Showing 96001 words to 99000 words out of 106121 words
Chapter 33 - kanin Ajali Book Complete by Zee Makawa .txt
har muka gama ya kasa furta komai gare mu.
Haka muka fito rai a bace don kudin ba suyi muna dadi ba kamar wa yanda suka sai da wani abu a kasuwa ba mahaifan su ne suka rasu ba.
Gidana muka nufa da kudin kai tsaye inda muka samu Jamil yana jiran mu a kage dashi kamar yai tsuntsuwa ya bimu gidan baba din inda ake rabon kudin.
Muna shiga yana ganin mi rai a bace yake fadin yaya akayi baffa ya ce kai rabu da mashiririciya kawai taje ta sa mutane a ciki kawai ashe ba haka na bane abin.
Nan ya tare shi da fadin kai abi abin nan a hankali zaku gane gaskiya fa ba abinda ba a iyawa yanzu wallahi.
Kana ganin ba hadin baki akayi a rage kudin ba a baku abinda bashi bane wai ma nawa ne suka baku wai ?
Baffa yaja tsuki ya mike ba tare da ya fada mai komai ba ya fice daga gidan .
Kallon mamaki Jamil ya bishi dashi har ya fice nan dai ya sakani gaba na fara mai bayanin shiririta cikin rashin fahinta.
Yace kai ina ba za a yarda ba wallahi zanbi in gani har sai na gano gaskiyar wanan maganan sai kudin nan sun fito wallahi.
Yace bari in nemi layin baba hamza wani dan uwan mahaifin mu dake aikin yan sanda shima a sokoto ne ya mike ya fita.
Don zuwa nema layin baba namu dake sokoto ya fita bai dade ba ya dawo yana fadin na samo layin baba hamza barj in kira baffa yazo muji yadda za a yi.
Ya zauna yana kiran layin baffa din har ya katse bai dauka ba ya ha tsuki ya kasa hakkuri ya kira layi wanan baban namu na sokoto can ya dauka.
Kun san mutanen yanzu sai a hankali maimakon ya gyara zancen sai cewa yayi da Jamil tunda ta fadi haka ta ganine.
Ni yanzu abinda zanyi shine zan nemo maku wayan wanan da aka saka gaba wurin fitowan kudin ku don muji gaskiyan maganan.
Idan ya kama kuzo ne sai ku shirya kuzo ku samay ni nan sokoto muje office din da ake abin muji komai.
Basu kashe waya ba suka shiga zagin su baba ina jin ban iya daukan matakain komai ba akai don nima a lokacin na hau sosai dasu a raina.
Nan dai muka bar zancen iba batun tashi in fita naji yace to yaya ake ciki ne wai banji kince dani komai ba har yanzu mana ?
Dakatawa nayi nace kamar na may fa yace a dake ba a baki kudin bane ko may nace ambani mana amma duka suna gurin baffa ai bai ba kowa nasa ba tukun.
Kamar ya suna gurin Baffa kudin ke baki da laluran yi da kudine da zai rike maki kudi ko rainin wayau ne kuma yin hakan ?
Nace suna dai guri shi ya rike baice dani komai ba har yanzu gaskiya yaja wani guntun tsuki ya mike yana fadin an sa muna da lalurar kudi zai wani rike kudi a hannun shi.
Ko ya fiki sanin duniya ne da zai wani rike kudi a hannun shi yana karami gare ku kuma nidai tunda na fadi hakan ban kara mai magana ba.
Sai dai nasan da wuya kudin nan su shiga hannun shi yadda aka saba don Baffa yasha alwashin shi zai rike namu din gaba daya dani da kanwata .
Washe gari da muka tashi da wuri ranan Jamil din ya tashi yana tambayana ko baffa yazo a daren jiya wuri na ?.
Nace tun fitan nan da yayi ba sake shigowa ba har yanzu ya ja tsukin da ya saba ja din kamar ko yaushe.
Kafin karfe biya ya tambaye ni sau ba adadi ko Baffa din ya shigo nace bai shigo sai ya ja tsuki ya fita.
Yinin ranan nan ya zauna a kofan gidan yana hira a camban yan unguwar wanda nasan zaman jiran Baffa yake ya bullo.
Sai yamma lis Baffa din yazo gidan yana hango shi da kyat ya daure ya jira karasowan shi inda inda ya dan tsaya na wani lokaci har ya dan bada time kada aga gazawan shi.
