Showing 36001 words to 39000 words out of 106121 words
Chapter 13 - kanin Ajali Book Complete by Zee Makawa .txt
imanin ubanginjin mu Amin.
Anyi zaman uku aka watse lafiya tare da jimamay rashin umma da mukayi lokacin bamu da kowa sai Allah sai baba kabir da matar shi anty da ta rikemu amana a hannun ta.
Do muna ganin tafi muna duk yan uwa a gurin mu tunda ta zauna damu da zuciya daya sai muka kara mayar da ita uwa sosai a gare mu da muke da ita yanzu a duniya.
Soyayyan mu da jamil yana nan duk da ba wani karuwa da nake samu a gurin shi a matsayin na wace zai aura sai dai zuciyata da gangan jikina ya yarda dashi dari bisa dari sosai.
Itama sumaiya duk da farin jinin da take dashi na samari hankalinta yafi karkata akan wanan usman din da jamil ya hada ta dashi saboda karin kwarin gwiwan da nake bata .
Wanda ita ma anty takan ce ai gara dashi din yafi mata jamil do shi yana da ilimi ana sa ran alheri a gare shi nan gaba don ilimin da yake dashi din.
Ya gama ya jona karatun master din shi duk suna tare da summaiya din har lokacin dole kowa ya kawo ido ta zuba muna don babu daman magana sai mutane damu suce ai don basu suka haife mu bane suke muna hakan.
Shinedalili su na saka muna ido a gidan ba tare da sun matsa muna ba sai dai yawan magana dake damun mahaifin mu din akan mu tundai ni na naki aure ya sa min ido yasa baba kabir din amincewa da jamil din yanzu.
Sai dai kuma inda matsalan yake babu wani zancen auren shi a gidan su don bai da wani sana,a takamaimai da yake amma koda yaushe zaka ganshi fes dashi kamar dan wani gwauna ne don karya.
Ban taba hango illan hakan da mutane ke gani ba akan Jamil din asalima ni dadin ganin shi hakan nake ji don ina ganin na haska a gari ai tunda ina da mutum kamar Jamil a tare dani.
Ana cikin haka ne mahaifin jamil ya tattaro ya dawo birni da zama gaba daya da iyalan shi suna zaune a gidan da yayan jamil din ya gina don yana aikin soja ne shi.
Yasa ya dankara gida a birni sai mahaifan nasu suka tare a ciki kanin shi kuma yai aure ya zauna tare da matar nasa a ciki baba kabir yana daukan shi wa a gurin shi sosai don alakan zamantakewan tare tun iyayye da kakanni a gida.
Yaje ya samay shi akan zancen namu sai mahaifin nasa yake fadin shikan ina zai masa aure yanzu baida wani cikakken sana,a da yakeyi.
Baba kabir ya dawo gida da bacin rai babu yadda zaiyi ya zuba min ido maganan ta zauna a kan hakan yace in fito da wani ya aura min tunda ga abinda mahaifan jamil din suka ce.
Anan inda akai maganar na bar zancen ban kara bi ta kan zancen ba zai zo wuna mu sha hiran mu ya tafi har dai abin ya ishi baba ya nemi shawaran yan uwan shi akan zancen namu da jamil din.
Baba musa yace idan ban fitar da wani ba ya aurani ga wanda yake so mana ai dole in zauna ko ban wa Allah tunda na zama abinda na zama a cikin dangi.
Shi bai taba ganin yarinya mai taurin kai irina ba a rayunwan shi sanyi hali irin na baba kabir din ya sa ya daga min kafa ga zancen.
Ina zaune gida ga masifa da kanne na a gidan ban bar diyan su sun sakata su wala yanzu za a ji mu dasu wanan abin yana yawan bakanta ran baba kabir sosai sai dai bai yarda yayi ko ayi muna abinda ran mu zai baci.
Da abin ya ishe shine ya tayar da yan hayan gidan mu da aka saya muna daga baya ya shiga gyaran gidan gadan gadan sai da ya kusa gamawa ne yake fadin ya tsayar da ranan bukin mu da jamil.
Ya samu iyayyen jamil ya sheda masu basuyi wani na,am da zancen ba sai dai a gaban shi matan mahaifin nashi sun nuna farin cikin su a gaban shi.
Babu kuya mahaifin Jamil bayan kwana biyu ya aika yana neman baba kabir da shawara bai ki zuwa ba ya samu lokaci yaje gurin amsa kiran mahaifin Jamil din.
