Showing 36001 words to 39000 words out of 169868 words

Chapter 13 - MAR'ADAM'S BOOK 2 COMPLETE DOCUMENT by Aisha Bagudu .txt

06 Nov 2024

10867

ne a wajenta ko kuma nuna mata kofar yi min abinda ta ga dama .”




“ sweet heart na aikata hakan ne abisa kuskure amman kiyi hakuri dan allah “ ta d’aura hannunta a saman nashi kawai batare da ta sake cewa komai ba tana jin tsananin qaunarsa .“Kiyi hakuri kiyi min addua sweetheart ko allah zai sa min son diyarki a zuciyata ko kad’an ne , sweetheart har yanzu na kasa manta mafarkina ina tsananin sonta gashi bansan inda zan sameta ba sannan duk yadda naso na cireta araina na manta daita na kasa manta komai nata .”bugun zuciyarta, numfashinta fuskarta da kamshinta idanuwanta murmushinta hawayenta sautin numfashinta sweetheart bazan boye miki ba na sha saduwa daita acikin mafarkina .”




Mami ta tsura masa idanunta tana kallonsa “na fara shan sigari duk dan saboda ita haka zalika a qoqarin na manta daita ne na fara shan giya ina danne zuciyata akanta ,nayi iya yina domin na manta daita amman wallahi sweetheart abun yaki aiki har yanzu koina na juya ciwo nake ji acikin zuciyata “mami tayi shiru zuciyata cike da tsananin tunani abu daya ne yayi mata dadi acikin magangunsa shine rokon adduarta na allah ya saka masa son mrym ko kad’an ne wannan abu ya sanyaya zuciyarta kuma daman tana wannna adduar .”




“Sweetheart nifa abun tausayi ne abun a tausayawa ne akwai ciwo mai zafi acikin qirjina bana buqatar tausayawar kowa sai taki kece kawai zaki tausaya min domin kece kawai kika san ciwona kuma kece kawai kike sona tsakanin da allah.“mami ta numfasa tana cewa “adamcy nah ina tsananin sonka da tausayinka kai ma ka sani ..”“na sani sweetheart amman akan yarinyar nan kin canza min koma nace kinfi sonta akaina,mami ta kallesa kawai “sweetheart ki janye maganarki akaina zan cigaba da rayuwa daita Kmr yadda kika bukata amman batu na samammarta farinciki babu shi domin ni kaina zuciyata baa cikin farinciki take ba dan haka dan Allah ki janye magarki akaina .”




Ta girgiza kai alamun a’a “sweetheart kin janye dan idan nayi kuskure kin bin umarninki wani abu zai faru dani idan kuma wani abu ya sameni kece kike da asara sam ita ba asararta bace kina ji kuma kina gani zata komawa wani ta bar miki d’anki da rayuwar daya tsinci kanshi .” muryarta a sanyaye tace “babu abinda zai sameka adamcy kuma Ina rokon Allah ya kawo maka saukin abinda Ke damunka "ta qarasa fada tana rufe fuskarta da tafin hanunta hadi da rushewa da kuka .”




“why sweetheart me yasa zaki min asarar hawayenki bayan kin min addua?”addua nafi bukata daga gareki kuma kinyi min na kuma gode Kiyi haquri don Allah ki daina kuka ni dai kin janye furucin ki akaina “na janye kai ma kuma kayi min alqawarin bazaka takura rayuwar maryam ba .”dan allah ka barta tayi farinciki a gidanka wallahi bancin mutane zasu zageni da na raba aurenku kowa ya huta“
“sweetheart babu mai zaginki kuma da zaki min haka wallahi da naji dadi da samun kwanciyar hankali “uhmm adamcy taa girgiza masa kai “kayi hakuri kawai adamcy zan maka addua kamar yadda ka bukata ya sauke wani numfashi yana mikewa ya zauna gefenta ya zauna yana kiran sunanta .”


