Showing 123001 words to 126000 words out of 169868 words

Chapter 42 - MAR'ADAM'S BOOK 2 COMPLETE DOCUMENT by Aisha Bagudu .txt

06 Nov 2024

10886

damawa dashi, yayinda idan ka kalleshi zaka d'auka d'an shekara talatin da biyar ne amma gaskiyar lamari shekararsa arba'in da wani abu yake, da sauri aka bude masa gidan baya ya shiga ya kame yana shan kamshi daya daga cikin wayoyin ne ta soma ringin ya dauka ya soma magana a natse yana ciccin magani har suka qaraso unguwarsu waya yake bai ji komai ajikinsa ba sai da suka shiga cikin haraban estate dinsu yaji gabanshi ya fad'i sakamakon bai san abinda zai tarar ba amman a kudurtawa ransa komai zai faru sai dai ya faru amman har abada bazai qara zama da mrym ba".






ahankali ya fito daga cikin motar ya nufi babban falon cikin isa da iza ga kamshin daddan turarensa Reed na tashi ,yasa hannu ya tura kofar glass din parlour’n ya shiga ya iske mami zaune kamar koda yaushe yayi sallama aciki fuskarsa a had’e tamkar zaki , itama aciki ta amsa masa ya ta’be baki yadda ta amsa masa yaso ya bashi dry amman sai ya maze ya d’age girarsa duka tare da dakewa ya gaisheta “sweetheart barka da rana “wannan karon kam shiru tayi bata masa ba bai qara cewa komai ba kai tsaye samansa ya nufa mami ta karkace tabi bayansa da kallo yana taku d’ay d’ay batare da wata damuwa ko tashin hankali ba sai ma wani kyau da kwanciyar hankali daya samu matsuguni ajikinsa su kuma ya bar zuciyarsu da tashin hankali.duk wani tarba da rawar jiki da mami take akanshi idan ta gansa yau kam babu dan kana kallon fuskarta zaka fahimci akwai damuwa .”yadda mami bata masa maganar wata maryam ba shima bai yi mata maganar ba abun ma yayi masa dadi ya cigaba da tsabgogin gabansa da mulkinsa daya saba dan babu abinda ya canja har kawo yanzu dan ji yayi kamar an raba zuciyarsa da matsala ne dan da kullum zuciyarsa cikin tuttukin bakinciki da kunci take idan ya tuna zai koma gida ya ga fuskarta kuma amatsayin matarsa .”






mami dai bata gaji ba ta sake tara ya’yanta “har yanzu shiru adamcy bai ce min komai ba ga mrym da ciki har wata uku akace dame zataji saboda Allah ga ciki ga kuma gurb'ata mata raywua da yayi, gashi ya dawo yayi wa mutane shiru kamar bashi yayi sakin ba , ni na gaji wallahi nayi waya daita mrym din ta fad’a min abinda ya faru akayi sakin taki sai kuka take min ,shi kuma ya dawo ya min dif wallahi na kasa komai gashi bana son lokaci ya tafi batare data koma dakinta ba dan da zarar mrym ta haihu a gidansu shikenan abu ya sake dawowa baya bazai ta’ba maidaita ba mami ta fad'a tana kallon ya’yanta d’aya byn d’aya da suke zaune.aunty khadija tace "kwantar da hankalin ki mami zamu san abun yi bubuwa daya ne kawai ya tabbata a aurensu samun cikin mrym in sha allahu sauran ma zasu tabbata ne"Yaushe? Kusan shekaru ana abu d'aya ace har yanzu an kasa cimma komai babu wanda adam yake shaka daga mami har mu na gaba dashi kowa shakkarsa yake gsky zuwa yanzu dai ya kamata mu tashi tsaye .”inji cewar aunty shahida .”




kallonsu kawai mami take zuciyar na karye wa “zaku cimma daman amman dole sai kunyi hak'uri sannan ku bisa ahankali dan karku dinga mgn kuna manta waye shi b'angaren zafin kai da zuciya dole sai kun sha wahala kafin ku samu ku ya sauko ya saurareku ni wallahi dan tani da an bar kome nan kowa ya huta “wai meye haka zabiba?” sai ki dimga magana kina cire kanki acikinmu idan Kinsan bazaki goya wa mami baya ba me yasa kika zo ?Inji cewar aunty Khadijat “to yanzu me nayi kuma ?ai bazan ki zuwan kiran mahaifiyata ba haka zalika bazan goyi da bayan a sake tursasa wa yaya ba “haba Auty zabiba ya kike magana kamar babu tausayi a zuciyarki ?karki manta kema fa mace ce inji cewar nana hauwa’u “hk ne nima mace ce amman da zaku fahimceni ma gata nayi mata dan banga amfani aure da wulakanci ba shi yace bayayi ita tace tana yi ita Ke aure ko shi ?“dan allah yasa isa karki sake saka baki tashi ma ki wuce an sallameki nan da nan parlour’n ya hargitse sai da mami ta tsawatar masu sannan sukai shiru suna cika suna batsewa “wannan wani iri bala’i ne adamcy duk ya dagula min lissafi ya hadani da dan’uwana yanzu kuma zai raba min kan ya’ya .” a zuciyar zabiba tace “babu ruwan yaya duk kece kika dagula lissafin komai .”




