Showing 60001 words to 63000 words out of 106121 words

Chapter 21 - kanin Ajali Book Complete by Zee Makawa .txt

01 Jan 2025

7476

abin kallo ne a gurin.
Aka kwasa zuwa gidan mahaifana kamar yadda akeyi a wuri mu sukai ta sa albarka suna fafin yarinya tazo da goshin ta inda yarinya taci sunan mahaifiyar Jamil data rasu watau maryam.
Kayan basu dauki lokaci ba aka bayar aka dawo min dasu kamar dai yadda akeyi idan an haihu ga al,adan gidan mu idan ka haihu zaka cire wa mahaifiyar ka da mahaifin ka turmi ka basu su saka maka albarka.
Amma haka nayi mirsisi na hana ma kowa wanan irin al,adan na hana masu ban basu komai ba nace nima na rama ai haka dai dan kudin da ake kawo min gudun mawa .
Na fitar nake bayarwa ana sawo min biscuet da butan da nake rano ina ba mutane don wanda ya sawo min ko dangin shi bai isa ba lokacin.
Na dai samu aka watse lafiya duk dan abinda na samu ya tafi gurin mutane sai dai ban damu ba don ni Jamil ya gama min komai tunda ya fitar dani a kunya.
Na gyara dakina da taimakon yar uwana data kai har dare a gidan mu ta soya min nama tare da wasu aiyuka muka gyara ko ina na gidan .
Muka gyara akwatin tsab har ta roke wani zani nace ta bari sai Jamil ya dawo naji kudin shi zan bata shi mijin ta yazo ya dauke ta suka tafi.
Gidan ya rage sai ni da yan hayana wanda suke part din su Jamil ya dawo abinda ya fara tambayana shine ina naman da aka kawo na mike na dauko mashi.
Ya karbi roban ya dan jujuya ya girgiza kai tare da fadin wanan naman za a bar muna duk rago dayan nan kato daya yanka sai wanan zamu ci.
Nace gidan ku fa sun cire nasu ankai nawa kason gidan mu suma sun cire na iyayye kamar yadda akeyi baiga laifin wanda yan uwan shi sukaci ba sai wanda yan uwa na sukaci ya hashi haushi.
Ya dan tsince tsoka daga ciki ya zauna yaci da drinks mai sanyi ya kora ya kwanta na dauki roban na duba babu komai sai kasusuwa suka rage.
Dole haka na fara amfani dashi wa gida dashi nake muna girki ina watsawa a cikin abinci idan zanyi.
Kwana biyu da suna tun da safe da yake ba sallah nakeyi ba ina barci ban ko tashi ba sai hayaniyar kattai naji suna fita da buhun abincin da baba kabiru ya aiko min na kunu da tuwo.
Don shine abincin da mace da ta haihu ya kamata taci nasan shine dalilin da baba kabiru ya saka min su don samun sauki a gare ni.
Sai gashi Jamil ashe ya sayar ya soke kudin shi bai min maganan komai ba ina kallon shi yana kallona ba dama inyi maganan komai ya hauni da fada kuma.
Kafin kwana uku da suna duk Jamil ya zauna ya tsotse kasusuwan nan daya rage ya cinye komai dana tanada wa kaina don haihuwa na in samu inci in sha indan na haihu din.
Ranan muna zaune dashi muna dan hira duk akan wa yanda suka zo min gun suna muke hira sai na jefo mai zancen ina son in danyi dinki daga cikin turamay nan daya saka min .
Sai cewa yayi idan ya shirya kai mun dinki shi zai kai da kanshi don haka in saka mai ido kawai yace tun wanan lokacin ban kara mai magana ba ni kuma.
Haihuwa na da sati biyu matar wani wanshi da suke zaune a gidan da wansu ya gina tare da mahaifiyar shi ta haihu .
Tun haihuwa da kwana uku ya turani wai in je in kama masu aiki nace kada ka manta nima haihuwa nayi ai waya zo ya kama min aiki lokacin har ya tare haka a gurina cikin su.
Yace ra,ayin shi ke nan shi don haka in shirya kawai in tafi in ba bacin ranshi nake son gani ba ba wanda ya sani haka na shirya na tafi ina mai jin kunya yadda zan tare wa mutane a gida nima da jego na haka.
