Showing 57001 words to 60000 words out of 106121 words

Chapter 20 - kanin Ajali Book Complete by Zee Makawa .txt

Advertisement

01 Jan 2025

8069

an samo sabon kaset ban zuwa ko ina kallon ina dakina zaune.
Shiyasa na matsa na sai wanan dan tv na hannu wanda ma bai kai nawa dana zo dashi gidan ba wanda baba kabiru suka saya min a lokacin aure na.
Kowa taji zancen kudina sun kare sai yayi mamaki sosai don abin akwai mamaki gaskiya don ba a gani a dakina ba da jikina ba inda ya nuna na more ma kudin ko kadan.
Muna a haka ne rikici na da uwar mijina yaki ci yaki karewa a tsakanin mu ga Jamil ya matsa min akan shifa zaman su a gidan damu ta ishe shi yanzu don suna hanashi walawa a gida.
Haka yasa na fara daure mata fuska ina mata abinda ban mata a da can baya yanzu hankalin ta ya tashi har yakai ga taje ta nemi wani gida don su kama haya su koma ciki.
Ina murna zamu rabu da kaya idan sun tashi wanda ban hango illan yin hakan da nai masu ba wanda da sunana suka tashi daga gidan bada sunan dan su Jamil ba.
Don ni sukace ina masu wulakanci tunda ni yake izawa inyi mata rashin mutunci a fili shiko yana nokewa kamar bai sani ba.
Yan uwana kaf sun dauke kafan su da gidan mu yanzu sun mayar da hankalin su gurin iyayye su sun ware mu inda muma muka kara dinkwa da junan mu a tsakanin mu.
Jamil ya bamu shawara muyi dabara karbe kudade su Baffa dake hannun baba kabir da sunan ajiya kada azo a nema a samu babu su a cewan sa wai gwano baya jin warin kanshi ashe.
Ni ga nawa tun ba akai ko ina ba duk ya halaka min su sai kamay kamay nake wa mutane da yan hayan gidan mu suka fahinci komai ya kare min sai habaici ya tashi tsakani na dasu.
Wata daya da muke shiri ne take fada min gaskiya ta kebe dani tana fadin kinyi wauta hadiza may yakaiki bawa namiji kudi irin haka masu yawa.
Na miji fa baida tabbas ko kadan baki gudun nan gaba ya karo maki kishiya da kudin naki may zaki fada nan dai tayi min nasiha sosai wanda yasa ni natsuwa.
Ta nuna min abinda mukai wa kanin mahaifin mu mai kaunar mu bamuyi daidai ba wallahi gara inje in nemi gafaran shi kan abinda mukai mai mu koma daidai da iyalin shi dake fushi damu.
Don ko wane ma haka ya faru dashi fushi zai dauka dakai tace da bakin ki kike fada min irin yadda yake nuna maku banbanci da iyalinshi har yau basu taba nuna jin zafin hakan ba don may zaku saka mai da hakan akan kudi ku ?
Ta dai yi min nasihs sosai a matsayin ta na mai kaunata a gidan kuma ba laifi nayi kamar yadda tace din inyi don naje mun sasanta da yan gidan mu an fahinci juna don sun gane muna amfani ne da zugin mazajen mu.
Don kanwata har ta fini daukan zugin mijin ta yanzu nake gani do ko ni banjin dadin ta bansan kuma irin yanayin da suke ciki da mijin ta ba a gidan su.
Don ko naje ban gane komai haka nake juyowa in dawo don bata bari in fahinci komai sai dai na gane itama din duk abinda ya kwaso ni shiya kwaso ta yanzu don babu kudin a hannun ta kuma.
