Showing 24001 words to 27000 words out of 106121 words
Chapter 9 - kanin Ajali Book Complete by Zee Makawa .txt
da kwana uku zamu wuce.
Bamu san matar ba da akace zamu tafi da ita mudai burin mu kawai muga mun koma Abujan gurin mahaifin mu ko ta halin kaka.
Ranan tafiyan mu yazo motar da baba kabiru yayo muna shata zata kaimu har abuja ta iso muka shirya sai lokacin ne muka san matar da zamu koma Abuja da ita ta zauna damu a can.
Muka dauki hanyan abuja cike da bacin ran rabuwa da yan uwa da abokan arziki da zamuyi a nan gida Allah ya sauke mu lafiya.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
5/18/21, 11:49 PM - 🤔🤔🤔: 🙆🏼♂️ KANIN AJALI 🙆🏼♂️
9️⃣
ZAINAB IDRIS MAKAWA
FATAN ALHERI DA CIKAWA DA IMANIN UBANGIJI A KARSHEN MU UBANGIJI YASA MUFI KARFIN ZUCIYAR MU AMIN 👏
TO ANCE KADA INJA ALLAH YA ISA BAI DACE BA, KUMA SAI KU MUNA ADALCI, KU DAINA FITAR MUNA DA NOVEL DON GIRMAN ALLAH, DON HAKA WACE TA FITAR KUMA KA GANI KA KARANTA SAI MU BARKU GA ALLAH SHIKE NAN SHI YASAN TSAKANIN MU DAKU, , ,
Bamu dade da dawowa daga gida ba sati daya na kara na koma school don na samu baba ya gama min shirin komawa makaranta.
Nan na bar kanne na da gwagon mu da muka zo da ita na barsu ban gama fahintar yadda rayuwan ta yake da yadda zata zauna tare da yan uwana.
Don hankalina sam bai kwanta da yanayi wanan matar ba don ina ganin zatayi fada don haka zata kwasa da kanne na a gida dana barsu tare.
Ban yi wani nisan zango ba mahaifina yakawo min ziyar sai dai na kula ya danyi rama kadan da baki wanda na dauka duk yana cikin damuwa rashin mahaifiyar mu da yanayin da yake ganin mu a ciki na ban tausayi.
Ga maganan auren shi tun bayan rasuwan mahaifiyar mu bamu kara jin magana ba a gidan itama kanta ta rage kiran shi kamar baya can.
Ashe rikici suka yi da ita wai ba zata zauna ta dubu yaran shi ba shikuma ya yace ba zai iya rabuwa da yaran shi ba gaskiya.
Shine rikicin da sukeyi a tsakanin su har ya kawo tsaikon auren mukaji shiru zuwa wanan lokacin don mun ki jinin matar tundai kauna ta summaiya bata kaunan ai maganan karin auren baba a gaban ta ko kadan.
Yanzu zata kama zagi tana aibanta matar har wace ta hada auren zata zage ko a gaban waye duk da ba wani shekuru ke gare ta ba amma akwaita da tsananin kishin tsiya.
Ita a dole tana taya mahaifiyar mu kishi tana fadin ai da baba baiyi zancen auren ta ba lafiya kalau maman mu ke haihuwanta.
Wanan ke nan wanan time din mun dawo gida na samu kanne na sun rama sunyi baki raina ya baci da ganin hakan ko ban tambaya ba nasan zaman su da gwagon namu ne babu dadi.
Mun samu kebewa da sune suke fada min ciwo sukai tayi har da kwanciya asibiti nayi masu sannu baba ma yai min bayanin irun ciwon da sukayi a bayana din sosai.
Abin farko dana fara kula dashi wanan gwagon tamu sam jinin mu baizo daya da ita ba idan ina falo tana daki idan kuma daki nake ita tana falo don a dakin mu ta sauka.
Ranan cikin dare ina barci na falka na ganta tsirara tsaye da wani kwarya a kaina wani irin ihu na yanka gashi mahaifin mu baya gida yana aikin dare ne ranan.
Ihu na ne ya tayar da yan uwana a tsorace duk da basu san may ya faru ba suma suka shiga tsoron a lokacin.
Ban iya fada ma kowa abinda ya faru ba ranan sai dai muna yar tsama da wanan matar da aka kira da gwagon mu mai zama damu.
Sai ta so ta dora min tsangwama tana fadawa mahaifi mu wai ina mata rashin kunya nan zai kamani ya zage ni fes a kanta.
Abinda bamu sani ba ashe matar manyace aka dauko aka kawota zama damu abuja cikin rashin sani wanan yawan ciwon da yan uwana ke fama dashi duk itace ummul,abasin ciwon su.