Da zan tafi yasa na dauki turmi daga cikin wanda na samu buki a gidan mu nakai wa mai jego cewan in ji shi nashi gudun mawan ke nan.
Na Kai ba wani godiya suka karba a na wani yatsune baki don gaba dayan su ba sona sukeyi ba a gidan don karara ake nuna min bambamci ba boyo.
Ina gidan har sati daya don ko bayan da akai suna sai da ya yasa na kara kwanaki a gidan kuma ranan dai da dare yaje ya dauko ni na dawo gida.
Na samu dakin yayi kaca kaca kin san yarda daki keyi ida an kwana biyu ba,a cikin sa dole na zage na shiga gyaran dakin kamar yadda ya kamata sai dai sama sama nayi aikin ba ko ina na gyara ba lokacin.
Sai waini faman daure fuska Jamil ke min wanda ban gane hakan ba a raina nace ai dole kai bakin ciki da dawowan mu tunda zamu hana ma jin dadin da yakeyi idan bamu nan.
Ban bi ta kanshi ba sai da muka cika kwana uku da dawowa ne nace bari dai in gyara dakina da kyau don har lokacin banga ya koma min daidai ba a idona.
Na shiga gyara inda na fara da falo ganin na gama da wuri yasa na shiga kuryan dakin don in gyara sharo nan kwakwalo nan har nakai wurin akwatuna na sai kawai naga sun biyo ni alaman dai babu komai a cikin sa ke nan.
Ban san lokacin da na yarda tsintsiyan dake hannu na ba na shiga bude akwatunan na sama na bude wanda kayan baby na ke ciki babu komai a cikin sa hatta permpers din ciki an kwashe.
Da sauri na jawo wanda kayan nawa ke cikin sa shima dai hakan na samay shi wayau ba komai a cikin sa hannun na dora akai na zurma ihu ni kadai a dakin.
Ba wanda ya jini jiki na rawa da makyarkyata na fito falo na zauna ina tunane kala kala idanuwana suka birkici a lokaci guda.
Sai wani zufa ke yanko min ta ko ina tunanen duniya na yishi a lokacin yafi a kirga a cikin dan lokaci kada ni kadai a daki ina jin hayaniyar matan gidan daga bangaren su.
Sai nake jin dariyan su kamar dani sukeyin shi sun san abin da ya samay ni ne suke rahan su a cikin gida.




ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
5/18/21, 11:56 PM - 🤔🤔🤔: WORLD




Zaman mu ya koma lafiya da kowa a gidan sai kuma fitina ya taso tsakanina da Jamil akan yadda nake shiri da yan hayan mu yanzu.
Yana fadin wai munafunci ne muke hadawa sai ya tsiri daure wa kowa fuska har ni da nake matar shi a gidan.
Wanan karon fita zancem shi nayi ban yarda na dauki maganan shi da wani muhinmanci ba sosai kamar yadda nake dauka a baya.
Yau tun safe nake wankin tufafin mu har nasa sai da na gama ke neman dutsen guga in goge kayan da suka bushe dutse yace in nemay sa a inda na aje.
Duk dakin sai dana burkuce ina neman dutse ban ganshi ba haka na hakkura na nike kayan na saka a akwati hakana ba guga.
Da dare daya dawo nake tambayan shi ko yaga min dutsen gugan mu sai ya hauni da fada wai na bashi ajiyan dutse ne da zan tambaye shi.
Dole ina ji ina gani na danne zuciyana akan dutsen don duk mutanen gidan mu na tambaye su sunce basu ganshi ba.
Sam a lokacin ban kawo shine ya dauki dutsen ba na dai sa a raina an sace min dutsen ne a dakina haka ba hakkura da zancen dutsen.
Haka rayuwa namu ke tafiya a ba wani ci gaban da muke samu daga ko wani bangare namu daga ni har shi sai yan kamay kamay da mukeyi na rayuwa.
Yayan shi da suke uba guda ya kara auren wata yar uwan maman shi haka yasa dole jamil yasa mu dinke da yarinyar don dole na kama hurda da ita nabar uwar gidan da muke yan uwa da ita tun a mahaifan mu.
Gashi amaryan na bata shekara uku a makaranta don har na kare secondry tana jiniour class a makaranta dana kare secondary dina haka dole nake kiran ta da anty.
