Showing 30001 words to 33000 words out of 106121 words

Chapter 11 - kanin Ajali Book Complete by Zee Makawa .txt

01 Jan 2025

7477

gama masu kwana biyu tare da gama sayen duk wani abinda nake bukata na juya zuwa gida.
Sai dai da farko naji kunyan yin talla don bantaba ba a rayuwana sai gani dauke da kaya buuuu a kaina ina shiga gidajen kauyokan mu dama ke waye ina tallatawa.
Allah a cikin ikon sa yasa ma sana,an tawa albarka sai gashi dan lokaci kadan nayi suna sosai don bayan kuloli har turamay nake sayarwa kuma.
Cikin dan lokaci kan kani nayi arziki da bai faduwa da wanan sana,an da nakeyi inda baba kabiru ya samu labari ya zo takanas ta kano har kauyen ya gana da umma akan barina da sukayi ina wanan ssna,an kamar mara gata a gari.
Sai umma tace ni naga zan iya banda rashin gata abinda na zabawa kaina ke nan bai min magana ba ya koma da bacin rai don mahaifiyar su, ta hanashi yi min fada.
Kudi na hada yakai dubu dari biyu jamil yazo gurina muna hira nake bashi labari yake fadin sai in samu wani sana an in dora a kai da riban nawa.
Ya dan jima gurina muna hira daya koma gida ya kasa zaune ya kasa kwance yana tunanen wanan kudin dana bashi labarin na mallaka a yanzu.
Washe gari bayan la,asar na dawo daga talla sai gashi nayi mamakin zuwan shi don ba lokacin zuwan shi bane kenan.
Bayan mun gaisa ne yake fadin dama wani shawarane yazo min dashi shine dalilin ganin shi da nayi a wanan lokacin.
Nace wani shawara ke nan yace eh gani yayi yanzu dai shi baida wani sana,an da yake yi mai zai hana shima ya fara sana,a da zaiyi saurin kawo muna kudi don mu samu mu fara shirin auren mu nan da dan lokaci kadan.
Don ni gashi sana,an ya karbeni da farawa na tara wanan uban kudin idan mun hada hannu sai abin yayi auki mu kashe mu birne ba wanda yasan tsakanin mu.
Nace ba tare da nayi wani tunane ba kana ganin haka zai fi muna yace kwarai kuwa don karuwan mune gaba daya.
Nace yanzu kai may kake ganin zakayi wanda zamu samu karuwa haka da sauri ya gyara tsayuwa da kyau yace dani shawaran dana yanke shine in dinga shiga birni ina sayo mai na fetur da gas ina shigowa dashi nan kinga babu mai wanan sana,an ai anan ko ga kuma masaya na dayawa .
Nace wanan shawaran yayi daidai gaskiya kaga a dan lokaci kankani zamu samu mu hada abinda muke so ke na yace shi ya gani shima.
Batare da jin wani darrr ba nace ya je da dare idan yazo zan fito mai da kudin don yanzu idon mutane yayi yawa a kan mu.
Ya gama min dadin bakin shi daya iya ya na shiga gida don jamil a gurin iya dadin baki baida tsara a kauyen mu nan da jin dadi na na shiga gida.
Sai ga umma na gyaran gurin da take kiyon awakanta ta dago tana fadin yanzu muka gama maganan ki da babakin yushau nake fada mai riban da kika samu da sana,an ki .
Shine ya kawo shawaran mai zai hana a sayo maki shanu a turke maki har lokacin da dabbobi zasuyi tsada a sayar nace ya bari ki shigo muyi shawara dake.
Fuska na bata tare da fadin kash umma baki fada min wanan maganan da wuri ba yanzu fitan nan da nayi har na bada sakon a saro min kaya don ni ba zan samu zuwa ba wanan satin da kaina.
Kuma gashi har mai sakon ya wuce ko fuska ta sauya tare da fadin Allah yasa haka shine alheri nace amin nayi saurin wuce guri don naga kamar bata yarda da magana ba a lokacin.
Don idan zan sari kaya da kaina nake zuwa in sari duk abinda nake so in dawo don ko gidan baba kabiru sai inyi shiga goma ban leka su ba duk ko da cewa tan uwana suna gidan.
Sai idan naga dama nakan dan leka su a gurguje in fito duk zuwa da zanyi sai anty tayi min korafin yadda na mayar da kaina wata gaja saboda da neman duniya ina karamar yarinya dani haka.
Takan ce arziki na Allah ne ko nayi ko banyi ba idan lokacin arzikina yazo Allah zai bani ne gama mu da kudin mahaifin mu ake saka ran fitowan shi a ko wani lokaci zamu iya samun abin mu.
