Showing 78001 words to 81000 words out of 106121 words

Chapter 27 - kanin Ajali Book Complete by Zee Makawa .txt

Advertisement

01 Jan 2025

8067

gari don zai sai min babban waya irin na kowa ni da ko nokia banda shi.
Sai yan uwa idan sunji haushi rashin wayana ya damay su zasu dan sai min yar nokia in rika bai kai wata daya a hannun na idan matsi ya kama mu in sayar in sai wani abin.
Gashi nima bakina yasaba da dadi irin na jamil yanzu ba ko wani abinci nakan iya ci ba in ba yan kayan kwalama ba da sauran su.
Ni dai ina jin shi yana ta tsara yadda yake so abin ya kasance wanan karon dariya nakan yi a raina kawai do ko da tsiya sai na gyara dakina wanan karon.
Nagaji da rufe kofa da boye boye wa kawayena idan sun zo gidana har kunyar yadda dakina yake nakeji don ko na wata tsohuwa yafi shi dadin kallo.
Ranan mondaya shi da kanshi ya rakani gidan baba kabiru tunda asuba don asubanci zamuyi mubar garin don mu isa da wurin during warking ahours.
Sai dai bai yarda mutanen gidan mu sun gashi ba yana isa kofa saida yaga na shiga ya koma shi bai shiga ba lokacin.
Nasan nasa wayau do kada aga zalaman shi a fili ne yasa ya boye hakan ya labe daga kofan gida yaki shiga daga ciki.
Mun isa lafiya mun samu wanan kudin a yadda sukai muna bayani suna da yawa sosai don haka zai fi na farko dana baya yawa ke nan .
Murna fal a zuciyana baki har kunne muka dawo gida da farin ciki zuciyar mu fara kal da jin wanan zancen.
Na samu ya gyara daki ya dafa abinci ya jera min yana jiran dawowana kamar ance mai da kudin zamu dawo dayani daga zuwan mu.
A gidana baba ya sauke ni suka tafi ina shiga na samu yana zaune yana jirana a cikin duhu duk da babu wuta a lokacin amma haka yake zaune kamar maye shi kadai a falon mu.
Nan yai muna sannu da zuwa ya karbi goyo na yana tambayan ta ya hanya kamar yarinyar ta iya magana lokacin.
Yace bari yai mata wanka don kada gajiyan hanya ya hanata barci shi yai mata wanka ya bata abinci taci ta kwanta tunda dama a gajiye muke.
Ya fara tambayana yadda akayi ina labarta mashi yayi wani irin ihun murna tare da fadin kice zamu faso gari ke nan sosai wanan karon.
Da yakw dan duniyan namiji ne bai barni na huta ba duk ko da gajiyan dana debo a hanya sai da ya kusanceni ranan .
Don kawai ya kara gyara min rai niko ina jin dadi a raina ga miji na tatali na ana sona don sai ka dauka ya daina halinshi ne yanzu na bariki.
Tun wanan ranan suka shiga yin meeting dashi da mijin kauwata wai idan kudi sun zo ga yadda zasuyi muna dashi .
Zakace abin na Allah ne ake shiryawa lokacin don sunce bazasu yarda su baba kabiru suna muna wayau ba ko wani lokaci duk da fa su baba basu karban ko kwandala daga cikin kason mu din.
Amma sun ce wai wayau suke muna kawai don sun dauke mu yara kanana suna yi muna yadda sukaga dama da hakkin mu .
Muko mun hau munga ga masoyan mu na asali masu kaunar mu da zuciya daya don Jamil yana cewa.
Da ke nan da baisan ciwon kan shi ba suke cinye kudin ba abin kwarai da mukeyi dashi yanzun kan tanadi sosai za a yi muna gaskiya.
Fadin haka da yakeyi yasa na kara yarda dashi sosai don na dauka talaucin da muke ciki yasa yanzu yayi hankali ne.
Mun dauka wani sati kudin zai fito a yadda aka nuna muna a can da mukaje abuja sai gashi shiru har mako uku ya share ba wani labari kuma na kudin .
Nan dai ya shiga kuma sake magana yana fadin kila ma su baba ne da sherin su kudin an sako basu fada muna ba kai ba dai abinda bai fadi kan kudin.
Har turani gida yayi in koma in tambayi baba cewa munji shiru baba dai yayi dariya yace hadiza banda abinki ko wancan karon ai haka akayi ko ?
Sai lokacin da muka ji su kin san gwaunati ba ayi mata dole tunda ba abin mutum daya bane abu ne na taro kowa dake cikin system din jira yake yi kamar mu.
Na dawo gida na fada mai abinda baba yace ya ja tsuki don takaicin da yake ji a lokacin yana fadin wanan shegen gwaunatin basu da tausayi wallahi.
Yakan yi maganan kudin nan kusan sau uku ko hudu a wuni shi dai ina ganin lokacin damuwan shi bai wuce yaji ance kudi sun shigo muna ba shine nasa.





ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU.
5/18/21, 11:57 PM - 🤔🤔🤔: Tun barin kanwata garin ya koma min ba dadi ni kadai nake harkokina don na dada maki tun farko jamil ya rabani da duk wata kawa da nake da ita a baya.
Haka kuma wa yanda ma a yanzu nakeyi baya bari muyi wani dogon hurda yake watse haduwan tamu a lokaci guda.
Sannu a hankali ya fara sayar da dan mashin din dana saya kudi suna dan shigo min ta hanyan mashi din .
Ni kadai naci kukana na share hawayena don ba wanda zan fadawa ya dube ni tunda kowa ya gama fahintar zaman mu da jamil din yanzu.
Don ko mutum ya nuna min kulawa ya shigs zancen mu daga baya zan iya ba mutum kunya in barshi a ciki da jin nauyi don zan dawo mu shirya da jamil din ne daram.
Wanan daliln yasa a yanzu ma ban san wanda zan kaiwa kuka na ya share min hawayena ba ta hanyar kiran jamil din yaji ba,asin zancen..
Har ya daukan mun mataki akan jamil din sai dai kassh babu mai iya kundun balun share min wanan hawayen nawa a lokaci daya.
Wanan dalilin yasa dole na hakkure da zancen nayi kuka na ni kadai ba tare da sanin kowa ba sai dai yan gidan mu suna dauka mashin din yana nan har yanzu.
Kanina Baffa na iya samu da maganan don yanzu ya tasa shima ranshi ya baci sosai da jin wanan maganan sai dai nasha fada a gurin shi sosai.
Na koma kamar nice kanwarc shi ba ya ba shi ya tunkari jamil da zancen mashin din kai tsaye ba tare da wani jin tsoro ba kamar yadda saura suke tsoron shiga maganan mu.
Sun buga sosai dashi don har ya kai su ga bacin rai sosai dashi inda ya fito fili ya nuna mashi yana cutawa rayuwana gaskiya.
Sai jamil din ya nuna mai ai shi ke da ikon komai nawa tunda shi yake aure na ba wani ba idan ina dashi muci in shike da ma ci zamuyi a tare.
Sai dai nayi zaton a yadda suka kwasa da Baffa din ba zai kara kallon kayana ba again sai dai ashe hali zanen dutse.
Don mai hali akace baya barin halin sa muna haka ne kamar ya lafa baya duban kayana sai harkokin shi yake yi .
Niko ina faman dan fadi tashi don kudi ya dan dinga shigo min tunda bai bani na kashi din koda ya sayar da abina kuwa.
Gidan iyayyen shi naje ranan gaida mahaifin shi ban wani dade ba na dawo gida misalin daya saura ina shiga falona a cikin sauri ban kula da cewa fridge dina bai falon ba sai bayan na dora girki na dawo don in huta.
Sai lokacin idona yakai gurin fridge din wayau na gani babu fridge babu dalilin shi a gurin .
Allah yasa a zaune nake don bansan lokacin da nayi bayan kujeran ba da yai min mazaune da wuyana na jingine dashi.
Sai dai na nemi kuka ko ihu na rasa a idona ko wani yaki zuwa a lokacin sai ajiyan zuciya nake faman saukewa don tashin hankalin da nake ciki.
Ina cikin wanan halin sai gashi ya shigo gidan niki niki da kayan abinci kala kala a hannun shi yana faman washe baki .
Ganina a wanan yanayin yasa ya sausauta fara,an da ya shigo gidan dashi yana tambayana ko lafiya ?
Da kyat na iya budan baki nace mai Jamil ina fridge dina cikin wani irin murya mai kama da ta mai kuka ko tashin hankali.
Bai bani amsa ba lokacin sai kokarin aje kayan abincin dake hannun shi da yakeyi ban damu da in san kayan ko damay damay ya sayo ba a lokacin.
Jin shiru yasa na mike tsaye daga zaunen da nake ina sake tambayan shi ina fridge dina jamil amsa ya bani a takaice da fadin na fitar.
