Showing 54001 words to 57000 words out of 169868 words

Chapter 19 - MAR'ADAM'S BOOK 2 COMPLETE DOCUMENT by Aisha Bagudu .txt

06 Nov 2024

10860

,ya zauna a mazauninsa yana kallonsa batare da yace komai ba "good morning sir ? ya gaishesa cike da girmamawa "uhm ! yayi gyara murya kawai alamun yana jinsa yana maida hankalinsa Kan system "uhm amm sir ko zan iya magana yanzu "uhm ! ya fad'a a takaice "adadin mutane kimanin dubu dari uku ne suke bukatar aiki a karkahainmu ,sir wannan shekara ko zaa hada da masu degree ? Ko kuma daga master zuwa sama ne zaa dauka ."?" ka ma da kake maganar daga wani mataki ka fara aiki ?"sorry sir ya fad'a a tsorace "duk mutumin da aka tabbatar takurdunsa sunyi kyau ayi masa interview idan ya cancata a d'aukesa ."
"sai abu na gaba kada a Kuskure akarba' kwabo duk wani mutun domin samar masa aiki a duba cancanta yana gama magana ya dauke idanunshi akan system zuwa wani bangare dabam yana cewa fatan" ka fahimta "yes sir sai kuma game da compaing dake kasar togo sun kira suna bukatar almustapha "me zance masu?" kai komai bazakayi da tunanin kanka ba sai ka tmby ? "am sorry sir"ya juya da sauri ya bar office din ."




Ranar monday tun asuba da maryama ta tashi tayi sallah bata koma ta kwanta ba ta soma shirin zuwa wajen interview duk abinda tasan zaa buqata ta had'asu waje d'aya acikin jakarta hatta kayan da zata saka ta fito dashi sannan ta shiga wanka karfe bakwa daidai ta gama shirinta ta fito parlour'n ta hango aunty tsaye a kitchen ta qarasa ta rungumeta ta baya "good morning mumy "ta kai hannunta ta shafa gefen fuskarta morning my princess har kin fito ?yes !ta fad'a tana duba agogon dake daure da tsintsiyar hannunta "muje ki karya kafin ki fita "aunty da kin bar breakfast din nan Kiyi min addua kawai" bakince akwai wanda zai tsaya maku ba ?aunty ta fad'a tana fitowa daga kitchen maryama ta biyo bayanta tana cewa "akwai but bashi zai mana interview ba amman dai ina ji ajikina zamu samu nida subai'a "to Allah yasa a dace "Ameen !ta fad'a a lokacin da wayarta ta d'auki qara ta ciro ta duba tana cewa "aunty subai'a ce ."




Tayi sauri ta d'auka tana "cewa hello suby okay gani nan fitowa mgnr second biyu sukai ta katse kiran tana cewa "aunty ni zan wuce subai'a har ta fito "kema yanzu zaki wuce ta kai cup din tea bakinta ta kurbi kad'an ta kai bread bakinta a haka ta shanye cup din tea tace "na gode sosai Allah bar min Ke mamana ina sonki ta kai mata kiss a kumatunta ta nufi kofar fita da sauri tana cewa aunty "bye ye sai na dawo "bye ta d'aga mata hannu tana kallon bayanta kai tsaye bangaren ummah ta shiga da sallamarta yaya sadam ta gani zaune Jiki a sanyaye ta gaishesa "yaya sadam ina kwana?"ya dago idanunshi ya kalleta sannan ya amsa da" lafiya !"


ta nufi hanyar dakin ummah sai ga umma ta fito"maryama har kin fito ?na fito umma to Allah yasa a dace tace Ameen " ina zata ?ya tambaya batare daya kallesu ba "interview ! ummah ta bashi amsa da haka "aiki zatayi kenan ?" to meye amfanin karatunta idan batayi aiki ba ya dan yi shiru can yace "nifa gsky bana da wannan raayin yana gama fad'ar haka ya mike yana cewa " ni na wuce tsaya ka sauke min ita "bai ce komai ba ya fita maryama tabishi da kallon mamaki dan bata ta'ba tunanin zata samu matsala dashi akan aiki ba ganin shima dan boko ne ita kam akan aikinta zata iya hakura da auren dan
sam aure baya ranta a yanzu mutuntakan umma ne ta duba da tausayin mahaifiyarta bawai son aure take ba ,ganin yadda yanayinta ya canza yasa ummah tace "karki wani damu zakiyi aikinki "amman ummah alamunsa ya nuna baya so "gsky ne sadam bai son amman zai yarda kinji wahalar karatunki bazai tafi a banza ba ,yana ma daga cikin abinda yasa ban bari an daura maku aure ba nafi son ki shiga da aikinki". kanta kawai ta gyada mata "maza bishi ya saukeki ."




