Showing 51001 words to 54000 words out of 106121 words
Chapter 18 - kanin Ajali Book Complete by Zee Makawa .txt
yaron ba yaron kirki bane sam ni dake fita a garin nan nasan ko waye Jamil don bai aje kanshi a kusa ba.
Baya hali irin na diyan tallakawa sai na diyan attajirai masu hali zaka dauka dan wani gwauna ne ko minister shi yaya ko mai wanan halin za a rabashi da neman mata.
Tun farko abinda hajiya tayi maki duba ke nan a kanshi wanan na daya daga cikin abinda take maki gudu da halin su.
Wani irin gululun bakin ciki ne ta ziyarci zuciyana a lokacin don may sai yanzu ake fada min abinda ni ba kasa hangowa kaina a baya aka rufeni ta baibai ina hauka.
Muryan baba ne ke fadin yanzu shi da yaron arziki ne har zamu kai maki kaya ya kwashe ya sayar don baida kunya data idanu ga iyayyen shi a gida basu fada muna komai ba kan hakan.
Tun wanan lokacin na raina halin shi dana mahaifin shi shine zaman da sukace zasu zo gidan su zauna daku don kada a barku ku yara zallah a gida babu babba a cikin ku din.
Sai kuma ya koma bani hakkuri akan in koma in san hanyar da zan bullo mashi ya daina wanan halin daya tsiro min don rainin wayau ma a cikin gidan daya kanwar yar hayana yake nema kuma.
Haka dai ya samu har na natsu na daina kukan fili da nakeyi sai na zuciya yanzu na koma yi ina maijin wani irin zafin Jamil din a raina ga wanan rainin wayau daya ja min gun yan hayan gida na.
Duk zaman lafiyan da nakeyi dasu sai da yayi kokari ya zubar min da mutunci na a gare su ta hanyar neman yar uwarsu da yajeyi wanda nake ganin kasawa ne a hakan gare ni.
Nan dai anty ta lalabani na koma daki na zauna aka kawo min abinci naci sai dai ban iya cin wani abin kirki ba duk da son abincin da nakeyi in ci a raina don tun safe ban samu na karya ba saboda ruwan saman da akai tayi da tun bayan sallah asuba din ranan.
Bayan la,asar sai ga mama matar mahaifin shi ta biyo bayana tana fadin ita bata san ban gidan ba ta dauka ko ina daki na kwanta ne bayan da aka gama hayaniya da yan hanya aka lafa.
Nan dai sukai ta magana kan hakan da matan baba inda suka nuna mata rashin dacewan hakan da yake min a gidan dake da mata da yawa.
Ta samu ta bada hakkuri muka koma gida tare da ita kamar komai bai faru ba a baya har dare gogan bai leko gida ba sai dai ban sani ba ko ya shigo bayana don ban ga alaman hakan ba tunda banga ta canza tufafi ba .
Daya shigo gidan kai tsaye abinci ya tambaya nace ban yi ba har da dan barazanan shi don may ba a girka abinci ba nima a hasale na bashi amsa da kaje gurin yan iskan da kuke watsewa su dafa maka ya juyo cikin mamaki yana kallo na .
Kafin ya furta wani abu muryan mahaifin shi ne yake kiran shi yasa shi juyawa a hasale ya fice daga falon zuwa karba kiran mahaifin nasa.
Ni dai ban san yadda akayi ba sai gashi ya dawo yana cicika yana fadin ni hussai zata dora wa sheri wai ke harda yarda da maganan ta.
Wallahi sai sun bar gidan nan a cikin kwanan nan kuwa nace sherin may kai kadai ne namiji a gidan nan da ba a dorawa sauran sheri ba sai kai kadai da yake yasan baida gaskiya sai ya shiga yan kamay kamay yana fada har na fara yarda da abinda yake fadi din.
Mun danyi zaman sama sama dashi na kwana biyu sai ranan naga ya dawo da wuri yana wani haba haba dani da yar goyona Amira .
Abinda bai saba yi min ba ni kuma rashin wayau ya hanani gane halin shi da sai wani abin arziki zai faru dani yake min hakan da naga yanayi din zaiyi.
Ashe sun hadu da kanina a waje yake fada mai ai mutumin nan ya kira baba yace mu sa rai a cikin sabon wata zamu samu kudin mu insha Allahu.
