Showing 84001 words to 87000 words out of 169868 words

Chapter 29 - MAR'ADAM'S BOOK 2 COMPLETE DOCUMENT by Aisha Bagudu .txt

06 Nov 2024

10875

da wulakanta mana godiyarmu ,ka dauka bata da gata ne, ita din fa matarka ce ba baiwarka bace ,tana magana tana nufosa, ATA ya dan ja baya kadan yana qare mata kallo tsab “ daga yanzu idan ka sake kai hannunka jikinta ko wulakantata hukuncinka agareni shine kisa.” ATA ya kankance idanunshi yana qare ma fuskarta kallo da abinda Ke fitowa bakinta da kuma yadda idanunta suka juye kamar gaske kamar kuma wasa tana matsoshi yana ja da baya.” bakasan karfin aljanin gagare bane shiyasa kake abinda kake yi wallahi duk ranar da ka sake bata mata rai na rantse bazan duba cewar matarka bace sai datse maka numfashi kafin ka kashe mana godiyarmu mune zamuyi ajalinka.”










Mmn sudais


💗💗💗💗💗💗
MAR'ADAMS
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗




*AYSHA A BAGUDO*


WATTPAD @HAUESH
AREWABOOKS USERNAME
AYSHAABAGUDO
bismillahirrahmanirrahim


Wannan littafin na kudi ne mai bukatar karantashi byn na kammalashi zai biya 1000 ta wannan account number din 1438775094 Aishat abdullahi access idan an tura sai a turawa wannan 09136918331 alert domin tabbatar da an tura domin sauraron littafaina a tuntubi chaneel dina (Hausa bakwai ) a YouTube.




Page 16






Daga inda yake tsaye yake qare mata kallon tsab yayinda gaba d'aya yanayin jikinta ya sauya exactly kamar yadda masu aljanu suke react, maryam tana fidda ido ta sake kallon ATA that's lookin at her wani iri, gashi nan dai kamar ya tsorata da yanayin ta kamar kuma bai tsorata ba ,amman zatayi komai dan ta tsorata shi ,shi kuwa he's thinking of gaskiya ne ko karyar aljanu zata masa. tana kallonsa ya sake d'an ja baya kad'an adaidai lokacin da wayarsa ta soma ringing iPod dinsa dake manne da kunnensa ya ta'ba taji ya soma magana can kasan makoshi ta yadda bazata iya jin me yake fad'a ba ,shirun da taji yayi ya cigaba da kallonta ya bata damar sake nufosa bai fi sauran taku d'aya ta isa garesa ba ,sai ji tayi ya buga mata wata razananniyar tsawa wacce tasa gabad'aya gidan ya amsa sautinsa ."




a zafafe yace "ke maryam meye haka ?wani irin hauka ne haka ? hahahaha ta cigaba da babbaka dariya cikin wata irin murya tace "sau nawa zamu fad'a maka wannan ba maryam bace god'i..." wani gigitaccen mari ya zuba mata wanda yasa nan take ta durkushe qasa dafe da kuncinta dan sai da taji ganinta da jinta tare da numfashinta ya d'auke na wani lokaci ,kafin ahankali numfashinta ya dawo ta saki wani marayan kuka mai cike da ban tausayi tana cewa "me nayi maka ? "ke ni zaki yiwa wannan iskancin da rashin hankali? ?ni zakiyiwa karyar aljanu ?gaban maryam ya bada rasss ya shiga bugawa da sauri sauri "kin manta ko waye tsaye a gabanki ?ko kinga alamun zuciyar tawa tana cike da tsoro ? ko nayi miki kama da matsoraci ?yayi mata tambayar a here tare da kai hannu ya damki wuyan rigarta ya kifa mata wani gigitaccen mari ."






