Showing 102001 words to 105000 words out of 106121 words

Chapter 35 - kanin Ajali Book Complete by Zee Makawa .txt

Advertisement

01 Jan 2025

8074

mu nan suka zauna don tsaban iya makirci na Jamil ya nuna mai karmar bashine mai fushi da fada ba a kan kudin.
Nan ya fara dadin baki wa baffa din yana fadin ba wani abu yasa nake son rike kudin nan ba sai don yanzu sana,an kifi yana tashi sosai daga nan zuwa kasan Niger nake son in dan juya in samu nima.
Baffa ya katse shi da fadin zuwa yaushe zaka dawo min da kudin ke nan yace zuwa nan da wata hudu idan damana ya sauko kasuwa ya kwanta ke nan.
Yace ba matsala yanzu a kawo takarda muyi shi a rubuce don gudun abinda kaje ya dawo nan gaba kaga kowa yasan munyi abu a cikin wayewan kai ke nan.
Bai ki ba nan ya mile ya dauko biro da takarda sukayi shi a rubuce yace dari biyu ko da hamsim yake son a bashi.
Baffa yace su dai tsaya a dari don shima yana son yin lalura da kudin ne nan gaba.
Ranshi ya bata sosai don jin abinda Baffa din yace amma ba yadda zaiyi ya karbi dari din a rubuce kamar yadda yace zai bashi.
Wanan ya kawo zaman lafiya a tsakanin mu yanzu kwana biyu da bashi kudin ya tattara ya bar garin ya tafi inda yake zuwa a cewar shi.
Sai bayan tafiyan shi ne na samu sauki ga duk alamuran gabana Baffa ya samay ni gida yana fada min cewa kudina saura suna ban zai shiga kano ya saro muna kanani atamfofi mu sayar.
Nayi murna kwarai da jin hakan inda bai kara kwanaki ba ya wuce zuwa kano komai daidai ya saya muna ya turo muna dashi.
Nan na fara sana,a dadi dadi ana saye ana sayo min wasu idan na sayar na tura mai kudin sai ya turo min da wasu.
Sana,an ya karbe ni sosai don dama haka nake da sana,a idan inayi sai ya karbe ni sai dai matsalan da aka samu daga baya shine.
Tun tafiyan Jamil ba aike ba waya shiru kamar an aiki bawa garin su ga yara dole muci abinci na fara amfani da dan kudin dake a hannu na na turamay da nake sayarwa din.
Sai kudin suka fara lalace min ga sana,a yanzu sai da bashi mutane sai su rike kudi kaita bi basu baka ba sai wani lokaci abaka su a lalace.
Abin dai nawa sai ya koma min kamar mai bakin iyayye akai ba wani ci gaba kuma har yakai na kasa tura ma Baffa din da kudin da nake aikawa a sayo min yan turamay dashi.
Kamar nawa matsalan itama sumaiya kanwata haka abin nata ya lalace sai dai ita ba a jin komai daga gareta don bata kusa da gida haka yasa ba a sanin halin da suke ciki da mijin ta can.
Sai ni dake kusa ake sanin nawa din kowa ke magana sai dai ko may ye ita ta fini dama gaskiya sosai.
Don ko ba komai ba aganin ta a gane don tana da yan suturorin ta na rufin asiri sai dai ba yanda mutum zaiyi tsamani bane.
Sannu sannu abubuwa suka fara rikice min na rayuwa na ramay na lalace duk na fita cikin hayaci banda komai kuma kowa ya sani aka kawo ido aka samun a hakan nake rayuwa.
Don an san ban son maganan da za a soki Jamil a gaba haka yasa haushina a rayukan yan uwa ya kara karuwa sai baba kabir me mai dan taimaka min wani lokaci can ba a rasa ba.