Bayan kwana biyu wanda ya kasance weekend tun karfe tara suka hallara da niyyar ayita ta qare ahankali yake saukowa daga saman mattakala jikinsa sanye da farin yadi inda kafafunsa ke sanye da farin silifas , agogon rolex ke daure da tsintsiyar hannunsa ,idanunshi na manne da wani hadadden farin glass ,a hankali ya cigaba da takowa cikin isa da izza shi din wani ne a fadin nigeria ,yana saukowa sanyayen kamshin turarensa REED ya soma tashi kamshin turarensa ne ya kaiwa hancinsu sakon fitowarsa . gabad’ayasu suka dago idanuwansu a natse suka tsura masa suna kallonsa tamkar ranar suka soma ganinsa shi kuwa ko kallo su bai yi ba hasalima yi yayi kamar bai ga wasu halitta a wajen ba .kai tsaye dinning área ya nufa yana shan kamshi , har ya samu guri ya tsaya tare da soke hannunsa daya cikin aljihun wondonsa ,basu dauke kwayar idanunsu akanshi ba ,gabdayansu an rasa wanda zai fara masa magana shi ya kamata yayi gaisuwa amman yaki “aunty khadija ta zunguri aunty shahida ta kalleta “gashi ya fito ya kenan ?






“Da alamun abinci zai ci bari ya gama ya samu waje ya zauna ya had’a coffee ya fara sha yana lumshe idanu su kuwa sai faman satar kallonsa suke ba qaramin kyau yayi musu ba cikin shigar da yayi ko dan bai fiyye saka kayan hausa bane yasa yayi masa kyau haka yunwa yake ji sosai amman ya kasa zuba ma kanshi abinci dan haka ya ja dogon tsaki mami ta fito sanye da doguwar rigar atamfa itama tayi kyau sosai ga tsufa ga tarin damuwa amman dake jikinta mai kyau ne wallahi bazakace tana da diya mai shekara 49 a duniya ba dauke kallonsa tayi ta girgiza kai kawai sannan ta zauna acikin ya’yanta .
zabiba ce ta fahimci abinda yake buqata dan haka ta mike a natse ta qarasa inda yake “ina kwana yaya ?lafiya !ya fad’a aciki batare da bata lokaci ba tayi serving dinsa ta ajiye masa plet din abinci gabansa. a hankali ya dauki cup ya kai bakinsa ya kurbi tea yana lumshe sexy eyes dinsa yana sosa keyarsa .”






Ahankali aunty shahida da aunty khadija suka mike suka nufi inda yake hajiya zualai tabi su da kallo gabanta na wani irin faduwa nana hauwa’u ta riko tafin hannunta “mami ki kwantar da hankalinki kiyi addua cike da sanyin jiki take duban kyakkya wan fuskarsa ya hade fuskarsa sosai ta yadda idan ba jarumta kayi ba bazaka iya fuskantar sa ba “karki damu mami everything will be fine “Allah yasa auta allah ya sanyaya zuciyarsa dan mrym na bani tausayi ina jin duk nice silar shigarta cikin damuwar nan nana hauwa’u ta damke hanunta sosai cikin nata tana danne kukanta dan itama mrym na bata tausayi tun shekaranjiya da sukai waya bata qara daukar wayarta ba saboda qara mata damuwa take .”a tare suka zauna suna fuskantar shi tun daya gansu ya fahimci abinda Ke tafe dasu kusan minti shabiyar suna zaune yaki daina cin abinci yasa ahankali aunty shahida ta soma magana “adamcy me yasa ka saki maryam ?”laifin me tayi maka ka saketa alhalin ga mami a raye baka sanar daita ba ka yanke hukunci kai tsaye ?”.






“bani ya kamata ki tmya ba ita da tace an saketa me tayi ?kuje ku tmbyeta abinda tayi aka saketa “nan da nan ran aunty khadija ya baci “wannan wace irin maganar banza ce ?”ta fad’a a fusace “ai mun san daita muka zo tmbyrka mara mutunci kawai so kake ka kashe mana uwa ka barmu da asara dan tuni mun kula baka da buri sai na ganin kasa mahaifiyar mu cikin bakinciki,to wallahi kasani zamanka da marym dole ne dan shi kadai zai sanyaya ran kowa acikin gidannan ,wallahi sam baka ma mami adalci ba kai kadai gareta amman kullum cikin sakata hawaye kake, kamata yayi ka dinga share mata hawaye amman tun baka kai haka ba kake sakata cikin damuwa.jin haka yasa mami ta share hawayenta . ta inda take shiga bata nan take fita ba sai zazzaga masa ruwan bala’i take shi kansa yayi mamaki maganganunta amman yayi shiru yana sauroronta yana tsakurar abincin gabansa batare da ya furta komai ba “.