ta saki qara mai sauti tana qoqarin kwatar wuyanta daga hannunsa amman ta kasa dan baqaramin damka yayi ma wuyanta ba yana huci tamkar zaki "wallahi idan hauka kike ji na fiki hauka "ya fad'a yana zaro mata idanu kamar zasu fad'o qasa kuka ta fashe dashi har da majina "ki sani ba aljanu ba ko haukacewa zakiyi babu ruwana kuma hakan bazai ta'ba girgiza zuciyata ba ."wani kuka ta sake saki tana rokonsa" dan allah kayi hakuri ka sakar min wuya numfashina. wai ma me nayi maka ne "?wata tsawa ya buga mata tare da sakinta da karfi sauran kad'an bayanta ya bugi center table din dake parlour'n tayi taga taga ta tsaya bisa qafafuwanta tana shafa wuyanta yayinda jikinta ke wani irin kyarma. ta tsura masa ido tana kallonsa hawaye na turereniyar zubowa "wannan fa zalinci ne daga shigowarka ka hau marina da shake min wuta tayi maganar cike da matsanancin tsoro sai dai jarumtar data aro ta sanyawa jikinta bai sa ya gane tsoronta ba ."




"Laifin me nayi maka ?ta sake tambayarsa yayi shiru yana kallonta a wulakance maryam ta share hawayenta ta cigaba da magana "ban maka laifin komai ba ,idan kuma key daka gani ne ,nice na cire domin bazan zauna yunwa ta kasheni ba , yau kwanaki goma kenan rabonka da gidan nan ,da kai a tunaninka haka zan zauna nayi rayuwa tattare da yunwa ? "me kake so dani yaya adam? gaskiya wallahi na gaji na gaji!! da wannan zalinci, ka tozartani ni daga ni sai kai ,ka tozartani agaban kowa ga azabtarwa ga horon yunwa "Enough is enough yaya adam da wannan tozarci da wulakanci biyayya fa ba hauka bane ..."ai bakin maryam tsayawa yayi cak sakamakon ganin "ATA ya nufota gadan gadan cikin tsananin fushi kamar mayunwanci zaki idanunshi sun kad'a sunyi jajur a matukar zuciye ya cigaba da magana yana hararta "shut dare kuma ki natsu ki saurare ni da kyau karki kuskura ki sake magana batare da izinina ba ".






Idan akwai abinda yafi shiru maryam tayi agurin rawar da jikinta yake kuwa sai ya baka mamaki "wato Ke gaki yar iska wuyanki ya isa yanka ni zaki dinga fad'awa magana son ranki ?"ba wai na fad'a maka maga..."I said shut up ki shiga hankalinki har yau baa haifi d'a ko 'yar da ina magana yana magana ba, ba'a min haka sai dai ni nayi kuma kinsan da zaman haka ni senior man ne you understand ba'a min haka koda kuwa ana min ke baki isa kiyi min ba saboda baki da wannan darajar da wannan matsayin a wajena .dan haka to be your first and last da zaki fad'a irin wad'an nan maganganun saboda bazan barki ba idan kin sake" shiru maryam tayi cike da tsoronsa wanda a yanzu ta fahimci girman tsoronsa da take ji ne yake sawa yake mata wasu abubuwan ta runtse idanunta hawayen ciki suka sake wanke fuskarta tana jin kamar ta kashe kanta ta huta saboda muguwar tsanar da yayi mata ta rasa me ta tsare masa a rayuwa daya tsaneta haka ?."hawaye maryam ta share wasu na sake zubowa ."




Bai barta taji da bakincikin da yayi mata dabaibayi dashi ba ya sake qara mata wata damuwar cikin wata irin murya yace "wato ni zaki tsorata da ace banyi saurin d'aukar mataki akanki ba shikenan haka zakiyi wasa da hankalin mutane wai ke mai aljanu yanzu ina aljanun suke ? tayi shiru tana dubansa "ina son ganinsu ido da ido kuma a yanzu ,idan basu fito a zahiri ba sai naci ubanki ."iya firgita maryam ta firgita jin abinda yake fitowa daga bakinsa kuma yadda yake kallonta sarai ta fahimci ya gane aljanun karya tayi . Idanunta gbdy sun yi ja har fitsari ta saki batare datasani ba ."ja da baya ta soma tana karkarwa da kyar take fad'in "kayi hakuri nifa bansan me nayi ba "wani kallo ya d'auketa dashi "kenan baki san Kiyi karyar aljanu ba yanzu sai dana zuba miki maruka kika dawo haiyacinki ?jikinta da bakinta na rawa tace "wallahi allah bansan nayi karyar aljanu ba" wani kallo yayi mata mai had'e da harara "na rantse maka da Allah ban san nayi ba "shiiiii ! ya furta a kasalance."