“sweetheart!”
“ina jinka adamcy “ina son zan qara aure“bazan hanaka qara aure ba adamcy amman dan allah ka bari zuwa nan gaba kad’an dan bazan ta’ba yarda ka shigo da wata gidanka ba alhalin diyata bata da matsayin komai a wajenka “why sweetheart “?mu bar wannan maganar adamcy muyi wata dan bana son jinta for now shiru kawai yayi yana mai runtse idanunshi shi kad’ai yasan zafin da ciwon da zuciyarsa keyi .”


“Sweetheart cikin satin nan in sha allahu zan bar kasar nan zuwa holland “da sauri mami ta kallesa sam maganar bata mata dadi ba ,kuma tasan dan ya nisanta kanshi da maryam ne “zaka bar kasar nan saboda maryam ko ?tayi maganar kamar zatayi kuka “ko d’aya sweetheart “saboda me zan yi tafiya saboda ita ?”kema kinsan tafiye tafiye yana cikin tsarin aikina” mami tayi shiru ya riko tafin hannunta cikin nashi “sweetheart!”ta sake kallonsa “ki kwantar da hankalinki nifa banki na daina tafiya zuwa koina ba saboda ke “wa na ajiye a inda zani ?”


“Me zakaje yi a hallond?yayi shiru yana kallonta “naga duka yaushe maryam ta tare da zaka tsiro tafiya gsky nidai idan son raina ne ka bar tafiyar nan ka wakilta wani ka d’an zauna da maryam “shikenan sweetheart “ya bata amsa da hakan cikin halin damuwa ya mike tsaye yana mata sallama murmushi ta sakar masa amman gida zaka wuce ko ? ya gyada mata kai kawai “to allah yayi maka albarka ka gaishe min da maryam anjima manu direba zai kawo maku abinci “to !kawai ya fad’a a takaice sannan yasa kai ya fice daga parlour’n massalacin ya nufa domin gabatar da sallar laasar .”


Hisham zaune akan kujera yana waya da nuzla “eh har yanzu ina office , allah kuwa da gaske nike amman bari nayi sallar laasar na tura miki babu mamaki ma idan na tashi aiki zanzo na gaki kafin na wuce gida , sosai kuwa ya fad’a yana murmushi kmr yana gabanta ,ahankali yaji ana Knocking din kofar office dinsa amman ya share yaki bada umarni shigowa ya cigaba da waya da nuzlah har kusan mintuna shabiyar sannan yace wa nuzla “bari zan kiraki nan da minti biyar acan bangaren nuzla cike da shagwaba tace “a’a ban yarda ba “okay to shikenan zakiji komai da zanyi “yana gama fadar haka ya bada umarni shigowa ga diyar aminin abbansa dake aiki akarkashinsa .”




Zakiya ta tura kofar office din ta shigo ahankali ta tsaya agabansa amman bai d’ago ya kalleta ba ya cigaba da wayar da yake .”a tsanake ta bude bakinta ta kira sunansa “hisha…yayi saurin d’aga mata hannu yana cewa alamun tayi shiru dan da yasan itace bazai bada umarnin shigowa ba “a’a abdull ne ya shigo akwai maganar da zamuyi dashi shiyasa nace ki bani minti biyar “okay naji da zarar na gama dashi zan kiraki ya katse kiran sannan ya kalli zakiya yace “yaya akayi ?sai data numfasa kana tace “akwai matsala fa “me ya faru “ya budurwa zata zauna ta dinga tayar maka da hankali haka?” nifa abokiyar aikinka ce kuma kusan yaruwarka wacce ko matarka tasan da zamana bata ta’ba nuna damuwarta ba sai wata can .”




“aa dakata zakiya banason haka matsayin nuzla dabam a wajena tana sama da kowacce mace a wajena ba wai wata bace kin fahimta ko ?“ kana nufin har matarka ?“eh bakiji nayi generalizing ba nace kowa , tafi kowace mace dan haka bana had’a maganarta data kowa ki kyaleni ke bani ma abinda ya kawoki ki bar min office menene ma ya kawoki “
? ”mr Ibrahim yace ka tura masa idan ka gama “tô naji zaki iya wucewa please ya fad’a yana nuna mata kofar fita da yatsun hannunsa .”




