Showing 81001 words to 84000 words out of 106121 words

Chapter 28 - kanin Ajali Book Complete by Zee Makawa .txt

Advertisement

01 Jan 2025

8062

ya tafi har abadan ibada.
Ban wani wahal da kaina gurin tambayan shi ba don nasan ko na tambaya din ma a banza ne.
Haka ko ya shigo min gida yana wani cicika wai shi rako ke nan yake min abu daya nasan na fada shine ko mai mutum yayi shida Allah.
Bai kula ni ba duk da yasan dashi nake ya mayar dani mahaukaciya mara hankali ga wani hali daya tsiro min dashi.
Idan ya daka min tsawa sai na rude ko gabana ya dinga faduwa ba wani dadin rai a tsakani na dashi cikin wanan lokacin.
Ga fita sai lokacin da yaga dama zai dawo gida don kan shi ba ruwan kowa da dan uwa sai idan yana da bukata na zai tayar dani a cikin dare ya biya bukatan shi a kaina.
Idan ya gama kuma zai fice daga dakin yaje gurin kwanan shi ya kyale mu don kullun cikin kiran zafi yake a dakin mu shi bai iya kwana a ciki wai.
Kowa a gari yana min kallon tausayi do abin ya daina ba mutane haushi sun koma tausayina yanzu kuma.
Don sun san ba karamin cutamin yake yi ba babu dai yadda zan yi don an fahinci sona ya rinjayi nasa a raina.
Nima kaina nasan ina son jamil fiye da komai arayuwa na don shi ma din da yake kokari nuna min haka ada can baya yanzu ya bari.
Zama kawai yake dani na hakkuri da juriya a rayuwan shi don ba yadda zaiyi damu ko may oho ?
Haka dai nake dauriyan yin hakkuri muna zaune da juna ba yabo ba fallasa a tsakani mu sai mutane ke jin haushin da takaicin zaman mu.


Kuyi hakuri dani wanan labarin haka yazo min koni na matsu ya kare don takaicin dake cikin sa ga kuma matsalan da ya shigo na waya sai dai yanzu Alhamdullahi gaskiya.