Wanan ya jawo yan uwan haihuwana sun tasani a gaba da sheri idan ina kiranta da anty ga ba zaman lafiya tsakanin ta da kishiyar ta.
Duk wani shawarana yana gurin ta shiko jamil da mijin ta ko yaushe tare suke kus,kus a tsakanin su yan kar kaunar da ban sani ba shine .
Ashe Jamil yana zaune da wata matar da zata girmay min ga shekaru zata bani akalla shekara sha ga haihuwa ma,ana dai ta tsofe muna dagani har jamil a gurin haihuwa.
Wanan matar ce suke soyayya da Jamil din sosai ashe har ta dauke mai hankali a gurin yawan neman matan da yakeyi a gari.
Ya koma kamar wani dan dangana sanda ko mai zaman dadiro da ita a gari mutane sai zunden shi akeyi kan abinda suke aikatawa da wanan matar a cikin gari.
Tun ban sani ba har ranan wata makwabciya ta da muke zaman mutunci sosai da ita Jamil din yana hanawa don bai son yaga kowa ya rabeni da sunan mutunci kamar yadda yake ga al,adan mata kowa nada wace nasu yazo daya suna sharing din idea din su na siri tare.
Haka ne tsakani na da wanan matar nima tana sona da tsakani da Allah har a zuciyar ta don zamu kai age mate da ita haka zata shigo ta dan zauna a gurina mu yi hira saboda ita mijinta ba mazauni gari bane yana aiki a Abuja ne.
Jamil na ganin haka ya fara matsa min shifa baison kwashe kwashen mutane bai son hakana sai dai ban yarda na nuna mata wani abuba ga hakan da yake min din na barshi a tsakanina da shi.
Wata rana tazo gidan mu muna zaune muna hira take fadin ita dai zata fada min magana don tsakani da Allah ne take tare dani.
Don ko nice naga abinda ke cuta mata tasan ba zanyi shiru ba ga hakan nace kwarai kuwa don ban kawo komai irin haka a raina ba lokacin.
Sai ta fara min hannun ka mai sanda tana fadin in kama mijina don ita bata jin dadin yadda take ganina ko wani lokaci a shekarun mu bai dace ace ina zama ba kwalliya ba a gida haka yadda nake.
Don mazan yanxu gyara suke so gun mace shike saka har su fita suna hangen wasu a waje da farko maganan nata ya dan soki zuciyana .
Nake cewa a raina mai wanan matar take nufi danine wai har itace zata wani koya min in gyara idan wani gyara ne akwai wanda yafi anty iyashine tama raina min da wayau wallahi.
Tace taji ana fadin wai mijina yana tare da wata mace mai zaman kanta a garin nan kuma a cikin unguwar nan namu shine take mamaki gashi da yarinya kamata a gida.
May zai kai shi gurin irin wa yan nan matan masu zaman kan su yaro dashi a shekarun shi haka, gabana ne ya wani irin faduwa lokacin jin maganan data fada min din.
Tace inyi kokari a matsayina na mace nima in gyara kaina in daina zama haka a cikin gida saboda mazajen mu yanzu basu da tabbas.
Irin matan nan suna da yawa da suka shigo barki don kawai su ci mazanjen mutane su ba aure zasuyi ba dasu saboda cuta kawai.
Ni dai har ta gama maganan ta tana fadin don Allah in boye ta don zancen akeyi a unguwa ta kara da fadin dama ba a cikin unguwa daya bane duk abinda namiji zaiyi dai baka gani ba.
Kuma mutanen dake tare dakai ma basu gani ba balle su fadi, dariyan yake kawai nake mata amma ban ganin wuri saboda bacin rai.
Sama sama muka karasa hiran mu ta koma gida don ta dora girki wa yaron ta don ita ma haihuwa daya tayi a lokacin.
Idona ya rufe rana ko girki ban iya dorawa ba a ranan don bacin rai jiran shi kawai nake ya dawo muyi bala,i dashi kan wanan maganan .
Don ranan duk naji ban wani wanan shegen son da nake mashi din nan sosai hakan nan saboda kishi da ke cina a raina.
Kamar yasan ina jiran shi sai bai dawo ba har daya da wani abu na dare kafin ya dawo gidan munyi barci da yar diyata a lokacin naci maganan zuciyata har na gaji ni kadai a dakin.
