Showing 12001 words to 15000 words out of 106121 words

Chapter 5 - kanin Ajali Book Complete by Zee Makawa .txt

01 Jan 2025

7494

ake kallon mu wai hausan mu daya canza yanzu.
Mama sai faman raba dan tsaraban da tayo take yi masu wanda sai yanzu na fahinci hikimarta nayo wanan tsaraban har baba na fada da ita wai ta dauki kaya da yawa.
Ashe da shirin ta tazo gida do fitar da kanta kunya mun samu baba kabiru ya auro wata mace a birni yar boko itace amaryan baba yanzu dake tashe a gidan.
Munje gidan kakanin mu na fannin mahaifiyar mu mun gaida su mun wuni acan tare dasu suna nuna muna so da kauna irin na kakani.
Satin mu daya da zuwa gida akai sallah baba na wanan shekaran mun shiga mun fita don ba laifi mahaifin mu ya muna dinkuna wanda zai fitar damu daban da mutane garin mu.
Mun fita tare da yan uwana mun zaga gidajen yan uwa da abokan arziki duk gidan da muka je maganan tufafin jikina suke wanda a lokacin ban gane may suke nufi ba.
Ranan sallah da dare mun fita wasa tunda sallah ne ba a hanamu fitan dare lokacin wasa ake irin na kauye maza da mata.
Sai ga wasu sun zo inda muke zaune saman dan dakalin kofar gidan mu yan uwan mu ne don zuri,an mu daya dasu nan muka buge da wasa dasu sai daya daga ciki yake cewa wai yana so na.
Maganan daya bata min wasana na ranan ke nan na shige gida ina kuka tare da fada ma umma nan umma ta fita da tujara ta zage shu tas har iyayyen shi.
Tare da fadin da safe zataje har gida ta yiwa iyayyen shi kashedi kan wanan wasan banzan daya tsiro min dashi don ni ban san wanan ba kada su lalatani.
Ashe tun shigowa ina kuka suka gudu daga kofan gidan don sun san dama umma na iya fitowa taci masu mutunci .
Can daga baya suka labe suna sauraren fadan ta har taci ta sude ta koma ciki ni a lokacin har nayi barci ban san shigowan ta ba gidan.
Washe gari ma da fitinan umma ta tashi sai da baba kabiru yai mata waigi kan maganan yace haba umma kurciyane fa yana ganin shima yana zuwa birni yana karatu.
Don yace yana son ta ai ba ana nufin shine son ba ko dole taja bakin ta tayi shiru don taga ran baba kabiru din ya baci yanzun ko ko dan ka ne idan yana da hali tsoron saba mashi kake ji.
Munyi hutu tun muna saka idon zuwan baba shiru baba bai zo ba har muka share wata da kwanaki shiru baba baizo ba.
Tun mama na damuwa da rashin zuwan shi akan lokaci don karatun mu da zamu rasa don rashin zuwan shi zai iya kawo illa ga karatun namu da mukeyi a can.
Sai dai shiru har wanan lokacin tun tana dan maneji da dan kudin dake hannun ta har komai ya fara yi muna tsaye sai dai baba kabiru yana yawan taimaka mata sosai ta fannin abin amfanin yau da kulun da abinda zamuci.
Haka yasa damuwa ya rage a zuciyar mama din don dan abinda take samu na taimako a wurin dan uwan baba din a yanzu ba kamar da can baya ba.
Dadai taga zaman ba mai karewa bane haka yasa ta dan fara sana, ar mata na cikin gida don rage zaman banza ga irin sana,an data ga anayi acan inda muka fito.
Mu kan bamu da wani damuwa ganin yan uwa ta ko ina bai barmu mun shiga damuwa kamar yadda mama ta shiga ba sai dai wanan Jamilun yana matsa min har yanzu a rayuwana.
Rana kasuwa garin zai dan sawo abu ya aiko mun dashi a boye umma bata sani ba don masu kawowan sun san halin umma har su zata iya yaga idan ta gani.
Haka yasa a can wani lungu suke ajewa sai suzo su kirani idan na fito su bani sai in hau kuka suna dariya zasu cinye a gaba su koma suce sun bani na karba.



ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
5/18/21, 11:46 PM - 🤔🤔🤔: 🙆🏼‍♂️ KANIN AJALI 🙆🏼‍♂️


5️⃣


ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU




Zaman gidan da mukayi baba kabiru ne yake tallabe damu da lalurorin mu bai taba nuna gajiya da abinda yake muna ba komai zai sayowa iyalin shi tare da namu ne.
A hankali muka fara shakuwa da jamilu don gurin wasan mu daya ne dasu ba wani fin mu girma sukayi ba sosai dan abinda ya saka shakuwa a tsakanin mu shine.
Karatu zamu zauna mu dinga fadar kalman turanci ina fasaara masu suna jin dadi ko in fada masu wani kallama yadda ake fadi da turanci.
Ranan kwatsan sai ga mahaifin mu ya dira gari murnan ganin shi gurin mu ba,a magana ba laifi yazo ya nuna ma yan uwa da abokan arziki kauna a garin.
Inda yake sheda ma umma da yan uwan shi samun sauyin wurin aiki ya samu yasa bamu ganshi da wuri ba don lokacin mun share kusan wata shidda a gida.
Don haka tare dashi zamu tafi idan ya tashi tafiya haka yasa muka fara shiri inda ba wani shiri sosai mukayi ba don ba wani abin mama ke da shi ba da zata dauka anan.
Satin shi biyu hutun daya samu ya kare don haka zamu koma jamil ya rubuta min wasika shifa da gaske yana so na ba wasa yake ba kada in manta da shi idan mun je.
Ban dauki takardan dawani muhinmanci ba don haka na tura a kasan bage na kawai muka dauki hanya sai garin abuja inda can yanzu aka mayar da mahaifin mu.
Kubuwa ya samu gida inda zamu zauna wani quaters ne da mai,aikata ke kamawa a cikin su ya samu ya kama daya muka tare a ciki.
Kamar gidan da ya saba kamawa ne dakuna biyu sai falo da makeyi da kitchen sai karamin filin tsakar gida kin dai san yadda zaman bariki yake a birni.
Satin mu biya muka shiga wani makaranta sai dai an mai dani baya ga karatuna don a katsina zan shiga primary five ne sai nan suka mayar dani primary four.
Banda matsalan karatu don bawai na daga Allah ne don haka nake saurin haddatace duk abinda aka koya min da sauri a kaina.
Ba laifi don mahaifin mu yana wadatar damu da abinci da sauran abubuwa sai dai fannin sutura ne bai faye muna tufafi ba akai sai sallah yake sai muna tufafi.
Mama na zama da makwabtanta lafiya saboda rashin hayanitar ta don ita haka Allah yayi ta bata faye shiga jamma,a ba sosai.
Don haka irin gulman bariki din nan da akeyi bata daga cikin masuyin don rashin hayaniyar ta tana gidan ta a ko wani lokaci.
Idan kaga mahaifiyan mu bazakace itace matar mahaifin mu ba don idan baki manta ba na fada maki mahaifin mu farin mutum ne dan gaye sosai mai jin lokacin shi.
Sabanin mahaifiyar mu da take baka yar kauye mara jiki ba wani kyau ne can da za a fada ba a kanta haka yasa matan bariki suke kawowa mahaifin mu hari kamar yadda sukewa maza idan sun shiga bariki.
Ko baka da kudi zaka samu mata bila,adadi iya yadda kake so wanan bai dauke hankalin mahaifina gare su ba don ya tsaya ga iya iyalin shi.
Akwai wata makwabcciyar mu ma,aikaciya ne da idan ta dawo aiki take shigowa gidan mu tana hira da maman mu daidai lokacin da tasan mahaifin mu yana dawowa a wurin aiki.
Ashe ita mahaifina take kyarkyara a ranta ga kudi da take kashe mu idan taga abu zata sayo muna zata kaimu kitso har mama itace ta gwada mata gidan kitson mu.
Sosai mama ta sake da wanan matar da sunan tana musulmane amma addini bai zauna a kanta ba sosai don mama tana yawan mata huduba sosai akan addinin ta.
Shakuwa ce mai karfi a tsakanin su don har harkan da take da wasu maza takan fadawa mama idan mama taga rashin dacewa da abinda tayi takan mata nasiha akan abin.
Ranan kanina baffa baida lafiya har yakai an kwantar dasu asibiti an basu gado yasa aka barmu gida daga mu sai mahaifin da idan ya dawo yake zama damu.