Kakai ina na tambaye shi dagowa yayi ya juyo ya fuskance ni da kyau yace ya kike son muyi idan ban sayar ba na sayo muna abincin da zamuci .
Ko haka zamu zauna da yunwa baya Allah ya hore muna abinda zamu sayar muci abinci dashi ba sai naje wurin wani ina tona ma kan mu asiri ba.
Wani irin kallon mamaki nayi mai tare da fadin kana nufin ke nan da kayana haka zamu tabbata da cin komai nawa ko may ?
Yace ciki daure fuska ko yau ma gorin naki ya tashi ne don kawai na sama ma kan mu mafita nace da abina din yace,
Yace ke nan kina nufin abinki ba nawa bane ga yadda kikai maganan nan a yanzu.
Nace ni ba haka nake nufi ba sai dai abin yayi yawa ne yanzun zakace wanan dan abin da ka shigo dashi shine iya kudin fridge din nawa ko may ?
Ke nan kina ganin cutar ki zanyi ko may da kike fadin hakan ?
Banda abin fada sai kawai na fice daga falon na barshi a ciki girki na fita na karasa har na gama na dawo na samay shi kwance saman tree seater yayi matangali da hannayen shi.
Har na shigo na aje mai abinci bai dago kai ya kalle ni ba nima hakan dana aje fita nayi daga dakin .
Har tsowon wani lokaci abinda nake ji a zuciya bai barni na bude ledojin da yashigo dasu dakin ba ya fito zuwa wurin randar ruwan mu yana deba da kanshi don zuwa yayi wanka.
Ban tankashi ba don nasan fushi dani yake sai nima na share shi mu tafi a hakan da yake so din laifin ni akaiwa kuma yana kokarin ya juye shi a kaina.
Ashe kamar yadda ya saba kirkiro min zuwa unguwa idan yana son zai cuta min haka ma wanan karon yayi min ya turani gaida mahaifin shi din don yaji dadin fita da fridge din gidan.
Don yasa idan ina nan ba zan yarda ba don ina samun dan taro da sisi da fridge din ina rufawa kaina asiri shine yayi dabara turani in gaida mahaifin shi din.
Don ya samu ya yaudare ni din ya kuma yaudara din sai dai ta annabawa yin hakkuri dashi yanzu.
Mun kai sati biyu a hakan shi da kanshi ya gaji ya sauko daga motar fushin da ya shiga ya nemi shiri dani.
Sai dai shirin nasa na yaudara ne ya yaudare ni idan mun shirya ya samu cutar da yai min daga baya kuma.
Dadi dadi da muka shirya sai da yaja wani dan lokaci baiyi yaudaran nasa ba har ina dauka a raina don maganan da nayi mai ne yasa shi yin laushi.
Sai dai matsalan neman matan shi abin gaba gaba yake sosai don yanzu bai boye min cewa suna tare da Ruth.
Don jita jita nazo min kala kala akan alakan shi da ita wanda har na kasa danne hakurina a lokacin haka yasa na tayar mai da hankali kan zancen.
Sannun a hankali ya nuna kamar ya daina harka da ita a yanzu hakan yai min dadi sannun a hankali na dan fara sana, a don dan kudi ya dinga shigo min na kashi.
Sai dai banyi dace ba don shi muke har cefane dashi muci tare da yayana ko dashi ma din hakan yasa ina sana a kamar ba yi nake ba.
Abin nawa ba karuwa sai ma rikicin dake shirin hawa kaina a lokacin don kudin mutane da nake hadawa a cikin sana, an tawa.
Don da zaran yaga dan kudadeb sun taru zai san dabaran da yayi ya karbe su a hannu na sai yaga ba abinda ya saura zai daina tambayana kudi.
Da zaran kuma yaga Allah ya rufa min asiri ta wani fannin zai kara dawowa ya lalabe ni ya karbi kudin da haka rikici da zaman gida ya fara gagarana a gida .
Ko yaushe ina wajen neman wa kaina abin rufin asiri ga yarana sun fara tasawa yanzu ga ragga yana batun kashe mu a gida.
Abinci kan duk inda zai shiga ya fita ya samo mai dan dadi yana yin shi don muna cin abinci lafiyayye ba laifi.