Mmn sudais


💗💗💗💗💗💗
MAR'ADAMS
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗




*AYSHA A BAGUDO*


WATTPAD @HAUESH
AREWABOOKS USERNAME
AYSHAABAGUDO
bismillahirrahmanirrahim


Wannan littafin na kudi ne mai bukatar karantashi byn na kammalashi zai biya 1000 ta wannan account number din 1438775094 Aishat abdullahi access idan an tura sai a turawa wannan 09136918331 alert domin tabbatar da an tura domin sauraron littafaina a tuntubi chaneel dina (Hausa bakwai ) a YouTube.




Page 11




Jiki a sanyaye maryama take taku gabad’aya kuzarin jikinta yayi kasa ,”aiki zatayi kenan nifa bana ra’ayi ? maganarsa ta shiga yawo acikin kwakwaluwa da zuciyarta , tana tafiya tana tunanin maganarsa , a qalla yaya sadam ya kusan minti shabiyar zaune acikin motarsa yana jiranta , ya dubi agogo a karo kusan na shabiyar yaja qaramin tsaki a lokacin da wayarsa ta soma ringing ya kai hannu ya d’auka ya duba yaga sunan ummanshi ke yawo akan screen din wayar. numfashi ya sauke sannan ya d’auka cike da girmamawa “sadam !”ta kira sunansa ya amsa da “na’am “ina son kaso maryama tun daga qasan zuciyarka ,sannan zaka iya zama madadi ko ka cike gurbin abubuwan da maryama ta rasa a rayuwarta na shekaru baya.”




“ina jin ciwon da qunci abubuwan da sukai ta faruwa daita amman ina fatan kai ne zaka wanke min wannan quncin ya dawo farinciki na har abada “naji ummah in sha Allahu zan yi iyakar qoqarin na kawo miki wannan farinciki “dan allah sadam ka son maryama “ yayi murmushi kawai yana sosai keyarsa yayinda idanunshi ke kallon hanyar da maryama zata bullo .”ahankali yaga tahowarta a natse take yin komai nata kamar bata son taka kasa koma yace tausayin kasar take “nayi magana ba kace komai ba ? “duk abinda ummanah take so ya zama dole naso “ya fad’a yana sake tsaida idanunshi akanta “






“na gode maka allah yayiwa rayuwarka albarka yadda kayi min biyayya kai ma allah ya baka ya’yan da zasu maka biyayya “Ameen ya hayyu ya qayyum “
qirjin maryama na tsananin fad’uwa ta qaraso bakin titin unguwarsu har ta tsaya jikin motarsa bai iya d’auke kwayar idanunshi akanta ba ,jikinta a matukar sanyaye ta bud’e gaban motar yaya sadam ta shiga yayinda zuciyarta Ke bugawa da karfin gaske ta zauna tare da rafka tagumi cikin rashin sanin madafa madadin taji yaja motar sun wuce sai taji yayi sallama ya ajiye wayar hannunsa ya kunna music yana bin wakar ahankali .”