Tunda baffa din ya shigo muka gaisa nake tambayan shi ko yaga Jamil din a waje yake tambayan may zan mai idan na ganshi.
Nake fadin kai yake jiran zuwan ka tundazun ai yaja tsuki yaci gaba da min bayanin abinda suka tsara da sauran yan uwana.
Kan mu mata zamu bada dubu ashiri su maza dubu hamsin a rabawa yan uwa na birni dana kauye mazajen mu kuma dubu hamsim daga cikin kudaden mu .
Sauran zai aje muna a gurin shi ya duba abinda ya dace asai muna dashi don gudun tabarbarewan kidin a hannun mu.
Ban kai ga magana ba Jamil din ya shigo gidan yana fadin Baffa ka shigo ai dazun na kira layin ka bai shiga ba tunda safe nake gwada layin naka.
Yace eh barci nake da safe na kashe wayana ne Jamil yace dama akan maganan kiran baba hamza ne don na samu layin nasa har na kirashi nayi mai bayani .
Amma yace hakan ba gaskiya bane don hakama ba zai yuyuba tunda tagani a rubuce lalai an rage kudin nan ne anbi wani hanya dasu.
Tsuki Baffa yaja tare da fadin kai wanan maganan a barshi kawai, don Allah, ba kamshin gaskiya ga maganan ta ko kadan .
Jamil yace a, ba hakana bane kada kayi mamakin sai azo abincika kaga kudin sun fito daga baya don sun mayar da ita mace ce kawai wallahi ya kawo haka.
Ni tun farko ban so aje da ita wanan tafiyan ba ita kadai haka, na riga da munyi magana da mutanen sun ce muna iya bi hakkin mu.
Wani kallon kai din Baffa yaiwa Jamil tare da fadin da kudin wa zakuyi wanan hidiman haka yana fadin haka ya fice yana dariya.
Ina zaune ina sauraren su, nan dai ya bi Baffa din zuwa waje sin dade suna magana dashi koda ya dawo naga fuskanshi a daure .
Sai dai yana ga bakan shi na son abi kidinkidin din kudin da yake tunanen an lake muna a sokoto.
Yana wanan maganan sai dai hankalin shi yana gun kaso na da baiji labarin shi ba har lokacin don haka a cikin dare ina barci ya tutseni ta hanyar tayar dani daga barci.
Sai na fada mai ina kudina suke akan may ba a bani ba yadda aka saba bani nawa a hannu na da farko wanan karon aka hana min.
Nace suna gun baffa duk kudin namu yana gurin shi ga baki daya ya rike ranan dai munyi fada sosai dashi kan kudin.
Da safe kamar baffa ya san munyi wanan fitinar sai gashi ya sallama min da kudi daya lissafa min din zai bawa kowa ya fara fitar wa sai ga Jamil ya fito daga daki fuska a daure yana shan kanshi kamar wani Alhaji dashi.
Sun gaisa da baffa a tsatsaye baffa ya kirgo kudin daya ware mai daga cikin kaso na dubu hamsin ya miko mai kallon kudin yayi shekeke tare da fadin wanan fa kudin may ye ?
Shima cikin daure fuska ya bashi amsa da fadin kason kane daga cikin kudin matan ku dana cire makowanin ku.
Kallon kudin yayi kamar ba zai karba sai kuma ya karba yana juya su a wullakance tare da fadin wanan ne kason nawa wanan karon?
Eh su muka cire maku inji baffa shima ya kara bashi amsa a wullakance kamar yadda yai mashi magana shima.
Yace kasan yadda mukai tsamanin kudin ba haka suka zo muna ba don haka ayi hakkuri da abinda aka gani kamar kowa.
Ya juya inda nake yaci gaba da fadin sai kudin da za a rabawa mutane gasu nan naso nakai masu amma ina ganin banda lokacin yin hakan don zan koma wurin services dina wanan satin.
Fita jamil yayi a dakin rai bace bai kara bi ta kan mu ba kuma ya fice gidan ga baki daya har muka gama maganan mu da baffa din.
Ashe komawa yayi kofan gida wurin wani icce ya zauna yana hadiyan rai don bakin ciki da takaicin da ke diban shi a lokacin.