Itama mijin ta ya kashe sunyi wani abinda kudin tunda kudin nata a hannun mijin nata suka gashi da daure fuska ga kowa bai sakin fuska balle ya bada kafa a fada mai wani magana.
Har gara Jamil don shi yana dan wasa da yan uwana idan yaso yana kuma ziyaran iyayyena idan ya tashi yaso don kan shi yana yi.
Ranan dai da talauci ya damay ni na shirya naje gidan wurin ta neman dan dubu daya in rike don lalurar yau da kullun don a takure nake ba walwala.
Sai nake ganin ita ta dan rage da wani abu a gurin ta sai cewa tayi min wanan kudin fa kamar yadda nima nake fadin babu su itama gaskiya babu su a hannun ta yanzu don ko abinda zasu karya yau uwar mijin tane ta aiko masu dashi.
Ban san lojacin da na bude baki nace sumaiyaay kikayi da kudi ki ba ni ansan mijina ne ya cinye min nawa naki fa ta hauni da fada tana daure fuska akan may zanzo in tasa ta gaba da tambaya kudi dai ne an bawa kowa hakkin sa ai.
Ban dai gane komai ba haka na bar wurin ta don mijin ta da ya dawo yana wani daure fuska kamar yaji zancen mu da ita dama ya shigo yana shan kamshi daya ganni a gidan.
Ban san dadin firan da ya kwashe wurin Jamil ba na kwashe zancen da mukayi da yar hayan gidan mu na fada mai ranan tun wanan lokacin ya matsa akan lalai sai na sallamay ta daga gidan din tana saka muna ido ga al,amuran mu dashi.
Ban so haka ba don a wurin ta nake dan samun shawaran karuwa sai na rasa yadda zan mata magana kan matsin da yake min a kan su gashi shida mijin ta suna shiri sosai a gidan na gani.
Amma haka yake matsa min a daki akan in kore su su bar gidan nan ko raina ya baci dashi banda yadda zanyi haka na daure na fara nuna mata wasu halaye na daban da ban saba nuna mata ba sai data ga haka ta fara jan jikin ta dani itama.
Har ya kaimu da fara sa,insa a tsakanin mu in rufe ido in mata cin mutunci ala dole ni ga maigida sai fadi nake sufita su ba ni gidana tunda bada su aka sai muna ba.
Takan ce ai nima saukin abin bani kadai ke da gidan ba namu na taro ne na algaje ni kadai sai munafukin miji dake yaudarana don banda wayo ya cinye min komai nawa tunda ina sakara yana fita yana neman mata da kudina.
Wanan zancen ya bata min rai sosai nake jin zafi a raina kan abinda ta fada min sai ya bata min da Jamil din da ita a lokaci guda.
Ko da ya shigo nan na haushi da sababi ina jidali kan zancen da maman Ahmed ta fada min nasa nake fadin idan har mata ya nema da kudina ba zan yafe mai ba.
Wanan magana ya bata mashi rai sosai yasa ya kara fushi da mama Ahmed din kan yau ba gobe ba zasu tashi gidan sai da maigidan ta yaje gurin iyayye na akai muna magana na hakkura da zancen sai idan sun samu gida don mijin yana gina bai karasa ba lokacin.
Wanan yasa muka dan samu saukin fitinan mu sai dai sama sama muka koma da ita a gidan ba wanan dogon shirin da mukeyi da ita.
Ya koma ban wani dogon shiri da kowa a gidan yanzu don duk sun hada min kai ban gane masu nima ban shiga shirgin su dana yaran su kamar yadda mukeyi a baya.




ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
5/18/21, 11:56 PM - 🤔🤔🤔: Ko dana koma gida na samu ya karasa min aikina kamar yadda yace zai mun din don har Amira na samu ya kimtsa min ita don bai bari na tafi da ita ba.
Ina shigo jikin shi har rawa yake wurin tambayana to yaya zancen kudin ne komay ake neman mu dashi kudin dake a jikina na fitar ina nuna mai take ya washe baki yana fadin alhamdullahi.
Allah ya rufa muna asiri dama ko barcin kirki ban samun yi kan rashin samun mafita da banyi ba yanzu kin ga Allah ya rufa muna asiri.
Nan ya shiga lissafin irin karyan da zamuyi idan na haihu yake fadin in kawo kudin tun yanzu yakai na mai shagon da yake sayayya da na haihu daukowa kawai zamuyi a gurin shi.
Ina kallo ya lissafa kudin da yake so ya kuma fitar da wanda zamu sai abinci har na suna idan na haihu din da za,a dafa gurin taron suna.
Da kyat da boni na samu yabar min wanda zan dan rika a hannu na don lalurori irin na mata sai cewa yayi dani ba ga baba kabiru nan ba yasa zai min idan na haihu.
Ni don sanin yadda muke da mutanen gidan mu yanzu sama sama yasa hankali bai kwanta da zasu yi min ba idan na haihu din ganin na na matsa mai ya firar da dubu talatin ya bani a cikin dubu dari tara da kyat ya mika min a hannu na wai sakaci gare ni kada in aje a wurina a kwashe.
Nasan abin da yakewa shine ganin haihuwana na farko an min abinda ma bai zata zasuyi min ba ga kuma kanwa ta data haihu itama an mata sha tara na arziki ya gani.
Ban san baida kunya ba sai da ya miko min kudin yana wani shan toka a fuskan shi tare da fadin ni ke nan naga kudi na daure fuska may zanyi dasu bayan baba kabiru yana muna komai idan mun haihu mafarin in koyi kashin kudi ke nan jifa.
Baba kabiru da ya gama zagi yana batawa a gurin mu ne yake kuma tunanen zai muna abin arziki yanzu saboda son banza daya iya a rayuwan shi.
Ni gani wawiya ta karshe ban koyi tunanen irin sakin da yake min ba a lokacin ni dai bukatana da tunane na dani kadai zai zauna ba wata mace da zaice zai kara aure nan gaba.
Don sam bani irin wanan tunane a raina saboda son shi daya rufe min idanuwana a lokacin har mutane na fadin wai ko asiri yai min ne haka wana abin ga kowa don sanin halina an kawo ido ansa min dashi banda makwabi a rayuwa na.
Don kowa yasan da ya fada min gaskiya zan kwashe in fada mai ya dora gaba da mutum har illa masha Allah.
Yanzun kan muna da abinci ga kudi don shi Jamil mutum ne da bai ci ko wani irin nau,in abincin daya danganci tuwo a rayuwan shi sai dai dan taliya makaroni shimkafa da miya ko tea kamar ba haihuwa kauye ba shi.
Sai daga kai nake wa mutanen gidan mu don komai ina dashi yanzu ban dan murya gun kowa don neman wani abu don tunda anty tai min fadan haka ga yan hayan gidana na daina tambayan su wani abu.
Da yake ni sakarai ce sai wanan samun yasa ina daga masu kai har suka fahinci hakan gare ni kowa ya jaye min daga harkana sai ni dashi da yan uwan shi muke bushashan mu a gidan.
Daka ji sallama yan uwanshi ne ba dai nawa ba yanzu zan hada masu delicious ko a sawo masu kayan sanyi susha su wuni suna cin dadi a gurin mu.
Sati kaman uku da haka na haihu na kara haihuwar diya mace ba laifi don yan uwa da matan baba suna asibiti a tare damu har na haihu aka dawo dani gida.
Tun yanda suka ga ni kaina da Jamil din muna masu kowa ya dauke kafan shi a gidan tun ranan matar mahaifin shi ce tazo ta zauna damu na satin da akeyi inda Jamil sai dadi yake cika mu dashi.
Niko ban tunanen komai a raina don sai fadin ake yarinya tazo da goshin ta don muna cikin wadata inji yan uwan shi suke fadin haka gare mu.
Ban wani damuwa ba na rashi ganin dangina basu tsayawa a gurina ni tunda ga dangi jamil sun tsaya min akan komai ai ya waddatar dani nake gani don haka ne ban nemi shawaran kowa ba.
Da anty ta kara shigowa duba mu take kebewa dani irin yadda akeyi din nan tana tambayana mai muka shirya ma bukin don sunji shiru ban tuntube su ba har yanzu.
Sai budan baki nayi nace kada su damu ai mun gama shirin komai da zamuyi tace kai madalla Allah ya raya muna bata dade ba ta fita .
