Showing 63001 words to 66000 words out of 106121 words

Chapter 22 - kanin Ajali Book Complete by Zee Makawa .txt

Advertisement

01 Jan 2025

8073

bashi ya kawo muna wai kayan sallah mu ke nan.
Da farko har ina munna na shirya zuwa gaida mutanen gidan mu anty na kallo na naga bacin rai karara a fuskan ta sai wata kanwata take ce min.
Ke ko anty harda sallah baku gyara kowa na zuwa acan acan dashi ke sai ki zo muna haka ba dadin gani dake har yar ki don tunda yan kayan yarinyar da anty ta saya muna masu tsada na haihuwa sukayi mata kadan yanzu na koma mata yan kamay kamay.
Don ban iya saya mata don banda shi gaba ban dashi baya sai dan abin da ya kawo muna muyi amfani dashi.
Raina bace nace wa kanwar tawa wanan da na saka kika raina shine ya saya muna shi na sallahn mu ke nan daya sawo muna.
Wanan ai mama ta mutu ne gwanjon lace din lagos aka gyara wani irin bacin rai naji da suke maganan nan dai na rufe ido naci masu mutunci yinin da banyi ba ke nan na fito na koma gida na cike da bacin rai.
Tun da na tun karo gaban unguwar mu naga mutane suna kallo na haka na dage kai na wuce ban tsaya gaida kowa ba.
Wai ashe sun shige ke nan dashi da ita na biyo gurin shine idon da mutane suka saka muna don gudun kada tsotsayi ya hada mu dasu a hanyan.
Ba wanda ya iya fada min hakan sai wata tobashiyan shi data zo muna yawon sallah take tsokana na da fadin yanzu shi kuma mijin ki har lalacewan shi ya kai shi ga bin arna arniyar ma wace ta haifeshi.
Har ya fito kerare yabi hanya da ita da uban ranan nan kowa yana kallon su bai ko jin kunyan idon mutane da nauyin su.
Wani iri naji a raina yake na kama mata har dai na samu ta wuce bata gaji da zubawa ba raina yanaz bace.
Fitan ta na shirya sai gidan da mahaifin shi yake naje da kuka na nakai masu maganan da nake ji a unguwa yana cewa karya da kazafi ake mashi.
Sai da mahaifin nasa ya gama saurare na yace min ke kin tabbatar da hakan ko kin gane su da idanuwan ki haka dai yayi min magana ta baibai ta yadda ban gane komai da nake fadan akai.
Abinda ban sani ba ashe tsohon yasan da wanan zancen har kayan sallah ta dinka mai da kayan azumi shine rashin kama min da bai yi din ba dana zo da zancen.
Sai daga baya duk nake jiyo hakan a wurin mutane sai dai nasa a raina cewa tunda yace naga hakan da idanuna na hake sai na kama su din da idona.
In da na na bar zancen a raina ba tare da na shedawa kowa zancen ba na koma normal life dina shima ya dauka na bar wanan zancen ne yaci gaba da harkokin shi kamar yadda yakeyi a baya.
Har akai shagalin sallah aka gama ban kara fita ko ina da sunan zuwa unguwa ba ina gidana kumshe sai wanda ya tuna dani yazo gurina dubani a cikin yan uwa.
Matsalan dake damun yan uwa na dani shine yarda da wanan zuwaira din danayi hundred pacent a raina don duk shawarana yana gurin ta duk da na girmay ta nisa ba kusa ba kuwa.
Don ko sa,an kanwa ta summaiya batayi ba ga haihuwa amma haka muke mu,amula da ita duk shawarana yana gurinta wanda ni ban ganin laifin hakan da mukeyi da ita.
Wanda hakan shi Jamil din ya kidanya min yana so dani adole in kirata da anty kuma mu kama mu,amula da juna kamar yan uwa.
Ashe ban sani ba kuma yadda muke haka ya dauki wanan farkan tashi yakai gurin su suna mu,amula da ita tana masu abin arziki wanda ni nawa sun gama dashi ko an taru an cinye duka an barni da tunane.
A cikin haka baba kabiru ya samo min aiki sure p da aka bude maimakon in bada nomber wayana sai Jamil yace in bada nasa don ni a lokacin banda waya a hannu na dole idan kudin sunzo zasu fada a wurin shi iyakata account dana bude da kaina kawai amma dole sai yaga alert ga wayan shi.