Lokacin har na kashe yan kaya haihuwana da anty tasa aka dinka min dana haihu har sun fara shan ruwa sosai banda zanin shiga jama,a na kwarai a dakina.
Sai daga bayane yake labarta min abinda ake ciki akan kudin yake fadin idan kudi sun zo sai mu gyara dakin mu muyi wanan muyi wancan.
Ni dai kallon shi nakeyi sai da ya kare nace ni duk ba wanan ba indai samu abinyin sana,a daga ciki shine burina a yanzu don zama haka ba sana,a ya fara isata a gidan .
Dan dadin bakin yace ki kwantar da hankalin ki sana,a ai kamar kinyi kin gama nima kaina sana, an nake son yi yanzu sosai don zaman nan haka ya isheni sosai.
Yan matan gidan mu ne suka kawo min ziyara ashe suna kule da zancen neman kanwar yar hayan da naje masu da labari yayi ranan dai sai da sukayi shi ba dadi da matar gidan namu inda suka zage ta fes daga ita har yar uwan nata da take kurin yana nema din.
Ya samu labari sai dai ban san a inda yaji labarin hakan ba nan yazo da cin mutunci wai shi nake son inwa tonon asiri da har zan gyato yan uwa suzo har gida suyi cin mutunci haka.
Sai daga baya nake ji wata yar gidan dake haya take fada min wai matar mahaifin shi ne ta tare shi waje ta labarta mai komai daya faru.
Wanan bai damay ni ba don cewa nayi idan da baiyi ba ai da hakan bai faru ba nima tan uwa sun kwatar min yanci ne a gurin su su san ba banza nake ba.
Yayi fushin shi ya gaji ya sake hakan bai sa ya fasa halin shi ba kullu fes yake kamar wani mai zuwa office dashi haka zai dauki wanka ya fice daga gidan sai wani lokaci ya dawo.
A cikin haka ne bukin kanwata Sumaiya ya kawo jiki ana ta shirin buki iyaka ta ido sai kamay kamay danakeyi do banda wani katabus a gurin sha,anin tunda banda shi.
An nuna mata gata sosai don an mata abinda ko rabin shi ba ai min ba don komai nata yafi nawa tsada sosai suma gida mijin sun nuna nasu bajintan sosai don set din akwatuna ne da zanuwa ciki masu tsada sosai suka saka mata.
Ana cikin harka bukin ne na dawo gida don daukan kayan dana manta na rista matar mahaifin Jamil mama suna gulma da yan hayan gidana inda suke shiga banan suke fita ba mama harda cewa wai ni din ba sa,an auren Jamil bace matsa mashi akayi ya aure ni.
Nan kan idona ya rufe ranan na mayar mata da ansa sosai ga maganan ta inda ta shiga kamay kamay wai nayi mata kage da sheri ba abinda tace ke nan ba ita.
Nan dai mukayishi ba dadi na dawo gidan mu ina labartawa yan uwana abinda mama din tayi min aiko suka shiga yaba bakar magana a kanta .
Kowa da irin abinda yake fadi mai zafi don bacin rai can kuma gida jamil na dawowa ra samay shi da kukan munafunci wai nayi mata tono asiri don anga bata haihu da mahaifin su ba ake mata haka.
Shiko Jamil ya daure min ko dana dawo yaki min magana nima na daure mai da safe na shirya zan tafi gidan mu ya hau bala,i wai na raina shi da iyayyen shi don naga basu da hali yasa nake masu wulakanci shi sai ya rabu dani ba komai bane a guri shi.
Nima nayi zuciya ranan nace arabu din mana sai may ko shi ya samu ana gulman shi yadda na samu mama da yan haya suna gulma na dole ya dauki mataki.
Yace ai shi ba haka ta fada mai ba nace ai ba zata fada ma gaskiya ba don tasan da kazo baka binkici zaka hauni da fada nan dai na kwashe yadda akayi na labarta mai komai.
Yace ita mama din ke fadin hakan nace kwarai kuwa don da kunne na naji ba wani ne ya labarta min ba yace yayi kyau nan ya fice nima na rufe zuwa gidan mu wurin bukin yar uwata ta haihuwa.
Anyi buki lafiya ankai amarya lafiya da na dawone naga canji sosai a gurin iyayyen mijina sai wata yar hayan ne take labarta min abinda ya faru a bayana tsakanin su da dan su.
