Showing 15001 words to 18000 words out of 106121 words
Chapter 6 - kanin Ajali Book Complete by Zee Makawa .txt
ai yasai mota bayana itace wanan din da nake gani nayi ta murna ina bin motar da kallo a cikin farin ciki.
Mun isa gida inda na samu mama ta shiryawa dawowan nawa haka muke cikin son juna da kauna na karbi dan kanina dake kama da mahaifin mu sak wurin kama.
Yaron ya shiga raina sosai a wanan hutun mahaifin mu yazo gida sai dai wanan karon shi kadai ya samu zuwa bada mu yace sai mun samu long voccation zamu tafi tare da mama.
Yaje gida yayi masu abin arziki sai dai shi baba halin yahudawa gare shi kyautan shi sai sa, a mutum ke samu wanda ba a zata ba yake samun alherin sa da zai dawo ya dawo tare da umma don taga inda muke zaune.
Mun ji dadin zuwan umma din mama ta kama ina aka saka da umma din cikin jin dadi da so da kauna hutun mu ya kare a nan nabar kakan mu na koma makaranta.
Yanzu Alhamdullahi iyayyen mu sun samu walwala kamar a gariki arzikin baba yake ga karin girma da yake samu a gurin aikin shi haka yasa muke tasowa a cikin jin dadi sosai.
Bamu da sauran damuwa ko kadan a tare damu komai a wadace mukeyin shi watan umma uku a wurin su ta koma gida dauke da abin arziki mai yawa.
Wanda hakan ya faranta ma mama rai sosai ta koma gida cikin jin dadi ga abubuwan da baba ya saya mata a can mota guda ya dauka zai kaita har gida ba tare da kowa ba.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
5/18/21, 11:46 PM - 🤔🤔🤔: 🙆🏼♂️ KANIN A JALI 🙆🏼♂️
5️6️⃣
ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
Yanzu zance alhamdullahi a gurin iyayyena don mahaifin mu ya samu ci gaban rayuwa sosai ya samu karin girma a gurin aikin shi.
Baba kabiru ne a cikin yan uwa yakan dan leko mu lokaci lokaci har tsawon shekara uku bamu je gida ba rasuwan kani mahaifin mamane mun yi hutu a lokacin muka shirya zuwa gida.
Alokavin mu hudu ne sai kannena guda uku mun tashi mu hudu ke nan wanan karon mahaifina ne ya kaimu gida da kan shi don muje ya samu gaisuwan shima don mai rasuwan yana kawu ne a wurin shi.
Yasa shi zuwa don ba abu kadan ne ke kawo shi gida haka ba kai tsaye kwanan shi biyu ya koma tun mutane suna marmarin shi.
Yana dawowa rayuwan gidan sai ta koma mashi wani iri sai dare sosai yake dawowa gidan da dan abinda zaici ya kwanta.
Haka yaba matan dake son kai mai hari nuna kan su a gare shi yana watsar dasu don irin tarbiyan da suka samu tun daga gurin iyayye a gida.
Muna gida mushiga nan mu fada can wurin ziyaran yan uwa ana ganin yan kanne na da basu sani ba don ni an fi bude ido dani a gida ni mutane suka sani sosai.
Duk inda mukaje da dan abinda muke kai masu na fannin tsaaran ban da mahaifiyar mu ta dauko don yan uwa a gida.
Mun samu baba kabiru da iyalin shi sun bar garin suna cikin birni a zaune don yanzu ya zama dan siyasa babba a jahar mu.
Sai koma na jin dadi idan munzo gidan ya rage muna gidan ya koma ba dadi a gare mu don rashin kanin mahaifin na mu dake ina aka saka damu idan mun zo.
Ya dai zo garin ya samay mu inda yai ma su mama alheri sosai bai kwana ba ya juya ya koma mama tayi mashi alkawarin zamu shigowa wirin su kafin mu koma.
Wanan zuwan ne muka sake, kullewa da Jamil sosai nake dan tsayawa mu kebe a boye dashi ba tare da wani ya sani ba a gidan mu.
Ba dai wani fira na iyaba a lokacin duk hiran na makaranta ne zamuyi kuma a tare da abokai na samu anyiwa wasu abokaina aure a gida.
Hakan ke sa muna fakewa da zamu gidan su ziyara mu samu kebewa dasu a can sai mun dauki lokaci mu dawo gida.