Fitowan farko aka bamu na wata uku a jere tunda ya like min sai da aka ga bayan kudin dan abinda zance na tsira dashi shine kawai kudin da ya sai muna abinci dashi na gida naci wanan ne kawai ba zan ratse ban ci ba daga cikin kudin.
Yanzu abin da dama sosai a tsakanin mu tunda ina samun yan kudade suna shigo min ta hannu na sai dai duk da hakan sunane don zaice nasa albashi yayi wani lalura dashi nawa zamuyi dan amfanin gida dashi saboda rashin tausayi.
Don yasan da zaran ya bata rai hankalina tashi yakeyi sosai sai na bashi ATM ya ciro su za a zauna lafiya tsakanina dashi.
Ga ido da yan gidan mu suka saka mi da yawan tambaya may nakeyi da kudina ne basu ga wani canji gurina ba ko a dakina da jikina.
Duk da kowa ya san shine may karbe kudin yana min wayau don shikan wallahi yayi kiban shi bulbul dashi ga sutura kamar zai kashe shi na alfara da yake sakawa jikin shi sai kamshi idan yabar guri da zai bar mutane suna shaka.
Na koma bagidajiyan dole saboda aure zaka rantse ban taba shiga boko nasan duniya ba idan ka ganni a cikin hakan na samu ciki na biyu a gidan shi.
Kanwata ta haihu bayan ta share shekara a dakin ta ba haihuwa anyi shagalin suna lafiya mijin ta yai mata sha tara na arziki duk da naji yan gidan mu suna fadin itama da kudin ta mijin ta yake mata abu sai dai yafi nawa.
Don su ana gani a jikin su da dakin su komai nasu acan acan yake ba kamar mu da muke a tauye ba nida yar diyata a gidan mijina.
Rufin asirina guda shine aikin da baba ya samo min wanda bai hana inga laifin baba din a idona ba duk wanan abinda yake min duk da shima yana da nasa diyan da ya haifa suna bukatan haka a gare shi kuma.
Amma ya rike mu fam yayi watsi da duk abinda mutane ke fadi a gamay dashi ya yi watsi da maganan kowa kan mu ya rungumay mu tsakani da Allah.
Sai dai zugin Jamil a kanshi yana aiki a kaina don duk wanan kokarin da yake muna sai jamil din yace wai bai da hali bai taimaka muna don bai bamu kudi .
Ko yace wai sun haye muna kudin gadon mu sun barmu muna wahala sun saka muna ido don basu suka haife mu ba idan da badon yana gudu mutane su gane ya cinye muna kudi ba ba abinda zai sa ma ya kula damu.
Ire iren wanan maganan da yakeyi tun bai tasiri a zuciyar mu har ya fara nan zamu taru a gidana da yan uwan haihuwana mu kulla mu warware a tsakanin mu.
Gashi kamar kudin uban shi ko da mahaifin shi ne ya mutu iya abinda zai iya ke nan a kan kudin mu gashi ban taba jin yana ma mahaifa addu,a ba a gaba na koda na rana daya ne.
Karamin mu ne da aka samu kudin nan anty tasa ya sai tabarmi da butoci ya baya a masallatai sadaka mukan ta bimu har ta gaji bamu sai komai mun bada sadaka ba.
Ni ina ma naga kudin tunda banda ta cewa alan kudin sai yadda akayi dani dasu yanzun ko ancinye an koma jin haushina.
Ni dai ga wautana burina shine a zauna lafiya a tsakani na dashi na dauka yi hakan shine zai kara sa muna yarda da kauna a tsakani mu dashi.
Ashe van san ba duka maza ne suka san hakan ba a rayuwan su don ba zance ba za, a rasa wanda keda rikon amana ba sam.




Don girman Allah kuyi hakkuri ba laifina bane haka Allah ya tsara ma lamarina wallahi wallahi wutane bamu da har yanzu nakai caji wayata ta samu matsala dole yau sai da na sayi wata still bamu da wuta har yanzu don trasfomer din mune ya buga.
5/18/21, 11:57 PM - 🤔🤔🤔: Na samu wannan kawana dake makwabtan mu tasa mijin ta ya dauko muna manja da garin rogo a can inda yake da zai dawo.