Inda tace Jamil din ya goyi bayana don anyi turke turke a gidan tun wanan lokaci ta fara tayar da hankalin ta a kan zama damu a gidan muka koma kamar kishiyoyi da ita kuma.
Zaman kanwata da mijin ta kowa yana yabawa don zamane na mutunci sosai sukeyi ko ni din banda matsalan wurin abinci don muna cin maikyau mu sha mai kyau.
Sai dai ta fannin sutura ne nake ganin ba daidai ba gare ni ga dakina ko macen data dade da aure ta bani lafiya har kunyan baki so zo min dakin nake ji sai in kama kamay kamay idan nayi baki.
Shiko gogon haka bai damun shi kullun a cikin jiran kudin magaifin mu su fito yake a gyara daki dashi shine burin shi a kullun bai ko jin kunyan hakan.
Neman mata kan sai ma abunda ya karu gare shi don yanzu baya kunya ko shayin kowa kai tsaye yake abinshi yadda yake son yi
ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
5/18/21, 11:56 PM - 🤔🤔🤔: Ganin rashin dawowa gidan shi da wuri yana ci mun rai ga kuma abinda mahaifin shi yace da nakai kara yasa na sa ido gare shi.
Yau ma da yamma yai wanka ya shirya ina zaune ina kallon shi yana ta faman feshe feshen jikin shi da turare har ya gama zai fita nake tambayan shi kudin cefane .
Ko kallon banza ban samu ba a wurin shi yasa kai ya fice daga gidan wana abin ya karas min jin haushi da takaici ranan dai sai garin rogo muka sha nida diyana ga ciki a jikina kuma.
Ina zaune ina kallo na dubi agogon dakin lokaci ya nuna sha biyu da rabi na dare tashi nayi na goya yar diyata a baya na sa hijjab dina.
Banji tsoron dare ba haka na fice tunda gidan namu a bakin titin unguwan mu yake nasan ba zan rasa mutaje ba a lokacin a waje.
Gidan hanyan da Ruth take na nufa don ba wani nisane a tsakanin mu ba don dama matan unguwan mu sun min kwatancen gidan har dakin da take zaune a ciki.
Ina shiga dakuna ne birjit sai kida ke tashi da kallo a wasu dakunan na gida dagani kasan gidan da kabila suke zaune ne a cikin sa.
Dakin na dosa inda cool music ke tashi ciki a hankali ban tsaya wata wata ba nayi nocking din kofan dakin da karfi ina duka iya karfina .
Muryan Jamil ne daga ciki yake fadin who is there ?
Na kara nockin iya karfina sai naji muryan ta tana fadin iam coming dan wani lokaci aka bude kofan tana dare da dan karamin towel iya cinyanta tayi daura gaba dashi.
Budan kofan mukai arba da ita da sauri ta koma tayiwa kofan key yadda ba zan iya shiga ciki ba nan take na dinga dukan kofan ina zagi sukaki budewa daga ita har shi.
Dukan kofan da nake da zagi ne ya jawo hankalin mazauna gidan suka fara fotowa daya bayan daua daga dakunan su suna tambaya lafiya.
Sai zagi nake ina fadin husband snercher shame for you ina mata ihu idona ya rufe sai kallo na mutanen gidan keyi sin kasa min magana.
Sai wani iyamiri daga shi sai dan gajeren wando ga katon ciki ne yazo wuri yana fadin madam kiyi hakkuri ki koma gida basu kyauta maki ba gaskiya amma kiyi hakkuri don Allah.
Kin ga nan gidan haya ne yaran mu sunyi barci zaki iya tayar dasu daga barci gashi gobe suna da school yana kokarin jan hannu na na fisge hannun nawa daga rikon da yake son yi min.
Na kokarin shi kaini wajen gidan ganin naki kula shi ya hada hannayen shi biyu guri daya yana fadin don Allah kiyi hakkuri ki koma gida ki jira mijin ki ya dawo sai kuyi ta can dashi tunda sunki bude kofan gidan.
Kallon shi nayi ido jawur sai ya kara hada hannayen shi wuri daya tare da fadin don Allah a cikin hausan shi da bai zauna ba sosai a bakin shi.