ZAINAB IDRIS MAKAWA
5/18/21, 11:57 PM - 🤔🤔🤔: Yanayi ya canza muna baki daya sai zaman kunci da zaman hakkuri ya rage min a gidan Jamil.
Gashi ba wani jin dadin Jamil din nake ji ba ko kadan tsawa da hattara ne a tsakanin mu ko mai nayi banyi daidai ba a gurin shi.
Hakana nake hakkuri da shi don son shi da nake ya rinjayi nasa a yanzu tunda ni tsakani da Allah nake son shi dama.
Sabanin shi da nake ji mutane na fadin don kwadayi ya aureni ba matar sa bane ni don ko ganin mu kayi ba zaka taba dauka shine mijina ba a yarda.
Don sai kace shine ya tashi a birni nice tashin kauye din yanzu don duk yanayina ya koma na tifical bakauya a baki daya.
Tun Mutane sun jin haushi na har sun koma tausaya min na zama abin tausayi da kwatance a gari ga kowa da ya sanni a baya.
Muna cikin wanan yanayin ne labarin barin garin Ruth wace ta musulunta yanzu ta koma maryam sunan mahaifiyar Jamil yazo min.
Naji dadin samun wanan labarin sosai a raina don ko ba komai na samu salama a raina yanzu in huta da wani abun takaicin da yake min din.
Ashe zance bai kare ba kwanton bauna yayi min sai gashi bayan kamar wata biyu da barin garin ta shima ya shirya wai gari zai bari zai koma Abuja ya fita nema.
Sun shirya da wani abokin shi ya bashi labarin ana samu sosai idan mutum yana sana, a a can din.
Shiri ya fara yi sosai don tafiya da yasa a ranshi nidai nawa ido ga tafiyan nashi don ban tada wani hankali na ba ga tafiya.
Har ya gama ya sa rana ba tare da ya barmu da wani abin kirki ba da zai tafi don kukan babun da yakeyi ko yaushe yanzu tunda komai ya kare.
Muna haka ne ya tafi ina jin dadi miji na ya tafi abuja neman kudi nasan yanzu zamu samu walwala mu sake don tsananin yayi yawa sosai.
Acewan shi da yaje zai yo muna sako ya aiko muna da abinda zamu ci ni da yara ni kuma na yarda da hakan saboda yadda yake cika bakin shi da tafiya.
Sai bayan tafiyan shi da kamar wata biyu shiru ba sako babu dalili ga dan kudin hayan da nake dan dogora dashi ya karbe yayi tafiyan shi wai da shi zai ja jari a can idan ya tafi.
Haka na kama dan buga buga ina samun abinda zanci da yarana ba wanda zan nufa a cikin yan uwa don da na samu kin su nayi a baya.
Don abin duniya da ya rufe min ido koda yake ba laifina bane idan nace zan ba wani abu yanzu zai bata rai yace shi may ya taba taimaka min dashi.
Amma shi nasa suna ci har na kauye sai sunzo idan sunji na samu kudi a lokacin yanzu ko duk da baya nan sun san irin wahalan da mukeyi bai sa sun taimaka min ba.
Bama wanda ke zuwa inda muke sai nice nakai dan je in ziyarce su wani lokacin haka zan dawo ba wanda zai ban komai a cikin su.
Ranan nayi bakuwa tazo wurina dan abincin dana dafa na zubo mata tare da ruwan sha duk da ba mai sanyi bane na kawo mata.
Na zubo ni da yarana kamar yadda muka saba zubawa idan zamuci mun yi nisa dacin abincin ne take fadin ashe maryam tabar garin nan ?
Sam na mance da wata maryam nake tambaya wace maryam take magana tace Ruth mana data musulunta kan miji ki nace.
Cikin bata rai wanan yar iskan har na manta da zancen ta yanzu ai na bata amsa cikin canza yanayin fuskana.
Tace aini su matar wan mijin ki suka ban namaki don da sanin su ake komai suka munafunce ki dkn ko shirin tafiyan dasu akayi shi.
Duk wani kayan da bata tafi dashi ba kuma su tabawa kyauta su kai wa yan na mutane ai basuyi ba ta kare zancen da fadi hakan.
Raina naji ya baci sosai sai dai nayi dauriya danne zuciya muka dan zage su da mugu;hali su sai yamma ta bar gidana na rakata ta hau mashin.
Ina dawowa gida hankalina ya daga sosai haka nake kamar zawo banda hakkuri ko kadan don haka ban iya kwana ba sai da naje gidan su mukayi tsiya dasu naji dan sanyi a raina.
Sai dai sun karyata zancen wai kazafi akai masu wanan ba zancen gaskiya bane su ko gidan su maryam bata zuwa har ta bar gari.
Haka yasa ni naji sanyi a raina har na basar da zancen don dama na kulla zan barsu har abada idan zancen ya zama gaskiya sai na samu ba haka zancen yake ba.
Ashe sun boye min ne gaskiya ne dasu akai duk wani kulle kullen tafiyan ita maryam din.