Sai kuma anty daga dan muna hade hade idan naje gidan taga irin yanayin da nake ciki nida yara na idan zan dawo sai ta dan hada min abubuwa kamar yadda iyayye mata ke yiwa diyan su wani lokaci.
Ranan kwatsan sai gashi da yammaci ya dawo min yanayin shi kawai na kalla nasan ba dawowan arziki yayi min ba a lokacin.
Bayan ya huta yai wanka yaci abinci ya kwanta yayi barci da ya taso ne yake ban labarin wai tafiya bai mai dadi ba yasa muka jishi shiru haka.
Don wanda suke sana, a tare ne ya gudu mai da kudi kasan mali da sunan zai tafi can ya saro masu kifi ashe gudu yayi da kudin sunje can kasan ance dasu baizo nan ba.
Nan dai ya shiga bani labarin karya ina taya shi zagin mutumin tare da bashi hakkuri kan abinda ya samay shi din.
Don sai ka rantse da Allah hakan daya tsara gaskiyane abin ya faru dashi ne a yadda ya tsara maganan nasa.
Haka na koma nike laluran komai a gidan wahalce dani sai dai yayi wanka ya saka kaya ya feshe jikin shi da turare da komai ritse baya rasa su ya fice yawo sai dare zai dawo gida.
Sai jefi jefi nake samu ya dan yo cefane a gidan duk wanan bai damuna idan dai zamu zauna lafiya a gidan dashi wanan bai damuna.
Sai dai mutane suji min haushin abinda yake min din nikan ko a jikina waini mai zaman auren hakkuri sai dai ga nawa wautan banyi tsamanin mutane suna fahintar halin da muke ciki ba dashi.
Na manta cewa yanzu mutum ake kiwo ba dabba ba komai da kakeyi akan idon mutane yake ban san may ya hada shi da yar hayan nan bahausa ba.
Sai ji nayi yana fadin ya kamata matar nan tabar gidan nan ita ma don halin ta baida kyau wallahi.
Sai kuma bayan ya fita ita kuma naji tana jinini wai haka kawai mutum zai lalata mata yara don iskanci ta kyale shi.
Nake tambayan da ita dawa ke fada kuma don muna dan shiri a lokacin takw ce min barni da dan iska ko waye ai yasan kanshi don wallahi sai na tona mashi asiri zai bari.
Tun lokacin nasha jinin jikina da Jamil ne saboda shima yayi min maganan ta kan ta bargidan bata da hali mai kyau zata iya kashe mai yara saboda bakin halin ta ko ta illanta ni nikaina idan bai gari.
Ai sai na dauki fushi da ita tun jin hakan da tace min nace bazatai ma mijina sheri in shirya da itaba niko.
Har ya gama zaman garin da yake damu don bai dade ba yace zai koma don zaman gari ba nasa bane nan dai ya tafi ya barmu muna rikici da wanan matar.
Rashin shi gida bai sa mun shirya da ita ba har wani lokaci ranan kan yar karamar ya ta mukai fada abunda take so ke nan ta fada min abinda ke ranta.
Naji cewa wai Jamil yana kokarin bata mata yaranta yan mata dake gabanta bayan ya nemay ta ita bai samay ta ba ya koma ga yaranta.
Wanan maganan da tai min ya bata min rai sosai don ban dauka Jamil din zai iya mata haka ba matar da ta haifi ganda gandan yan mata kamar ta mai Jamil din zai nema a gurin tayi kuma.
Na hau fada nace sai ta bar min gida na tunda sherin ta yakai har ga mijina kuma yanzu.
Yanzu tace ba zata tashi ba sai mijin ta ya dawo kuma ko ya dawo din sai kudin su na shakara ya kare zasu tashi min gida.


ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
5/18/21, 11:57 PM - 🤔🤔🤔: Tafiyan jamil yasa na samu sakata a zuciyana sosai duk da ya tafi bamu a cikin dadin rai dashi kan zancen cikin dake jikina din.
Sai dai tafiyan nasa yasa na samu sakata ta hanyar da zanbi in dinga sana,ata ba a cikin takura ba ko tsangwama irin nasa.
Don zan iya fita tun safe sai rana zan dawo ya danganta da lokacin da na samu buntun shinkafa din ga bakin wahalan yawon da nake sha wurin neman butu din.
Na koma kamar wata sabuwar mahaukaciya dani don sana,a ba na tsabata bane ko gyaran jiki da mutum zai samu yayi.
Sai dai duk wanan wahalan da nake zancen cikin jikina yana matukar damuna a raina sosai don nima ban so samu cikin a wanan lokacin ba ko kadan don wahalan da yai min yawa din.
Ban samu zuwa gidan mu ba tunda akai karamar sallah don rashin walwalan da mutane basu a ciki don corona da aikawa mutane takunkumi dashi a ko ina a cikin kasan nan.
Duk da hakan mu nan bai shafe mu sosai ba tunda ba alkarya muke ba kamar yadda yan alkarya suka wahala da wanan takunkumin .
Ina shiga gidan mu ko gaisawa banyi da kowa ba anty dana samu a tsakar gida tana shan iska sai cewa tayi dama cikine dake ashe bamu sani ba ?
Nan na fara irin halin mata idan wanda ya gane suna da ciki babbane gare su ina fadin ni wallahi banda komai a jikina.
Sai cewa tayi wanan tunbi ne don samun lafiya da kikayi haka komay ga alama nan ya nuna ko ina kina da ciki kina wanan rantse rantsen haka ?
Haka dai na shashantar da zancen ta kyale ni sai dai tun wanan lokacin haka duk wanda zan hadu dashi yake fada min ina da cikine zasu tambaye ni ?
Amsa daya nake ba kowa ni banda komai sai abin ya fara damuna nima har wanan lokacin ba wani sako daga gurin Jamil tun lokacin da ya tafi.
Ranan ina zaune sai ga kanina ya kawo min waya wai Jamil ne ke son magana dani a wayan shi.
Na karba muka gaisa dashi inda ba wani gaisuwan dadi bane sai tambayan lafiyan mu dayayi zan fara korafi ya kashe wayan shi.
Nabi wayan da kallon mamaki nasawa kanina dake waje zaune yana hira da abokin shi kira ya shigo na mika mai wayan shi.
Yake ce min ke yanzu baki da ko wayan da mijin ki zai kiraki dashi don Allah ?
Ni anty hadiza na rasa irin rayun kin nan idan kuma an baki mutun kwana biyu ba zai ga wayan ba inji kani dan wajen anty da ya kira ya bani waya yake wanan magana.
Maimakon in fushi sai dariya nayi mai ina fadin kai yaro ne do Allah baka san komai ba yanzu yace ga waya zan baki idan ban ganki dashi ba wanan ne na karshe da zan baki..
Nan ya cire sim din karamar wayan shi ya miko min na hau murna da tsale ina mai godiya inda na dauko tsohon sim dina na saka.
Ranan da farin ciki na kwana a raina don murnan samun wayan da nayi ba don komai ba sai don na samu abinda zan rika ji daga gun jamil din kawai tunda dama rashin waya nake gani baisa mu jin labarin juna din.
Nakan kira ko ya kira sai dai duk da ba wani magana da zai farauta rai bane karshe ma ya fake da hira da yaran shi.
A haka dai abubuwa suke tafiya cikin yakai wata hudu ga yanzu sana,a ya kwanta babu shinkafa don lokacin shi ya wuce.
Ba kamar farkon kakan shi da muke samu sosai ba haka zan wuni ina bin injimomin gari ace ba aiki yanzu a gurin su.
Ba zai wuce a wuni in samu dan rabin buhu ba in zo in sheke gaida wahalan rayuwa nan ya taru yayi min yawa a kaina.
A haka ragga ya kara muna sallama dani da yarana bamu da sutiran shiga jama,a ko daya sai dai akance wai ban iya tanadi bane.
Yo ina wani tanadin tunda wanda ma ake muna a cikin shekara din yanzu ko samu banyi ni kuma nemana na abinda zamu ci ne kada mu kwana da yunwa.
Haka yasa ban shiga mutane ko abu ya samu yan uwa sai in share ban zuwa don dama ba kula yan uwa nakeyi ba.
Ina ya Allah ranan kwatsan a cikin dare ina barci na shawo wahalan yawon neman butun da zan sheke ban samu ba can cikin barci na naji marana yana min wani irin ciwo .
Koda na falka sai ganina nayi a cikin jini cikin jikina yana neman barewa don bakar wahalan da yai min yawa lokacin ina cikin wata na hudu da makwani dashi a jikina.