Sai cewa yayi da baba yana nema alfarma akan maganan da yazo mai da ita yana son gidan da zamu zauna da jamil din a gyara masu dayan part din amaryan shi ta zauna a ciki don barin yara su kaidai haka bai da alfanu.
Kawaici irin na baba kabir sai baiki hakan ba amma yayi mamaki da jin hakan daga gurin dattijon da ya iya taro shi da wanan maganan haka babu kunya babu tsoron Allah a cikin sa.
Sai a lokacin ya kara hasko maganan mahaifiyar su umma sosai akan zurian su Jamil din da take fadi har ta kwanta damanta ba mutanen arziki bane su.
Ya dawo gida da zancen nan matan shi suka shiga tofa albarkacin bakin su kan zancen don mai zai yardan masu da hakan yasan ai ba ni kadai bace da gadon gidan da za a mamaye ma yan uwana samun su a hana su don wasu.
Fada baba yayi kan su bar zancen a dai samu ayi auren kowa ya hutu zaifi alfanu idan anyi hakkuri komai sai yazo ya wuce ai dole suka ja bakin su sukai shiru akan zancen.
Ni dai duk hakan ina ganin ai ba illa bane a gareni don an taimaka masu da wurin zama ba zai zama abin magana ba kuma.
Ga abin magana mutaje na gani babu halin a maganta don baba ya hana maganan sai dai ayi a bayan shi don bai ba da kafan yin hakan ba shi dai gurin shi ya sauke nauyin daya rataya namu a wuyan shi yanzu.
Dole ba don anso ba kowa ya saka ma zancen auren nawa ido aga iya gudun mu da baba kabir din har iyayyen nasa da suka zo da wanan korafin .
Sannun a hankali kamar yadda ko wace budurwa takan yi shiri bukin ta nima haka din ne a gurina sai dai mai karatu idan nace maki ko cibi ban aje ba na kaina duk ko da Sana,an danayi a baya kada kiyi mamaki.
Amma haka baba kabiru ya fitar da makudan kudi ana mun sayayya yakuma ce a tambaye ni irin kayan da nake so na daki ai min anty ta ritsani sai cewa nayi ni roses nake so tace dani yanzu an bar yayin du ka crystal nan sun fito su ake yayi nace ni dai roses nake so a lokacin haka yasa ta shiga nema min roses din ta samo masu kyau da daukan ido aka saya min.
Duk wani kaya na jin dadin amare sai da baba kabiru din ya saya min su don dai kawai ya fitar min da hakkina a kanshi nan aka fara kudindumin a cikin dangi kan zance shi dai baice da kowa kala ba kan bukin.
Ance rana bata karya sai dai uwar diya tayi kunya don ranan buki yazo saura sati uku bukin mu da jamil iyayyen shi suka tare a gidan namu.
Babu kunya ko nauyin hakan a tare dasu alai,alai abinsu a gidan namu na gado babu nauyi ko kunyan hakan a tare dasu udan anyi magana sai suce ai gidan diyan dan uwan su ne suka zauna ciki.
Don dan su dake soja ya nuna masu bacin ranshi kan hakan da yake mahaifin nasu mutum ne mai bin ra,ayin matan shi sai bai ganin illan yin hakan don ita amaryan nasa burin ta tabar gidan dan kishiyar nata da take zaune a cikin sa a lokaci.
Ni kuma na samu daurin gindi a gurin baba kabir ba wanda ya isa ya fada min gaskiya abinda ake kullawa kan hakan akwai illa a cikin sa.
Gani raguwa inji anty yaya zama da sarakai zaiyi dadi irin yadda nake nan ban san ciwon kaina sai dai ance fadan dayafi karfin ka sai ido kawai.
Haka yasa dole suka saka ido har saura yan kwanaki buki dangi suka fara halara gurin bukin inda a bangaren Jamil ma haka ne don dangin shi sun fara isowa gidan.
Kai duniya wanda baida mafadi baiji dadin duniya ba wallahi don rawan kan da nake wai ni a dole ga amarya kowa na kallo na a hankade niko ban damu ba gurina kawai inga na malki mijina a hannu na a lokacin.
In huta da zama gida cikin wahala da maraicin iyayye dake damuna ko yaushe don duk wanan gatan da kokarin baba kabiru a kan ni ban ganin hakan komai da ake muna ragaggene a gurina.