Ba dadi da dadi akoma sana,ata ta kayan mata ina kuma dan yin sana,an yara madara aya da sauran su a gida yara na shigowa suna saye.
Sai da ya share wata hudu kafin kacar yayo min sakon dubu biyar mu sai abincin da zamuci.
Jifa dubu biyar mai zai min nida yara da duk sun isa cin abinci yanzu haka na hakkura na karbi kudin muka sai dan abin bukatan mu dashi.
A cikin hakan da muke ne na samu na dan sai tufafin dana dinka nida yarana karo na farko a rayuwana ke nan koshi bashi naci ina bada dan abin daya samu a hankali.
Wanan yasa har ina da shiga jama, a yanzu tunda ina da dan nashiga mutane din da ko bukin dangi ya tashi duk yadda muke da mutum ba zai ganni ba.
A cikin hakan kanwata suka zo ganin gida karo na farko tun tafiyan su kano da mijin ta da ya dauke ta suka tafi.
Sai dai ba wanda yaji dadin gani yadda duk ta ramay ta kalmashe da gani itama dai zaman ana dai yin shine hakana.
Sai dai ita tana da zurfin ciki sosai don bata fadawa kowa halin da take ciki a gidan ta duk da yanzu mutum ake kiwo ba dabba ba gun mutane.
Bata fada ba amma an fahinci hakan a gareta do a san halin da take ciki ba mai dadi bane don ba jiki mai kyau ba suturan kware a gareta sai dai ta dan darani ga hakan .
Don tana dana canzawa gaskiya sosai sai dai ba wani na birgewa ba ne sosai hakan da za a gani asan miji yana kulla da ita .
Abi mamaki shine duk mazaje namu sai kiba suke mulkawa a jikin su muko muna rama kamar ana diban mu kullun.
Don ko shi mijin nata yadda nawa yayi kiba haka shima ya mulka kiban shi ga mota har ya saye na hawa da fara aikin shi .
Shikan zaka gane shi ka gane da birni ne sosai ga wayewa a fuskan shi sai itace ta zama wata yar kunju da ita.
Sai da muka samu kebewa ne da ita nake tambayan ta halin da suke ciki da mijin nata sai take fada min komai.
Babu dai dadi sai dai ta dan dara nine kadan wurin samun walwala amma shima kusan mayau dari ne mijin nata don bai bari ta rike komai a hannun ta karshe kuma yace ba kudin kamar na Jamil dina.
Kuka mukayi sosai muna ba juna magana kn halim da maza suka jefa mu a ciki sai da mu kayi sai da muka gaji muka ba kan mu hakku.
Nace ta boye wanan zancen kada ta bari kowa yaji halin da take ciki a gidan ta tace ai ba zata iya fadi ba ko don anty .
Tunda tun farko saida ta fada muna haka zasuyi muna bamu ji ba yanzu wa zamu tun kara da zancen.
Duk da mun boye sai da anty ta gane muna a cikin wani hali tundai summaiya din don dai ni idan da sabo sun saba da nawa matsalan ko.
Tare muka shigo gidan da kanwata bayan mun gaisa anty ke fadin anya Summaiya kina cikin dadin rai kuwa ?
Dariya tayi na anty kawai tare da tambayan may ta gani halan tace yanayin ki ya nuna akwai abinda ke damun zuciyar ki gaskiya.
Bata samu wani amsa kwarai ba ta bar zancen aka dauko wani hira sai dai hankalinta bai kwanta da ita ba.
Don yawan kallon kanwar tawa da take yi akai akai yasa duk muka tsargu da zama tare da ita.
Karshe tashi mukayi zuwa dakin yan matan gidan muka zauna ana hira mun kai har yamma a gidan kafin mu koma gidajen mu.
A hanya muke maganan abinda yafaru tsakamin mu da anty har muka kai gidan mu muna magana daya akan matsalolin mu.
Bayan kwana biyu ban san inda taji zance a gari ba wanda ni ma dake garin ban sani ba sai ita da tazo daga baya.
Sai gata min hankali tashe tana tambayana wai Jamil wani gari yace min yake ?
Cikin washe baki nake fadin yana abuja ai kila ma ya dawo kafin ku koma don yace kwanan nan zai leko gida.
Ke kin yarda da cewan shi a Abuja yake zaune ne ta tambayane cikin son jin abinda zance mata din.
Nace can yake don haka yace min da zai tafi sai naga tayi shiru taja bakin ta batai wani dadewa ba tace zata koma gida.
Nace tun yanzu zaki koma barin dan dafa muna wani abu muci mana, kai ta girgiza min tare da fadin ita zata tafi.
Don a gidan mahaifan mijin ta suka sauka don sun sake gidan da suke haya da farko.
Rakiya nayi mata har ta samu abin hawa da zai kaita gida sai dai ina dawowa tunanen maganan ta ya hanani sukuni a raina.
Da kyat na basar da maganan cikin zuciyana don kaina ya kulle da tambayan da tai min din wanda ban san dalilin ta na min wanan tambayan ba haka kan jamil din.