Ta juya ranta a matukar bace yace “idan kina shiga harkata zan iya sallamarki aiki , akwai wata mace ne bayan nuzla acikin zuciyata da zaki zo kina wasu surutan banza ?tsaki yaja ya fara duba file din data ajiye agabansa .”tana fita daga office din hisham office din abdull ta shiga tana kiran sunansa “abdull !! “menene ?ya tmbyeta tare da barin abinda yake ya dago ya zuba mata ido “wai me abokinka ya taka akan wannan banzar yarinyar nuzla ne da zai iya ciwa kowa mutunci akanta wai me tafi sauran mata ne ?kaga irin wulakanci da yayi min yanzu saboda suna yin waya daita “kinsan me ?ta girgiza masa kai alamun tana jinsa “hakuri zakiyi zakiya dan wannan yarinyar itace muradin ransa dan ko matarsa baya sakewa daita akan wannan yarinyar kuma bata son yana muamula da kowace mace “ai kuwa wallahi tayi kadan dan bata isa ta hanashi muamula da kowa ba .”




“Ita din me ? sannan akan me ?to sai dai idan a gidinta zai tare ko kuma ya cicibota ya dawo daita office dinsa inyaso duk abinda yake tana gani ko kuma ta dinga binshi duk inda za shi .”yayi murmushi yace “ko dai kina kishi daita ne naga duk kin damu ?”“kishi ?meye tsakanina da hisham da zanyi kishi akanshi bayan aiki da kuma dangantar dad dinsa da nawa ?”kawai dai wallahi naji ina tausayin matarsa ne yarinyar kirki ce ga hankali ga ladabi shine kawai nake tausaya mata saboda nasan duk lokacin daya auri wannan banzar yarinyar ina tausayawa rayuwar matarsa duk da nasan yarinyar nan bazata yarda ta auresa ba wata manufa gareta .”




“Me yasa kika fada haka ?ince guduwa tayi lokacin da zaayi aurensu dashi sannan yanzu ta dawo masa ai kasan akwai abinda take nufi dashi wallahi , wakilla haushi taji dan ya auri nana hauwa’u kawai ta dawo ta hanashi zaman lafiya da matarsa kuma tasan idan batayi amfani da karfin soyayyar da yake mata ba bazata yi galaba akanshi ba shi kuma dake qaramar kwakwaluwa ce dashi yake wani biye mata yarinyar daya kamata yaci ubanta laada waje “.
Abdull ya sake yin murmushi wanda dagani na takaici ne “ kinsa me ? kije kawai Kiyi aikinki zai fiyye miki amman hisham kam bai ji bai gani akan nuzla bancin nasan gidansu nuzla basa biye biye da ni kaina nace anyi masa wani abu ne “.




“gsky kam amman ni matarsa nake ji ka duba kaga ranar d muka je gidansa baka ga yanayinta ba kamar tana jin tsoronsa komai a dar dar take yi shi kuma ko kallon biyayyar da take masa baya yi sai ma wayar da yake da wannan banzar yarinyar ina ma ni ya samu da naci ubansu daga shi har ita “gsky nana hauwa’u bazata iya ba Ke dai zai fi kiyi abinda Ke gabanki sarkin shiga abinda babu ruwanta “kana ji ko abdull “dan allah Zakiya kije na gaji da mgnr hisham nayi masa mgn har na gaji idan zai canza ya canza idan bai zai canza ba tare dani allah zai wa hukunci ba daga haka bai sake cewa kala bata juya ta bar office din cike da takaici .”


Qarfe biyar daidai motocin ata suka shigo gidan yayinda maryam ke zaune a parlour’n kasa cikin tsananin tashin hankali tana waya da nana hauwa’u “wallahi sister duka fa kwanaki biyu ne kawai nayi acikin gidan nan amman ji nake tamkr a makabarta nike zagi kuwa acikin kwanakin nan sai dai kawai nace Alhamdulillah ,shi kawai baya ganin abubuwan da yake min kuskure ne shi kawai kanshi ya sani eh ko jiya ya sha yanzu haka ma cikin matsala nike dan daren jiya na kwashe kwalin sigarin na zubar a shara ashe da saura aciki kuma yace lallai sai na dawo masa da abunsa ,ni yanzu tashin hankalina na aika a siyo masa sigarin baa samo exactly irin wanda yake sha ba ….”