Ranan da rana ya baci muna ne umma ta rutsa mu a wurin da muke zama muyi hira dasu mun shagala muna tsakiyan hiran mu sai jin muryan ta mukayi kamar daga sama akan mu.
Tana fadin muna fukan Allah ta,allah ya ya kama ku yau zuwa wurin Hannatu din ke nan da kukace zakuyi jikina yana rawa na dago da sauri ina neman hanyar guduwa.
Tace kul kika fara kika daga daga wurin nan sai na bata maki rai yau kai kuma bari kaji daga yau daga rana mai kaman ta yau.
Kada inji kada in kara ganin ka tsaya min da jika na bani ba irin gidan ku a zuri,ana har duniya ta kare mai na gaba yaci balle na baya ya lasa.
Yanzu ba sai gobe ba gidan ku zanje in ma iyayyen ka iyayyaka dakai cikin zuria ta ke kuma wuce mu tafi mufuka banza da wofi kawai.
Ta juya tare da fasa zuwa unguwar da zata tana gaba tana zagina Ainau da muke tare ta biyo ni ta juyo tace kul kika biyo mu sai na saba maki rai.
Duk munafuncin nan kece mai kulla shi keda hafsa na sani ba yau ba kar nake kallon ku dama irin ranan nan nake jira gare ku.
Banda lalacewa mai ya hada ki da wanan zurian marasa mutunci da tarbiya dama barewa bata gudu danta yai rarafe ai.
Har muka kai gida tana saman bakin ta gurin fitina da tonon asiri wanda a lokacin ina jin kamar in magare ta ta bayan da nake binta don haushi.
Lungin mu muna shiga take kwalawa maman mu kira ta fito da saurin don da jin kiran bana alheri bane an tabota ko wani abu ya faru.
Mama na fitowa take fadin yanzu saude da sanin ki yar nan ke wanan iya shegen a gari haka yaron nan dana rabata dashi ashe suna tare har yanzu.
Cikin mamaki mama tace umma wani yaro kuma tace dan gidan babbako mana shegen yaron nan mai son karyan tsiya.
Karamin yaro ya dauki karya irin na ubanshi ya sawa kanshi tun yanzu gata nan can na tsura su wurin gidan wanzan sun labe suna zance da ita.
Zance umma mama ta fadi a cikin mamaki tana mayar da kallon ta gurin da nake tsaye na sada kaina kasa da sauri don kunya da tsoron dake raina a lokacin.
Ta juya tana fadin yanzu gidan su nayi gurin iyayyen shi ai mashi kashedi akan jikata bani ba irin zurian su a cikin kayana su sun sani dama.
Umma kiyi hakkuri zan mata fada basai kinje ba muryan baba yusha,u dake dakin matar shi ne ya fito don jin abinda umma ke fadi.
Tace kaidai barin je don da zafi zafi ake buga karfe kada yazo ya bata muna yarinya bamu sani ba don ba mutanen kwarai bane ka sani.
Ya sake fadin umma yi hakkuri don mutuncin dake tsakanin mu dasu kinga duk gida ne nine ya kamata inje in tsawata mai tunda maganan mazane ai.
Tace to shike nan tunda kace zaka amma duk na sake ganin haka ya zama dole in fada ma ubanki don yasan abinda kike zuwa nan kinayi.
Da sauri nace don Allah umma kiyi hakkuri ba zan sake ba ko yanzu karatu ya tsayar dani ina koya masu shine kika samay mu tare a wurin ta daka min wani uwar harara sai da nasha jinin jikina don kallon da tayi min.
Tsorona Allah tsorona ta fada ma mahaifin mu nasan dukan tsiya zansha kuma ya hanani zuwa gida idan mun tashi zuwa.
Ranan duka nane mahaifiyata bata yi ba don ta nuna min iya bacin ranta itama sosai sai da na bata hakkuri sosai ta kyale ni sai dai ba wani sakin fuska a tsakanin mu.
Haka har dare na nemi wuri na kwanta ba tare da naci abincin dare ba ranan ina tunane kala kala wanda duk haushin kakata umma nake ji a raina tunda itace ta hadani da mahaifiyata take wanan fushin dani haka.
Ranan dai haka yazo min ba dadi tun wanan ranan ban kara fita ko ina ba koda yaushe ina gida da mahaifitya idan na fita sai dai idan naje wani lungu na gidan namu ne.
Jamilu yabi duk hanyan da zaibi yaga mun hadu dashi amma abin ya gagara don kullun ina gida tare da mama da kanne na haka yasa yake turo min sako daga wurin su hafsa.
