Showing 42001 words to 45000 words out of 106121 words

Chapter 15 - kanin Ajali Book Complete by Zee Makawa .txt

01 Jan 2025

7478

gama girki itace wai zata raba wai ina sa masu nama kadan da kashi mijin ta bai iya ci wanda nake sa mashi din.
Wanan dalilin yasa idan na gama girki sai in dauki tukunyar in kai mata itace zata raba ta diban muna namu sai dai arziki na daya Jamil ba mai zama gida bane yana cin abinci sai yamma yakan shigo ya dauki wanka ya fita kuma.
Haka yasa abincin ke isana har in samu in ba yan kanne na dake zuwa wani lokaci wurina ga shi ta dauko min idan nayi baki zata shigo ta zauna a falona har sai hakin sun tafi zata bar dakin nawa.
Wanan halin da take min yana damuna sosai sai dai banda halin yin magana don a cewan ta tana kulawa ne da bakin nawa ai ya kawo hakan .
Wata rana yar shi ta haihu da dare da ya dawo gida yake ce min ina turamay nan da aka bani na aure nace suna cikin akwati yace in dauko mai turmi daya zai ara ne yaba yar uwar shi idan ya samu hali sai ya sai min wani.
Da saurina na shiga daki na dauko mai wanda ban faye so ba daga ciki na kawo mai ya fita dakin dashi zuwa wurin iyayyen shi ya kai musu nashi gudun mawan na haihuwa da akai masu din suka shiga saka mai albarka.
Tun ranan ban kara jin zancen turumin a bakin shi ba haka yai ta min wayo yana karbe turamen nan ban dinka ko daya ba daga cikin su saukina ma ina da kayan da baba yai min tun a gida dashi da anty amarya nayi fitan buki dashi.
Ga matan hayan gidan ina gani da sallah tazo mazajen su suna saya masu kayan sallah niko ba wanda yai maganan nawa inda nasan da sanin iyayyen shi turamay na da yake karbewa a gidan sai banji sun min maganan dinki kayana ba sam ko tashin zancen babu a bakin su.
Ashe ni ban sani ba idan ya fita da turmin sarakuwa ja da muke tare yake ba ta kadar mai dasu gidan dillalai abasu kudin suyi abinda suke so dashi.
Hakanayi sallah da dan kamay kamay don babu tufafin kwarai a gare ni da zanyi firan sallah dashi haka dai wanan ya wuce kanne na sun zo suke min hira irin kayan da mijin yar uwana ya dinka mata yar wirin baba kabiru dake aure a kusa damu don babu da nisa sosai kusan duk unguwa daya muke har iyayuen namu sai dai akwai dan tazara damu dasu amma duk unguwa daya ne gidajen mu.
Da sallah kan muci mun sha shi shan minerals a gurin mu ba wani aiki bane don duk dare yana shigowa da dan ledan shi gidan damu da iyayyen shi.
Munje gidan gaida iyayyena da sallah mun fara shiga wurin iyayyena mata muka gaisa dasu ina kallon irin kallon da anty ke min sai dai batayi magana ba bayan kallon akai muna iso gurin baba kabiru.
Mu kaje gaidashi a falon shi yayi murna da ganin mu ya tambayi iyayyen mu muka ce suna lafiya har zamu daga sai yake ce min dama yana son ganin mu.
Muka koma muka zauna muna sauraren shi yace dani dama maganan aiki ne ya samu a lokal goverment yake son ji wa zai bawa aikin cikin mu niko mijina zai bawa aikin ?
Har bakina na rawa don ban bari yakai aya ba nace abawa Jamil yace kina ganin haka yayi maki kada daga baya inzo inji wani magana nace na amince baba a bashi.
Haka yasa aka buga offer na aiki da sunan Jamil din ya fara amsan albashin shi yan gidan mu kaf sun nuna min bakin ciki akan hakan danayi kowa sai fadan albarkacin bakin shi yakeyi kan hakan.
Niko saima takaicin su da nake ji don may zasu hana in bawa mijina aikin da muka samu ni a ganina hakan zai kara muna dankon soyayya a tsakanin mu tunda har na sadaukar mai da aikin dana samu nawa.
Idan wata yayi ya karbi kudin shi ban sani sai dai inga ya dinka sutura ya sai turare da sauran abubuwan bukatan shi da dan cafenen kwana biyu da yake sayowa muci.
Gani ragga ya fara yi min sallama a jikina a lokacin sai dai ban daukan hakan wani abu don nasan ba karfi ne ga mijin nawa ba mahaifin shi kuma yayi ritaya yanzu daga aikin asibitin da yake na kauye mafarin tattarowan shi ke na ya dawo birni da zama a cewan shi.
