Showing 129001 words to 132000 words out of 169868 words

Chapter 44 - MAR'ADAM'S BOOK 2 COMPLETE DOCUMENT by Aisha Bagudu .txt

06 Nov 2024

10863

tana ganinsa ta mike da sauri cike da girmamawa ta biyosa office dinsa har sai data ga ya samu wuri ya zauna "good morning sir cewar sectary ya gyada mata kai ta wuce domin komawa bakin aikinta , a can waje kuwa tabe baki ma'aikatan sukai sannan suka koma office bakin aikinsu ."wanda yake rike da katon zanen adam Ya nufi inda aka ajiye sauran zanen da mutane suke kawo ."




, ATA ya zauan tare da kunna system dinsa sai dai zuciyarsa ta kasa samun kwanciyar hankali amman haka ya cigaba da aikinsa amman ya kasa samun natsuwar yin aiki ji yayi duk wani kuzari nasa yayi kasa wata irin soyayya princess dinsa ce ta dinga taso masa daga zuciya yana jin kansa muddin babu ita arayuwarsa tabbas nashi rayuwar bashi da wani amfani ya furzar da iska mai zafi yana ture system zuwa gefe ya dauki waya ya kira number sectary dinsa mgnr daya yayi ya katse ya sake janyo system gabansa ,byn kamar second uku ta bayyana a gabansa rike da wani file cike da girmamawa tace "sir !"yaake ciki game da masu zanen danace?sir ai kwararrun masu zane sun kawo irin zanensu "me yasa baki fad'a min ba ?sir ganin baka da time shiyasa ban maka magana ba "ni nace miki bani da time ?yayi mata tambayar a tsawace nan take jikinta ya kama rawa ta sake kankame file din hannunta "kayi hakuri sir nayi kuskure numfashi ya sauke yana cewa "get out ."




Ta rusuna masa sannan ta juya byn Kmr mintuna talatin ya fito yayi hanyar waje yana kiranta ta biyosa da sauri bai tsaya akoina ba sai bakin koridoor ya tsaya yana bata umarni " call ja....kafin ma ya qarasa ta nufi office dinsa ,basu wani jima ba suka dawo tare dashi "good morning sir “amm james muje naga creations din da'akawo "okay sir !
Da sauri yayi gaba ATA na biye dashi wanda da kyar yake iya daga kafafunsa yayinda sectary dinsa ke biye dashi har zuwa babban dakin daaka tanada domin ajiye duk wani creations din da'aka kawo yana gama shiga dakin ya já Ya tsaya batare daya basu umarni ba suka shiga bude masa duk wani creation da'aka kawo yayi shiru yana kallon creation daya bayan daya wasu zanen kaya sukai doguwar , wasu suit da riga wasu kuma zanen mutane haka yayita kallo duk babu wanda ya dauki hankalinsa dan haka yayita jan tsaki yana qarawa har ma ya soma gajiya da kallon creations din har ya juya James yace "sir kalli wannan ka gani juyowa yayi sosai yana kallon zanen da shine aka zana sak




Mmn sudais


💗💗💗💗💗💗
MAR'ADAMS
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗




*AYSHA A BAGUDO*


WATTPAD @HAUESH
AREWABOOKS USERNAME
AYSHAABAGUDO
bismillahirrahmanirrahim


Wannan littafin na kudi ne mai bukatar karantashi byn na kammalashi zai biya 1000 ta wannan account number din 1438775094 Aishat abdullahi access idan an tura sai a turawa wannan 09136918331 alert domin tabbatar da an tura domin sauraron littafaina a tuntubi chaneel dina (Hausa bakwai ) a YouTube.




Page 24




yadda yake fari tas tmkr balarabe da yadda idanusa suke da d'an girma da dogon hancisa yanayin tsayinsa fuskarsa sai gashin bakinshi dake zagaye da gemunshi komai shine hatta yanayin fuskarsa da take a d'aure ba'a bari ba."muryarsa a kasalance "very nice !ya fad'a yana sauke numfashi had'e da gyara tsayuwarsa yana kallon zanen kansa ."cike da tsinkewar zuciya yace "a kira number wayar wanda yayi zanen nan kasancewar yaga kowani creations dake ajiye ajikinsa akwai farar takarda makale mai dauke da number waya da address sai dai ita maryama iya number wayarta kawai tasa "okay sir cewar James cikin abinda bai wuce one second ba ya juya har ya kai bakin kofa ya tsaya batare daya juyo ba "ka biyoni da creations din "James ya sake cewa "okay sir!"Cikin abun da bai wuce minti goma ba James ya shiga neman layin maryama da number compaing dinsu amman number a kashe ya jaraba kiran yafi sau goma still dai swcth off ake maimaita masa dan haka ya shiga office din ATA cike da girmamawa ya rusuna yana cewa "sir nayita qoqarin neman layin amman swcth off ake cewa "okay keep trying !ya fad'a yana cigaba da operating system." wuni ranar James duk akan kiran layin maryama ya qare amman still the same thing ake fad'a masa ."






