Showing 117001 words to 120000 words out of 169868 words
Chapter 40 - MAR'ADAM'S BOOK 2 COMPLETE DOCUMENT by Aisha Bagudu .txt
mijin naki bai ɗaukeki da daraja ba, hatta komai ma dake cikin gidan mai amfani da mara amfani ya fiki muhimmanci agurinsa” maryam tayi shuru kawai tana kallon Ni'ima da sauraronta “wannan auren zumuncin da akayi muku gsky ke aka cuta”
Maryam ta karkata kai tana cigaba da kallon Ni'ima “haka kike gani?ai kinfi kowa sani wannan maimaci ne nayi miki amman kinsan ke aka cuta” “nifa ba cuceni ba ni'ima dan ina son yaya adam tun asali in takaice miki tun kafin mahaifiyarsa tayi tunanin haɗamu dan gsky da ban samesa ba da haƙurina zai gaza domin kuwa ciwon zuciya ne zai kamani”
“ke da Allah rabani da maganar wata shegiyar soyayya uwarsa tasan duk wannan cin kashin
da yake miki?” “tasan komai kuma tana iyakacin ƙoƙarinta, bata son duk wani abinda zai ɗaga min hankali duk abinda yayi muddin zata gani ko taji labari sai inda ƙarfinta ya ƙare” “dai-dai kenan idan ya ɗaga miki hankali ki dinga kirata ki ɗaga mata hankali, idan kuma tsoronsa ya hanaki aikatawa sai ki zauna da baƙin ciki” Ni'ima ta soma yafa gyalenta tana kallonta “zo mu jera sai mu rabu a titi” maryam ta gyara zaman mayafinta ta ɗauki wayarta tare da sakala hand bag suka nufi kofar fita daga parlour'n .
Mai gadi ya buɗe tafkeken get ɗin gidan motocin ATA suka nufo kofar a hankali zasu fita a dai-dai lokacin maryam da Ni'ima suka fito daga parlour suka ga motocinsa. “lah Ni'ima kinga bai tafi bama ashe, bari in tsaida shi basai naja mota ba kema ki shiga mu rage miki hanya” ta nufi motar da sauri tana ɗaga masa hannu “yaya Adam! Yaya Adam..!!” yana kallonta amman bai bada umarnin a tsaya ba motocin a guje suka fice daga gidan ."maryam ta tsaya tana kallon Ni'ima mai gadi ya rufe get din Ni'ima ta iso gaban maryam cikin fushi tana kallonta. “haba maryam! akan me zakiyi irin wannan zaman rashin darajar kamar wata baiwa?wallahi in baki ƙwaci ƴancinki ba ciwon zuciya ne zai kasheki a banza da wofi” cike da damuwa Maryam tace.“To ni yanzu ya zanyi? babu abinda ban masa ba tun daga Kan tsafta biyayya duk nayi kamar yadda na fad’a miki hatta taimako umma tasha aiko min akansa amman duk a banza ko kallon arziki ban ishesa ba” “na baki shawara?” da sauri maryam ta gyaɗa mata kai. “Kawo kunneki” maryam ta matso kusa daita sosai tayi mata raɗa a kunne nan take maryam ta girgiza kai “ke kan wannan mutumin fa baya jin komai gara kawai na cigaba da zama haka idan da rabon zai canza ina fatan haka .”
Tare suka jero inda motar maryam take a parking space ni’ima na cewa “ki samu lokaci ki shiga Zuru da kanki yarinyar wallahi sai yadda kikayi dashi duk wannan taurin kan sai kin nema kin rasa “akwai wata tukunya da umma tace zaa aiko min daga can , “eh nasan dashi ai zuwa wani sati zaa aiko zan sa a hado miki da wasu abubuwa ma ,”ta fad’a adaidai lokacin da suka shiga mota suka bar gidan niima na cigaba da magana “ai ina fad’a miki muddin kikayi masa amfani dashi zakiyi mamakin yadda zai rikice ai wallahi sam ya’yan zuru basu cancaci wulakanci a gidan miji ba mu dake juya maza son ranmu amman ace ke kin bigi a wulakance a gidan mini “wallahi ni’ima ni kaina abun na damuna kamar na tattara na bar gidan amman bazan iya ba darajan mami da kuma karfin soyayyarsa “masu aikin mami ne a sunkuye a gaban dinning suna jere food flask.