Sai dai shi yana kula iyalin shi don yana masu sutura sosai yana kuma basu suna ci da babban sallah yazo an kawo turamay a gidan uban mijin nawa yayiwa matan shi sayayya sosai lokacin ne na samu ya laba dani yake fadin in boye kada sauran sarakan shi su san da ya sai min zani din .
Ina ta murna yace in kai a dinka min zai biya kudin dinkin sallah saura yan kwana ki ne Jamil ya shigo min da wasu wando da riga na wani material da aka dinka mai sulbi.
Ina ta murna yan gidan mu na zuwa waini an min abin arziki da murna na na dauko kayan ina nuna masu sai cewa summaiya kanwa ta tayi a cikin tsuki .
Yanzu ke wanan gwajon da aka gyara ne kike wa murna wana zanin kuma fa karami ne naji haushin maganan ta nan dai na hauta da fada sosai inda nake shiga ba nan nake fita ba.
Sunje gida suke fada wa iyayyen mu mata sai cewa anty tayi shi Allah ya hore mashi ya sai mata ina laifin hakan ai ta samu kudai ku daina sa ido ga abinda bai shafe ku ba tsakanin miji da mata sai Allah.
Sai cewa dayan tayi kamar kin sani anty don dakin ta tun auren ta da sati biyu da mukaje har yau babu komai a cikin sa duk an sayar wai za a canza mata wasu.
Cikin dafe kirji anty tace wasu kaya kuke magana nata an sayar nan dai suka shiga fada mata abinda nace dasu anyi da kayan dakin nawa.
Hankalin anty ya tashi sosai a lokacin take fadin an sayar fa da kayan kuka ce sukace idan karya ne taje gidan ta gani da idon ta.
Batai nauyi a kafa ba sai gurin baba tana fada mashi shima baba da makmaki yake fadin sun sayar fa kuma malam bai fada min ba gashi duk jumma,a ina zuwa gaida shi da sallah.
Ran baba ya baci sosai da wanan maganan dayaji ya danyi shiru na dan wani lokaci kafin ya furta ku kyaleta muga iya gudun ta kan wanan magana don dole wata rana magana ya taso ai.
Ba haka anty taso ba taso baba ya barsu su tafi gidan su gani da kan su sai dai hakan bai samu ba dole taja bakin ta tayi shiru sai dai ta kwana da takaicin hakan a ranta.
Gashi tunda aka kaini bata je dakin nawa ba saboda kawaici irin nasu don dauka na da takeyi tankar yar cikin ta tun wanan lokacin hurdan mu da anty yayi sanyi sosai.
Duk da nasan laifin na a gurin su sai dai fushin ta dani yana damuna sosai da sallah ma yadda yan uwana da sauran masu kawo masu abincin sallah sukeyi nawa ya sha banbam dana saura don ba wani cika ido da yake masu ga komai nan dai a lalace a gurina.
Sa,adatu diyar baba ta haihu akai suna inda baba yayi mata sha tara na arziki don shi baba mutum ne mai kula da hakkin iyalin shi gaskiya.
Na dawo gida ina fadin irin abin arzikin da baba kabiru yayiwa kanwata da ta haihu sai sarakuwa na ke fadin nima inyi in samu ciki su dangwali arziki a cikin gatse.
Gashi turmi turmi yayan mu yasa muna ni ban samu turmin da zan saka ba sai anty ne ta saya ta bani in bayar a lokacin amma da zan dawo sai da aka cika min leda babba da kayan buki.
Zaman dai muna yinsa da dadi da wuya sai dai duk abinda suke min ina shanyewa ban fadi gidan mu don boye sirin gidan aure na.
Jamil ya tsiro min da zuwa gida kauyen mu wai bukin dan uwan shi inda yace idan naje inyi sati hudu kuma kada in sauka a gurin dangi na sai gidan yan uwan shi.
Nace zuwa bukin ne zanje in share har sati hudu a kauye har mutane su gaji dani kan hakan yace su yaga daman bani kuma su yake son inyi a gida idan naje.
Dole haka na shirya na tafi ya danyi min dinki kala biyu na fitan buki muka je kauye aka sha buki lafiya bayan kowa ya watse ne aka ga ni banda niyar komawa gida.
Sai suka tambaye ni nace sati hudu yace inyi idan nazo gidan sunyi mamakin jin hakan sai dai basuyi magana ba tunda gidane na zo ko nan din.
Wasa wasa na share har sati shida bai zo ba gashi yace kada in dawo sai idan yazo ga zaman kauye ya ishe ni tun ana min abin arziki har aka koma gashi mun maki shegiya.
A cikin satin na bakwai da zamu shiga ne yazo gaida wani mara lafiya a kauyen na fara shirin komawa tunda naga ya dira garin nan yace wai ba dani zai koma ba.