Idan ya tafi aiki ko asibiti muke komawa mu kadai a gidan, kwana biyu da zaman su mama asibiti ranan matar da muke kiranta da anty sady ta shigo take tambayan mu har yanzu ba a sallamo mama daga asibiti ba nace eh ance sai an kara ma baffa jini kuma.
Take tambayan mu a can mahaifin mu yake kwana nace a, a agida muke kwana tare dashi can mahaifin mu ya kusa dawowa gida daga asibiti sai ga anty sady ta kwankwasa gida na bude mata ta shigo.
Nan ta zauna damu tana hira wanda ni hiran nata yayi min nauyi sosai amma haka muke ta hiran har barci ya dauke mu muka barta a zaune tana kallon tv.
Can mahaifin mu ya dawo sai ya samu gida a bude da fushi ya shigo da zuman muna fada sai anty sady ya gani a zaune tana kallo munyi barci.
Da mamaki yake kallon ta tace mashi sannu da zuwa ya mai jikin fa fuska daure yace da sauki don kallo daya yai mata ya kawar da kanshi gare ta saboda shegen kayan dake jikin ta rabin jikin ta duk a waje yake.
Mikewa tayi ta dauko mai ruwa da abincin data girka ta aje a gaban shi yana zama ya dago yana kallon ta tana wani farr da idanu tana kada jikin ta ko ina rawa yakeyi.
Wanan kuma daga ina ya tambaye ta tace nice na dafa don ka na dade ina son wanan daman da zan samu kebewa dakai in gwada maka irin yadda nake jinka a raina.
Kina da hankali kuwa ya fada ta dago daga inda take zaune tazo inda yake cikin wani tako na yan iska tana kokarin ruguman shi.
Cikin zafin rai ya dago ya wanka mata marin da sai data dafe kuncinta don zafi yace stupid idiout ki fice min daga gida banza kawai.
Bata dadara ba ta kara yowa cikin shi zata kara rungumar shi tana fadin na kasa controling din kaina akanka ba komai naka nake bukata ba ka yarda dani kawai shine muradina.
Mikewa yayi ya turata waje tare da wulgi da kayan abincin suka bare can ya rufo kofan gidan da karfi ya dawo yana mai sake tsuki.
Ranan ta saka shi kwana a cikin bacin rai don har ya kwashe mu yakai mu dakin kwanan mu ya dawo ya kashe kayan wutan falon ya kwanta ranshi a bace yake.
Da safe da muka tashi nayi gyaran falon mu da na saba yi duk safe kafin in wuce school ya hada muna breakfast da kanshi muka karya a gida muka je da wani.
Mun dawo gida da yamma mun samu an sallamo su mama daga asibiti har ta gyara ko ina na gidan ya koma fes dashi badai tsabata ba a gurin mahaifiyar mu kan don bata son kazanta ko kadan.
Wata makwaciyan mu ne ta shigo duba jikin baffa sun dan taba hira da mama a cikin hiran take fadawa mama tayi hankali da anty sady don bata yarda da ita ba.
Don sun dawo cikin gari da mijin ta da dare sosai ta ganta ta fito gidan mu alhalin tasan mama din bata gida.
Mama bata dauki wanan wani abu ba sai take ganin ai don dai mutuncin dake tsakanin su ne kawai yasa tazo gidan don duba yara.
Kwana biyu sai ta dan lura baba baya son zancen anty sady sam ko ya dawo ya samay ta a gidan tana gaida shi baya amsa mata zai kama fushi har ta tsagu ta fita.
Ranan ma haka ya kasance bayan fitanta muna falo dayaji firanta ya fito ya zauna a falon sai mama tace ban san abinda yasa kakewa matar nan haka ba yanzu idan ta shigo gidan nan.
Wani tsawa ya daka mata tare da fadin ko ke idan baki fita harkanta ba sai na saba maki rai don ban son alakan ki da irin yan iskan matan nan don haka ki fita harkan ta.
Kada in sake ganin takawo wani abu a gidan nan kin karba idan na ga haka zan saba maki sosai kinji na fada maki gaskiya.
Baidai fito fili ya fada mata abinda ya faru a tsakanin su ba sai wanka da kamar jurwaye da yai mata kan anty sady kawai haka yasa mama shiga damuwa sosai a ranta yadda zata kakabe ta a jikin ta alhalin itace ke binta.
Don gudun bacin ran mahaifin mu dole mama ta fara sakewa anty sady din ko ta shigo sai ta tsiri aikin karya da zai dauke mata hankali har ta gaji ta wuce don kanta.