Ban iya amsa mai don ina son in kiyayye kamar yadda mahaifiyata tayi mun kashedi a kanshi sosai na dauka kuma a raina.
Anyi haka da sati biyu ne muka kai ma baba kabiru ziyara a local govenment din mu inda yake zaune da iyalin shi da matar shi ma,aikaciyar asibiti.
Mun ji dadin zuwa wanan ziyaran don irin yadda baba kabiru yake nuna muna kulawanshi akan mu sosai wanda nina san mahaifin iya mu iyalin shi ne ya sani zai iya nuna muna hakan.
Don ba damuwa yayi shi da nasu iyalin ba sam don ina yawan jin mama na mashi wanan korafin sosai idan dan abu ya hada su a gaban mu.
Hakan bai sa ya canza halin shi sai ma cewan da yake shi ba haka nashi tsarin yake ba don kowa nasa yasani a yanzu idan bai muna tanadi ba wayake so yayi muna.
Ire iten wanan maganan dai yana hadasu lokaci da dama don nasha jin suna wanan maganan wasa wasa sai da muka share kusan wata daya a gurin baba kabiru.
Da zamu koma ma mahaifin mu shi yayowa waya kan ya samu a mota a dauki shata a dawo damu har abuja sai da muka koma gida mukai sallama da mutanen gida inda na dan samu kebewa a sace da jamil mukai sallama.
Inda ya nuna min shifa da gaske yake maganan shi don haka in rike alkawarin mu idan munje can ni dai dariya nayi kawai ba tare dana nuna mashi wani alaman na yarda ba ko ban yarda da maganan shi ba.
Wanan karon mun fi dauko kaya fiye da kullun idan zamu dawo wanda duk yawanci abin daga wurin baba kabiru ne ya fito don yin tsaraba dashi ga kayan daya dinka muna masu kyau dukkan mu har mahaifiyar mu.
Mun sauka abuja lafiya sai washe gari ne mama ke nuna mashi kayan da dawainiyar da baba kabiru din yayi damu a wurin shi.
Sai kallon kayan baba yayi yana fadin aiko kabiru yayi kokari sai dai idan yana hakan ai ba zai tara komai ba da mamaki mama ke kallin shi don jin furicin mahaifin mu din ta kasa hakkuri sai da tace mai.
Wai kai wani irin mutum ne haka dan uwanka yai ma iyalinka abu haka na yabawa babu godiya sai wani magana can da bai dace ba haka , ?
Murmushi kawai yayi tare da fadin ai dama idan zancen kabiru ne baki son a fadi a gaban ki ni gani nayi bai abinda ya dace a kanshi yasa na fadi wanan maganan.
Ban dade ba na koma makaranta sai babane ya kaini da kansa don hutun dana kara yayi yawa bisa ga dokan makarantar mu sai da kyat suka karbe ni ma.
A cikin wanan shekaran ne baba kabiru yakai mahaifiyar su saudiya ta sauke farali don itace ta fara kaiwa kafin shi ya tafi ya sauke nasa.
Idan da son samu ne mahaifi yana da halin da zai kaita saudiya din sai dai baiyi dabaran hakan ba har Allah yaba baba kabiru ikon kaita ta sauke faralin.
Muna ta daukin zamu je mu ganeta don muna dauka idan mutum yaje saudiya yana wani canzawa ne idan ya dawo.
Ashe abin ba haka yake ba a fili ta aiko muna da tsaraban mu ta hannun wani mutumin garin mu daya gane gidan mu yake shigowa Abuja yin sana,an shi.
Munyi murna sosai da ganin tsaraban zuwan da mahaifin mu yayi gaida umma ne yayi shawaran sayen fili don yai gina a garin da baba kabiru yake don nan ne local govenment din mu.
Bai dawo ba sai da yaga komai ya kan kama na ginan ya dawo yabar baba kabiru da sauran aikin ginan gidan yadda yake son a tsara mashi ginan gidan.
Akan ginan ne baba kabiru ya shigo Abuja wurin mahaifina munyi murna da ganin shi sai dai haduwan su baida dadi don bai koma ba sai da suka samu sabani sosai akan ginan da mahaifin mu.
Don yace shi bai gane kan ginan ba don ba haka akai mashi lissafin komai ba kafin ya dawo wanan maganan ne ya tunzura baba kabiru din yai fushi ya fada ma mahaifin bakaken maganganu shima.