Ban samu magana dashi ba sai da asuba da yake ina da magana ranan fitina nane ya tayar damu da asuba inda nake shiga ba nan nake fita ba wurin bala,i dashi.
Sai ya hau dan kamay kamay yana fada wai shi bai son shirmay waya fada min haka shi sai yayi karan mai shi don bata mai sunan da akayi.
Haka muka kai wani lokaci muna ji dalin dashi kan sai na fada mai wanda yazo min da wanan maganan ko mu samu matsala a tsakanin mu.
Har ta gaji ya fita daga gidan yana wani tuku buri a ran shi dani bayan fitan shi ne na dan fito don hada muna abin karyawa duk wanda ya ganni ranan yasan akwai abinda ke damuna a zuciyana.
Don yadda na koma saboda masifa da muka sha dashi da safen maman Ahmed dai ce da muke dan dasawa sama sama take tambayana ko lafiya nake.
Ban iya boye mata ba ranan sai da na gama magana na take fadin wai ashe naji take fadin maman Amira wa zai fada maki wanan maganan ki kwashe ki fada ma mijin ki mashi.
Wanan maganan ai ya dade yana yawo a cikin unguwae nan gaskiya nan dai take kara fada min wani abinda kawata bata fada min ba akan maganan.
Hankalina ya kara tashi da jin zancen satin mu biyu muna rikici dashi na dauka ya saduda ne ya daina don naga yayi sanyi sosai yana dawowa da wuri idan ya fita yanzu.
Sai dai abinda ban sani ba hakan takone na mayaudaran maza da suka iya mu,amula da matan banza zuwa ga matan su na sunna.
Kwanton bauna yayi min sun canza tako da wanan matar don yana ganin mutane sun saka masu ido yanzu.
Sabon sallon da ya tsiro min dashi shine zai wuni gida dami da mu da rana a daidai lokacin da matar take fita gurin aiki don ma aikaciyar gwaunati ce ita.
Sai ya wuni a gida yana barci sai ya kwantaci bayan la, asar zaiyi wanka ya fice gidan lokacin ta dawo daga wurin aiki ke nan.
Ba zai dawo ba sai daya darabi ko biyun dare zai shigo ya kwanta a takure idan nayi magana sai yace min zafine yayi yawa yanzu yasa ya ke rage dare a gurin hiran su.
A zatona ya rabu da wanan matar sai da wani watan azumi mijin ma kwabciyar mu yace tazo gurina in san mata attarudu don shi ya manta bai sawo ba.
Amma yaga jamil ya sai kayan miya kila ya sayo da attarudun shi ina zaune ina jiran shi ya kawo min kayan miya wanan matar ta shigo.
Tana tambaya na nace bai riga da ya iso gida ba a lokacin yau zanga jamil ya dawo gidan da kayan miya shiru har aikai maggariba ya dawo hannu a sake.
Nake tambayan shi ina kayan miya shi nake jira ban karasa girki ba sai cewa yayi na bashi ajiyan kudin da zai sawo kayan miya ne ina ganin shi da safe ai haka ya fita gidan ba wani kudi a hamnun shi ko naga yana sana, a ne da zai samo kudi.
Nace kayan miyan da aka ganka ka saya fa na waye shi nan ya fara fada wai ya gane dai yanzu ido aka saka mai a unguwar nan haka da yawa to baban shine ya aike shi ya sawo masu daya je gaida su.
Jin haka hankalina ya dan kwanta har ina fadin aida ka fada mai baka da kudi muma ko zai sai muna yanzu ga shinkafa na dafa ba miyan da za,a ci kum, yace yanzu sai in san dabara ai.
Ashe cefanan da aka ga yayi can gidan Ruth ya nufa dashi suka dafa a cewan ta yanzun ta musulunta tana son ta auri musulmi.
Hakana rana muka ci abinci da mai har ya fara ci yace ba zai iya ba kada ya jawo mai ulcer ya sha ruwa ya fita zuwa gidan Ruth din yaci wanda ta dafa masu dashi.
Sai dai ban kawo komai ba a raina tunda yace mahaifin shine ya aike shi saya na dauka bai da shine yasa bai sayo muna ba.
Ban tsinke ba sai da sallah ya kwaso min gwanjon kaya da ta zauna ta gyara masu dinki dagani har yara ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login