Showing 6001 words to 9000 words out of 106121 words
Chapter 3 - kanin Ajali Book Complete by Zee Makawa .txt
dago daga duken da take tana fadin umma ban karasa bane yau wankin kayan yaran nan daya taru nake yi kwana biyu ban samu yin wanki ba don jikin shamsiyan.
A,a dai inji umma don dai ba uwarki nake ba yasa zaki barni da yunwa har wanan lokaci da kinsan darajana da mutunci na ai ba zaki maida hankali gurin wankin kayan diyan ki ba ki barni da yunwa.
Murya a sanyaye mamatace umma kiyi hakkuri iccen ne baya kamu sosai taja tsuki tace haka kuke ai matan yanzu da shegen kiuya gurin aiki.
Kwala min kira tayi in zo in karbo mata goro wurin mai tiredan unguwar mu inda take saya sai da tayi min kashedi tare da dangwara ta mika min kudin goron.
Illar ya jani ina fita na hadu da kawata hafsa an aketa tace in rakata idan mun dawo sai mu sayo goron mu kaiwa umma har naso na kiya don tuna halin umma .
Sai dai jin gidan da zata yasa nace muje in rakata din don ina son zuwa gidan kanwar mahaufiyar hafsa gida ne daya fi ko wani gida a gari kkyau gashi idan munje bamu fitowa sai ta bamu wani abu da bazamu manta mun je gidan ba.
Mun zauna harda cin abincin mu hankali a kwance kamar ba nice masifafiyar kakan mu ta aika ba tare da jan kunne kada in dade gurin aiken nata sai gashi duk gidajen dake makwabtaka damu umma ta shiga nema na ance ban shigo ba.
Sai da muka gama kwadiyan mu muka tun karo gidane na tuna da zancen aiken umma gabana ne ya fadi na lalaba aljihuna naji gudin suna nan inda na aje su kudin da aka bamu ne na kara na sai mata goro manya guda uku na tunkaro gida da murna na.
Ina sallama ta lalayo min wani uban ashar sai da na girgiza tazo kamani na gudu ta buge baba kabiru dake dakin shi ya fito yana asha subbanallahi umma ya akayi haka ya faru kuma.
Ta mike da kyar tana fadin banda yar banzan nan da na aika tun dazun ta sayo min goro nan da shagon awali mai tireda ta tafi gantalin ta sai yanzu na ganta.
Juyowa yayi gare ni inda nake tsaye ina kyarma cikin sanyin murya yace hadizatul kubura ina kika je da umma ta aike ki ne tun dazun.
Dan kwala na fara kiu,kiu da idona ina kyarma a cikin inda inda nake fadin hafsa ne tace in rakata gidan mai kare an aike ta tana jin tsoro shine muka je tare.
Baba yace watau kice baki jin tsoron karen ko hadizatu nayi narai narai da manyan idanuwana yace kinci abinci kai na gyada mai yayin da umna ke fadin ina fa taci tun kan muguwar uwata ta kare muna girki na aike ta fa.
Haba umma may ye laifin saude a wanan magana don da zaki tona zuciyar saude da kinga rashin jin dadin abin da yarinyar nan tayi yanzu.
Kiyi hakkuri umma tunda bata taba aikata hakan ba yau ne ta fara don Allah kiyi hakkuri kada ki dake ta.
Wani kallo tayi wa baba din dake magana a cikin tsigan lalashi tace gidan uban wa kika ci abinci bakin ki haka duk maiko.
Na dukar da kaina kasa ta kara daga murya tana tambayana da karfi da sauri na dan girgiza tare da fadin can ina nunawa da hannu.
Oh kin fara yawon kwadayi gidajen mutane ki nuna wa duniya ubanki ya watsar daku a gari kuna gararanba kai kai haba umma wanan maganan haka ina yafito maki kuma haka ,?
Dan naki ne yaje yawon gararanba ya watsar da iyalin shi da yawon gararan ba yake zai dawo muna da abin arziki idan ya tashi dawo haka.
Umma idan wani ya fadi haka yaya zaki ji a matsayinki na mahaifiyar mu duk gari an san ida yake ansan kuma aikin da yakeyi a can.
Jikin ta ne yai sanyi don itama din dai tuntuben harshe tayi wanan maganan ya fito saboda masifan ta har ta kai ga fadin hakan.
Ta kama kamay kamay tana fadin bafa haka nake nufi ba yaya zan wa dana wanan kalamin da ita dai nake da wanan mai manyan udanuwan nake magana tana nunani inda nake tsaye.