Kwatsam sai ga umma ta dira abuja kamar daga sama tana zuwa matar tasha jinin jikin ta nan umma ta shiga yadda magana kamar haka.
Mugu sai dai ya harari kayana ya barshi, idan yace zai taba kayana sai dai su tafi tare da maishi banci dan kowa ba babu mai zuwa ya taba min nawa.
Idan mutum yace shi takaman shi sheri ne ya zo karshen sheri a rayuwan shi don asirin shi ya kusa tonowa a garin nan ire iren maganganun da umma kan zauna a falo tana sakewa ke nan.
Idan baba yana gida zai tambayi umma wai da ita da waye take wanan magana haka sai tace mai ya barta ta fadi ai mashi yasan kanshi.
Ranan dai gwagon ta tayar da hankali wai zata koma gida tunda umma tazo dama don babu kowa tare da mune baba kabiru ya roketa tazo.
Batai wani kwanaki ba ta tafi ta barmu bayan baba yayi mata goma sha tara na arziki tana ta godiya aka sakata a mota da zai kaita jahan mu.
Ranan ne umma ta zauna da baba tana fada mashi mugun halin gwagon namu da taji daga baya wanda hakan ne ya tayar mata hankali ta biyo mu.
Mahaifin mu dariya yayi yana fadin may yasa kuke yarda da irin maganganun nan don Allah wanan duk camfine wallahi.
Nan nake fada masu yadda na ganta ranan da bamu kara shiri da ita ba har ta tafi ke nan umma tace kaji ba aniyar kura ta bita ba a cikin kayana ba kan.
Na koma school na bar gwagon mu a nan inda wanan zuwa da yar gurin baba musa tazo sai da mahaifina ya nuna rashin yardan shi akan zuwan da tayi da yarinyar da farko.
Don shi bai ra,ayin rike dan wani a rayuwan shi yasa nashi ma bai yarda yan uwa suka dauka ba ina makaranta ne ciwo ya kama mahaifin mu lokacin mahaifitar mu tana da shekara biyu da rasuwa ke nan.
Sai dai bai kwanta ba tsatsaye yake jiya muna samun hutun makaranta umma tace tunda yaji sauki gida zatazo damu mu kwana biyu.
Mun dawo gidane muka barshi can sai kuma ya samu sauyin wurin aiki ya koma Niger state da aikin shi satin mu uku da zuwa gida ke nan ya samu wanan sauyin.
Lokacin ne abubuwa suka taru sukai mai yawa dole yazo yayi reporting don kada ya samu matsala satin shi biyu a minna har ya samu gida inda zai zauna da iyalin shi sai kuma ciwo ya dawo mashi sabo.
Da yan wuein aikin sukaga ba zasu iya ba aka tada mota a kawo shi gida wurin iyalin shi da yamma lis suka iso wurin baba kabiru dashi.
Hankalin baba kabiru ya tashi sosai yadda yaga dan uwan shi ya koma a lokaci guda ciwon dai baiyi kama dana asibiti ba sam.
Haka dai suka dauke shi zuwa asibiti suna hadawa dana gargajiya da farkon zuwan shi yana magana don har yana ma baba kabiru bayanin yadda yake jin jikin nasa a lokacin.
Nan dai baba kabiru ya gane abin kamar sammune akai mashi hankali ta kara tashi sosai umma ta samu labarin ciwon nasa inda hankalin ta yayi matukar tashi da zancen.
Washe gari ta shirya sai birni inda baba yake kwance a asibiti jikin ba sauki addua,a tayi mai ta dawo gida da yamma lis babu wani walwala a tare da ita ko kadan.
Mun taru a dakin ta don son jin yaya jikin mahaifin namu da ta baro a can sai cewa tayi yace a gaida mu ya samu sauki sosai da taje .
Munyi ta murnan jin hakan dama da zata tafi munce zamu tace mu bari idan ta dawo sai mu shirya mu zo mu duba shi da jiki don haka muka kasa kunnuwan mu don muji tace ga ranan da zamu mu duba mahaifin mu din kafin ya koma.
Tunda tace damu ya samu lafiya ko banza mun san idan mun samu ganin shi zamu samu kudin kashi a gurin shi wanan shine burin yan kannena a lokacin sai lissafin abinda zasu saye da kudin sukeyi.
Kwatsam muka wayi gari da mumunan labari kuma Allah yaiwa mahaifin mu rasuwa washe garin da dawowan umma daga wurin shi din .