“To kasani idan ka saki maryam dan ka yar da kwallon mangaro ka huta da kuda kasani kayi aikin banza dan ciki ne daita na wata uku kaga kayi aikin banza duk kinka daita kun zama abu daya “What ?” ya furta da mugun karfi yana sakin spoon din hannunsa “eh !yanzu haka jininka na can a jininta yana yawo idanunshi ya tsura mata yana nazari kafin ahankali ya mike tsaye yana girgiza mata kai
dukkansu kallonsa sukeyi yadda jikinsa ke rawa kamar anjona masa shocking , nan da nan idansa yayi wani irin canzawa " impossible! waitt,hw can dis even b possible ?tana dauke da cikina na wata uku alhalin ni duka wata guda kenan da sati biyu dana kusanceta”to kaga dole dai cikin dake jikinta naka ne, a ina aka tabayin haka? ya fad’a a fusace taya za'ayi cikin jikinta ya zama nawa “?gbdy hankalinsu ya tashi har mami wacce batasan sanda ta qaraso inda suke ba tana dubansa “bamu gane nufinka ba ?ko dai ka sha wani abu ne ?babu abinda na sha garas nike amman wallahi cikin jikinta ba nawa bane cikin wani kato ne a jikinta kuje ku tambayeta uban da yayi mata ciki wata uku .”






da wani uban murya mami tace" kalleni adamcy ka san da wacce kake magana ka kuma dinga tauna min mgn kafinka sakosu, niba tsohohuwar banza bace, kai har ka isa kace cikin wani kato ne a jikin maryam dan ubanka ai kaine katon kenan tunda kai kamata cikin dan iska yaron kawai “.mami ta fad’a tana hawaye domin karo na farko kenan da ta furta masa wannan kalmar garesa. hakan yasa ta fashe da wani sabon kuka jin kalamn da ida wani ne ya jifesa dashi Allah kawai zai rabata dashi amman gashi itace da kanta ta furta masa haka gbdyn suka rikice sai suka dawo bawa mami hakuri ,ya isa haka mami don Allah karki sake zaginsa suka fada suna wani irin kuka mai tsuma rai “ku daina bani hakuri shi zaku bawa hakuri abinda mami take fad’a kenan "yanzu bayan ya sake nayi shiru yanzu har da cikin jikinta zai yi rejecting yanzu adamcy ka kyautawa
danka ?d’a daya tak tilo, daza fara samu a duniya zakayi wa haka .da wanne mrym zata ji da sakin daka mata ga sharri”. sweetheart trust ur son wIhh wannan cikin ba nawa bane ni ban mata ciki ba, nana hauwa’u ta goge hawayenta “Kace bakai kayi mata ciki ba “? Ki lissafa sweetheart ranar da kika bani umarni zuwa wajenta yau kwanaki nawa ne ?mami tayi shiru tana lissafi byn Kmr second biyu ta d’ago tana dubansa tabbas baayi wata uku ba to meke faruwa ?”




“Sweetheart idan kin gama lissafi ku san yadda zakuyi daita domin mazinaciya kika aura min baki sani ba yana gama fad’ar haka ya juya da nufin fita daga parlour’n da sauri nana hauwa’u ta tareshi tana kallonsa fuskarta da tsananin damuwa karara ya dago yana kallon idanunta itama shi take kallo eyes to eyes muryarta cike da kuka tace “wallahi yaya mrym ba mazinaciya bace cikin jikinta naka ne jininka ne acikinta “ni babu wani jinina dake yawo ajikinta dan ban mata ciki ba and wIh wlh idan kuna yi dan na maidaita ne bazan maida auren nan ba na gama zama daita kenan “naji yaya amman ka yarda ni cikinka ne hannunsa ya d’aga zai sauke mata mari yaji an rike hannunsa ta baya .”






Mmn sudais


💗💗💗💗💗💗
MAR'ADAMS
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗




*AYSHA A BAGUDO*


WATTPAD @HAUESH
AREWABOOKS USERNAME
AYSHAABAGUDO
bismillahirrahmanirrahim


Wannan littafin na kudi ne mai bukatar karantashi byn na kammalashi zai biya 1000 ta wannan account number din 1438775094 Aishat abdullahi access idan an tura sai a turawa wannan 09136918331 alert domin tabbatar da an tura domin sauraron littafaina a tuntubi chaneel dina (Hausa bakwai ) a YouTube.