Mami ta fito daga kitchen Riƙe da tray me ɗauke da lemuka a hannunta ta nufo dinnig dasu.tabawa mai aikinta ta iso gabanta da sauri ta karɓa taje ta ajiye mami ta ɗauki air-frshner ta soma feshe falon sannan ta ɗan tsaya alamun sauraro, ta juyo ta kalli tabawa mai aikinta tabawa ta juyo ta kalleta sanda take ƙara gyara zaman kujerun. “Tabawa!” “Na'am mami” “naji tsayuwar mota ina zaton adamcy ne suka iso , hanzarta ki bawa sauran masu aiki umarni su ƙarasa gyara wajen su bar nan tun kafin ya ƙaraso”
ATA ya shigo cikin parlour'n da sallama mami ta amsa da “Amin wa'alaikas salam” ATA ya iso gaban mami ya rusuna yana gaisheta “sweetheart barka da rana” cikin sakin fuska mami tace. “barka da zuwa adamcy Nah ɗan albarka ya gida ya kuma ƙarfin jikin?” “Alhamdulillah” Mami tace. “ka ganmu muna ta shirin tarbanku kamar wasu baƙi ko?” ya miƙe yana kallon ɓangaren dining sannan ya zauna.
Yana cewa. “sweetheart da kanki kikayi komai?” “Ƙwarai kuwa, ni da tabawa muka shirya muku abinci sai sauran masu aiki da suka taimaka ” ATA yayi shiru kawai suna cikin magana suka jiyo sallamar zabiba ta karaɗe falon mami ta ɗago ta kalleta tana cewa. “Zabiba har kin ƙaraso?” Zabiba tace. “Eh mami na ƙaraso suma suna hanya yanzu muka gama waya dasu ina yini?” “lafiya lau zabiba ya yaran suke?” “suna lafiya suna gida tare da babansu khaira ce ta maƙale wai lallai sai ta biyoni taga hajiya mami nace ban zuwa daita tazo takurawa rayuwata” “ai wannan takwarartawa sai ahankali last time da kuka zo ta dameni da aunty girl”. mami ta faɗa cike da farinciki tana murmushi .”
muryar zabiba cike da tsoro tace. “yaya ina yini?” bai ce mata komai ba dan tunda ta shigo ya maida fuskarsa wani ɓangare. Mami tace. “adamcy ana gaisheka” a taƙaice yace. “Lafiya” ahankali ta samu waje kusa dashi ta zauna “yaya Adam!” yana jinta yayi mata banza ahankali tace. “please yaya kayi hakuri ka yafe mana wallahi bazamu sake ba” tsaki yaja yace. “ai daman haka kukeyi idan kuka ɓatawa mutun rai kuyita nacin ban haƙuri kamar bazaku sake ba amman da zaran mutun ya haƙura ƙoƙarin aikata wani kuke yi dan haka gara ku riƙe haƙurinku dan ni tuni na cireku a rayuwata” nan da nan zabiba ta shiga aikin nan wato bashi hakuri da kuka amman ko ajikinsa girgiza kafarsa ɗaya kawai yake zabiba kuwa kuka take kamar ranta zai fita ahaka sauran ƴan'uwanta suka shigo suka isketa gabaɗayasu suka sakashi a tsakiyarsu suna masa magana amma ko motsa laɓɓansa bai yi ba. “ku rabu dashi Ke kuma zabiba ki daina asarar hawayenki kuna zaune zai huce” cewar Mami dogon numfashi ya sauke yana taɓe baki.aransa yace “ai kuwa zan baku mamaki .”