Ina aiken da tayi maki baba yake tambayana ledan dana dunkule na saka a aljihuna na ciro na mika mai ya karba ya mika mata ta karba tare da kutawa tana fadin yau kin kuru wallahi.
Tana magana tana kallon goron nace na hada da kudin da hajiya ta bamu na sayo maki duka rufa min baki tace cikin tsawa na dan kara ja da baya.
Umma har yanzu fadan bai kare bane duk da kudin da ta samo wurin rakiyan aiken ta nayi da zata ce ta cika min.
Juyawa baba yayi gurina yana fadin ke kuma daga yau idan kin kara wuce wurin da aka aike ki sai na yanke maki kaunan ki gidan nan da sauri na daga kaina alaman naji ina kyarma yace shige shiyan ku maza sai da yaga na shige wurin mu ya ja ya wuce.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
5/18/21, 11:45 PM - 🤔🤔🤔: 🙆🏼♂️ KANIN AJALI NA 🙆🏼♂️
3️⃣
ZAINAB IDRIS MAKAWA
MARUBUCIYAR TAKARI TARKO FUREN JUJI SARAUTAR MATA, ALOKACIN MUKE, MARUCIN KAN DUTSE, BAHAGO, BA MU KADAI BANE, MIJIN BUZUWA, DA KANIN AJALI.
MAI SON NOVEL DINA ZATA IYA NEMA NA A WANAN LAYIN 080 36959257 KO 090 36938192 DON TURA KUDIN NOVEL ZAKI IYA TURAWA A WANAN ACCOUNT DIN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KAN DARI UKU KO WANI LITTAFINA DON FADAKARWA DA NISHADI.
NAGODE DA DAMAN KU DA KUKE BANI A KULUN ALLAH YA BADA IKON SHIGA DON JIN RAYUWAN WANAN BOYAR ALLAH.
WACCE KEDA LABARI DA TAKE SON A HASKA MA YAN UWA MATA SU FARGA ZATA IYA NEMA NA TA WANAN LAYIN DAKE SAMA DON BANI LABARIN TA IN HASKA MATA SU FARGA., , , ,
Mama mace ce mai tsabta da tanadi yau ma kamar kulun tana tsakar gida tana gyaran guraren da take da ikon gyarawa har ma da wanda ba nata ba ta gyara idan gyaran ta ya tashi.
Ta gama ta dora girki ba dai wani girki bane dan kullun ne tuwon masara ko na dawa sai wani lokaci jumma,a ake girka shikafa da wake muda nama sai idan sallah tazo ko Allah ya tsaga zamu ci .
Ta kare komai akan lokaci tace zata kitso bayan muma ta sance muna kawonan mu daki ta rufo muka nufi gurin umma tayi mata sallama.
Don gidan kitson namu a makwabtan mu ne ba wani nisa sosai a kofan shiga wurin umma taja ta tsaya tana mata sallama kamar ba zata amsa mata ba sai can tace a dawo lafiya.
Kitson shuku akaiwa maman mu inda mu kuma akai muna zanen yawo na hannu ta biya kudin kitson muka dawo gida.
Lokacin har anyi sallah azahar ko a gagauce mama tayi sallah don ta makara saboda kitson da aka tsaya mata.
Sai da ta idar da sallah ta bamu abinci muka fara ci tare da ita muna tsaka dacin abincin ne mukaji muryan umma da itama shigowan ta gidan ke nan daga makwabta.
Take fadin umma mun dawo tun dazun sai yanzun kuka shigo kamae kitson wata mai miji a kusa mama dai sai murmushi tayiwa umma din ta fara aikin ta na tsakar gida.
Kafa dare yai mata kuma ya zama matsala gurin umma da bata raina laifi mutum gare ta gab da zata karasa aikin ne muka ji sallaman mahaifina da isowan shi ke nan garin sai shigo mashi da kaya akeyi wanda wanan karon yafi na kulkun zuwa da kaya masu yawa.
Murna da farin ciki muka shiga yi na zuwan shi duk gidan in ka debe mama da take kawaici kada umma tace bata da kunyan idon su.
Baza ka iya gane farin cikin mama ba duk yadda ka iya fahintar ta don kawaici irin na mutanen karkara da kawar da kai ga komai.
Dakin umma ya fara shiga ya dade a gurin umma din don kayanshi da komai da komai da yazo dashi , yana dakin umma din son irin karfin da take dashi akan diyan ta.