Washegari ATA na zaune akan kujera yana kallon screen din system dinsa gefe guda kuma yana jin bayanin James bai ce uhm ba bare uhm umm har sanda ya dasa aya inda a karshen maganarsa ya dan nemi ya rikitashi a natse ya ture system din gabansa ya mike tsaye ya zagayo ya zauna akan table yana dubansa "okay itace girl din jiya kenan ?cike da tashin hankali yayi shiru ya kasa bashi amsa "da kai nake magana fa cike da matsanancin tsoro yace"Yes sir itace !shiru yayi yana sake jin bugun zuciyarsa na qaruwa akan na jiya ya kai idanunshi kan tangamemen zanen dake ajiye a office dinsa yana kallo yana jin wani irin sanyi ajikinsa tunda yake bai ta'ba jin abinda ya tsaya masa arai ba Kmr princess dinsa sai yarinyar jiya da kuma wannan zanen "wanna duk kuskuren ku ne mutun yazo da irin abu haka mai matukar mahimanci ai ko dan darajan kokarin da mai shi yayi wurin zanani ya kamata ku bashi kulawa ta musaman sannan kafin ku aiwatar da komai ku nemeni but wannan laifi stupid sectary ce bani da time dinta yanzu zanji daita later gabdaya zanenta yafi na kowa kyau ina son ganinta eyes to eyes ina son nasan yadda akayi ta zanani haka
bansan me yasa kuke wa masu zuwa ma'aikatan da wata bukata haka ba ?yayi maganar a matuqar fusace “we are sorry sir “ shiru ATA yayi yana ciza lip’s dinsa da karfi ."






Maryama suna zaune a parlour’nsu tare da yaya sadam suna hira kira ya shigo wayarsa kamar koda yaushe shiru yayi gabansa na faduwa ya rasa dalili yasa bata kiransa sai lokacin da yake tare da maryama daga maryama har yaya sadam shiru sukai suna kallon juna muryarta a matukar sanyaye tace “yaya sadam ko akwai damuwa ne ? ya girgiza mata kai alamun babu komai “no yaya sadam karka boye min idan akwai damuwa ka fad'a min zan fahimceka “nace babu wata damuwa still kira ne ya sake shigowa wannan shine karo na biyar ana kiranka baka dauka kuma kace babu komai kuma duk sanda zamu kasance tare zayita kiranka bazaka d’auka ba amman shikenan tunda ni ban kai matsayin da zaka sharing problem’s dinka dani ba gara kawai a fasa auren nan dan ina ganin Kmr akwai damuwar da kake boyewa “ta fad'a tana mikewa tsaye zata shiga da sauri ya rike hannuta yana cewa " haba sauraniyata Kiyi hakuri babu wani damuwa kema kinsan idan akwai zan fada miki idan kika fasa auren nan ai sai dai kisan yadda zakiyi dani da ummah nah dan mutuwa zamuyi ya qarasa mgnr a marairaice.”




murmushi tayi wanda ya bayyana wushiyarta sama da kasa sannan ta koma ta zauna tana cewa “haba yaya sadam wasa nake maka amman bani wayar naga su wa ke kiranka haka “ ta kai hannunta zata d’auki wayar ya dauke wayar da sauri yana cewa “no no!!” oh am sorry shikenan kayi hakuri na shiga rayuwarka ,no karki damu kace kana sona yanzu ?
”sosai kuwa dan zan iya rasa raina idan kika barni amman me yasa baka son fad'a min damuwarka matsalarka sannan ni ina son ka dinga tmbyta wasu abubuwa da suka shafi rayuwata sirrikana me nayi da sauransu "yanzu duk abinda nake miki bakya gani ? Ta gyada masa kai alamun a’a “zan fashe miki da kuka fa maryama yana rufe bakinsa kira ya sake shigowa wannan karon yace “ excuse me tare da mikewa tsaye “ am very sorry yaya sadam saboda ni ka kasa daukar kiran daake maka ,babu komai kaje daga waje ka amsa kiran ya gyad’a mata kai ya fito waje yana amsa kiran muryarsa can qasa qasa.”