Sai dai kafin ya dawo sai da mama tasan yadda tayi ta shirya tsakanin su dashi har ya hakkura ya karbi aikin akan zaici gaba da kula mashi da aikin a can.
Washe gari ya juya ya koma sai da yai muna alheri sosai kafin ya tafi din muna ta murna da hakan shiyasa muke son zuwan shi ga kifi da sauran abin marmari dayazo muna dashi na tsaraba.
Hutun mu ya kare na koma makaranta cike da kewan yan uwana dana bari a gida don sune abokan hiran nawa a gida tunda ba kawaye nakeyi ba ni.
Karatuna ba wani matsala don baba yana alfahari dani sosai don bani cin na kasa da uku duk hutu don hakane ma nake samun kyauta daga gurin mahaifin namu.
Matsalata daya da baba yawan ce mun banda wayo da yakeyi ko yaushe alhalin niko naga ina da wayau ai amma daga baba har mama abinda suke ce min ke nan danayi dan abu kadan yanzu zansha fada sosai a gurin su.
Umma tazo ta kwana biyu a gurin mu lokacin na dawo gida na samay ta haka muka zauna a cikin tsangwama irin nata .
Tsangwaman ta akainane da kanina baffa da yanzu ya tasa bai son zaman gida ko yaushe suna kwasa da baba akan fitan da yakeyi waje.
Haka yasa itama zuwan ta ta karbe korafin da ta fita yanzu zata haushi da masifa ta bal,balleshi da masifa wai idan ya fita wanan garin da babu kai ba a gane gabas din shi don yawa.
Ranan tare da da kanne na muka je bukin wani birthday sai ba a fara program din da wuri ba har muka kai dare muna can wurin wasan.
Mahaifin mu ya dawo gida ya samu bamu nan nan ya hau mahaifiyar mu da fada don birthday din dan kawar tane muka je dan da kyat ya yarda mu tafi don umma ta saka baki yasa ya yarda muje din.
Ya fita ya bimu a can ya samay mu ana sallaman mu don komawa gida sai gashi tun a gaban mai bukin ya fara bal,balan mu da fada tana bashi hakkuri.
A mota ma mun shs fada sosai a furin shi inda duk laifin ani ya dora min don nice babba a cikin mu muna shigowa gidan umma ce ta tare ni da wani fadan kuma again har yafi na baba ma fadan nata.
A cikin fadan take fadin da wanan wautar har kike son wanan yaron mai shegen wayau din da son banza da sauri baba yake tambayan ta wani yaro kuma umma.
Ita hadiza din har take soyayya ban sani ba ni wai ma wani yaro ne take so din tace rabu da yar nema mara wayau kawai bata san sherin mutanen garin nan bane.
Allah ya rufa muna asiri ya rabaku dasu kike son wanan dan banzan yaeon ya hure maki kunne wa yanda ke cikin garin ma mai suka zama har yanzu.
Wani kallo nayi mata ta watso min dakuwa da hannun ta na noke kaina da sauri tace don na zage shi zaki min kallon banza ko ke gaki issasa ko ?
Baba ya sake tambayan wani yaro ne wai take magana a kanshi tace bar yar nema ai na balbale ta babanta yushau kuma yaje yai mai iyaka da ita har gidan su.
Don ubanshi yazo ya ban hakkuri har gida don yasan halina sarai ba kyalesu zanyi ba wurin mahaifiyana ya juya yana mata kallon tuhuma.
Tayi saurin fadin ga umma nan ka tambaye ta idan da masaniyana haka ya faru din ta yi saurin kare kanta daga masifan shi.
Kutawa yayi ya shige daki na koma na rakube a guri daya ina ganin kamar zai dauki matakine a kaina ranan.
Umma duk abinta Allah yayi ta mace mai rikon ibada sosai dama ance mutum dan tara ne bai cika goma ba gata da yawan saka ma diyan ta albarka.
Bata da sakaci da ibadan ta don ko yaushe a cikin lazimi take tana zikiri da sauran abin ibada daya dace mutum yayi a ganuwan shekaran shi ta karshe.
Tun wanan ranan nake dari dari da mahaifina don ban san irin matakin da zai dauka a kaina kan maganan daya ji daga bakin umma din ba.
Sai dai shiru har hutun mu ya kare muka koma makaranta na barsu a gida daya kaini tun a mota yake min fada mai kama da nasiha akan in mayar da