Ita nata zata aika dashi ne gidan su a sayar ni kuma tace in saida nawa a nan cikin unguwar mu din tabar min sai idan mun sayar zamu tura mai kudin ya kara sayo muna wani.
Alhamdullahi don sana,ar ta karbu min a cikin unguwar tamu da farko da Jamil ya gani ya fara tambaya a ina na samo kudin da na sai wanan abin ?
Ban so in fada mai ba amma danaga matsin yai yawa yana tambaya don zargina yake ko na samu wasu kudine naki fada mai don har bugun cikin baffa kanina yayi a waje bai ji komai ba.
Dole na fada mai inda na samu kayan ina sayarwa din nan ya hau fada wai yarabani da wanan matar don ta fini wayewa shi bai son rikici da dauko magana.
Na dai kyaleshi yayi fadan shi ya gaji ya sa mun ido mutane sai shigowa suke dare da rana suna fadin abasu manja ko gatin kwaki da sugar.
Dadi dadi na hada kudin farko don a cikin sati biyu komai ya kare muka tura ya sake turo min da wani don ita ma an sayar mata da nata acan gida da ta kai.
Wanan ma yayi saurin karewa da wuri don yanzu mutane sun sanda ina sayarwa kuma a cikin sauki na hada kudin mijin kawata cif da sunan washe gari in kai mata ta tura muna wurin mijin nata.
Washe gari tun da safe Jamil ya fita kan zai tafi wani kauye yace min a can zai kwana don haka sai dana gaba duk aikin gida na shirya na nufi inda na aje kudin don in shiga in mika mata.
Kudi yace dauke ni inda kika aje sai da na dafe kirji na nakai kasa don capert nake dagawa na aje ba wanda yasan inda nake aje kudi a dakin idan na hada su.
Don gudun haka tunda nasan halin shi da kudi ni kadai a daki sai zufa ke karyo min a lokacin don nasan babu wanda zai dauki kudin nan sai Jamil din don ba mai shiga dakina har kurya.
Ko baki nayi a falo nake ajesu basu shiga min daki, don kunyan dakin da nake ji ni kaina ban son wata mace yar uwana ta shiga min dakin.
Don haka ban zargi kowa ya shigo min daki ba na rasa yadda zanyi a lokacin sai daukan diyana nayi na nufi gidan da mahaifi shi yake.
Duk da nasan abu mawuci ne ya goyi bayan dan nasa a lokacin sai banda yadda zanyi dole in je gurin shi da wanan maganan.
A gigice na isa gidan muka gaisa dasu sai na fashe da kuka na fara fada masu halin da ake ciki budan bakin mahaifin nashi tun ban karasa ba shine.
Kina nufin Jamil ke nan yai maki sata ko wa da kika zo nan din ranan matar mahaifin nashi tayi min abin kwarai don kafin in magana tace .
Haba malam idan bata zo nan ba ina kake son taje da wanan abin kunyan kai kullun danka bai laifi itace mai laifi haba a rika yin abu don Allah mana.
Yarinyar ga dai tana iya kokarin ta wurin ganin ta kyautata mashi amma hakan bai isa ba sai an hada da dauke na mutane da ta dauko kuma yanzu mai kake son tace ma mai kudin do Allah.
Ai sunan danka ne zai baci a unguwar tunda kowa yasa halin shi a gareta ido kawai mutane suka sa masu hakanan.
Naji dadin wanan maganan har cikin raina don yau ta fadi alheri a gamay dani bayi son zuciyan da suka saba ba.
Fada ya hau yi da ita amma bata barshi ba dole tsohon ya sauko tare da fadin nawa ne kudin na fada mai yana gyaran zama yace sai dai ayi raba daidai kije ki nemi saura ki cika masu kudin su.
Ya kirga rabi kamar yadda yace din ya bani na fito ina share hawaye ina zan shiga cikin garin nan in samo rancen kudi in ba mutane kudin su.
Ko dana koma yan gidan mu ke fadin matar tazo nema na sai da gaba na ya fadi lokacin haka na daure na shiga gidan ban boye mata komai ba na fada mata halin da nake ciki da kudin na bata rabin da mahaifin shi din ya bani.
Na bata hakkuri kan zan nemo sauran in karkare mata in an kwana biyu hakkuri ta bani na fito ina hawaye gidan zuwa gidana.