Nana hauwa'u tace. “mami ina auntynmu take?” nan da nan mami ta kallesa sai lokacin kanta ya kawo wuta “Ina Maryam ɗin da nace kazo min daita Ko tana cikin mota ne?” ATA ya ɗan sosa ƙeya “na barota a gida a cewarta tayi baƙuwa” da mamaki mami ta tsura masa ido “ka barota a gida adamcy acewarta tayi baƙuwa kuma?”eh !haka tace idan ta gama zata taho don bazan iya zaman jiranta ba, kuma wallahi sweetheart kiyi ma yarinyar congret warning dan kwanakin nan wasu ƴan iska qawayenta take tara min a gida alhalin ni gidana ba dan ƴan iska na ginashi ba” cikin fushi mami tace. “adamcy kasan me kake faɗa kuwa? Ƴar tawa da take aurenka zaka cewa Ƴar iska tana tara ƴan iska ?” “ai sweetheart wannan yarinyar ta wuce ƴar iska a gaban ita wanna Ƴar iska ƙawartata take ce min wa..” hannu mami ta ɗaga masa cikin fushi ta fara magana. “saurara! bana son jin komai daga bakinka, ka tashi yanzu ka koma gidan ka ɗaukota tun rai na bai gama ɓaci ba...” ATA ya gyara zamansa cikin damuwa yana kallonta kafin ahankali ya motsa laɓɓansa “haba sweetheart me yasa kike nuna mini wariyar launin fata a tsakanina da yarinyar nan ? Ni fa kika haifa ba ita ba” cikin fushi tace.“dan kana ɗan cikina sai in goyi bayan riƙon sakainar kashin da kake mata?” ATA yace. “To ai bata gama shiryawa bane tana hira da Ƴar iskar ƙawarta”
“Yanzu ka tashi ka koma gidan ka jirata har sai ta gama kimtsawa idan ma sai ta sallami ƙawarta ne ka jira sannan kuzo min tare yanda nace” mami bata kai ga rufe bakinta ba Ni'ima da maryam suka shigo cikin falon Ni'ima na riƙe da Maryam a kafaɗarta wanda goshinta yake a fashe yana ɗigar da jini, mayafinta da ɗankwalinta yana a hannun Ni'ima nana hauwa'u ce ta fara lura dasu ta soma salati tare da faɗin.“lnnalilahi wa'inna ilaihir raji'un!”jinj !
Nan mami da sauran ƴaƴanta suka juya da sauri suka kalli maryam “Subhanallahi!” mami ta furta a ruɗe tana kallon ATA “Adamcy kaga abinda ka janyo ko? don me ka barta a gida Kashe min ƴa zakayi?”Adamcy ya kalli mami a natse ya juya ya kalli inda maryam take gbɗy ya kasa magana juwa ne ya ɗibi maryam ta sulale ƙasa a sume, nana hauwa'u ta ƙarasa da gudu suka tallafo ta ita da Ni'ima
mami da ƴaƴanta suka nufi wajenta da sauri suna jijigata jikin mami na rawa tace. “ku kwantar da ita akan kujera shahida taimaka ki duba min ita” duk mami ta ruɗe shi kuwa gogan ko ajikinsa dan haka nan yaji ajikinsa suman ƙarya tayi.Mami banzo da kayan aiki na ba, a kira doctor nasir” da sauri mami tace. “Auta maza shiga ɗakina ki ɗauko min wayata” da sauri nana hauwa'u ta nufi ɗakin mami ta ɗauko wayar tana niman layinsa yayinda aunty shahida ke bata taimakon gaugauwa shi kuwa ATA mikewa tsaye yayi yana jan tsaki ya ra’ba ta gefensu ya fice yama bar gidan gbdy .”
Bayan awa uku
Maryam na zaune a kujera tana sauke numfashi ansa auduga da plasta an rufe raunin goshinta yayinda mami ke zaune a gefenta riƙe da hannunta Dr.Nasir Ya miƙe tsaye sanye da coat da farin gilashi hannunsa riƙe da first-aid box ya miƙawa mami Ƙaramar takardan magunguna “hajiya ga wannan takardar magungunan da zatayi amfani dashi ne insha Allah da zarar tasha a hankali ƙarfin jikinta zai dawo baboda naga Allah ya taƙaita babu wani babban rauni da zai sa muyi admitting ɗinta asibiti ko kuma yiwa cikin jikinta illa Wannan treating ɗin ma da nayi mata is okay for her” mami ta jinjina kai tana faɗaɗa fuska cikin farinciki tace. “doctor kace ciki gareta?” Doctor Nasir yace. “ƙwarai kuwa hajiya in sha allahu ranar monday akawota hospital domin yi mata scan dan mu san iya adadin kwanakinsa” “masha Allah Dr.Nasir nagode sosai ka min albishiri mai daɗi” na dade ba’a fada min maganar data saka zuciyata farinciki ba dr nasir ya kalli maryam da murmushi a fuskarsa “to hajiya Mar-Adam zance ko Mrs Adam? Allah ya bada lafiya” maryam tayi murmushin ƙarfin hali tana kallonsa zuciyarta na rawa dan tun daya fara maganar ciki ta shiga damuwa mai tsananin dan ita kanta tana zargin ciki gareta duba da watan ta na uku kenan bata ga period ɗinta ba. “Allah ya sauwaƙe ya bada lafiya” da “Amin” ta amsa cikin ƙarfin hali.