Ganin yana ta hada ni da Allah gasu su kuma sunki bude kofan yasa na juya na fara tafiya na fito daga gidan mutumin yana biye dani a baya yana bani hakkuri.
Yace mun san basu kyauta ba muma muna magana don abin nasu yayi yawa sosai har muna tunanen yana da mata kuwa akace muna kece matar shi ai.
Kiyi ma mijin ki nan fada sosai don Allah ko mu a gurin mu wanan abin kunya ne haka da sukeyi har sai da ya fitar dani a lungin gidan da sai yanzu nake jin tsoron wurin mutumin ya koma gida.
Ni kuma na wuce zuwa gidana hankali a tashe kowa yayi barci a gidan haka na zauna kamar manya ina dakon jiran shi ya dawo.
Karfe daya da wani abu ya shigo gidan yana wani muzurai da shan kamshi a fuskan shi yana shigowa na dora mugu azzalumi macuci ma,hainci kawai fita min daga daki kada ka goga min zunibin da ka kwaso a daki.
Wani kallo ya watsa min yana kokarin shiga dakin na tare kofan da sauri ya bangaje ni na fadi ta bayana sai da kashina ya amsa min don yadda naje baya din.
Ya shige abinshi na tashi da kyat na bishi ciki rikici sosai mukayi dashi har da saki ya bani a cikin daren nan kafin gari ya waye don ya zagu sosai a wurina.
Da asuban farko ya fita gidan ashe gurin mahaifin shi yaje ya fada mai abinda ya faru a tsakanin mu inda ya nuna mai rashin gaskiyan shi kan abinda yayi min din .
Ina zaune inda na idar da sallah sai lokacin nake jin ciwo a kwankwaso na a inda na buge din daya ture ni da dare yake min ciwo sai sallaman su naji har da matar baban shi sun shigo.
Ban daga ba daga inda nake zaune anan suka samay ni muka gaisa dasu sai gashi ya shigo falon yana muzurai da idanuwan shi.
Nan mahaifin ya fara bayani ya nuna ma kowan mu kuskuren shi ni dai laifina wai don may ban jirashi gida ba har ya dawo muyi abinda zamuyi dashi na bishi can.
Budan bakina nace baba kai kace min na sheda abinda ake fadi din ne a kansu, baba danaje fa matar daga ita sai towel ta fito min dashi a gaba.
Yace bake kika je mata gida ba koma yaya kika samay ta aike kika jawa kanki mugun gani na dauka wani fada sosai mahaifin nasa zai mashi sai ji nayi yana mashi fada akan sakin da yai min kawai.
Inda ya kare zancen shi da fadin mu ruwa kan mu asiri mu boye maganan kada in bari gidan mu suji zancen sakin nan don nasan ba aure na da Jamil din suke so ba.
Tun daga wanan ranan abubuwa suka kara jagulai muna don sai yayi min kamar basu haduwa da matar ashe sallon tako suka canza min don kada in gane suna tare da ita.
Da zaran ya fita da safe yana gurin ta sai in yamma tayi zai dawo yayi wanka ya kara fita baya wuce sha daya zai dawo gida ya kwanta sai kuma gobe indan ya fita kuma.
Cikin jikina yana ta kara girma a lokacin ga ba komai a hannun mu sai tunanen fitar da kai kunya da nake faman yi inda shima a bangaren shi haka din ne ke gudana wurin shi.
Bai aje ba baiba wani ajiya ba sai ranan naga bai fita ba kamar yadda ya saba fita yawon shi na banza din har na gama abinda nakeyi na samay shi muka zauna muna hira dashi.
Yake ce min wai yaya zancen filin mu na wani gari da mahaifin mu ya saya nace filin na nan baba yana kula muna dashi sai nan gaba za ai shawaran abinda za a yi da fili.
Yace to may zai hana a sayar da fili in samu abinda zanyi na haihuwa da kudin shi yana ganin shine mafita a gare mu tunda dai naga shi baida shi ai.
Nace wai wai nifa tsoro nake ji da kunya in tunkari baba da wanan zancen haka gaskiya a dai canza dabara zai fi nake gani.
Da yake sarkin iya tsari ne nan ya zauna ya tsara min yadda zamuyi yace ai sai na fara neman hadin kan yan uwana tukun mun daidaita zan tukari baba da zancen