Shi a ganin shi an mashi rainin wayau don may za a yanka mai abinda za a bashi daga cikin kaso na kuma don wullakanci.
Ya dade gurin zaune yana sake sake a zuciyar shi har ya gaji ya mike ya shiga gari don kudin basu usan shi ko biyan bashin gari balle na can inda yake zuwa din.
Cikin dare ya dawo har lokacin fuskan shi ba wani walwala a tare dashi sai bacin rai zalla da yake tare dashi.
Muna zaune da yarana muna hira ya shigo falon ya samay mu a zaune muka gaida shi da dawowa gida.
Ya amsa muna wani iri dashi ni dai ina zaune ina jiran jin abinda zai ce min din wuri ya samu ya zauna tare da bude abincin dake rufe nasa.
Ya juyo yana kallo na da tambayan yaya naga miyar ba komai a cikin sa kuma ?
Nace ba komai da zan saka ka fita baka dawo ba tu dazun kuma naga yamma bayi na dora hakana.
Na bashi amsa ina kawar da kaina gefe daya yace naga alaman kun shiry yi min cin mutunci ke da yan uwanki a gidan nan .
Kuna son mayar dani wanda bai san ciwon kanshi ba ko wani gara can dai kuke kokarin mayar dani ?
Wanan ai wullakanci ne da rainin wayau ni ake gudu da kudin ki ko may yanzu don ban gane may kuke nufi dani ba haka ?
Shiru nayi ina kallon shi yaci gaba da fadin don kun raina ni za a dauki wani dubu hamsin a bani anga mabukaci ko may ?
Na kasa hakkuri da maganan da yake fadi din nace ni may ye nawa a cikin maganan nan tunda bani na tsara hakan ba.
Idan bake kika tsara ba waya tsara hakan kudin su ne ko naki idan ba da yardan ki aikai hakan ba yaya zasuyi hakan da kudin ki ?
To bari kiji ni ba zan yarda da wanan tsarin da aka fito dashi ba yanzu dole ne ki karbi kudin ki hannun baffa ki bani in juya su yadda muka saba.
Nace ni wanan ba magana na bane ka samu baffa din kuyi magana dashi zaifi amma kazo ka samay ni kana fadin kai baka yarda va nima naga kudin nawa ne.
Yace sai sun cire kudin su da kaci na haya aciki saura kuma kadan kadan zai dinga bani ina sayen abu dashi idan bukatan hakan ya taso min.
Bai bari nakai aya ba yace a harzuke ida baki karbo kudin na ba wallahi sai rayuka su baci a gidan nan ni za a kawo wa raini hankalin banza ko wa ?
Ya kare da fadin don rashin tausayi zakiyi wa yara abinci haka babu komai a ciki may ye amfanin kudin da kika samu yanzu yana fadin haka ya shige daki ya bar ni a gurin zaune.
Wasa wasa ya tayar min da hankali sosai kan kudin ya hana mu zaman lafiya shi kuma ya kasa yiwa baffa maganan kufin da bakin sa sai ni yake turawa in mashi.
Tun ina boyo har yakai na kira baffa din na fada mai halin da ake ciki akan kudin baffa yace idan yana son kudin ya nemay shi mana ai bani zaiwa magana ba.
Kudin da baffa ya bani in kai wa yan uwana a kauye yasa ni gaba a kansu su da yake gani a kusa sai da ya kwaci dubu talatin a cikin su da fada da komai kuwa.
Sai lissafin ya bace min yadda zan raba kudin wa mutane tu ina boyo har dai najewa anty da naganan bata so saka muna baki ha amma haka ta hakkura ta yi min bayani.
Ta gane cewa Jamil ne ya karbe duk da na boye nace ban gane kan lissafin da baffa yai min bane.
Da taimakon shawaran ta na samu na dan tsankwarawa mutane kudin abinda ya zama abin magana daga baya gareni ke nan.
Don baffa yayi fada yayi jininin yadda nayi da kudin har ya gaji ya kyale ni hakana ga Jamil ya kasa hakkuri sai da suka zauna da baffa kan yana son a ra mai kudi daga cikin kudina ya juya.