Kanta taji ya sara mata ganin bashi da niyyar tafiya ga lokaci na wucewa ya sata kallonsa kamar mai shirin yin kuka tace “yaya sadam !”tamkar ba magana take yi masa ba haka ya cigaba da bin wakarsa babu alamun damuwa ko nadama a fuskarsa hannu ta mika hakan yasa sukayi daf da juna wanda da zata qara matsar da hannunta zata iya yin masauki a jikinsa, a natse ta kashe wakar ta sake kallonsa tace “i am talking to you yaya sadam “.“me kike son na yi ?ya fad’a a sanyaye “kayi hakuri dan allah idan wani laifi nayi maka lokacin na tafiya gashi naga baka da niyyar tafiya wannan aikin shine rayuwata bana son rasashi .”




ya d’an matsota yana cewa “ni dana zauna jiranki tsawon mintuna shabiyar bani da aikin yi ne ?”ko bani da wajen zuwa ne?” ko kuma aikina bashi da mahimanci ne ?”yayi mata tambayar ajere yana sake kunna wakarsa .”sake kashe wakar tayi ta kallesa a marairaice sannan tace “am sorry duk maganarka ce ta rikitani har yasa kuzarina yayi kasa wallahi da kyar na kawo kaina bakin titin nan shiru yayi yana kallonta fuskarsa a d’aure tmkr wanda bai ta’ba dariya ba “ka d’an saki fuska nan dan fushi baya maka kyau “ ta furta cikin wani irin salo da sautin murya mai sanyi huci bakinta da numfashinta duka na dukan wuyansa wanda sanadiyyar hakan ya haddasawa tsigar jikinsa mikewa ya kuma qara bugawar da zuciyarsa take .”






ajiyar zuciya ya sauke yana jin wani iri a ilahirin jikinsa “saboda nace bana ra’ayin aiki ?”wallahi duk shi ya sanyayyar min da jiki da dai zaka amince zanyi farinciki da hakan “bai sake cewa uffan ba ya kunna motar ya soma tafiya kamar wasu kurame haka suka cigaba da tafiya .”qarfe tara saura wasu mintuna suka isa bakin tafkeken get din Z&A yaja ya tsaya batare daya kashe motar ba cikin siririyar muryarta tace “yaya sadam na gode sosai allah ya kai lafiya “ ta fad’a tana qoqarin fitowa daga cikin motar adaidai lokacin da hancin motar ammar ta sanyo kai “Ameen ki kula da kanki “I will !ta fad’a tana sakar masa murmushi duk da bawani sonshi take ji ba amman taji dadi sosai kuma zata iya rayuwa dashi muddin rai .ammar yana kallo sukayi bankwana “




da sanyi jiki ta shige cikin sadam ya cigaba da tsayuwa yana kallon bayanta har ta ,bace masa sannan ya lumshe idanunshi lokaci d’aya kuma ya bud’e “oh my goodness god “ya furta a can qasan zuciyarsa ta yadda idan ba bakinsa ka kalla da kyau ba bazaka fahimci abinda yace ba .”murmushi ya kwace masa a saman fuska wa zai same kamar maryam yace bai so ?”sai dai wani dalili na dabam ya haifar da hakan ,sam ya manta a inda yake sai da yaji mutane ana masa hon a she fa motoci ya tare duk suna tsaye suna jiransa murmushi yayi sannan ya kama gabansa yayinda maryama tuni ta shige cikin ma’aikata bata ma san lokacin da yaya sadam ya wuce ba .”




tana shiga sauran abokan aikinta suka qaraso suna mata magana suna shirin shiga inda zaa wa masu neman aiki interview amman ita maryama hankalinta bai garesu yana kan neman inda subia ta shige ,tunda tasan a tun lokacin da sukai waya daita ya cancanci ace tana wajen koma anyi mata interview an gama .”taja ta tsaya tana cewa” kuje zanzo na sameku daga baya “.ta bud’e jakarta ta ciro qaramar wayarta ta shiga neman layin subai’a ,ganin an bud’ewa ammar mota ya fito yana nufota yasa ta sauke wayar daga kunnenta tare da kashewa gabad’aya “ya iso har inda take tsaye yana gama qarasowa wayar hannunta ya amsa ya rike ta kallesa tana murmushi sannan tace “barka da safiya ?