Maganan yaso ya tsaya min a rai ko washe gari, sai dai na basar da zancen don ban san dalilin ta na tambayana ba dai.
Yan tsunmakaran ta da na yaranta ta debo ta bamu mu kara duk da banda su hakana na amsa sai dai na raina kayan .
Har fada mata nayi yanzun ke wanan raggadudan zaki bamu don Allah tace ai itama bata da wadattacen kaya da zata bamu wanda yafi wanan din.
Bayan kwana biyu suka fara shiri komawa kano har lokacin Jamil bai dawo ba sai ana jibi zasu koma ne ya dira a garin.
Abin mamaki ga wanda yaje nema ana sa ran zai dawo da abin arziki baje baje sai dai shi Jamil sabani haka na gani a gare shi.
Don daga shi sai yar jakkar tafiya irin ta maza ya dawo garin babu komai a tare dashi.
Sai na dauka kudi ya riko ya dawo dasu gidan don wahalan daukan kayan da zaiyi daga can .
Sai dai har aka kwana aka wuni banji wani abu daga guri shi ba sai kwasan barcin da yake faman yi tun da yadawo a gida bai fita ba.
Abinci lafiyayye na hada mai har da ciwo bashin kayan miya a makwabatar mu na hada mai abincin.
Ya tashi daga barci ya nemi ruwan wanka nakai mai da soso da sabulu ya fito lokacin na gama abinci sai da ya shirya idan ya gama zai fita.
Yar karamar yar mu ce tazo wurin shi tana fadin baba mai ka sawo muna can da zaka dawo shafa kan yarinyar yayi yana fadin..
Ka dai ba kinga babanki ya iso gida lafiya ba mamana da yanzu yan fashi sun kashe maki baba a ganya ai.
Cikin faduwan gabx nace yan fashi kuma ban ya shiga rabtabo min karyan da ya shirya mi duk nabi na rude.
Hankalina ya tashi yadda yake bamu labarin a cikin tashin hankali nan nayi muna barka da arziki da Allah ya tsirar muna dashi daga hannun yan fashi basu kashe shiba ko su illanta shi.
Yana ganin karyan shi ya kamani yace zai tafi gidan mahaifan shi ya gaida su ya fada masu arzikin daya auna a hanya.
Nace tunda dai rayuwan ka ya tsira ai mun gode ma Allah arziki kuma idan da rabon muyi mayi a gaba ai.
Yaji dadin magana na yace wai da Allah yasa yazo gida da kudin nan da mun warke wallahi mun fita daga talaucin don ya samo kudi sosai acan.
Nace ba rabon mu mare masu bane Allah ya kawo hakan nan nayi ta kwantar mai da hankali da dadden magana har ya samu ya fita daga gidan.
Yana fita na nima na fita wurin yan hayan mu ina fada masu suyi min barka da arziki yan fashi Jamil ya hadu dasu a hanya sun kwace mai komai nasa da zai dawo.
A gabana sun min jaje sosai da Allah ya kare gaba kuna sai dai ina basa baya sukace wawiya ya tsarata ta yarda.
Nan dai suka zauna suna gulmana a gurin suna zagina kan irin watauna gurin miji daya tsara ni sai in yarda da karyan shi.
Yinin rana duk wanda na gani sai ba bashi labarin mijina ya auna arziki da yan fashi a hanyar shi na dawowa gida.
Komai basu barshi dashi rayuwan shi kawai ya tsira dashi a gurin su wasu suna yarda wasu kuma suna mn kallon shasha ban sani ba.
Da yamma yar uwata tazo nake fada mata abinda ya faru da jamil din a hanya.
Sai cewa naji tayi kai amma Jamil din nan bai ma ko iya karya ba wallahi da wani irin kallo mamaki na dago kai ina kallo ta.
Ban bari ta karasa maganan ta ba na hauta da fada harda zagi inda nake shiga ba nan nake fita ba don raina ya baci sosai da kalamin ta.
Tace Allah baki hakkuri anty nima rigima na ya kaini fafin haka ai ta mike tare da fadin zata karasa gidan baba kabiru tayi masu sallama.
Ko kallon arziki bata samu ba a gurin balle a dawo lafiya yadda muka saba yi idan tazo gurina sai mu dade muna zuba hira dasu.
Ba yar uwata ba a lokacin duk wanda yayi gigin tara ta ya fada min wanan magana wanke mai shi zanyi tas don idona da rufe.
Sai kuma yadda na yarda da Jamil ya sa ban iya gano illar shi ta ko ina aka fito da zancen sukan shi a gabana.
Don haka kowa yaja bakin shi yayi shiru tunda ban bari a fadi har wasu na zuwa gida yi min jaja suna muna barka da arziki.
Niko sai rabbata masu labarin yadda abin ya faru nakeyi kamar a gaba hakan ya faru yadda nake bada labarin kamar yadda ya fada min.
Kwana biyu muka fara dan ciye dan kudin dake hannu na ina dan juyawa ya fara karewa sai kama kama

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login