Kira ya kwalawa maman mu dake kara gyara dakin ta don taron baban mu da ya iso garin a bazata sai gata ta shigo da saurin ta .
Ba tare daya kalli fuskan umma ba ko jin wani dar din ta irin da yace kwashe wanan kayan da yaran nan suka tara min a nan kikai daki mana.
Dan darr mama tayi don jin abinda umma zata iya fadi a lokacin sai dai taji shiru bata ce kalla ba har ta duka ta fara kwashe kayan zuwa dakin mu.
Sai dai fuska da umma ta bata gashi babu halin magana don yadda mahaufin namu yai mata kwarjini a idon ta sosai ya waye ya zama dan birni babu alaman kauyanci a tare dashi.
Tana kallo ba yadda ta iya haka mama ta kwashe kayan kaf zuwa dakin mu karshe ya mike yabi bayan ta zuwa namu shiyan .
Zaune muke inawa shamsiya wasa ya shigo na mike da murna ina taron shi yace a, a hadiza kina gidan nan dama baki fita ba shine ban gan ku ba ?
Banji nauyi ko kunyan idon shi ko kurciyane sai bude baki nayi ina fadin idan naje umma zata kore ni ne baba na bashi amsa da hakan.
Kai ya jijiga shigowan mama dakin dauke da ruwan sha a kofi da ta kawo mai ya samu yin shiru daga ni har baba din ta aje a gaban shi tana mai sannu da zuwa.
Kiran da umma tayi min ne yasa na bar dakin da sauri zuwa amsa kiran nata da fadan nan nata ta tare ni wai na fado mata daki kamar an koro ni saboda gulma.
Aikena tayi sayen goro na fita da sauri nan na samu daman fada ma kawayena da ma wasu da ba sa,a naba da naga suna mutunci da iyayyena ina fada masu zuwan mahaifina.
Ko da na dawo na samu baba ya bude tsaraban shi ba abinda ya dauke min hankali kamar lemo da ayaba dana gani a cikin kayan anfitar daga cikin buhun da suke.
Mama tana ta famsn kakasawa mutanen gida ina shigowa tace in dauka in kaiwa inna da sauri na shiga kawai inda take fada min sai godiya sukeyi zan kai na karshe ne umma ta dakatar dani da kuma kwala wa mama kira.
Mama ta fito da sauri tana fadin gani umma tace yanzu dan tsaraban da mijin naki ya kawo ne mu tada komada kike kwashewa mutanen gidan saboda neman suna.
Eh ai ki kwashe tunda ganin abin kiyi daga sama baki san wahalan da yayi ya sayo ba a can muryan mshaifina ne daya fito daga wanka yake fadin.
Haba umma waye bare a gidan nan ina duk a yan uwana ta raba wanan abin dai don Allah ki bar yin haka mana umma kamata yayi ki godewa Allah daya bani halin sayowa ai.
Baki umma ta tabe ta shiga gyara goron ta da ta mayar kamar abincin ta ta saka a baki ba tare da tace mai komai ba.
Yan gidan mu sai shigowa suke gaida baba da masa godiyan tsaraba wanda hakan yake mashi dadi sosai mu kan muna cin abinci barci ya kwashe ni a gurin .
Washe garine ya zauna da yan uwan shi da umma din yake fada masu zancen aikin daya samu na dan sanda sunyi farin ciki dajin wanan labarin sosai sai umma ta tuma ta kafe da ita bata yarda da wanan aikin ba.
Baba kabiru ne yayi karfin halin yin magana tare da katse umma din yana fadin umma da wani ya fada min wanan zancen ba zan taba yarda ba.
Sai gashi a gaba Allah ya nuna min akayi ashe wanan ba bin farin ciki bane a gurin ki garin nan kaf babu wanda ya fara wanan aikin sai tsatson ki ashe haka ya zama abin alfari a gare ki.
May ye amfanin yin karatun da kika jajirce muyi Allah ya fara kawo muna mafita da bakin ki zaki fadi wanan maganan yanzu.
Kamata yayi ki sa mai albarka da fatan alheri Allah ya tsare ya kare ya ba da sa,a ya kamata ki fada mashi.
Umma da bakin ki fa kike kokarin fadin rashin aikin shi takamaimai a can yanzun Allah ya kawo mai mafita zaki kawo wani magana kuma umma.
Jikin ta ne yayi sanyi tace idan haka ne Allah ya tsare ya bada sa, a kowa a gurin yace amin nan yake fada masu bai dawo ba sai da komai ya kammala a gare shi hae gidan da zai zauna sai da ya samu a can .