Mikewa tayi cike da sanyin jiki ta fito haraban gidan tana tafiya a hankali tana tunanin yanayin yaya sadam wayarta ce ta dauki qara ta duba taga number compaing din da taje neman aiki ne suka mata wulakanci "taja dogon tsaki ta katse kiran wani kiran ya shigo still tayi discounting kira na uku ya sake shigowa " ta sake jan tsaki "ina ganin sai na kashe wayata gabad’aya zasu daina kirana ta kashe wayar tana cewa “marasa mutunci bayan kun gama wulakantani sannan ku dawo kuna kirana kiran me kuke min? .dan girman Allah nadia ki daina damun kanki da yawon kuka ,nima ina sonki amman maganar da nake miki yanzu aurena ma ya kusa ana daf da daura min aure da yaruwata , ki manta dani kawai komai ya rigada yazo karshe a tsakaninmu Allah ya baki wanda ya fini , look nadiya dan allah karki sake kirana ..” yana juyowa yaga maryama tsaye a bayansa “kai dawa kuke waya har kake cewa karta kara kiranka aurenka ya kusa ?”shiru yayi ya rasa amsar da zai bata dan haka ta juya zata bar masa wurin ya riko tsintsiyar hannunta "please maryama! ta juyo tare da tsura masa narkakkun idanunta wad’an da ‘bacin rai ya qara narkar dasu “ka tsaya kana kallona tambaya ce mai sauki nayi maka.”




“ shikenan wata yarinya ce dake sona tare mukai karatu daita amman na rigada na fad'a mata bazai yuwu muyi aure daita ba dan na kusa aure nan bada jima ba ,amman gbdy ta kasa fahimtata numfashi ta sauke tare da cewa “ maza Kenan " allah ki yarda dani Kiyi hakuri idan kinji babu dadi aranki yaya sadam mai yasa zaka wani damu kanka haka ai babu komai? “ tayi shiru tare da kamo lip’s dinta tana jin zafi a zuciyarta , yanzu taji da kunnenta yana furta mata yana sonta amman kuma wai ita Ke sonshi tô su maza zuciya nawa garesu ?”numfashi ta sauke tace “amman duk lokacin da zamu kasance tare tana kiranka amman idan na tmbyarka sai ka boye min why yaya sadam alhalin zuciyarka na sonta ?” shiru yayi ya kasa furta komai yana kallonta gabad’aya yanayinta ya canza har kwayar idanunta ? ni kinji na fad’a miki ina sonta ?da mamaki take kallonsa lallai halin maza sai su idan suna da mata biyu soyayyarsu biyu ce fa byn ta gama kallonsa tace “yaya sadam ban san me yasa ba zuciyata ta kasa yarda da baka son yarinyar nan domin gbdy yanayinka ya nuna akwai soyayyarta mai karfi a zuciyarka ,do you know something yaya sadam ?cigaba da kallonta yayi ya kasa cewa komai “idan kasan tsakani da Allah kana sonta ka aureta dan ni bana son boye boye arayuwata komai nafi son gsky da gsky amman kai gbdy baka son mu gina soyayyar mu akan hakan“.




“no karki yi wannan tunani “ ni dai idan kasan zuciyarka ta rabu gida biyu dan allah ka hakura dani ka tsaida zuciyarka wuri daya” tana gama mgnr ta zare hannuwanta zata juya ya riko tsintsiyar hannunta bata juyo ba ya zagayo ya tsaya gabanta yana kallonta tare da kamo d’ayan hannunta ya kai bakinsa yayi kissing sannan ya cigaba da mgn “ina sonta amman nafi sonki maryama akanta ki yarda dani tunda har zan iya hakura daita na aureki ya kamata ki gane sonki yafi nata ,amman wannan ba adalci bane yaya sadam ya kake son tayi da sonka ?ka kuwa san yadda mace take ji acikin zuciyarta idan an kayi breaking heart dinta ?kasan halin damuwar da take ciki a yanzu ?ya zanyi maryam kafin na shigo da maganarta ummah ta zarta da hukunci akaina kin fi kowa sanin komai ya kamata ki fahimceni ki min adalci . magana ta gskiya ni yanzu Ke nake so shiyasa nake bata hakuri ,kiyi hakuri karki yi fushi dashi ahankali ya dinga kwantar mata da hankali . hankalin maryama ya kwanta “kin hakura ? na hakura tana gama fad’ar haka ta zare hannuwanta cikin nashi shige part dinsu shiru yayi kafin a hankali ya juya ya bar wajen ."


***


ATA na zaune a office haka nan zuciyarsa ta kasa samun natsuwa James ya shigo hannusa rike da cup din coffee ,sir ga coffee ATA ya karba ya curbi kadan ya ajiye "dan allah sir ko zan iya cewa wani abu yace “uhm !”me yasa ka damu kanka sosai dan an kira yarinyar nan taki dauka ? sai akayi ya kenan ? ya fad'a yana d’ago kansa” wannan shine abinda ya shigo da kai ?”no sir kawai dai bana son ganinka cikin damuwa ne ya numfasa kana ya cigaba da motsa lip’s finds “ni ba damuwa nayi daita ba yadda aka wulakantata ne ya dameni ,amman sir babu abinda aka mata na wulakanci kawai bayani aka mata akan lokacin da zata samu amsarmu, ni ina ganin damar kamar ranta a bace yake. “enough James ka dameni zaka iya fita please “james ya daga kafafunsa ya bar office din bayan kamar minti goma ya sake neman izinin shigowa cike da girmamawa ya tsaya gabansa “sir akwai wani dayazo yana son ganinka "babu wanda zan gani yanzu sai dai gobe ya fad’a tsawace .”