Sam ban kawo magana na wani katobara bane a lokacin don haka na shiga harkokina ba wani damuwa don ina ganin ai muna dashi.
Summaiy kanwata ce tazo tana tambayana nake fada mata yadda mukayi da anty tace kai amma ke anty hadiza wai wata irin wawiyace haka don Allah.
Anty ce zaki fadawa kun kun gama shirin komai da mijin ki kina ganin ke yanzu baki da bukatan komai a wuri su ke nan ?
Nace may zamu bukata tunda muna da kudi a hannun mu yanzu tace to shike nan ita yanzu gida zata taji irin shirin da akeyi a gida don tasan yau ya kamata ace anyi su cicin da sauran su.
Nace sai ta dawo ta fita zuwa gidan mu niko ban wani damuwa ba a raina don nasan zamu burge kowa da wanan haihuwa ko suyi ko kada suyi ban damu ba ni.
Da ta shiga gida sai ganin gidan tayi wayau ba kowa anty ma tana dakin ta tana barcin ta a lokacin don tana up a wurin aiki.
Bayan sun gaisa ne take tambayan ta ko akwai wani abinda za a yi a gidan sai take cewa ai mai haihuwa tace ta hutar damu don sun gama shirin komai.
Tace a ina ta shirya anty har gashi gobe suna ni banga wani shiri da takeyi ba tace summaiya kin san shirin da sukayi ita da mijin ta ne ki sa masu ido aga ni mana.
Abinka da dan uwa sai hankalin ta bai kwanta ba ta kara dawowa gidana tana fadin ita fa taje gidan mu bata ga wani shiri da akeyi ba a can yanzu idan mutane sun taru mai zan raba masu na buki ?
Nan dai dabara ya fado min nace buta zan sayo sai alale da taliya da zan dafa kuma da dambu .
Tace duk a ina za ai maki wanan aikin to nace a gidan yaya sani wanan Jamil din nan da suke kamar abokai wanda ya tilasta min kiran matan shi da anty.
Wani tsoki taja tana fadin yanzu ke a can za ai maki aiki sai kace wace bata da gata a gari gaskiya bai kamata mu nuna wa baba kabiru da matan shi haka ba anty.
Fada mukayi da ita sosai a gurin don ta fahinci ina haka ne don gyarawa Jamil dina rai kawai ban damu da abinda dangi zasu fada ba a kaina.
Nan na fitar da kudi cikin wanda ya dan rage min na bashi ya sawo min buta sai gashi da kananin butoci kuma dozen uku ni da na bashi kudin dozen biyar yana fadin.
Wai ya samu sun tashi shine ya sawo min wa yan nan nace ai ba zasu isheni ba yake fadin wai har wasu mutane zasu zo da zan saye da yawa don barnan kudi kawai.
Dinki kala uku yai min duk a cikin kudina shiko ya dinka sun kai kala goma sha kamar shine mai haihuwan da zai fita bani ba.
Washe gari a gidan su aka yanka katon ragon da ya sayo aka gyara sai dan hanjin da aka aiko min dashi wai sun raba a can suma zasuyi amdani dashi ne.
Sannu sannu gida ya fara cika da mutanen arziki yan uwa da abokan arziki suka fara zuwa min suna gashi ba a kawo min abinda zan ba su ba.
Yan uwana da suka zo tayani aikin suna daga gidan mu sai tambayana sukeyi mai zasu yi nake cewa ba wani aiki a can gidan su Jamil ake abinci.
Koda za a kawo min sai ga taliya wani iri dashi ba mai kuma dan kadan kasan kula sai dana dafe kaina don takaici da bakin ciki ga alale shima kamar hakan aka kawo min din.
Haka na aka raba ma wa yanda ke gidan a lokacin aka barni ina kamay kamay idan mutane sunzo mi don ba abinda zan basu anan.
Yan uwana suka kwasa suka wuce gidan mu don a can suna nasu dahuwan don dangin mu da suka zo daga wurare anan suka sauka.
Dama kuma a ka,ida hakan yake ga al,adan bahaushe yan uwan mai haihuwa zasu taru ne a gidan mahaifanta har zuwa wani lokaci kafin su zo gidan ta da dan abinda suka tanada don ta.
Sai da sukaci suka sha a can suka dauko dan turamay dana samu wanan karon turmi hudu ne kawai daga gidan mu sai buhu biyu na abinci gero da masara da baba kabiru ya saka min.
Aka nufo gidana dashi tun da naga haka naji raina ya baci dasu a zuciyata fadi nake aiko in haka ne zasu sha kunya don ni dama a shirye nake abina don haka.
Nan gidan su Jamil suka shigo da akwatinan daya gabatar masu a ranan don ba wanda yai tsammanin haka daga gare mu.
Sai wani washe baki nakeyi ina sallo ni adole mun faso gari muma sai fadi mutane ke yi basu taba ganin itin set din akwatinan ba a gurin.
Da aka bude kuma sai da kowa ya kama baki don kyawon kayan dake cikin akwatinan danawa dana baby duk

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login