Dr.Nasir Ya juya ya fita daga gidan farinciki agurin mami da ƴaƴanta ba'a magana kowa ka kalli fuskarsa kwance yake da annurin farinciki gabaɗayansu murna suke har sun kasa ɓoye murnarsu mami ta riƙo hannun maryam cikin nata tana kallonta cike da kulawa tace “ke kuwa Maryam garin ya akayi kika samu rauni?” maraym tace. “walalhi mami muna qoqarin karya kwana ne akayi akasi wani me mashin ya kwaso a guje, ganin kamar zai yo kan motar ne sai ido na ya rufe daga hk ni dai bansan yadda akayi ba kaina ya bugu da stearing” mami tace. “yanzu banda Allah ya taƙaita ai da abun ya wuce haka ga ciki ajikinki” .nana hauwa'u tace. “Alhamdulillah da Allah ya taƙaita” cike da murna ta ƙarasa maganar. “ai duk adamcy ne ya janyo da yanzu wani abu ya samu cikin jikinta me za'ace?” nan da nan mami ta shiga zuba wa Adam faɗa da baya nan akan me yasa bai jira Maryam ta gama shiryawa sun fito tare ba? cikin raunin murya “daman ai duk shi yaja mana wannan matsalar, wallahi mami in kinga abubuwan da yayi mata agabana sai kin tausaya mata” cewar ni'ima “kamar wata baiwa ya ajiye a gidansa ba matarsa ba” mami ta tsurawa Ni'ima ido tana kallon fuskarta kar dai itace Ƴar iskar ƙawarta da yake faɗa? “ko abinci ta girka sai yaga dama yake ci, komai tayi bata masa gwaninta, sai yayi tayi mata tsawa yana hantarar ta wannan wani irin aure ne?” mrym tayi saurin take ƙafar Ni'ima “kinga malama ki bari ayi magana yanzu an daina auren wahala idan bazai iya ba ya sallame ki, ki kama gabanki idan kin haife abinda yake cikinki ki kawo masa ki dire ai namiji goma ba uba goma bane " Hjy zulai da mamaki take cigaba da kallon Ni'ima tana tunanin in da tasan fuskar “haba Ni'ima wai meye haka ne ?dan Allah kizo ki wuce gida dan Allah nace miki ina son rabuwa da mijina ne? koni na faɗa miki yana min duk abinda kika furta “au karesa zakiyi saboda baki da hankali ai duk abinda idanuna suka gane min kamar na faɗawa ummah na gama” tana gama faɗar haka ta juya cikin tsananin fushi.”
Cike da ɓacin rai nana hauwa'u tace. “sister wannan fa wacece ita? Jiki a sanyaye ” Maryam tace. “ɗiyar sister ɗin ummammu ce “kai shiyasa nake ta mata kallon sani kar dai ɗiyar umaima ce?” Maryam ta gyaɗa mata kai alamun eh. “shine zata dinga faɗar magana akan yaya? kuma ai kice kika bata wannan damar” “kamar ya sister?” maryam ta faɗa jikinta na ɗan rawa “idan baki faɗa mata komai akanshi ba ya'akayi tasan irin zaman da kuke yi?” aunty shahida ta faɗa ranta a ɓace “karfa kiga duk muna bayanki ki ɗauka bama son shi ne, adam rayuwarmu ne kema kuma kinsan da haka Maryam ta runtse idanunta sai ga hawaye masu zafi cike da tashin hankali take jin yadda numfashinta ke sauka da ƙarfi. shi kenan Ni'ima ta haɗa mata bala'i “duk muna bayanki sakamakon irin tsanar da yake nuna miki da kuma irin ƙaunar da mahaifiyarmu ke miki” “ dan Allah aunty shahida kuyi hakuri ba'a bakina taji komai ba ummace ta faɗa amman..” katseta aunty khadija tayi ta hanyar cewa. “ita umman taki meye amfanin faɗawa mutane? mun sani sarai adam bai kyautawa amman kuma meye abun faɗawa mutane anan? mufa mun sani sarai ummanki bata ƙaunar danuwanmu, amman mu dai-dai rana ɗaya mun taɓa sauke haushin haka akanki ? kullum yanda rayuwarki zata samu cigaba a gidansa muke" .