“Shiru tayi sakamakon turo kofar parlour’n da akayi idanunta data zubawa kofar suka sauka akanshi sanda yake qoqarin takuwa ,sosai ya dauki hankalinta koda yaushe fuskarsa tashi a daure take kallo daya yayi mata ya janye idanunshi akanta “sannu da zuwa” ta fad’a a matukar tsorace tana qoqarin mikewa ta bar parlour’n tun kafin ya soma cin ubanta , bai amsa ba yace “me na fad’a miki ?bana ce karki sake na dawo na ga wannan fuskar ba ? ya qara taku biyu taja baya da sauri “dan allah kayi hakuri ta fad’a cikin tsananin tashin hankali“.ina sigarina ?”






Mmn sudais


💗💗💗💗💗💗
MAR'ADAMS
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗




*AYSHA A BAGUDO*


WATTPAD @HAUESH
AREWABOOKS USERNAME
AYSHAABAGUDO
bismillahirrahmanirrahim


Wannan littafin na kudi ne mai bukatar karantashi byn na kammalashi zai biya 1000 ta wannan account number din 1438775094 Aishat abdullahi access idan an tura sai a turawa wannan 09136918331 alert domin tabbatar da an tura domin sauraron littafaina a tuntubi chaneel dina (Hausa bakwai ) a YouTube.




Page 8




A matukar razane maryam take kallonsa jikinta na wani irin rawa idanunta suka canza kala sakamakon hawayen data soma d'an taruwa acikin kwayar idanunta cikin tsananin fad'uwar gaba maryam tace "ga ..gashi can akan table sai dai ba'a samo exactly irin ..."sai kuma tayi shiru ta kasa qarasa maganarta dan tasan me karshen maganar tata zata janyo mata, ta tsura masa ido kawai tana cigaba da kallonsa hawaye na gangaro mata akan kuncinta ."




"exactly irin me ye ba'a samu ba ? yayi maganar a tsawace yana sake had'e fuska "ta runtse idanunta gam hawaye masu zafi suka biyo kuncinta "irin wanda kake sha né ba'a samo ba "me yasa ba'a samu irinsa ba ?"ya tambayeta yana tsareta da tsuma mmun idanunshi masu matukar firgitarwa "tayi shiru tana kallonsa hawaye na faman turereniyar zubo mata "nima ban....ban sani ba ?"ta fad'a a muryarta na rawa tana share hawayenta da hannunta d'aya tare da kai tafin hannunta daidai saitin zuciyarta dake beating very fast ."




Tsumammun idanunshi ya ware sosai akanta yaga yadda ta qara shiga tashin hankali wanda hakan Ke masa dadi, a duk lokacin daya ganta cikin damuwa yana jin sukuni aransa, wani abu ya had'iye mai d'aci a makoshinsa kafin ahankali ya motsa lip's dinsa da kyar "babu ruwana ki nemo min exactly irin sigarina shi nake bukata kuma a yau dan kinsan halina sai dai ki bawa wani labari ,ban ta'ba d'agawa kowa kafa ba kuma bazan fara akanki ba yana gama fad'ar haka ya juya a zafafe ya soma d'aga kafafunsa zai haye sama ."




jiki a sanyaye ta qara taku biyu tana wasa da yatsun hannunta tace "wallahi yaya Adam ban san yadda zanyi a samo maka irinsa ba sai dai kayi hakuri ka aika wanda ya saba zuwa inda yake siyo maka ko kuma kayi amfani da sauran na jiya ."wanda kika zubar a shara kike nufi ?ya juyo a fusace tare da fad'ar haka, taja baya da sauri tana gyad'a masa kai gabanta na dukan uku uku "you are very stupid ,ki nemo min ko kuma inci ubanki acikin gidan nan yau ."