Baffan yaki ya bashi a cikin lalama sai ya shigo ya samay ni yayi min bambami ya fice kan zai iya sakina kan maganan nan don baiga amfanin aure na ba yanzu tunda zan iya samu in hana shi.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
5/18/21, 11:57 PM - 🤔🤔🤔: Mun kai wani lokaci ba zaman lafiya a tare damu a gidana ni da yar hayar nan sai da iyayyen ta suka zo suka shirya mu sama sama dai muke zaune da ita yanzu.
Ranan naje gidan mu gaida su anty ke min fada don may na yarda da sherin mijina na biye mai akn zancen kudin da nasan ba gaskiya bane.
Tace ke kin fi kowa sanin waye baban ku hadiza amma wai ace ki biye mai kun tafi sokoto binciken nawa ne kudin da aka turo mai ainihi a account naku ?
Nauyi da kunya suka rufeni a lokaci daya don ban taba tsamanin zasuji wanan maganan ba sai gashi an tare ni dashi yanzu.
Ta ci gaba da fadin wanan halin da kukeyi kunawa kanin mahaifin ku adalci ke nan ?
Duk irin kokarin da yake daku may yasa baku gani kada fa ku zamo cikin irin marayun da basu da godiyan Allah nan gaba duk ko da irin tarbiyan da muka baku dan zaman da mukayi da ku.
Kaina na dukar kasa don ban san abinda zance da ita ba kuma don dai bamu kyauta ba gaskiya nan dai na fara kamay kamay ina fadin .
Anty kin san halin Jamil akan kudi idan yaji maganan kudi bai iya zama duk shi ya rikita wanan maganan haka wallahi.
Tace don Allah ki bar wanan maganan banza idan ke baki nuna mashi cewa yana da right din tsoma baki a cikin maganan ku ba wane shi har yace zai soki mahaifin ki .
Ranan dai naji nauyin kaina da kunya sosai don nice naba Jamil duk wani kafa nayin duk abinda yake so acikin maganan tamu.
Amma idan ba haka ba ina shi ona zuwa wai bincike akan yadda kudin suke bayan iyakan shi ci idan an bani rabona ko yaushe in sun kare kuma in ga wullakanci.
Ni kaina bansan ya tafi sokoto yana bincike akan kudin nan ba sai daga baya nake jin wai ya tafi sokoto ya bincika idan gaskiya haka aka ba da kudin kamar yadda baba ya fada an turo mai.
Ina cikin wanan jimamay ne sai ga Jamil ya dawo a lokacin da banyi zaton dawowan shi ba garin.
Ban san may yazo yi ba ni dai ranan ina waje koda na shigo na samu ya share dakina tas ya kwashe harda cinnakun da kiyashi yana zubawa a cikin leda.
Tsaye nayi ina kallon shi da mamaki har ya gama abinda yake baice dani uffan ba yana kokarin fita daga dakin.
Na iya bude bakina da kyat ina son in tambaye shi ina zai tafi da abinda ya kwasa a dakin sai hannu ya daga min alaman in bari ya dawo ya fice da saurin shi.
Na bishi da kallon mamaki tare da daukan abinda zan dauka nabar dakin ba tare da wani damuwa da abinda naga yanayi din a dakin ba.
Washe gari ya tattara yabar garin ya koma inda ya fito ba tare da bar muna komai ba da zamuyi amfani dashi kamar ba mutane yake bari gida ba ya tafi.
Don yadda yake barin mu ya wuce bai aje muna komai na amfanin gida ba da ya kamata a jewa mace idan za ai tafiya da za, a dade ba,a dawo ba.
Sannu sannu na fara aiki shikan shikafa ina sayar da tsakin buntun shikafan don samun abinda zan ci dani da yara na.
Sana,an shika ya matukar karbe ni sosai ina zan dinga bin duk wani injin din nikan shimkafa ina bukin din butun shikafa idan sun fitar da mai kyau.
Na fara a boye gidan mu da yan uwana ba wanda yasan ina wanan sana,an abu ga mara wayau ko dabara nan na fara ba mutane labarin irin amfanin da nake samu ta hanyar sana, an da nakeyi din.
Baki na fadi takashi na fadi take ko mutane suka gane akaiwa sanan an ruuuuu kowa shi sai dai duk da hakan ina samu fiye da tsamanin mai karatu gaskiya.
Alokacin na karkare komawa wata irin bagidajiya don baka saye na kwabo ka dauka daga ni har yarana dake a wahalce dasu.
Saukin