Maryam tasa kuka cikin tsananin damuwa .”
“dan Allah ya isa karku saka min yarinya gaba da bala'i dame zataji ?da maseefar ɗan'uwanku ko da naku sai kun harbe mata zuciya ta mutu kowa ya huta ? kuma ai bai barku ba bare ku shigar masa” kuma karya aka fada akanshi ?halinsa ne fa ?“koma dai menene mami bazamu lamunta ba kuma kar mu sake jin taje gidanki daman shima yace ayiwa ƴar iskar ƙawarki congrent warning karta sake shigar masa gida ilai kuwa ashe ƴar iskar ce ai duk abinda kika ji yaya yayi mgn akai mai mahimanci ne” cewar zabiba nana hauwa'u kam tun maganar farko bata sake cewa komai ba, atare suka miƙe aunty shahida aunty Khadija da zabiba sukai ma mami sallama tayi masu addu'a tare da yi masu fatan alkhairi nana hauwa'u bata sake cewa komai ba mami ta laluɓo wayarta daga gefenta ta ɗauka ta soma ƙoƙarin kiran ATA “Bari ina zuwa na kirasa dani yake zancen wato cin mutunci da tozarci har agaban mutane?" maraym tayi saurin riko hannun mami tana kuka tace. “dan Allah mami ki rufa min asiri kar kiyi masa magana yanzu idan ma son samu ne karki ce masa komai” mami ta ƙara wayar a kunnenta tana cewa. “rabu dani gara na faɗa masa halin da'ake ciki tun kafin baƙin cikinsa yasa a rasa cikin jikinki .”
alokacin da mami take neman layinsa yana zaune acikin wani ƙayataccen gida me ɗauke da komai na manyan masu kuɗi da manyan ƴan boko gidan kamar aljanar duniya tsabar haɗuwa wannan gidan bana kowa bane face gidan ammar ATA na zaune a gaban ammar suna tautaunawa akan kasuwanci kiran mami ya shigo ya ɗauki wayar ya manna a kunne “hello kana ina?“ina gidan ammar” abinda ya faɗa kenan yana lumshe ido “to in ka fito kazo gida da gaggawa ina son ganinka” katse ta yayi da faɗin. “lafiya sweetheart?” Mami tace. “ita ta kawo haka bazaka ma tambayi Jikin maryam ba kaji halin da take ciki? ka bar ƴar mutane cikin wani hali gashi..” tun kafin ta faɗi abinda take son faɗa taji ya katse wayar “Hello.. Hello... adamcy” tuni ya sauke wayar daga kunnensa ya kalli screen ɗin sannan ya sauya kujerar sa yana dafe goshinsa da hannuwansa duka ammar ya dawo gabansa ya fuskancesa yan faɗin. “lafiya ?waya kiraka ?ya ɗaga maka hankali gashi bamu gama tattaunawarmu ba?” “sweetheart ce ni dai allah yasa karsu kashe ni akan ƴar iskar yarinyar nan..” “yanzu me ya faru kuma?” “ban sani ba ni dai na barsu wai ta suma” “wa kenan ta suma?” shiru yayi na second biyu sannan ya ɗago kanshi ya kalli ammar “Sweetheart ke son ganina amma zamu iya ƙarasa maganar Okay, Sai dai kuma ya kamata a ce ka ɗau tsanttsauran mataki akan sauran yaran daka faɗa min saboda har kullum