Page 23






A matuqar fusace ya juya bayansa yaya hisham ya gani tsaye cikin kananan kaya fuskarsa dauke da murmushi ,a natse ya sakar masa hannu yana cewa "ranka shi dade babban yaya laifin me auta tayi haka ?" maganarsa cikin sanyi rai yayi wanda yasa nana hauwa'u ta fashe da wani rikitaccen kuka, ina ma yayanta zai kasance kamar mijinta mai sanyi hali da tausayi tare da shagwaba mace da kyautata wa ?bata san tayi sa'ar samun miji ba sai da komai ya daidaita a tsakninsu tasan wa take aure ,kuka take sosai tana kiran "wallahi yaya cikin jikin maryam naka ne, ni sheida ce tana gama fad'ar
haka durkushe a gabansa tana zayyane masa komai daya faru tun daga farko. a matuqar tsorace yake kallonta "take kwakwaluwarsa ta shiga caji na tunani babu abinda yazo zuciyarsa sai maganar doctor nasir akan ciwon kan da yake fama dashi wanda yayi tunanin duniya ya rasa a inda ya sha maganin da yayi masa illa "shi kam wasu irin yan'uwa allah ya bashi masu son kansu dayawa ?"laifin me yayi masu ?duk wani bala'i da yan' uwana ake had'a baki."yadda taga yanayinsa ya canza har tana iya hango yadda jijiyon kanshi sukai rud'u rud'u yasa ta zabura ta mike tsaye gabanta na wani irin fad'u wa da matsanancin karfin gaske ."




ya tsura mata ido ya balain canza mata daga yanayin farko ganin ya fara taku zuwa inda take ta fara yin baya yana biyota kafin ya qarasa inda take yaya hisham ya shiga tsakaninsu yasa hannuwansa duka ya qare matarsa yana bashi hakuri ,yaya hisham bai san ya'akyi ba sai gani yayi ATA ya fixgota da karfi zai buga bayanta da bango a matuqar agigice ya rungume matarsa yana cewa "kayi hakuri tayi laifi amman dan girman allah ka yafe mata ,idan ba cikin jikinta ba wallahi zan barka ka yi mata duk irin hukuncin da kake so amamn kayi hakuri ciki ne ajikinta ."sai lokacin idanunshi ya kai ga cikin jikinta wanda har ya fara nuna alama ,saurin sakar mata hannu yayi yana dungule hannunsa yannayin bugun zuciyarsa bai saisaita ba, yannayin tsoratarsa kuwa sai ya baka mamaki gabad'aya tsigar jikinsa suka mike "ciki hisham yayi mata ?ya tamabyi kansa yana mai furzar da iska mai zafi jiki a sanyaye ya yake dubanta cike da tsananin fushi yana sauke numfashi da karfi dan bancin zuwan hisham wallahi da wata killa ba wannna zance ake yi ba."






ahankali take cigaba da rera kuka Kiyi shirunki baby yayanmu zai miki afuwa ."cikin kaukausar murya ATA ya soma tashi acikin parlour'n "ba ciki ba idan duniyar nan gbdy zata haifa min ku saka aranku ni adam tariq abdullah bana só ba kuma na bukata gabadayansu suka kallesa cikin tsananin tashin hankali aunty shahida zatai magana ya d'aga mata hannu "wlhh yadda bana só auren nan ba zai yiwu na karbi komai daga gareta ba, sai abu na gaba kafin na saketa nayi tunanin qarasa rayuqata daita amman na kamata da abu mafi muni wanda nasan bazata ta'ba sheida maku laifin da tayi ba abinda yasa na saketa kamata nayi dumu dumu da tukunyar tsafi zata saka min akarkashin gadona "hakika Mahaifiyata bata cutar dani ba kamar yadda auta ta cutar dani domin cikin nan an samesa kafin umarnin mami if not haka zamu rabu daita zero amman koma menene ni dai banaso sai dai idan ku ku zama ubansa amamn bani ba idan kuma akace zaa tursasa ni na rantse da girman Allah ran kowa zai yi mummunar baci yadda mami ke kallonsa a tsorace haka sauran yan'uwansa ke binsa da kallo zukatansu na rawa dan bakinsu ya mutu da girman laifin mrym yana gama fada ya haye sama ya barsu cikin jimami da tashin hankali ."




Wani irin naunayen ajiyar zuciya suka sauke kafin ahankali yaya hisham ya zaunar da nana hauwa'u akan kujera ya zauna kusa daita yana rarrashinta d'aya bayan d'aya suka samu waje suka zauna duk jikinsu a sanyaye yayinda zuciayarsu ke cike da mamaki mami kam kasa cewa komai tayi domin daman ita ta d'an yi zargin wani abu akan haka sai dai taki yarda zuciyarta ta amince da hakan "mai yasa marym ?"me yasa zaki

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login