Da anty sady ta fahinci haka da kanta ta jaye a gidan sai dai can takan shigo jefi jefi neman wani abu ko tace tazo gaida mune.
Shakaran mu biyu a madalla har mukai comman intrance na shiga secondary school na gama primary dina ke nan sai gaba zaman gida nake ban fita ko ina sai islamiya da muke zuwa wanda ke da dan nisa sosai da gidan mu.
Ranan amaryan baba kabiru ta shigo abuja wurin yan uwanta sai gata a gidan mu muyi murna sosai da ganin ta itace ta farkon zuwa wurin mu a cikin yan uwan mu na gida.
Kwanan ta biyu a wurin mu naji kamar kada ta wuce yarta ko yaushe tana gurina ina giyon ta ranan da zata tafi nayi kuka sosai da tafiyanta.
Saboda ban raina abin kuka bayan tafiyan ta da kamar wata biyu na dawo daga islamiya na samu mama tana ta hada kayan mu da mamaki nake kallon ta ban hakkura ba na tambaye ta.
Take fada min baba yace zamu tashi mu koma garki ne sai naji ba dadi a raina ko ina sai mun saba da mutane sai kuma mu tashi.
Wurin tone tone nane na tono takardan da jamil ya bani da zan mu zo abuja din na dauka na bude karo na farko da kyat na iya karanta abinda ke cikin takardan wanda a lokacin na fara fahintar may yake nufi dani.
Ranan haka na kwana karanta takardan a boye kada mahaifana su gani barci ne ya dauke da takardan a hannu na har baba ya shigo dakin mu ya samay ni dashi.
Ya dauka ya karanta sai da kanshi ya daure don ganin takardan da yayi da alama kuma takardan ya dade don har ya fara canza launi don ajiya.
Dukan da naji ne a cikin barci ya falkar dani a gigice uban wa ya aiko maki da takardan nan yace dani sai lokcin na tuna da zancen wani takarda .
Cikin inda inda nake fadin baba baba Jamilu ne na gida ya bani shi da zamu zo shine shine sai yau na gani ban san may ya rubuta a takardan ba nima.
Ina karantawa ne ban gane ba barci ya dauke ni idon shi yai ja yace koma ki kwanta ya fita falo wurin mama da takardan a hannun shi yana fada.
Yana fadin yaya tayi sakaci dani haka har maza suka fara min wasika har nawa nake da zan fara samun wasikun maza haka.
Rantsuwan duniya mama tayi mai akan takarda yai fadan shi ya kare ya fice sai da safe ne mama take min fada akan takardan na nuna mata ban san ko na may ye ba nima.
Mun koma garki wanan gidan yafi duk gidajen da muka zauna a baya girma sosai ga gari muna gani komai da zamuyi a saukake mukeyin shi gurin.
Nan ma mun hadu da abokan arziki da dama inda mama har tana sa,a a nan tana sa kankara yan sari na zuwa suna kwashewa.
Naci makarantar bowari Abuja na kwana don haka boarding zan tafi karatun secondry dina sai faman shiri ake muna don tafiyan na can din.
Ban dade ba na tafi karanta inda kowa yasan dan aji daya irin wahalan da yake fuskanta farkon zuwan shi makaranta haka nima nayi ta fuskantar wanan daga mutane .
Mun dawo hutun farko ina ta dokin ganin mahaifana da yan uwa na a gida sai na samu mama da ciki kuma a jikin ta.
Bandai yi magana ba sai binta da kallo da nakeyi idan ta gilma har ya kai ta tsargu tayi min magana tace ai kila in haihu kuna makaranta wanan karon.
Nace lah mama kina da ciki ne dakuwa tayi min na kama dariya tace wanan manyatacen kallon da kike min na maiye shi in ba cikin kike kallo ba.
Na kama dariya ta wuce ina ta murnan zamu kara yawa a gidan mu muma har hutu ya kare na koma mama bata haihu ba.
Da mahaifina yazo min visting yake fada min haihuwan mama ta samu namiji har anyi suna ko nayi ta murna da dokin son ganin jaririn da mama ta haifa din.
Sai da aka samu hutu muka je gida inda mahaina ne ke zuwa dauka na sai gashi na ganshi yazo da mota.
A hanya ne yake fada min

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login