Nan take tasa hannu ta rufe bakinta idanuta sunyi zuru zuru kamar yace "arr ta zunduma a guje "kafeta yayi da ido yayinda zuciyarsa ke tafasa yace "woww gsky wannan yarinyar kin qaro iskanci mai upgrade ya kai hannu zai damko hannunta tayi saurin zamewa tana ja baya da sauri dan tasan bazai mata da kyau ba muddin ta shiga hannunsa duk ta rud'e sai hawaye take tana fitar da zufa "tsaki yaketa yi yana kallonta dan dole sai ya gano gaskiyar data boye ,yayinda duk jikin maryam kyar yake tana yarfe masa hannu duk kwaliyar data 'bata tsawon lokacin akanta ruwan hawaye ya wanketa cikin kuka tace "gabad'aya ban fahimci inda maganarta ta dosa ba "ni dai nasan na sauko naga kana cire takalmanka ka tashi ka nufoni bayan haka ni bansan komai akan maganar aljanu ba ."






juyawa yayi yaje ya kulle kofar shigowa sannan ya dawo ya tsaya yace "banason jin komai kawai aljanun nake buqatar gani kuma a yanzu maryam ta durkushe qasa "ta ina zan fara yaya dan girman allah kayi hakuri ka bar zuciyata haka karka qara min wani sabon tashin hankali akan wanda nike ciki "you are very stupid I mean ina son ki sake wannan acting din aljanu kuma a yanzu" maryam na kuka tana rokonsa "okay tunda baza kiyi ba kiyi frog jump kuma zanyi bincike mai karfi idan na gano baki da aljanu na karya kikayi kin mutu "okay naji amman na manta yaake frog jump ." wani mari ya kai mata yace "bismillah start !maryam ta kama kunne kawai "kina hauka ne frog jump nace kiyi kuma wannan shine karoki na farko da karshe da zaki sake acting aljanu acikin gidan nan ko da kuwa da gaske kina dashi ki fad'a masu mijin da'aka masa dole ya aurenki yafi su hauka ."




"Allah yaya adam ka yarda dani ban san nayi maka haka ba ,zata cigaba da rantse rantse ya dakatar daita yace "karki qara kiran sunana idan ba haka ba zan mugun baki mamaki ,kuma dan allah naji kin sanarwa sweetheart ko wani a gida abinda nake miki kad'an ne wanda zan miki sai yafi shi ,maryam na kuka tana frog jump sai daya balain bata wahala jikinta rawa ko ina na mata ciwo sannan yace "leave this place?aikuwa da mugun sauri ta suri jakarta tayi sama ta shige d'akinta tare da kulle kofar, ta shiga sheshekar kuka har da rike kai tana "wayyo allah na shiga ukuna wannan wace irin maseefa ce ? "wallahi na gaji ta jima tana kuka tukun tayi shiru ta zuba tagumi tana tunani mafuta dan zuwa yanzu ya dace tasan inda Ke mata ciwo tayi shiru tana tunani " kuma fa da fari yaya adam yaji tsoro acting dinta wannan marin da yayi mata ne bai kyauta mata ba if not da tayi galaba akansa yama akayi ya gane ba aljanun gaske bane ?"