Muka fara rikici dashi har abin ya kaimu ga saki daya naje na samu wan mahaifin mu da suka hada uba dashi da kuka na fada mai abinda Jamil yayi min.
Nan dai aka kirashi akai mai fada sosai aka shirya mu ba tare da gida sun sani ba ya kuma ce ba tare dani zai koma ba sai dai idan ya koma da kwana biyu in koma.
Hakan akayi ko da na dawo ina shan kamshi dashi kan sakin dayai min din ko may ya gani ya sauko da kan shi ya bar fushin da yake yi din dani.
Ashe abinda ban sani ba bayan tafiyana Jamil mata yake daukowa ya kwana dasu har dakina ya bude ta baya inda iyayyen shi basu ganin abinda yakeyi don muna da kofan baya a cikin falon mu ba lalai ne su san abinda yakeyi a gidan ba.
Kanne na duk sun san wanan labarin suna kallo na ne kawai an rasa wanda zai iya fada min don gudun tashin hankali sai dai su basu sani ba aikin gama ya gama ko in ma har saki suke gudu a gare ni.
Don haushin cewa da nayi zan koma gida yasa shi ya sake ni a kauye don zan bata mai jin dadin shi da yake a nan din.
Jamil yakai dan duniya sosai don har abokiyar ta gwaicin yar hayan gidan mu ashe wata yar duniya ita batai aure ba kamar yar uwarta ya samu suna shedan cin su a dakina da ita.
Na dawo ina hura hanci wai ni ga mai miji suna kallona sara mai bisa ruwa duk da dawowan nawa bai rage shi da komai ba don sai ya raba dare a waje suna iya shegen su can da ita wai shi auren ta zaiyi a cewar shi kuji fa yan uwa.
Na dawo ban dade ba Allah ya ban ciki dama a can kauye nasha maganin gargajiya na mara wai mara ne ke damuna sukace wai shiyasa har lokacin aure da shekara ban samu haihuwa ba.
A fili ya nuna min farin cikin shi na samun cikin da mukayi sai dai a can kasan zuciyar shi ba haka yaso ba don yace shi bai shirya ma haihuwa ba yanzu.
Daga yin aure ace wai an fara samun ciki mafarin a tara iyali ke nan da wuri tun muna da kurciyar mu ke nan zamu fara tara iyali.
Nikan dadin samun cikin nakeyi sai faman planning nakeyi ni da yan uwa na dake tayani murna na gaskiya kan cikin da na samu din a yanzu.
Lokacin da kanwata Saadatu ta samu ciki ta kusa haihuwa ta danyi tanadin ta takai gida don taimakawa iyayyen mu dashi duk da baba yayi fadan haka yace ta bar shi tayi laluran gaban ta ai itaka tana da hidimar da zatayi na kawayen ta.
Sai dai ni ba wani labari kan hakan don ban aje ba ban ba wani ajiya ba ko turmin zanin da baba kabiru ya aiko min dashi da sallah yaso ya lalashe ni ya karbe sai dana nuna mashi hakan ba mai yuyuwa bane don tare da sauran yan uwana dake aure baba din ya saya muna kayan .
Dole yana kallon abin kudi a wurina ya kyale ni ba yadda zaiyi yayi fushin shi ya gaji har ya sake don yasan na fishi gaskiya a kan zancen zanin.
Iskanci ko yanzu baijin kunya a gabana zai dinga waya da yan mata suna hira da farko naso in sa mashi ido sai naga zanja wa kaina damuwa gurin kyale hakan.
Ranan ina zaune wata ta kirashi ya dauka sun fara fira ke nan na wauce wayan daga hannun shi na fara dura mata ashar cikin dakiyar fuska ya dauka zanji tsoron shi dana saba ji ne ya fara daka min tsawa akan in bashi wayan har yana fadin you very stupid ki ban wayana nace.
Nima tsawa ba daka mai take na birkice mashi a dakin yana gudun iyayyen shi suji ko daya daga cikin yan hayan mu suji.
Girman shi ya zube a gurin su don idan zai shigo gida sai ya daure fuska kamar hadarin marance fuska ba annuri ko kadan.
Zakace shine maigidan da muke cikin sa yadda yake basu doka da iko a gidan nasan badon baba yasa yan hayan ba da zai iya koran su ma.
Ganin da gaske ina shirin tona mai asiri yasa ya sauko yana fadi amma ke baki da wayau dafa budurwan yayana sa,idu nake waya kin dauka ko budurwa tace.
Da yake wawiya nake sai na yarda da maganan shi na miko mai wayan yayi saurin kashewa ya kuta ya fita daga dakin bai dawo gida ba sai da dare ya raba sosai ya dawo.






ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
5/18/21, 11:56 PM - 🤔🤔🤔: ZIM




Ina zaune ina kare mai kallo yana shirin fita da yamma don duk yamma haka yake wanan al,adan ya tsala ado a jikin shi ga kamshin turare mai tsada yana tashi.
Sai daya gama shirin shi yana batun fita nace gida nake son zuwa in duba su yau kamar baiji abinda na fada ba ya kara dauko kwalban turaren shi ya kara fesa ma jikin shi yadda yake so.
Bakajini bane na fadi daga inda nake zaune ina kallon shi cikin tagumi yace najiki mana sai dai ban san abinda zaki je yi gidan bane.
Zuwa zanyi in gaida su kawai don nasan in ka fita ba lalai ne ka dawo da wuri ba yace ni na rasa ma may zance maki hadiza .
Wai da kike dadin zaki ki duba su ina ko dazun naga shigowan Baffa gidan nan shekaran jiya kuma summaiya sun zo nan gurin ki.
Nace su kadai ne a gidan halan yace ke kika damu dasu su basu damu dake ba ni dai da zaki bi shawarana ki hade kan uan uwanki kuzama tsintsiya daya madaurin ku daya ku hudu da zai fi maki alheri.
Nace ban gane may kake nufi ba har yanzu yace eh bazaki gane ba muddin baki kwantar da hankalin ki yanzu kin fahinci magana na ba.
Don yawan zuwa gidan nan da kike yi ko wani lokaci yana daya daga cikin daman da zasu samu su cinye maku kudin ku idan ya fito nan gaba.
Wani kallo na watsa mashi tare da fadin kudin ina baba kabiru ne mai muna fafutukan fito dashi yace ko yanayi ai da wata manufa yake yin su don shima ya debi rabon shi daga ciki.
Kara mai kallon mamaki nayi don jin furucin shi akan baba kabiru din yace yes waye bai san da dukiyan ku yake tunkaho ba a garin nan.
Sai ku da har gobe baku wayau da zaku gane hakan sai idan sun gama maku barna zaki dawo kina fadin dama na fada maki kinki ji a baya.
Ni fa ban fahinci inda maganan nan naka ya dosa ba har yanzu zama yayi a kusa dani don ya fahinci banda saurin zurmawa idan ya tsarani da magana.
Yace ni abinda naga yafi maku shine kiyi kokari ku hade kai da yan uwan ki tun yanzu ta inda bakin ku zaizo daya a kasa gane tsakanin ku.
Nace ai muna hakan ko yanzu wani shu,umin kallo yayi min tare da fadin ke har yanzu dai yarinya ce hadiza ana gabas kina yamma ni zan fita idan na samu lokaci zan maki bayani a tsanake.
Daga haka yasa takalman shi ya fita kallon inda yaci abinci nayi naga ledan kazan daya shigo dashi da rana yaci yashe saman dan table din da muke cin abinci a falon namu.
Naja tsuki tare da mikewa ina duba ledan kazan na samu ya rage dan guntu a ciki zama nayi na karasa cinye sauran tare da sude kasusuwan da bai karasa cinye tsokan su ba na gama na kwashe kayan na fita

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login