Wanan fadan da takan min nakan ji zafin shi don ina fanin tana min hassada ga samun da taga inayi ne a yanzu ga zugin Jamil dake shiga kaina kan in raba yan uwana da can din ma gurin su anty din.
Ga maganganun da wasu dangin mu yan hana ruwa gudu da sukan min kan dukiyan mahaifin mu wai su baba kabiru sun karbe sun cinye su da iyalin su.
Maganan yanzu da nasan kudi sosai ya zauna min a raina sai nake ganin haka din ne don su ko yaushe yanzu a cikin wadatata suke don basu rashi sam.
Dare yayi jamil yazo na fito da kudin zuwa gurin shi muna gaisawa yake fadin to yaya ina can ina Allah Allah kar gimbiyar tawa ta canza shawara don nasan idan umma ta sani zancen ta baci.
Nayi murmushi tare da fadin ina zan bari umma ta san wanan zancen kaiko sai dai ina shiga dazun ta tare ni da zancen wai in kawo kudin a sawo min saniya da kudin.
Da sauri yace sa may injin baki bata ba dai nace gasu tare dani yanzun haka ban yarda na bata ba don karya nayi mata kan cewa nabada sakon su a saro min kaya ai.
Yayi wani irin shu,umin dariya tare da fadin da kyau ta wurina ita umma may tasani kan kudi yanzu su burin su ke nan idan mutum ya dan samu kudi ace wai yasai abin kiwo dashi.
Nace ai ni ba zan yarda da wanan shawaran nata ba ga kudi ina ganin inda zamu samu karuwa wani zancen kiwo ake yanzu kuma da za a zo a girke a gida karshen tama ba wani riba a ciki.
Na kawo kudin dana kulle a cikin bakin leda na mika mai yana rawan jiki ya karba tare da fadin gobe asubanci zanyi don in samu in dawo da wuri kin ga har rumfa na kafa dazun bayan rabuwan mu dake inda zan fara sana,an tawa.
Bai dade ba yace zai tafi don ya samu barci issashe don asubancin da zaiyi a gobe din mukayi sallama dashi ya tafi na koma ciki cike da murnan wanan shawaran da jamil din ya kawo muna.
Don ina ganin zai ma fini samun riba a yadda ake cinikin man fetur da gas a kauyu kan mu don masu noman rani dake amfani da injin da sauran abubuwan bukata don rashin wutan lantarki da muke dashi a garin.
Washe gari sabo da murna ban fita talla ba barci na nayi sosai a gida sai zuwa sha daya da umma ta jini shiru ne ta leko dakin mu tana fadin.
Yar kabiru yau nace ba fita tallan kayan ne ko hutu kikeyi ne haka na bude idona da kyar tare da fadin umma yau hutu nake yi don ba wasu kaya da yawa a tare dani sosai.
Takai dubanta gurin da nake aje kayan tana fadin lalaikan kaya sun fada sosai wallahi kila zuwa gobe sakon ki ya iso ai kinga sai ki fita da tushe.
Sai zuwa a zahar na fito na debi ruwa na watsa ma jikina na nemi abinda zanci don tun safe ban ci wani abin kirki a cikina ba don dauki da nakeyi jira kawai nakeyi inji ance ga jamil can ya bude rumfar shi ai.
Sai dai har yamma banji komai ba yasa na dan fito na fita nabi ta wurin har lijacin ba jamil babu labarin shi a garin sai zuwa gab da magariba ne nake jin labari wai an tare jamil a hanya ko may ko may ban karasa jin maganan ba don faduwan da gabana yayi a lokacin.
Fita nayi a gagauce don in tabbatar da zancen da nake ji nan nake ganin mutane gungu gungu kin san abu ga kauye basu iya samun magana ba.
Yana kuka shabe shabe wai an tare shi a hanyan shi na zuwa birni sayan mai an kwace kudin an mashi dukan tsiya ko mashin din don sunga tsofo ne suka barshi dashi don ko sun dauka basu dauki komai ba don wahalanta.
Jikina yayi sanyi nadai gode ma Allah da suka barmin shi da rai suka tsaya ga kudin kawai basu taba lafiyan shi ba sai dai ban yarda na nuna wani abinda zai kara tayar mashi da hankali ba a wanda yake ciki.
Sai da dare muka samu kebewa dashi yake ban labarin abinda ya samay shi din inda hankalina yayi matukar tashi sosai na daiyi wa Allah godiya da ya dawo min dashi lafiya a lokacin.
Satin shi daya sai gashi yazo min wai zai yi tafiya wani abokin baban shi yaji labarin abinda ya samay shi yace yazo ya taimaka mashi.
