step sanye da kananan kaya jikinsa sai fitar da sihirtaccen kamshin turarensa yake ,ya qaraso parlour’n qasa hannuwansa duka zube cikin aljihun wondonsa tun daga nesa ya hango mami zaune tana breakfast da ruwan tea zalla babu wani abun hadi danginsu soyayyen Kwai da bread ko arish da sauransu abinda yasan ba d’abiarta bace, abun yayi matuqar bashi mamaki dan haka kai tsaye store ya shiga adaidai lokacin maryam ta mike ta nufi hanyar sama d’auko chazar wayarta .”






yana shiga dube dube ya fara bai ga komai ba ya fito ya shig kitchen duk sai daya duba cabinet din kitchen din nan ma bai ga wani abun kirki da zaa had’awa mutun breakfast mai kyau dashi ba dan haka jiki a

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login