Sai da ta fannin sutura ba kai muna kallo biyu ranka bai baci ba da mu don kamar wasu yan kauye muka koma dan da diyana.
Don ko dinki zai muna sai sallah kuma ba wani abin kwarai zai dinka muna ba daga wando da riga sai wani shegen yadi da ban san inda yake samo su ba.
Sai daga baya nake ji a gurin yan uwan mu wai ai Ruth ce ke zama ta dinka muna kayan mai kama da gwajo muna sakawa.
Duk yadda na iya gaye zuwa gidan mu sai inji yan kanne na suna kushe ma kwalliyan da nayi din wanan abin yana matukar bankanta raina sosai.
Har dai suka kai ga fada min gaskiya ranan naji bacin rai sosai a zuciyana jin wai farkan shi ce ke muna dinki ashe.
Don ni cewa yake min wai wani telan shi ne ke dinka muna don dinkin yaran zaka ganshi kamar yar kanti na gaskiya don ta iya dinki sosai ba laifi.
Na dawo gida na aza mashi jidali da zage zage sai da ya fice ya bar min gidan don haushi yana matukar mamakin yadda yan gidan mu ke saurin gane sirin shi a saukake.
Wanan abin ya kara jawo kiyayya a tsakanin shi dasu inda anty ke yawan shan zagi a gurin shi komai yace wanan matar ai shu,umace ta kwarai.
Bakajin kalamin dadi a bakin shi daya shafi yn gidan babana kabiru kullun sai aibanta su yake a bakin shi.
Wani lokaci nakan ji haushin hakan wani lokacin kuma idan ni aka batawa zan biye mashi mu zage su a tare.
Gashi dai ba damuwa sukayi da suzo gidan mu ba su sai can ba a rasa ba zaka ga sun zo gidan sai dan gurin anty ne karamin bai kwana uku shi bai zo gurina ba ya duba ni koda kuwa yana sauri ne.
Wanan yasa namu yazo daya da yaron sosai don har shawara nakan yi dashi sosai har shi Jamil din ma yana sakewa yaron saboda yawan kawo muna ziyaran da yake akoda yaushe.
A cikin hikima jamil yayi muna dabaran karban kudin yan hayan mu ya koma ta hannun shi.
Wanda yasan cewa bani kadai keda hakkin kudin hayan ba amma bai hana shi karbewa ba idan an bayar da kudin shekara.
Sai gashi wasa wasa Jamil sai canza yan hayan gidan ya keyi idan dan sabani ya hadasu da mutum yanzu zakaji ya fara korafin, korar mutum a gida.
Sai ya zama dani da yan uwana sai abinda yace damu duk sunayi ne akan suna bashi girman shi ne hakan da sukeyi.
Wanan dan uwan nawa shine nake dan samu yana ban shawara duk da kankantan shekarun shi kuma hakan yana mun dadi sosai.
Don ina amfani da shawaran shi kuma ina ganin fa,idan hakan sosai ina kuma samun karuwa da walwala da hakan .
Zan tura shi duk inda nake son abu zaije ya biya mun bukatana a cikin lokaci batare da bata rai ba.
Ranan ina gida nazo gaida mutanen gidan mu sai ga kanin nawa ya shigo ganin a gida mun gaisa shine yake fada min ai yaga Jamil yanzu da carpet din dakina ko wurin wanki zai kai ne yake tambayana ?
Gabana ne ya fadi don jin abinda ya fada min din ba tantama ko ba a fada ba nasan ya dauka zai sayar ke nan.
Da yake gida nake sai ban nuna wani abu ba na aje zancen da fadin eh wanki yakai muna sai kuma godiya ga Allah ba kowa a gurin da yake fada min zance.
Ban wani dade ba a gidan dole na shirya zuwa gida hankali a tashe na shiga falo na sai wayau.
Ya kwashe carpet din ya fita dashi nasan sunana sorry don nayi bye bye da shi ke nan don ba dawowa gidan zai yi ba .
Kamar yadda sauran suka fice babu dawowa gidan shima wanan din haka

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login