James ya juya da sauri zai bar office din yajiyo sautin muryarsa cikin fushi idan ka fita kace wa umar da sauransu suzo ina son ganinsu a conference room “okay sir ya qarasa fita da sauri "ATA ya mike yana zariya a office can kuma ya tsaya cak gaban zanensa yana kallo ya kai hannu yana shafa fuskarsa dake cikin zanen”hakika zuciyata na matuqar qaunar son ganin yarinyar nan zan so ta zana min zanen princess dina a qarshe na ajiyeta a qarqashin ikon AGC domin zatayi mata amfani .ya kai hannunsa ya shafa sumar kanshi yana furzar da iska mai zafi sannan ya d’auki zanen ya nufi wani d’aki dake cikin office dinsa “ kafin kace me manyan ma’aikatansa sun hadu conference hall a natse ya soma magan fuskarsa a hade “abinda zan fad'a maku shine ina bukatar ganin yarinyar data zana zanena acikin kwanaki biyu kacal a nemota a duk inda take acikin garin nan idan ba haka duk zaku rasa aikinku . a lokacin da yakewa maaikatansa magana system ne a hannunsa yana operating yana masu bayani “fatan kun fahimceni .”




“yes sir ."! suka furta gabadayansu ya juya a natse
ya koma office dinsa "ya zamuyi kenan ?suka furta atare cikin tsananin tashin hankali “ya kuwa zamuyi kawai mu dudduba muce masa bamu ganta ba ko kuma mu zakalu d’aya daga cikin wadan da suka kawo nasu muce itace .falalu ya kallesu gbdy yace” wai me yarinyar zata masa ?wata yarinyar mafarkinsa yake nema, ya zanata da kansa yau tsawon shekaru sama da goma sha kenan yana nemanta shine yayi tunanin may be bai zanata yadda ya ka mata bane yasa bai ganta a duniyasa ba shine fa yace a nemo masa kwararrun masu zane zai fad'a masu yadda take su zana masa ya gani tô cikin wad’an da suka kawo gwajin su aka samu mutun d’aya wacce ta zana shi kuma itace zanenta yafi d’aukar hankalisa “falalu yayi masu bayani atakaice “gbdy suka sauke ajiyar zuciya suna jinjina girman lamarin mai gidansu sun dade suna tautaunawa akan yadda zasu bullowa lamarin kafin daga baya duk suka watse ."




Tsaye James yake a gaban ATA a office dinsa cike da girmamawa yana masa bayani “sir yarinyar nan dana baka labari kwanakin baya akan tana da kwarewa sosai akan ilimin lissafi duk wani calculations na Z&A itace take yi wanda yasa ta samu gurbi aiki a karkashin Z&A amman taki, itace the same yarinyar da tayi zanenka ,kaf a garin nan itace ta iya zane mai matuqar daukar hankali ,intakaice maka sir yarinyar ta had’a komai na samu nayi waya daita amman tace bata bukatar yi mana zane “da mugun sauri ATA ya d’ago yana dubansa cikin tsananin fad’uwar gaba yace “ what ? She rejected our job again duk yadda masu zane suke shan wahala a kasar nan kafin a karbi zanensu .”wallahi sir nima nayi matuqar mamakinta babu yadda banyi daita ba amman ta kafe bata son aiki damu .”ATA yayi murmushin ciki sannan ya koma ya zauna sosai akan kujera yana jan numfashi da kyar “wannan shine karo na biyu da aka fad’a masa baa son yin aiki a masikatarsa, yaji abun ya damesa matuqar . “






a hankali ya cigaba da murmushin gefen baki wanda da gani kasan na bakinciki ne “ina ganin wannan yarinyar tana da damuwa a rayuwarta amman me yasa ka kawo min wannan dogon bayanin akanta tun kasan bazatayi aiki damu ba ?”kawai dai wai dan ..” dogon tsakin daya ja tare da furta “noncess.”yasa james yayi saurin cewa“Am very sorry sir ,amman tace zuwa nan gaba zata iya kasancewa damu tunda ATA yayi shiru bai sake yin mgn ba kawai bakinciki ne ke cin zuciyarsa sai faman tsaki yake ja yayinda kwakwaluwarsa na shirya masa yadda zai yi tazo hannu cikin sauki “lallai tunda zuciyarta ta zabeta dan dole sai ta kasance a qarqashin ikonsa kuma

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login