“Barka !
“me ya tsayar dake da sai yanzu kika qaraso ?ya tmbyeta yana duba screen din wayarta sunan wacce ya gani ne yasa ya mika mata wayar “wallahi wanda zan aura ne ya ‘bata min lokaci “ tayi maganar cikin salon jan hankalin duk wanda yake tare daita, ammar kasa magana yayi kafin daga baya da kyar cikin fad’a yace “wato har zaki iya fad’a min wanda zaki aura ne ya ‘bata miki lokaci ? tayi shiru tana wasa da yatsun hannunta dan batayi tsamanin zai ji haushi maganarta ba ganin babu komai a tsakaninsu sai mutunci da girmamawa “amman ki sani wannan ba mutuncinki bane ko nace zaki zubda mutuncin family d’inku ne .”




“Ai shima family dinmu ne da mahaifinsa da mahaifina the same mother the same father wani irin kallo yayi mata mai cike da tunhuma,itama kallonsa tayi numfashi ya fesar yace “shi kuma mijin da nayi miki fa ya zanyi dashi ?tayi murmushi tana cewa “allah sir ka daina min haka wallahi kana d’aga min hankali ,kai kanka kasan kafi karfina bare wanda kake fad’a wannan sai dai na qara dagewa da aikin ibada wata killa na samu irinsa a aljanna yayi murmushi yace muje “.




Ahankali suke takawa yayinda mutane suke gaishesa wasu ya amsa wasu kuma ya d’aga masu hannu “kefa ko anyi miki interview ko ba’ayi miki ba dole zaki yi aiki damu “sure tunda inda kai ba ,ai sunanki na can tuntuni kinga office dinki can ta kalli inda ya nuna mata “woow gsky naji dadi sosai “kinga ga office dinki ga na mijinki in sha allahu “tayi murmushi kawai tana cewa “subai’a fa ?nifa nafi son naji kana magana kana had’awa daita zai yi magana kenan, wayarsa ta d’auki qara sauti ,ya soma qoqarin d’auka bata tsaya jiransa ba ta cigaba da tafiya dan daman da kyar take iya jirawa dashi da sauri ta qarasa tana shiga aka kira sunanta .”




Sai da tayi addu’a sannan ta shiga office din ta gaishe da mutumin data gani zaune mai suna wale yana duba wasu fararen takardu,ya d’ago ya kalleta a natse sannan ya sake kiran sunanta “maryama hussein !”tace yes sir ! sai daya bata izinin zama sannan ta zauna a natse tana wasa da yatsun hannunta wanda ya zame mata jiki ,ya d’an saci kallonta yana mamakin matsayin da aka bata ,domin kujera ne da suka dade suna neman wanda zai maye gurbinsa , sai dai lokacin daya fara auno mata tambayoyi akan kasuwanci da kuma matsayin da zata taka ya ajiye mamakinsa a gefe domin kuwa ta cancanci ta hau matsayin kuma irinta mai kamfanin ya dade yana nema .”






bata wani jima ba ta fito har da award aka bata sakamakon aikin da tayi dasu daman kuma sun ajiye ne domin rana irin ta yau “congratulations sauran abokan aikinta suka shiga yi mata tana amsa masu da “thank you tare da rungumar mata daga cikinsu duk wannan farinciki da take ciki bai kawo mata natsuwa ba saboda rashin ganin subai’a da batayi ba ta ciro wayarta ta soma nemanta tana tafiya ahankali har ta fito haraban ma’aikatan subai’a ta d’auka tana kuka hankalin maryama ya sake tashi sosai ciki tsanani tashin hankali tace “subai’a kina ne na shigo har an d’aukeni aiki banganki ba ? tana shirin sake yin magana ta hangota a bayan wata bishi tana qoqarin fitowa .”






Da sauri maryama ta qaraso ta tsaya tana qare mata kallo tsab hawayenta yasa zuciyar maryama tsananin bugawa “me Ke faru dake subai’a ?kukan me kike yi ?muryata cike da kuka tace “na rasa aikin nan ,da yawa wad’an da suka d’auka alfarma ne yanzu bansan ta yaya zamu cigaba da rayuwa ba daman da allah da aikin nan na dogara gashi ban samu ba muddin sai da wata alfarma zan samu aikin nasan har abada bazan samu ba .”ta riko hannunta maryama tana cigaba da kuka ta soma rokonta “dan girman allah maryama karki barni haka ki taimakeni ki bar min aikin nan nasan zaki samu wanda yafishi gabad’aya idanun subai’a sun rufe har sai da maryama ta kira sunanta sannan ta tsaigaita kukanta “ki kwantar da hankalinki ki bar kuka nan haka” amman ta yaya babu sunanki bayan ..”sai kuma tayi shiru ta janyo hannuta zuwa ciki “zo muje .”