Don nakan ce da mahaifana su na raye da abinda za ai min sai yafi hakan ai ga gulman dagi yan hana ruwa gudu da suke zugani wai ai da dukiyan mu ne baba kabiru yake mun komai.
Wanda wauta da kurciya a lokacin ya hana ni hango gaskiyar maganan da zufan shi yake muna komai da yake yi din bada dukiyan mu bane don har lokacin komai na mahaifin mu bai fara fitowa ba.
Har aka sakani a lallai babu wani motsi na al,ada daga gidan su Jamil da akewa amare irin kayan da ake kawowa din nan.
An gulma ya fara tashi a tsakanin yan uwa da abokan arziki kan rashin wani motsi daga bangaren angon nawa inda shi jamil sai harkan yadda bukin namu zai kawatar yake a bangare shi.
Sai ana saura kwana biyu ne daurin aure wata yar shi da suke uwa daya suka zo gidan mu anyi masu taro na mutunci sosai inda suka kebe da anty uwar amarya suna bada hakkurin rashin jin su da ba ayi ba din akan lokaci.
Anty cikin fara,a take fadin ai babu komai duk gida ne damu dasu bata nuna masu komai a fuska sun dan zauna sai can dai a kunyace ta bude hijjabinta ta fito da yan turamay ko a leda tsiya bai bari sun saka su ba guda shidda wai gasu nan in fitan buki dasu daga baya idan sun samu hali ina gidan su zasu saya min.
An karba da godiya da sa albarka sai dan shin kafa shima kwano biyar da suka gabatar mata wai a kara ayi hidimar buki dashi.
Anty tace ai da baku wahal da kan ku ba don mahaifinta komai ya tanadar muna a nan sukace a daiyi hakuri a karba din Allah.
Bayan tafiyan su ne ta fitar da kayan wa mutane nan kuma zance ya tashi karshe sai fita daga gidan nayi don ban iya sauraren maganan su.
Dama baba ya saya min set din akwatuna da yan tufafin da yai min da zan saka aka kara zuba kayan da suka kawo a cikin akwatin.
Shi dai baba sai fadin Allah dai ya bamu zaman lafiya ace gara da akayi albarkan auren ake nema ba kyalekyalin auren ba.
Ga gida ya cika da yan uwa da abokan arziki ta ko ina a gidan don bukina kawai suka hallara wasu tsakani da Allah suka zo wasu kuma gulma aga karshen abin ne ya kawo su daga kauyen mu.
Shiko gogan sai waya muke a tsakanin mu inda yake kara karfafa min yadda nake a rayuwan shi da irin taimakon da nayiwa rayuwan shi din.
Anje an gyara min dakina komai tsone gwanin ban sha,awa dai kowa ya dawo yana yabawa irin kokarin da baba kabir din yayi don ba a ma maganan matan shi duk da suma sunyi iya kokarin su kan sha,anin.
Party kan har kala biyu aka sha don jin dadin buki wanda ya shirya da abokan shi yan karya anci ansha an gwangwaje a gurin an dawo ana bada labarin komai.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
5/18/21, 11:55 PM - 🤔🤔🤔: 🙆🏼♂️ KANIN AJALI 🙆🏼♂️
1️⃣4️⃣
ZAINAB IDRIS MAKAWA
LITTTAFIN KUDI NE IDAN KIN SAYE KIJI TSORON UBANGIJI KADA KI FITAR MIN DASHI DON AMANA NE A TSAKANIN MU KI GUJI NAUYIN AMANA A KANKI YAR UWA IDAN KIN GA MARA TSORON ALLAH TA FITAR KI GUJI SHIGA HAKKIN WANI YAR UWA DON NA BIKI DARI UKU AKAN NOVEL, , , , , , , , , ,
Duk wani abin al,ada na buki angama lafiya sai fatan Alheri ga auren mu da yan uwa da abokan arziki ke gabatarwa a gare ni.
Abokan ango sun rako ango daki daya sha gyara sai kyali yake don katan alatun dayaji wanda a kauyen mu kaf idan da ca muke nabar tarihi a kauyen namu don haduwan dakin namu.
Sai dai may bayan tafiyan abokan ango da kamar minti goma Jamil ya dawo daga rakiyan su yace hadizatul kubura yau dai Allah ya cika muna gurin mu akan jajircewan mu da juna.