"Ubana kuma !?"yes of course ubanki ko zaki rama ne da kika tsaya kina tambayata ?ta sauke numfashi tana girgiza masa kai "okay ki nemi min abata kuma irin wanda kika wulakanta min “cikin kasa da murya tace "ni dai gsky ban san yadda zanyi ba kai dadin me ma kake ji a shan sigari abinda zai cutar da kai ?”
”ni zaki fad'awa haka ? kanta ta gyad'a masa alamun Eh !to ai gsky ne me zakayi da wani sigari abinda yake saurin kashe mutun "are you out of your sense ?."




"ni kike fad'awa haka "? shiru tayi tana tunani amsar da zata bashi wanda kafin nan idanunta sun sake kawo hawaye tace "yanzu meye illar maganata bayan gsky na fad'a maka "?"Are you mad ?"da sauri ta girgiza masa kai alamun a'a "okay iskanci ne kenan yasa ina magana kina magana ?"ta sake girgiza masa kai idanunta na kawo ruwan hawaye domin dai gbdy a tsorace take dashi ,maganar ma allah ya sani dauriya ne kawai take yi da kuma son rage tsoronsa dake kunshe a zuciyarta ".




cikin rawar murya tace "am sorry"!da sauri yace "sorry for your self "amman dai kuma kasan shan sigari yana da matuqar illa sosai arayuwar d'an adam "so what? ina ruwanki da rayuwata ?gabanta taji yayi mummunar fad'uwa ta shiga girgiza masa kai hawaye na sake fita daga idanunta ."ahankali taga ya soma takowa zuwa inda take tsaye yana mata wani mugun kallo ."nan da nan jikinta ya fara rawa ganin idan ta tsaya kanta zata cuta yasa ta juya da sauri ta fad'a d'akin dake manne da parlour'n ta murd'a key ."ta jingina bayanta da kofar ta tsaya tana sauke numfashi.”






A zafafe ya qaraso jikin kofar ya tsaya tare da runtse idanushi kafin ya dunkule hannunsa ya kai wa kofar naushi yace "me yasa kika gudu baki tsaya ba kiga yadda zanyi dake shasha duwaf din banza kawai ?”
”wallahi wallahi da kin tsaya da sai na karya miki kafa sai dai uwarki ta haifi wata mai kama dake nonsense "muryarta a sanyaye tace "kayi hakuri dan allah bazan sake ba ."yana jin yadda take kuka take bashi hakuri tana tsaye kusan minti biyar dafe da saitin zuciyarta dake bugawa da sauri sauri , taji alamun tafiyarsa amman ta kasa fitowa har sai da minti biyar ta wuce bata sake jin motsinsa ba hakan ya tabbatar mata ya bar gurin .”




ta bud'e kofar ahankali ta fito tana maida numfashi tare da goge hawayenta ta hau sama, ahankali ta sanya kai cikin d'akinsa ta leka tsaye ta samesa ya bawa kofar baya hannuwansa hard'e a saman faffad'an qirjinsa sai huci yake fesarwa tmkr zakin daya nemi abincinsa ya rasa ,gefe guda kuma duk ilahirin gashin dake kwance a jikinsa sun mike tsabar bala'i ji tayi kamar taje ta rungume shi ta baya ta sake bashi hakuri ya sauko dan bata son ganin yana fushi most especially daita ."




Wani dogon tsaki yaja yana sauke hannuwansa ya rike kugunsa da hannu d'aya acikin ransa yace "wannan wace irin jaraba ce ?yarinya kamar mayya duk abinda zai mata bata damuwa ko ya zagi uwarta ya zagi ubanta duk a banza baya mata ciwo sai dai tayita bashi hakuri "ya fahimci mugun hakuri ne daita ,kuma shine dalilin da yasa mahaifiyarsa tayi masa sha'awar aurenta" tsaki yaja ya soma cire kayan jikinsa ya fad'a bathroom ya sakarwa kanshi ruwa ya fito ."




Bai sauya wasu kaya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login