maryama na gaba subai’a na bayanta har suka qarasa bakin office din james ta nemi izinin ganinsa aka bata damar shiga ,wanda ta samu wannan damar ne saboda ammar domin yadda yake mata yasa mutane dayawa d’aukar sonta yake maryama ta shiga tare da subai’a dake kuka har lokacin .”bayan ta gaishesa cike da ladabi tace “dan allah ina neman wata alfarma agareka ya kalleta dan shima ta burgesa yadda ma’akatan suka dinga yaba kwazonta tun kafin tazo kuma zuwanta wale ya sake tabbatar masa iri irinsu basu dayawa a duniya dan tunda ya sheida masa ya kira mai gidansa seun ya sheida masa muryarta a matukar sanyaye ta soma magana kamar zatayi kuka “dan allah sir wannan yaruwa tawa nake son ta maye gurbina ma’ana acire sunana a saka nata .”ya kalleta a tsanake domin yasan yadda ake shan wahalar neman aiki yanzu da kudinka ma baka samu “.






“Saboda allah zakayi karka tsaya tunanin komai ni inda aikin da zanyi domin tallafa rayuwata for now ,ita kuma bata dashi da wannan aiki Kawai ta dogara ga mahaifinta ya rasu ko da yake nima marainiya ce amman dai tafini bukatan aikin nan saboda tana da kanne dayawa da mahaifiya mara lafiya dake karkashin kulawarta itace komai nasu “da wannan maganar ta karyar da zuciyar James ya kalli subai’a cike da tausayawa yace “sorry oo !”zan iya miki wannan alfarma sai dai bazata maye gurbin kujerarki ba “tayi shiru tana tunani abinda zata ce kafin tayi magana ya cigaba” kujerarki ke kad’ai ake bukata sakamakon oga ammar sunanki ya bayar gashi yanzu kinzo da wata magana “karka ji komai a saka a duk inda zaa sakata nidai burina ta samu aikin ni zuwa gaba in sha allahu zanyi aiki daku amman a yanzu burina subai’a ta samu aiki .”






Mr James ya saka sunan Subai’a ya cire sunan maryama “ suka fito zuwa gindin wata bishiya maryama na cewa subai’a “congratulations na tayaki murna kawata yanzu kin zama cikakkiyar maaikaciya ta fad’a tana murmushi subai’a ta rungumeta cike da farinciki “na gode na gode maryama allah ya saka miki da mafifincinsa nayi imani zaki samu aikin da yafi wannan da kika bar min tana kuka tana gode mata” haba subai ki daina kuka kawai dan na sadaukar miki da aikina kike wannan godiya da kuka haka ?” ta goge mata hawaye tana cewa ni na zan bar ki na wuce gida nasan akwai abubuwan da zaku yi kafin ku wuce ina miki fatan alkhairi allah yasa ki fara aiki a saa ta juya a hankali ta soma taku subai’a tabi bayanta da kallo hakika bazata ta’ba manta alkhairinta gareta ba .”






Da wuri maryama ta dawo gida koda ta shigo kai tsaye bangaren ummah ta shiga ta sheida mata amman ta isketa a dakinta tana bacci dan haka ta fito ta shiga bangarensu ta zauna a parlour’n tana sauke numfashi tare da dafe goshinta ko cikakken minti biyar batayi ba ,Aunty ta fito da mamaki take kallonta “lafiya naga har kin dawo ?lafiya aunty nan ta zayyane mata komai sosai ran aunty ya baci kamar ta rufeta da duka musaman data lura ko ajikin maryama dan babu alamun damuwa atare daita “me yasa zaki bada aikinki bayan Kinsan muma muna fama da kanmu ? “aunty kiyi hakuri kin sani ni zan iya cigaba da aikin zanena

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login