Da sauri umma tace amma kai kadai zaka zauna a can din ko baba kabiru ne ya karba da fadin haba dai ai gara dai yaje da iyalin shi a kusa dashi zaifi mai sauki da kwanciyan hankali.
Baba yushau yace nima dai haka naga yafi mai sauki kaga muna mun samu wurin zuwa a birni ke nan .
Kai rufe muna baki da wanan shirmay yana nufin da saude duk da yaran zai tafi ke nan baba kabiru yace kwarai kuwa don ya kama inda zasu zauna ma a can tun kan yazo din.
Don haka tare zasu tafi ke nan idan zai koma baba yushau tace kai amma naji dadin
Wanan maganan don ko ba za a barni a nan ba nima kafan ku kafana.
Da sauri umma tace babu inda zaka tafi shidai din da iyalin nasa Allah ya sa aje a sa,a yakai lafiya .
Sai dai zanso ku barmin kubura a nan mu zauna tare wanan karon mahaifina ne yayi magana yace umma zan so mu tafi da ita don su samu karatun zamani mai kyau a can don rashin karatun da basu samu a nan yana damuna.
Wanan mara makarin wani karatu zata gane ko sunje can kayi fatan Allah ya baka diya maza su samu ilimin kamar yadda kuma kuka samu.
Kowa cikin iyayyen nawa maganan yayi mai zafi sai dai babu yadda zasuyi da mahaifiyar tasu baba kabiru ne ya murje ido yace dani mahaifa na zasu tafi.
Tunda aka fadawa mama zancen tafiyan mu take jin dadi a ranta ta shiga sallaman yan uwa da bokan arziki suna mata fatan alheri da murnan fita cikin kangin umma da suke kallon tana gallaza ma rayuwan auren ta.
Mama bata dauki wasu kaya ba sosai don baba ya hana yace ko can din basu da tabbas din zama za a iya daga su ko wani lokaci don haka aikin su ya gada kamad fulani suke su.
Wanan shine fitar mu daga kauyen mu asalin garin mu na iyayyen mu ka shigo birni sai dai idan munje ziraya kuma.
Mun isa birni kano unguwa madawari baba ya kama dan gida madaidaici mai dakuna biyu da falo sai kicin da makewayi, sai dan tsakae gidan ba wani mai girma ba sai dai duk an shafe shi da suminti kamar dakunan.
Kauyawa muka zama a gidan don har kayan kallo a falin an shimfida ledan kasa a ko ina na gidan ga yan kayan aiki da baba ya sayawa mama na amfani irin na yan birni da alama bada itace zata dinga girki ba a garin.
Murna fal a zuciyana muma mun zama yan birni ina kallon yadda baba ke koya wa mama yadda zatayi amfani da resho da karamin gas din da ke kitchen din.
Satin biyu aka sani makaranta sai dai ta gwaunati ce amma duk da haka akwai banbanci sosai bisa ga karatun garin mu.
Baba bai dauki wani lokaci yana kaini makarantar ba har na gane hanya don baida isashen lokacin da zai rika kaini ya dauko ni.
Da yake mama ba karatun boko tayi ba sai hakan ya rage ma karatuna gudu don babu mai taimaka min a gida idan an bamu aikin gida muyi.
Sai dai hakan bai hanani kokari ba don Allah ya bani kokari sosai na fahintar abu hakan ya jawo min farin jini ga malamai da yan ajin mu.
Idan na dawo gida da yamma nake zuwa islamiyan uguwar mu gurin daukan karatu sai shidda na yamma ake tayar damu.
Mama ma ta shiga wani islamiya a nan unguwar suje goma na safe su dawo da sha biyun rana wanan karatun da mama ta shiga ba karamin ci gaba ta samu ba sosai.
Don ta fara koyon rayuwan yan birni tana fahintar zamantakewa da mutane zan iya cewa mun dai fito birni ne don a nan ma ba ganin mahaufi mu muke koda yaushe ba.
Haka na dai yafi muna zaman can din da fitinan umma sai da muka share shekara daya a kano baba kabiru ya kawo muna ziyara.
Ranan nayi murna sosai da ganin kanin mahaifina ya kawo muna ziyara na farko a gidan mu wanda tun tarewa mu kanon zance bamu taba yin bako ba a gidan mu.
Sai faman rawan kai nake mai yana dariyan jin dadi da ganin yadda muka sauya a dan lokaci mama tayi kyauta kamar ba ita ba ga dan matashin