Showing 48001 words to 51000 words out of 106121 words

Chapter 17 - kanin Ajali Book Complete by Zee Makawa .txt

Advertisement

01 Jan 2025

8068

anty da serious take maganan ta.
Ina kallo aka kira tela yazo har gida ya karbi dinkin kayan inda anty ta biya rabi ta sa mu kuma mu biya rabi din fitan rabin daga gurin jamil yayi wuya ashe don ina gida ne ya kyale ni.
Nayi kiba sosai don jwgon yayi min kyau saboda ina samun hutu da kulawa sosai a zaman da nakeyi a gidan mu din.
A kwana a tashi har mukai arba,in da kyat da boni don jamil duk ya matsu mu dawo kamar abin arziki har nima na fara kasa hakkuri da zaman gidan.
Haka muka ga munyi arba,in a dadafe a gidan mahaifan nawa da zamu koma ne baba yayi muna sayayyan buhuhunan abinci gero masara shinkafa da su mangyda da kayan miya.
Aka tarkata ni aka mayar dani gidan Jamil din dani da yar goyo na koda muka koma mun samu dakin kaca kaca ba gyara ko ina dole suka dan kama min muka dan gyara hakana kafin su tafi.
Sarakuwa na sai murna take a gaban iyayyena da suka rakoni ta karbi yarinyar ta goyata tun suna gidan basu tafi ba kamar abin arziki.
Jamil na gurin yawon shi koda muka dawo sai dare sosai ya dawo gidan yana fadin ashe da gaske yau zaku dawo din ?
Kallon shi nayi da mamakin abinda yace din nace ba an aiko gidan mu a gyara min daki kafin in dawo yace shi ba wanda ya fada mai.
Ya shiga daki ya na kallon kayan da muka dawo dashi ya wani ya tsune baki zai juya nake ce mai buhuhunan abinci suna sashen baba an aje da cewa mahaifin shi.
Ya juyo da sauri cikin washe baki yana fadin har da abinci nace eh buhu uku ne sai kayan miya da sauran tarkace ya juya da sauri zuwa ganin kayan dana fada mai.
Sai can gashi ya dawo yana washe baki tare da fadin shi baba bai san bamu cin masara bane da gero nace gero ai don kunu aka kawo min shi masara kuma don tuwo.
Yace ba za mu sha kunnu a gidan nan ba don kin san bamu sha kunu ya fice yana murna ya dawo da leda a hannun shi kaza ce da zafin ta tare da abinsha ya shigo dashi.
Mukaci muka kwanta tunda safe washe gari ya tashi ya fita sai gashi ya dawo da wani mutum a bayan shi ya sallama muna sai gani nayi kawai Jamil yana cicibo buhuhunan nan yana fita dasu waje gurin mutumin .
Can sai gashi ya shigo yana washe baki yana murna da farin ciki sosai a fili na dauka zai ban wani abu a cikin kudi sai gani nayi ya soke abinshi ya fita.
Ban kara ganin shi ba sai daren sosai ya shigo gidan yana wani daure fuskan shi ni dai ban tanka mashi ba na kama lamarin gabana.
Ya gaji ya bari ya dawo ya sake da kanshi yana wani haba haba dani, niko kaina sai wani dadi nake ji a raina wai ni miji yana so na .
Da rana tsaka sai gashi ya dawo a cikin fara,an shi yana kwala min kira nazo da sauri ina karbawa na amsa mai yana tsaye tsakiyan falon mu na samay shi yace dauko min kayan sunan nan naki in duba akwai abinda nake so a ciki.
Kallon shi nayi galala nace wasu kaya ke nan yace cikin canza fuska turamay da kika samu da suna mana .
Gaba nane naji ya buga gashi ban gama sululin wasu turamay na diyar kanwar mahaifiyar mu da ta kawo min dinkin su har na koma gida ban samu dinkawa ba na barsu a dakin namu.
Ina gidan baba kabir ne ta aiko a karbar mata dinkin sai lokacin na tuna da turamay na tura summaiya kanwa ta ta kwaso min a dakina.
Sai gata ta dawo tana fada min bata gansu ba a inda na aje su hankalina ya daga da yazo na tambaye shi sai cewa yayi shi bai gansu ba a dakin tun tafiya na.