Nayi murnan jin hakan sosai mukai sallama ya tafi akan washe gari zai tafi amsa kiran abokin mahaifin nasa a can birni.
Abinda ban sani ba ashe kudina zai shiga birni yasha garalin shi dasu don abinda ya faru yana barin yankin kauyen mu da jarkokin daya dauka na sawo mai na bat da kama dayayi ya watsar dasu a hanya a cikin jeji.
Ya shiga gari ya yi sayayan yadudukan shi na maza dasu takalma da sauran abin da yake da burin bukata a rayuwan shi.
Sune ya koma ta karbi dinkunan shi ya karasa kashe kudin daya saura a hannun shi don rashin tausayi da imani da bai dashi.
Nabi ruwa nabi iska na bi rana da sanyi na samo su rana daya jamil ya zo yaci amana ta ranan ko barci ban yi ba sai faman sakawa da kwancewa nake a raina.
Ina kallon kayan sana,ata da dan abinda ya rage min a ciki wanda basu taka kara sin karya ba a lokacin wanan abin har zazzabin dole ya ja min sai da nayi jinya akan hakan.
Bayan kamar sati uku ina dan bubugawa har tiren sana,an ya dan fara dagowa kaya ya fara samuwa min ga kuma kewan shi dake damuna a lokacin don tunda ya tafi ban samu labarin shi ba.
Kwatsam sai gashi ya dawo garin kowa sai da ya girgiza da ganin canzawan da yayi a dan kankanin lokaci ya murje yayi kiba ga shiga ta alfarma da yakeyi kamar ba dan kauyen mu ba.
Ban dai san inda umma taji rabarin ai nice na bashi kudin da yake karyan sun zube ba sai ji nayi tana fada tana fadin dama wanda baiji bari ba yaji hoho gashi yanzu ya fara nuna maki irin gidan su mayaudara.
Na fada maki ki rabu da yaron nan ba dan arziki bane da yake ke mai taurin kan tsiya ne kika dauki kudi kika bashi ya shiga birni yasha garalin shi dashi.
Yar nan kina arziki kuwa da wanan yaron da kika lakanta dama na fada maki ko mutuwa nayi sai na taso maku fatalwa idan kika ce wanan shegen yaron zaki nacewa.
Yanzun dai ga magana ta nan ya fara fitowa fili ai ya yaudare ki ya raba ki da komai naki sai kamay kamay da ya barki kina yi a gari yanzu.
Gabana ne ki faduwa don jin abinda umma take fada sai dai ni yace min abokin mahaifin shi ne ta bashi kudi ai yace ya sai kaya ya kuma koma karatu idan yana son ci gaba.
Sai dai yaga ni banci gababa saboda shi ta yaya zai tafi ya barni a cikin wani hali ire iren dadin bakin da yai min ke nan lokacin daya dawo garin na gashi a cikin wadatan da ya dawo dashi.
Na kasa hakkuri da dare daya zo sai dana fito mai da wanan maganan da umma tayi min ya dan yi shiru kafin ya hau fada yana fadin .
Kai mutane basu son suga mutun ya samu karuwa yanzu, yazun kuma sherin da aka lakakamin ke nan shiyasa sai da na nunama baba sabo cewa ya bani kudin inzo in rage maki hasaran da mukayi.
Amma ya nuna min ba haka ba yace in har kina sona tsakani da Allah aike ba zaki yarda da hakan ba a tsakanin mu.
Jin wanan maganan ne yasa jikina yayi sanyi na kara yarda dashi hundred pacent naji ina son shi sosai a raina na watsar da maganan umma da na hau da farko.
Yanzu bini bini Jamil sai yace yayi birni idan yaje sai ya share makonni a can yana sheke ayar shi kafin ya dawo gari duk wanan baisa naga laifin a raina ko kadan.
Sai ma nake ganin na faso gari ai ina da saurayin da duk garin mu ba mai irin sa a garin kamar ni a yanzu mutane suna ganan min illar cutar da yake da buri a kaina wanda ni ban taba hango hakan ba.
Gashi duk zuwan da zaiyi gurina sai ya fito min da zancen kudin mu na gado wanda ni ban kawo komai ga hakan sai ganin nuna damuwan shi ne da kulawa a kan mu yakeyi.
Sannu a hankali mutanen dake ara min kudi ina bunkasa sana,a ta suka fara janye kudin su a gurina sai sana, an ya koma min gashi na yika nakeyi a yanzu.
Ga kuma yan canjin da yake karbe min daga yace ya tashi bai da ko kobon da zai kashe sai ya kawo min wani lalura can ya aza min dole in lale kudin in bashi ya shige birni yaja garalin shi dasu.




ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
5/18/21, 11:53 PM - 🤔🤔🤔: 🙆🏼‍♂️ KANIN AJALI 🙆🏼‍♂️




1️⃣2️⃣


ZAINAB IDRIS MAKAWA




Wanan yawan maganan da umma ke ta yada min a gida tare da korafi ga kuma wanda na karbi kudin a hannun su na dan kara ina juyawa sun sakani a gaba akan in basu kudin su.
Sai nayi shawaran zuwa birni gidan baba kabiru ko zan samu sauki a raina a ranan da nazo ban samu baba a gida yayi tafiya zuwa headquater jahar mu don halartan wani taro da zasuyi a can.
Na samu taro na mutunci kamar yadda suka saba min idan nazo na kebe da kanne na ina tambayan lafiyan su da yanayin zaman su a gidan inda suka nuna min basu cikin wani damuwa.
Da dare ne muna hira anty ta sako min zancen kudin dana ba wa jamil ya ce ya bace din take min fada akan hakan zafi naji sosai a raina da sukaji wanan maganan.
Haka ya hasalani na rufe ido nayi mata tujaran da sai da ta kwanmace batayi min maganan ba don komawa nayi kamar wata zarara na dora hannu a kai na dinga yanka masu ihu a gida har makwabta sai da suka shigo tambayan ko lafiya.
Ina fadin don anga iyayyen mu basu da raine ake muna wanan nuna bambanci haka komai nayi sai ace banyi daidai ba a rayuwana ranan dai ba karamin tujara nayiwa wanan matar mai kainan mu ba da zuciya daya akan dan maganan gyara kayan ka kawai da tayi min.
Don duk abinda zai bata min jamil bani kaunan shi a lokacin a raina sai nake ganin zata iya tunzura baba kabiru wanda nake da hope akan shi zai aura min jamil mu zauna lafiya a lokacin.
Sai daga baya ne naji kunyan abinda na aikata mata din don washe gari bata dauke ni da komai a ranta ba yadda na zata zata fita batun mu.
Wanan abin da nayi mata ya dawo yana damuna har baba ya dawo na dauka zata fada mai sai banji yai min maganan komai ba.
Har na gama kwanakin da zan masu don ban iya zama a inda babu masoyi na a lokacin na tattara na koma kauyen inda nake jin dadin rayuwa kowa na zuba min ido ina dauka sona suke a hakan da suke min.
Zaman na kauye a lokacin dai gashi nan dai ne a gare ni don yanzu ban wani sana,an kwarai don duk ya cinye min jarin da nake dashi wanda ni a lokacin ban dauki hakan komai ba a rayuwa na.
Zaman hakana ga maganganu suna zuwa wa baba kabiru a kaina don har ya kai yanzu ina zuwa dakin jamil muna hira a can wanda hakan a kauye wani abin magana ne sosai koma birni ne wace duk ta san kanta da mutuncin kanta ba zata aikata hakan ba.
Haka yasa baba kabiru ya shiga nema min addmition na nursing school don kokarin da nake dashi burin shi shine mu zama wani abu a rayuwan mu da zamu iya rike kan mu a gaba.
Alhamdullahi an sama min addimition din baba ya saya min komai da zan tafi inda ya aika min kwantsam in taso tafiya makarantana ya tashi.
Hankalina ya tashi da jin wanan maganan don ban taba tsanmanin hakan ba don ni burina shine muyi aure da jamil ko zan huta da kalubalin rayuwan da nake fuskanta a yanzu.
Sai ga zancen tafiya ya taso min inda jamil ya zugani sosai kan shi sam bai yarda da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login