Ganin mutanen gidan mu nata kokekoke idan an ganmu sai a kama yan kamay kamay don kada mu gane nice na fara fahintar abinda ke wakana a gidan namu.
Inda na tsura umma da taron mutane a dakin ta masu zuwa ta,aziya suna fadin ashe ba nisa tsakanin shi da matar shi don yanzu da rasuwanta shekara biyu ke nan tsakanin su.
Duk da hankali bai gama shigana ba lokacin hakan bai hanani fahintar maganan da sukeyi ba ihun da na yanka daga inda nake ne ina fadin wayo baba, ya fargar dasu ina wurin tsaye .
Kafin su taso zuwa inda nake na zube a somay kasa take sukayo kaina gaba dayan su sai fadin suke basu san da labarin rasuwan nasa bane dama ?
Umma fadi take may zan gani haka kuma Allah ka dubeni da ido rahaman ka ya Allah tana fadi a cikin wani irin yanayi na tashin hankali ganin ana zuba min ruwa ban farfado ba yasa take wanan maganan hankali a tashe.
Kururuwan da sukeyi ne ya dawo da hankalin mazan dake waje a cikin gidan hankali a tashe suka shigo don ganin abinda ke faruwa.
Can kuma kanina wani ya tare shi yana fadin Allah sarki ashe kuma mahaifin ku shima ya rasu bayan mahaifiyar ku din.
Da ya fara ihu daga van bai tsaya sauraren maganan shi ba yayo gida yana yanka ihu a cikin tashin hankali sai ya samu kuma ana fama danibin farfado daga suman da nayi.
Daidai lokacin da ya shigone aka samu nayi dogon ajiyan zuciya sai fadi suke barka ta farfado yayo kaina yana kuka tare da fadin hadiza mun shiga uku ance baban mu ya rasu yau.
Rungumay juna mukayi gaba dayan mu muna sake wani irin kuka na maraici a tsakanin mu da yan uwana duk tsawan da suke muna bama jin su a lokacin.
Don haka dole aka kyale mu don abin kuka ya samay mu a lokacin ba mai iya hana mu yin kukan don suma kukan sukeyi a lokacin.
Ranan dai muna a cikin tashin hankali da ba zan iya muku bayanin shi ba saboda halin da muke ciki ba wanda yai zancen cin abincin da ake kawo muna a ranan .
Washegari ne baba kabiru ya iso da yan kayan da baban mu yayi jinya a wurin tare da yan kudaden da ya bari wanan ya kara tayar muna da hankali muka tabbatar da mahaifin namu ya rasu kuwa.
Muna manne dashi yana kokarin ganin mun da sake sai magana yake bamu don mu dan sake jikin mu dasu.
Sai dai ina nikan kamar kara tunzura ni ma sukeyi don ban iya ci ban iya sha a lokacin sai aikin kukan da nakeyi don tashin hankalin da nake ciki don na fi sauran fahintar halin da muka shiga a yanzu na rashin iyayyen mu din.
Sai da baba kabiru ya nuna min bacin rashi sosai ga rashin kin cin komai da nakeyi ne yasa na dan daure nasha kunu a gaban shi kadan.
Muna manne da umma wace yanzu nauyin mu ya koma kanta muna ganin ta komai namu a duniya duk da mahaifiyar maman mu tana nan da ranta a duniya.
Sai dai ba sabawa mukayi sosai da ita ba don mun fi sabawa da umma don da ita muke zaune akoda yaushe.
Wanan mutuwan ya tayar da hankalin mutane sosai a kauyen mu don yanzu ne mahaifin mu yake a ganuwan samun arzikin shi sosai a duniya.
Sai kuma Allah yai nasa ikon akan shi ya raba mu dasu a daidai lokacin da mukafi kowa bukatan su daga shi har mahaifiyar mu a duniya.
Kwanan baba kabiru uku bayan sadakan uku ne ya kebe damu yake fada muna shi zai koma zai tafi ya tattara kayan mu dake can abuja.
Don yanzu zaman mu ya dawo nan ke nan da sauri nace baba karatun mu fa yace zamu duba wanan idan mun dawo sai mu san abinda za ayi akai.
Abinda nake so daku shi ku kwantar da hankalin ku ku natsu ku rage wanan damuwan da kukeyi alabashin hakan zai sa muma hankalin mu ya kwanta mu samu natsuwan yin abinda ya dace a kan ku.
Ya bar muna wanan kudin da yazo dashi yace muyi amfani dashi kafin ya dawo mukai mashi godiya ya tafi bayan ya gana da umma da yan uwan shi.