Wanan abin kusan yaso ya hada mu fada har da sister din mahaifiyar mu uwar yarinyar gashi ita kadai ce ta rage muna uwa da muke ganin dakin su daya da mahaifiyar mu.
Amma ta rufe idon ta kan yar tace sai na biya turamay nan ni kuma na kasa dauka daga cikin turamay na in bata sai yanzu kuma shi gashi ya dawo min da zancen kayan dana samu din da haihuwa.
Bai tsaya jin abinda zance ba ya fada daki ya fito da akwatunan zuwa falo ya fara budan su sai naga ya dago da sauri yana kallona tare da tambayana ina turamay suke ?
Nace ai na fada ma mun kai dinkin su tun kan in dawo gidan ko sharan yan gidan mune hakan don sunce banda tufafi goyo kuma tufafi yake so sai.
A hasale yace inji uban wa yace ki dinke wanan kayan masu uban yawa da tsada ki sa ma jikin ki kin ko san kudin kayan nan sai kallon shi nake a cikin mamaki na kasa magana ban iya furta mai komai ba.
Ina kallo ya tattara sauran turamay bayan ya zabi guda biyar ya fita dasu da haka sai da ya jide kayan nan kaf ya fita dasu ya sayar.
Idan nayi magana sai ya hauni da cin mutunci kamar zai duke ni idan mahaifin shi yaji mu sai yace idan ban rufawa mijina asiri ba wa zan rufawa duniyan nan.
Haka dai rayuwan yake tafiya muna tun dawowana daga gidan na samu uwar mijina da muke zama da ita ta canza min sosai har gara lokacin da ban haihu ba din da dan dama.
Yanzu ba nasiha a tsakanina da ita ga gori da take min akan gida dan abu kadan zatace idan don gidane nake son raina ta sai a fada masu kudin haya su biya ko su fita su bamu gidan mu.
Ina dai hakkuri ban tanka ta duk fadan da zatayi har ta kare bana kulata sam sai idan ta huce ne zata dan dauki diyata ta dan wuni a gurin ta na dan wani lokaci.
Wanan bai sa na canza daga abinda nake mata ba a matsayin ta na sarakuwa na a gurin su ina bata girman ta sosai da yin aikin dana san nawa ne inyi.
Ranan dai ban san ko may ya hadasu fada ba da Jamil ya shigo yana jan tsaki har ya gaji ya kai ga fadin anzo an zauna zaman sa wa mutane ido ana faman takura muna.
Wallahi daga yau idan tayi maki ki dinga ramawa ninace nasan bacin ran abinda tayi mai ne yasa ya fadi haka sai ban bi ta kan shi ba kan maganan tsakanin shi ne da ita wanan.
Neman matan shi yanzu zanga zanga ne ya kara turani zuwa kauye wai inkai yarinya su gani don wasu da yawa basu santa ba tun kan ya karasa nake ce mai ni dai gaskiya idan yasan zanje ya barni can ne ba zan tafi ba.
Wai ashe yaji haushin maganan sai gashi ya kaini kara wurin mahaifin shi ya kirani yai min fada sosai har yana fadin waini yanzu ya gane ina gudun zuwa kauyen mu ne don ina ganin nafisu.
Mahaifin nasa yasa alla dole in shirya babu ko wani tsaraba dana tanadar masu na tafi kauye ganin gida tsomai tsomai dani ba laifi tunda nima garina ne yan uwa kuma suna jin tausayina ga maraici ga rashin dace da miji na gari da banyi a cewan su.
Wanda ni hakan yana matukar ban haushi sosai don ni banga laifin Jamil ba ai ba gare shine rashi ya yanke cibi ba don ni dauka nake karfi ne baida yasa bai min abinda ya dace yayi na zaman shi miji a gare ni.
Abinda ta dawo dani gari wanan karon bayan na shafe sati hudu da kwanaki masu kyau nayi baki duk na fige idan ka ganni bazakace na taba yin boko ba a rayuwana.
Zancen kudin mu ne da ya taso yasa baba kabir aikwa in zo zamu tafi abuja muyi wani sgning a can shine dalilin dawowa na dawuri da bansan ranan dawowa na ba gidan.
Ko da na dawo na samay su a cikin jin dadi don mahaifin shi ya samu kudin aikin shi da yai retaya ya fito sai dadi suke ci a gidan babu kama hannun yaro.