"oh my god wallahi yadda ya tsorata da farko abun yayi mata dadi ,ta d'an saki dariya ta nufi gado ta jingina tana shafa kuncinta daya d'an tashi tana ciza lip's dinta "da'ace allah ya taimaketa da wata killa shikenan ta dan samu sausauci daga garesa, ya allah ka kawo min mafuta duk yadda ta dauko shirinta sai ya wargaza ga tukunyar maganin ma haka ya gama kwanakisa sai jiya ta shiga ta ciro daga karkashin gadonsa yanzu kuma tayi iskan karya ya gane anya kuwa yaya adam mutun ne kamar sauran mutane ?wai sai yaga aljani ido da ido ko idan yaga aljani zai tsaya ."?ina ma tana da aljanun gaske su gyara masa zama, mugu kawai bancin son da take maka wallahi da tuni ta tattara ta gudu ta barsa . tana zaune wayarta ta soma ringing ko baa fad'a mata ba tasan sister ce tana dauka tace "sister kinji shiru ko ?ai babu maganar fita nan ta koro mata komai nan take nana hauwa'u tashiga kyalkyata dariya har da rike ciki "haba sister ina fad'a miki wahalar dana sha amamn zaki bige da min dariya haka ."




bangaren nana hauwa'u tace "wallahi sister na tausaya miki kawai karyar aljanu ne ya bani dariya ai yaya adam sam bashi da tsoro lokacin yana bording school shike zane masu aljanu da kin fad'a min zakiyi karyar aljanu wallahi bazan goyi bayan Kiyi ba dan bazaki ga duro ba wahala zaki sha kawai a banza .kuma fa wallahi komai ya tafi min daidai gigitaccen marin da yayi min ne ya 'bata komai "karki sake ganganci nan allah ya rabamu da lamarin aljanu ,ameen yace zai yi bincike dan Allah ko ya kiraki kice da gaske ne ina dasu "kai bazan daura miki wannan lalurar ba .Kiyiwa girman allah ki rufa min asiri idan ba haka ba na tattara na gudu tun dare bai min ba ."nana hauwa'u ta sake kyalkyalewa da dariya tana cewa "dan girman allah ki rage tsoransa kema fa ya kamata ki kai masa ziyara "ziyara kamar wani irin ziyara kenan kike nufi ?."






"haba maryam yanzu sai na tsaya na koya miki "menene amfanin social media din da kike yi ?group's gareki fa sunfi ashirin da wani abu sannan ina karatun novels din da kike? uhm maryam ta sauke numfashi da ajiyar zuciya tana cewa " nifa wallahi yayanki tsorata yake, ko nayi niyya yi wani abu sai tsoransa ya shigeni na fasa .da dabara zaki dinga shige masa kawai Kiyi qoqarin kisan weekpoint dinsa bazai ki ba "sister nasan duk wani week point din nmj ,kunnuwansa nipples dinsa sumar kanshi uwa uba jijiyarsu amman yayanki baya yarda na ra'bi inda yake bai ma son ya bud'e idanu ya gani bare a kusa dashi ai shiyasa nake fad'a miki yaya hisham mutumin kirki ne ,wallahi sister kin samu miji a yadda kuke gudanar da rayuwarku yanzu bana jin zai auri nuzla .ke babu ruwanki da sheidar nmj na fad'a miki duk nmj dake da mata da buduruwa a waje baki biyu garesu idan ma zai aureta suje can su qarata ni dai a kwantar min da hankali abinda zan fad'a miki Kiyi qoqarin ki rage tsoransa kinji sun jima suna waya kafin sukai sallama ."




Bayan kwana biyu suna cikin waya da nana hauwa'u taji yana buga kofar d'akin da karfi da sauri tace "sister gashi nan yana buga kofa ina zuwa ,ta ajiye wayar batare data kashe ba, ta mike tsaye tun kafin ta isa bakin kofar taji yana cewa "gidan ubanki ne da zaki dinga kulle kofa ?maryam najin abinda ya fad'a tayi hanzarin ta bud'e masa kofa tana "cewa duk abinda zakayi yaya adam kayi kuma ya tsaya a iya kaina kawai amman zagin iyaye bazan sake d'auka ba ATA najin abinda ta fad'a ya gyara tsayuwarsa da kyau abun ya mugun girgizasa ganin yadda yake kallonta ta juya ta shige cikin d'akin tana cewa "ka zageni kaci zarafina ni naji na gani zan d'auka amman iyaye please kayi qoqarin ka daina sakosu ."ai ko babu komai dady mahaifi ne gareka idan bakayi masa addua ba ai kuma bai cancanci zagi ba ta fad'a tana rungume hannuwanta duka a qirji ."