A kwana na uku ne mukaga su baba yushau da baba musa sun shirya ashe tare zasu tafi abujan don ganin abinda mahaifin mu ya bari a can din.
Har lokacin gani nake a raina kamar zamu koma Abuja ne ba a nan zamu zauna ba ban da wani sukuni a tare dani idan kaji muryana sai idan yan kannena ke wani abinda bai dace ba na tsawa ta masu.
A rana ta bakwai da rasuwan mahaifin mu ina kwance saman gadon karfen umma dake dakin don yanzu gaba daya a dakinta na tare din tsoron dakin mu nake ji gaba daya.
Yaro yazo yace wai Jamil yana sallama dani kamar banji yaron ba sai umma ne ta bashi amsa da fadin wanan mai bakin nacin kaje kace dashi ba zata zo ba.
Summaiya ce tace haba umma ki bari taje su gaisa mana kila gaisuwa yazo yai muna kuma kin kore shi da fadan kin nan.
Dakuwa ta sakar ma summaiya da hannun ta tana fadin ungo naki ni kike fadawa wai gaisuwa yazo yai maku kunfini rashi ne ni da dana ne ta rasu kuma nayi hakkuri da rashin shi.
Sai mikewa nayi daga inda nake kwance ba tare danayi mata magana ba zan fita tace wai fitan zakiyi ko baya na hana.
Umma ba dadewa zanyi ba gaisawa kawai zamuyi dashi in dawo na bata amsa na fice ban tsaya jin abinda zata fada min ba.
Na samu ya juya zai tafi na kirashi ina fadin gani ya juyo fuskan shi ba yabo ba fallasa a cikin shi bayan mun gaisa ne suke fadin ashe kuma baba lokaci yayi.
Idanuwana suka kawo hawaye nace muma haka wanan zancen yazo muna ashe iyakar mu dashi ke nan daya rakomu shiga mota da zamu zo nan.
Sai hakkuri do mutum baya wuce lokacin shi kece babba idan yan uqan ki suna ganin ki a cikin damuwa suma ba zasu sake ba yace.
Duk maganan da take kaina yana kasa ina hawaye a lokacin don ban iya kara furta komai saboda tunanen mahaifina da nakeyi a lokacin.
Abokin nasa ne yace yanzu komawa zakuyi abujan ko may ake ciki tunda ance kuna da gida a can ai nace cikin muryan kuka ban sani ba sai dai babu alaman zamu koma can din .
Don naji su baba kabiru sun tafi hada kayan mu dake can yanzun haka suna can basu dawo ba tun shekaran jiya suka tafi.
Ajiyan zuciya naji jamil din ya sauke tare da fadin nima tunanen da nakeyi ke nan idan kun koma can dawa zaku zauna acan yanzu kuma.
Muryan umma ne ta fito da tocilan ta tana haska muna tare da fadin kaikan wanan yaron idan kana maita sai ka cinye yan gaein nan a baki dayan su.
Ke kuma munafuka maza ki shige tun ban bata maki rai ba a furin nan yanzu simi simi na wuce ta tare da fadin sai da safe ku na gode na barsu da ita a gurin.
Bata shigo ba sai data dan dade dasu ban san dai yadda suka kwashe da ita ba don ko da ta shigo har na kwanta abina ta karashi fadan ta kala bance mata bani dai.
Kuyi hakkuri da wanan yanzu muka dan samu wuta kuma har sun dauke muna ko wai gyara sukeyi.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
5/18/21, 11:49 PM - 🤔🤔🤔: 🙆🏼♂️ KANIN AJALI 🙆🏼♂️
🔟
ZAINAB IDRIS MAKAWA
FATAN ALHERI GA YAN UWA MUSULMAI ALLAH YA BAMU IKON CIKAWA DA IMANI A ZUKATAN MU YA BAMU IKON BAUTA MASHI BAUTA TSAKAKKIYA ALLAHUMA AMIN 👏👏👏👏
LITTAFINA NA KUDINE DON ALLAH IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA YAR UWA DON GUDUN SHIGA HAKKIN JUNAN MU , , , , ,
Dawowan su baba kabiru daga abuja muna ta jiran muji wani bayani sai mukaji sheru ba suyi muna bayanin komai ba ga hutun makaranta ya kare ana shirin komawa a lokacin.
Hakan ne ya kara tayar muna da hankali so sai ganin bamu san mafitan mu ba a wanan lokacin zamu koma ko ba zamu koma abujan ba mu dai gamu nan dai ne.
Baba kabiru ya shigo garin ya samay mu yake fadin mu shirya muzo birmi don a san abin yi a kan karatun mu.
Da muka tashi zuwa tare muka zo da