Atm din shi ma yana a hannun Jamil ashe idan tsohon yace ya ciro mai dubu biyar sai yaje ya cire dubu hamsin ko arba,in yasha garalin shi dashi.
Na dawo muna shirin zuwa abuja da baba kabir da kani na Baffa ne suka tashi da rikici a gidan da tsohon nashi ya tura wani kanin Jamil din ya ciro mai kudi aka samu saura dubu goma kacal a banki.
Wanan abin ne ya kawo rikici tsakanin shi da mahaifin nasa sukai fada sosao ranan da dan son nasa haushin wanan abinda yaji yace duk zugin matar shi ce .
Don itace mai zugashi a kanshi don ta tsane shi saboda ba ita ta haife shi ba niko ala dole sai naji zafin abin na shigar ma mijina fada.
Har muka tafi abuja ban magana na kirki da ita ba wani abu bani hannu kawai muka sa a takarda muka juyo zuwa gida.
Ina shigowa na samu Jamil ya gyara min daki ranan bai fita ko ina ba don dama muna ta wayan dashi ganin muna tare dasu baba ne yasa bai tambaye ni tun ina can ba zancen kudin namu.
Ina dawowa ya tare ni da murnan shi har da karbar min jakka na ya karbi yarinya yayi mata wanka ya shirya ta sai da zzamu kwanta yake tambayana nayi mai bayani.
Tsoki yaja ya bani baya bai kara magana sai safe ya tashi a cikin daure fuskan daya saba bai dade a gidan ba ya fice gaba daya.




ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
5/18/21, 11:56 PM - 🤔🤔🤔: Tun wanan ranan da muka dawo daga Jamil har iyayyen shi ban kara gane kan su ba a gidan kowa zafi zafi yake dani a gidan har Jamil din kan shi ba wani maganan girma da arzikin dake hada mu dashi inji sanyi.
Daki nake kwance da yar diyana anyi ruwan sama an dauke a lokacin misalin karfe goma na safe na ranan laraba hayaniya nake ji na mutanen gidan mu sama sama yasa na mike na fito don in ganewa idona abinda ke faruwa.
Na samu data daga cikin matan hanyan gidan mu ne suke fitina sai dai ban san da wanda take fadan ba a lokacin maimakon in tsaya sauraren ta in gane kan maganan sai kawai na shiga aiki abina don lokacin dora girki na yayi kusa.
Wanke wanke na tara don in yi sai da na hada kayan a gurin da muke zama mu wanke kayan mu na koma daki in dauko omo da zanyi amfani dashi gurin wanke kayan na fito naji matar na fadin mu za aiwa burgan aiki ana muna kurin ana da arziki babu kwarjini ga miji.
Tambayan ta nayi wai yau waya taba ki ne haka da wanan sanyin haka ta wani kallo ni shekeke tare da fadin wai ke baki ma san da wanda nake fada ba ke nan ?
Kai na girgiza mata ba tare da niyar yin hakan ba a gare ta take fadin amma ke kin kai yar rainin hankali wallahi to dake da mijin ki nake fada ba da kowa ba.
A cikin mamaki nake fadin nidin nan kuma may mukai maki haka mai zafi da zaki tashi damu a rai haka da sanyin safiyan nan naga tun asuba dana fito hadari ya kora mu daki ban kara fitowa ba sai yanzu.
Zaki ce hakan mana tunda kun san abinda kuka kulla min tun jiya din to bari kiji ni ba irin ki bane da miji ya mayar wata bi can don nasan ciwon kaina dana iyayyena da kuma darajan aure na.
Tsaye nayi galala ina son jin inda wanan maganan nata ya nufa akan mu haka da take ta faman budan baki har makwabta zasu iya jin mu a lokacin.
Ganin ban fahince ta ba ta buda baki tana fadin kina nufin baki san da zaman mijin ki ya fara jan baban Ahmed zuwa wurin shiririnta shi ba har tsakiyan dare jiya baban Ahmed bai dawo ba gidan nan.
Ni ba yar rakiyan mata nake ba da zan saka ido wanan abin yana gudana a tsakanin su haka a zafafe nace wai ko kina da hankali maman Ahmed may ye nawa yanzu ni a cikin wanan zancen.