Yar hayan gidan mu wata kabila ce ta taimaka min a cikin daren nan mukaje asibiti muna zuwa ya karasa fita daga jikina inda suka dan taimaka min da yan allurori don samun lafiya ta.
Wanan matar itace tabiya komai da akai min akan cewa idan ya dawo zai biya don ta kirashi tun a gida kafin muzo asibiti din ta sheda mai halin da muke ciki zamu tafi asibiti.
A asibiti ma ya kira take sheda mai abin ya fadi ana bani allura ne yace da ita ayi komai zai bata idan yazo tace ba komai ai ana tare.
Mun dawo har na samu lafiya baizo kuma ba kira tunda ya kirani sau daya yaji lafiya ta bai kara kirana ba nima ban kirashi ba.
Wahalolin rayuwa sun min yawa sosai don yanzu abinci yana neman gagara muna ni da yarana shi sutura ma ba,a zancen shi ai.
Har yakai anyi sallah babba still bai zo ba bai aiko muna da abinci ba ko kudin da zamu saye ga mutane sai tambaya na sukeyi shi idan sun shigo wurina.
Dole na fara shiga yan uwa hakana a kunyace ina neman abinda zamuci kada mu halaka duk da su basu nuna min komai akan kin su da nayi da farko din.
Duk lokacin ana cikin tsananin harkan corna virus din nan dake yawo a kafafen yada labarai amma ni ta kaina nake da yarana a gari.
Ganin halin da ya barni yasa ran kanina baffa ya baci don ya gama service yazo gida a lokacin nan ya fara matsa mashi akan yana bukatan kudin shi dake hannun shi.
Zaiyi lalura dasu ne don haka ya aiko mashi da abinsa a cikin lokaci don lokacin da ya diba zai bada ya shige harda wata shidda ko.
Tun ban san suna yar tsama da baffan ba har takai na sani nima baffan ya fara ganin laifina wai duk nice ai najawa kaina wullakanci a gun Jamil din.
Ranan dai na gaji da safe na dauki waya na tura mai da text massage kamar haka.
Jamil ko kare mutum ya bari aka ce mai ya samu matsala zai wawayo shi ya duba lafiyan shi.
Balle dan mutum mai rai ka tuna ni marainiya ce banda uwa banda uba sai Allah da yan uwana dakai.
Saukin abin Duk abinda mutum yayi Allah na ganin sa kuna can matan duniya suna rudin zuciyar ku ka jefar damu nan ka manta damu.
Ina gamawa na tura masa bai bani amsa ba run ina duba wayata har na daina don bai turo min da amsa ba bai kuma kirani ba.
Ni na dauka ba zai amsa min ba sai can dare misalin goma da rabi ya kirani sai Amira ta dauka tana gaida shi.
Yake tambayan ina maman ku tace gata nan tana tambayan shi baba yaushe zaka zo yace yana nan tafe ki ba maman ku wayan.
Ta miko min na karba da yi mashi sallama bai karba ba sai cewan da yayi kece kika turo min da sako ?
Shiru nayi ban bashi amsa ba yace maman Amira kina jina nace eh yace na sake ki ma,ana sauran saki daya dake tsakani mu na yanke shi yau.
Yana fadin haka ya kashe wayan shi ya barni a gurin sandare zuciyana tana famtsama da al,amarin shi ba abinda yazo min a rai sai maganan anty da tasha fada muna akan mazajen mu shine.
Kuyi hankali da mazajen nan naku wallahi watarana zaku wayi gari sun baku baya indai namiji ne kun dauki rayuwan ku gaba daya kun ba mazajen ku amna kun manta da kowa naku.
Kun maida su sune uwa sune uban ku duk kokarin da dangin mahaifan ku ke maku baku gani sai gani kuke kowa makiyin ku ne yanzu.
Zasu iya sakin ku a lokacin da komai naku ya kare ko su kara aure abokiyar rayuwan jin dadi nan gaba bayan kun gaba batar da komai naku a kansu .
Don haka wallahi ku gyara tun abu bai lalace maku ba gaba don mazan yanzu basu da tabbas a rayuwa wanan lokaci na ba maza amana gaba daya ya wuce ko.
Idan anty tana wanan maganan mukan ji zafin ta ko muga tana muna baki ne sai muje gefe mu zage ta muce bakin da take muna ya koma kan diyan ta ba mu ba.
Yau sai gashi maganan ta ya zama gaskiya a gare ni a lokaci guda nayi tunane kala kala a raina banda abokin kuka a dakin kuma hawaye bai zo min ba ko zan samu sauki a zuciyana.
Murya yata amira ne ya dawo dani ga tunanen da nake a gurin tana fadin yanzu mama baba ya sakeki ina zamu koma ke nan kuma ?
Sai lokacin hawayen da nake nema yazo min a lokaci daya na fara sakesu a fuskana nan muka taru dani dasu muna kuka a dakin ba mai bamu hakkuri.
Don yanzu yara wayon su yafi shekarun su don sun fahinci abinda

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login