Bai dawo ba sai bayan kwana uku ya dawo in da ya samay ni zaune a cikin tagumi ban ko iya mai sannu da dawowa ba don zakace ba kauye ya fito ba da yace yaje.
Shi sai wani fresh yake karawa ni ko ina figewa banda wani kumari a jikina ko kadan daka ganni, kasan damuwa ya samu gurin zama a zuciyana.
Ganin yadda na fuske shima ya fuske ya shiga daki ko may yayi a ciki can ya fito yana fadin ke lafiya kuwa mutum ya dawo ko sannu da zuwa ba zaki mai ba.
Wani kallo na watsa mashi tare da kawar da kaina daga kallon shi ina fadin azzalumi baiji dadi ba wallahi.
Ka rasa wanda zaka yaudara sai matar ka ta gida mai dawainiya da yayan ka duk wani nauyi da hakkin ka ka rataya a kaina .
Haka bai ishe kaba sai ka hada da kudin mutune ka kwashe ka tona min asiri a gari.
Ya zaro ido yana fadin wa kika mayar barawon ki gida nan nace kai tas ya kwashe ni da mari sai da ba dafe wurin don zafi.
Hakan bai sa na fasa magana ba nace ka kashe ni ka huta dama nasan mutuwa ta kake son ji macuci kawai azzalumi.
Ba wanda zai shigo ya daukan min kudi dakin nan sai kai ba zan zargi kowa ba wallahi don kaine ka kwashe su .
A harzuke yace an kwashe din kiyi abinda zakiyi in zaki iya wawiyar banza kawai kan wasu raggan kudin ki zaki dinga kirana da macuci can kudin da ko mota basu isheni shiga ba.
Nace baka nayi da zakace kada in kiraka da macuci ya kara daga hannun zai mare ni na sa mai ihu sai ga yan hanyan gidan a sukwane sun shigo suna tambayan ko lafiya ?
Ina kuka na fara fada masu abinda yai min don duk cin kudina da jamil keyi wanan din yafi bata min rai sosai wallahi.
Don ya nuna min bai damu ba duk halin da zan shiga da mutane ni na sani ke nan shi ba damuwan shi bane hakan.
Bayan sun gama ji ba mai shiga tsakanin miji da mata sai cewa sukayi inyi hakkuri in kyaleshi mu san yadda zamuyi kudin mutane ya fito.
Haka suka dinga fita daya bayan daya suka barmu a dakin dagani sai shi ya shiga kuryan daki ya fito yana fadin wawiya da bata san ciwon kanta ba.
Da kika fada masu kwatar maki zasuyi ko may ai na dauka zasu sa in biya ki ne dole ina kuka nace Allah dai zai kwatar min hakkina ba wani ba.
Mu kai ta yada ma juna bakaken magana har ya gajibya fita daga gidan ya barni nan ina tukukin bakin ciki da na daman auren shi.
Sai mutum daya ne cikin yan hayan mu ya iya mai magana kan abinda yakeyi din bai kyauta ba gaskiya kudi mutane ne fa ya dauka kuma ya sani yaya yake son inyi.
Don Allah Jamil idan ka samu kudi kaba wanan yarinyar kudin ta don hakan zubar mutunci ne a gurin mace wallahi .
Kaga dai duk cikin matan mu tafi kowa hakkuri yau gashi kakai har ta tona maka asiri a bainan jamma,a haka ai irin haka babu dadi.
Jamil din yace ta dai tona ma kanta tunda bata da wayau don kawai na dauki kudin ta zatai min wanan tonon asirin haka a idon jamma, a.
Mutumin ya sake fadin ai abin ne da cin rai jamil yace malam naga fa kana son shiga hurumin da ba naka ba gaskiya yace a, a niba haka na bane ina dai guje maka hakkin marainiya ne a kan ka.
Kada ka manta matar ka marainiyar Allah ce ta gaskiya kowa kuma nan yasa tare kuke cin kudin gadon ta idan ya samu aiko kaga hakan tayi kokari wallahi.
Don ba ko wace mace bace yanzu zaka samu haka nan yace kada ka fada min maganan banza Nasir ina ruwan ka ne da zancen mu wai da matana.
Basuji dadin juna ba da mutumin nan kowa ya fadawa dan uwan shi bakaken magana ya kulla da wanan mutumin da yake gani wai ya raina mashi wayau shi.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login