Tace keko keda ruwa a wanan zancen don haka kiwa mijin ki kashedi akan mijina don zan debe kunyan da nake ji nasa in masa rashin mutunci yanzu a gidan nan idan bai fita harkata ba.
Sale salin ya fara koya mai neman kannen da yan uwan matan gidan nan ke nan don shi ba abin kunya bane a gurin shi yin hakan.
Nace na gane dai dani kike jin fada ba da baban Amira ba don shi bai gidan bai san kina yi ba ma san nan kuma yar uwar wace daga cikin mu kika ga baban Amira yana nema.
Kafin ta bani amsa sai ga dayan ta fito daga daki tana fadin dama nasan dani kike wanan maganganun naki ai don ki fada mata mijin ta yana neman yar uwar tagwaici na ko.
To ko taji may zatayi tunda shi yaje ba ita taje neman shi ba idona na ne naji ya rufe ga maganganun da suke yaba min dukkan su su biyu din a lokacin.
Na rasa abinda zance kan zancen don raina yakai kololuwar baci da maganan su duk kokarin da nakeyi inga na kaice ma wani fitina dasu hakan bai yuyu ba sai da Jamil yayi sanadin hada ni fitina dasu a gidan nan .
Kafin inyi yunkurin basu amsa sai ga sarakuwana ta fito daga dakin su tana fadin nasan dama wanan magana da kuke tun asuba da wata manufa kuke yin shi don ku tayar da zaune tsaye a gidan nan tsakanin yaran nan biyu ne.
Idan ma ya nema mace nawa aka halasta wa namiji ya nema a rayuwan shi yayi idan ma har kun fada mata din taji za ta hanashi kara abinda Allah yace yayi ne ke da kike fadan yana jan mijin ki zai koya mai yawon banza daure shi yayi a kafan shi ko may ?
Wanke wanke nakeyi ina jin raina yana min zafi nan dai sukai ta sa insa a tsakanin su ban iya tanka masu ba don mijina nane yaja min haka a gurin su din.
Da ya kama kan shi da mutuncin shi kamar yadda sauran mazan gidan suka kama da duk wanan abin bai faru haka ba a yanzu har ana kokarin fada min magana a kan shi.
Na gama na shiga daki sai naji ba zan iya zama ba na fakaici idon mutane na nufi gidan mu hankali a tashe dani na isa gidan kowa ya ganni yasan ba lafiya nake ba.
Ban samu anty gida ba tana gurin aiki sai mama uwar gidan baba kabiru na sama a gidan da ita muka fara zancen abinda ke damuna kafin anty ta dawo daga gurin aiki da ta tafi.
Muna kan zancen ne ta dawo ta samay ni a gidan da mamaki take kallona don tasan ban faye shigowa gidan haka da rana ba sai da dare nafi zuwa gaida su.
Bayan mun gaisa ne take tambaya na ko lafiya a yadda ta samay ni naci kuka har na gaji nan mama ke fada mata abinda ke faruwa a gidan namu.
Allah ya sauwaka tace min wanda ni ba haka naso naji daga gare su ba so nayi su goya min baya akan maganan sai kuma ba wace ta furta komai daga hakan sai cewa da sukayi a bari baban mu ya shigo gidan.
Wanda ni naji haushin hakan sosai a raina don haka na dauka ko baba yazo shima abinda zai fada min ke nan bayan wanan.
Na dora hannu a kai na fara rusa masu kuka a gidan cikin tashin hankali duk na daga masu hankali sosai a gidan ba, a fi minti talatin ba baba kabiru ya dawo gida.
Tun daga kofa yake tambayan may ke faruwa ne a gidan nan dai anty ke fada mai maganan dana zo dashi gida kai ya gyada kawai tare da fadin abinda kowa ya guje maki ke nan tun farko.
Kika nuna don bamu haife ki bane yasa bamu son abinda kike so din yanzu sai ki koma kiyi hakkuri zan ganshi in masa magana daga baya.
Ba haka naso ji daga gurin baba kabiru din ba naso ya goya min baya ne akan maganan sai kuma ban samu haka din ba a gurin shi haka yasa na kara kargin kukana a lokacin.
Anty tace hadiza wa zai furta wani kalami mara kyau akan mijin ki idan zuciyar ki tayi sanyi ki kwashe ki fada mai babu abinda zamuce sai hakkuri da zamu baki a yanzu.
Raina ya kara baci sosai baba yace wanan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login