Ina dan murmushi na bude fuskana ina fadin bisa ga taimakon baba kabiru bawan Allah muka samu wanan cikan gurin namu da yake Allah yace ni matar kace jamil.
Banda abinda zance da baba kabiru sai fatan Allah ya saka mashi da alheri yadda ya rike zumuci Allah ya bashi ladan zumunci kamar haka.
Duk maganan da nakeyi jamil sai bin dakin da wani irin kallo yake wanda ba zan iya fassara shi a lokacin na burgewa ne ko na wani abu ba.
Budan bakin shi bayan na gama magana sai cewa yayi dani amma dai ke har yanzu yarinya ce khadija wani kokari sukai maki a nan daki kamar na kauyawa.
Da mamaki na juyo ina kallon shi ya ce eh duk irin dukiyan da mahaifin ku ya bari da wanda ya tara maku wanan abin zasuyi maki ga auren ki ?
Yanzu dai ai kinga abinda nake fada maki ko da ina fada baki yarda yanzu don Allah wanan kayan yan kauyen tsohon yayi ya dace ace sunyi maki ?
Tsaye nayi galala ina kallon shi don jin abinda yake fada a lokaci wanda ban san amsan da zan bashi ba kan maganan da yakeyi din.
Yace eh na fada kuma gaskiya nake fadi da ke yar su ce wallahi ba zasuyi maki wanan wullakancin ba haka da komai na zamani zasu kawo muna.
Amma da yake ke baki da wayau har wani addua kike kokarin zabga mashi irin haka ni har kunya naji da abokai na suka shigo suka samu dakin namu a haka.
Yanzu jamil duk wanan uban kayan basuyi maka ba kake nufi yace wallahi basuyi min ba hadiza duk sake su zamuyi musai na zamani da ake yayi mu saka don abin kunya ne a gurina abokai na su zo suga dakin matana haka a wullakance bayan sun san yar gidan wanda na aura.
Na fada maki ba son ku suke da zuciya daya ba kece baki yarda kin kasa fahinta na duk lokacin da nake fada maki sai ki dinga daukan magana kamar ina son hadaki dasu ne.
To ai yanzu kin gani da idanuwan ki abinda sukai maki yar bare kike a gurin su kin fi nan gare su jima wani karamin tv da wasu kujeru na raini da suka saka maki a daki don Allah.
Yar su da suka aurar haka kikaga sunyi mata ke baki tunanen haka da bakin ki ke fada min irin tsaruwan dakin hajara yadda suka gyara mata dakin.
Kasa magana nayi sai tsayjn danayi galala ina kallon shi don yau na tabbatar mutum bai da kunya shi da ko pant ya kasa saya ya kawo min a matsayina na wace zai aura da kowa nasa ya kasa yi mai wani abin azo a gani a matsayin shi na dan su.
Sannan iyayyena sunyi min abin arziki zai zo ya rena mamakon ya yaba da kokarin su a kaina da yake dan duniya ne sai yace koda yake ke har yanzun baki san komai ba ai.
Don wallahi wanda suka sayar da gidan mahaifin ki a abuja ya fadi inda ba a karya kudin da aka sai wanan gidan naku zai iya sai maku ukun wanan ma don girman gidan mahaifin naku.
Kuma kin san gida a abuja tsadane dashi nina dauka ya aje sauran kudin ne ai don laluran ku kawai wallahi nan hankalina ya daga sai dai ina tuna zancen baba kabir akan maganan baba na bashin da banki ke binshi sai nace niko ina ganin baba kabiru ba zai muna haka ba gaskiya.
Ya bata rai sosai yana fadin ke may kika sani don Allah an barku a duhu ana cutan ku ya ja tsuki yana cire tufafin dake jikin shi fuska a daure.
Idan akwai abinda naki baga jamil ya daure mun fuskan shi shima yasan da hakan yaune daren auren mu dashi duk da ba farkon kasancewar mu tare ke nan ba.
Amma sai na koma fadin sun cuci kansu wallahi don mu basu cuce mu ba don amana muke a gare su dan uwansu ya haifa ya bar masu amana duk abinda sukayi mun barsu ga Allah.
Wanan maganan da nayi yasa ya dan sassauta daure fuskan dayayi da farko don ya fara shawo kaina ke nan don duk takona ya sani kamar yunwar cikin shi.
Mun raya dare mu kamar na sauran ango da amarya sai dai da safe kuma ya tashi yana cika yana batsewa duk a kan maganan