A wulakance ya d'auki kallonta daga qasa har sama kafin a hankali ya shigo har cikin d'akin ya tsaya yana kallon yatsun kafafuwansa a hankali ya motsa lip's dinsa "say what you said again ina son tabbatar da najiki da kyau tayi shiru taki cewa komai "gidan nan ba gidan ubanki bane ba kuma da kudin ubanki na gidana shi ba na maimaita abinda na fad'a ina son kema idan kin isa ki maimata abinda kika fad'a yanzu ." ya fad'a mata haka kai tsaye kamar bashi ba "daman baa sonki ko digon d'aya baki da matsayi acikin nan ya nuna daidai saitin zuciyarsa da yatsan hannunsa "baa sonki amman kike qoqarin shigo da wani salo rashin kunya to zaki sha wahala akan wahala dan ko ina sonki bazan d'auka ba bare babu d'igo sonki acikin nan.ina dai zaune dake darajan iyaye ,rayuwar mahaifiyata ke rike da aurenki yau ta fad'i ta mutu kisani aurenki dani ya qare dan rabuwa zanyi dake da huta ."




"yanzu mami na mutuwa zaka rabu dani "?yes of course zaman me zan cigaba da yi dake zan rabu da kwallon mangaro na huta da kuda ,baki san kin zame min qaya bane ? ta runtse idanunta she's so much in love with him amman shi kullum tunaninsa yadda zai rabu daita , "dan allah meye ribar ka yaya adam da baka son yiwa mami biyayya ?ta tambayesa muryarta cike da rauni "ai duk akanki ne na kasa wannan biyayyar kinga kuwa bazan ta'ba sonki ba har na koma ga allah" bazakayi mata biyayya bayan ranta ba "ubanki zanyi ba biyayya bayan rai ba "ya fad'a a zafafe yana jan tsaki yare da dafe goshinsa can kuma yace "me keyn d'akina yake ajikin keyn kitchen?tayi shiru tana dubansa a matukar tsorace "me keyn d'akina yake ajikin keyn kitchen?" ya sake maimaitawa a karo na biyu hankalin maryam ya tashi sosai ta masa baya da sauri tun kafin ya sauke mata mari ".




"don't let me rept my self wallahi idan baki fad'a min abinda yasa yazo hannunki ba zan baki mamaki yanzu .maryam ta sake tsorata dan tasan zai iya aikata komai tunda ya rantse muryarta na rawa "tace daman saboda na dinga gyara maka d'akin ne "na buqaci haka daga gareki ?"a'a kawai dai ni naga dacewar haka ne shiyasa "tunda nayi tafiya kina sharewa ?tace "eh ina sharewa "kina sharewa amman kuma naji d'akin yana warin mushe ya d'ago yana kallonta tsab yana nazarinta "dan allah dan annabi dan darajan iyayenka karka min komai ta fad'a haka ne saboda kusancin da suka samu komai zai iya faruwa.tunda ya tsura mata tsumammun idanunshi bai sake cewa uhm bare uhm uhm ba sai dai kana kallonsa zaka fahimci ya gaji da damuwarta
"Dan girma allah Ke wace irin halitta ce ?duk abinda mutun bai so shi kike yi ni wallahi na gaji dake dan hannuna ya gaji da ta'ba jikinki."




"Kayi hakuri nima jikina ya gaji da duka da mari
"To zaman me kike yi ?"ai sai kin bar gidan kuma bari na har abada ba

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login