Showing 84001 words to 87000 words out of 106121 words

Chapter 29 - kanin Ajali Book Complete by Zee Makawa .txt

Advertisement

01 Jan 2025

8064

ya rage munayi.
Gadai miji yaje nema amma haka ya dawo muna hannu rabbana babu ko ledan burudi ya dawo muna gida.




ZAINAB IDRIS MAKAWA
5/18/21, 11:57 PM - 🤔🤔🤔: Ya gama yaudaran shi na yan fashi sun tare shi a hanya sun kwace komai ni kuma na gaji na sake yanzu.
Baifi wata daya ba yace zai koma ya nade ya juya zuwa inda ya fito naci gaba da rayuwana a yadda na saba a baya.
Ba wayan shi ba sako tunda ya tafi don haka fadi tashi ya taso ma rayuwana don nema wa kaina abinda zamu ci.
Tunda ba zancen sutura bane yanzu gare ni sai dai na abinda zamu ci wa cikin mu kullun shine abin yi gare ni.
Ina kallo yan uwa ba zuwa buki ni ba hali inje don ko nace zan tafi babu abinda zan sa a jiki babu wanda zan kai gudu mawa a guri bukin.
Haka yasa na daina duk wani hurda da ya uwa na yanzu sai zagina ban so zumunci ban shiga dangi ga dai magana nan kala kala a kaina ba dadi anayi.
Ni kuma ni nasan abinda nake ciki da miji na ba wai a cikin dadin rai nake ba gashi ya raba ni da kowa daga cikin yan uwana.
Babu mau zuwa gurina da sunan zumunci kamar yadda nima ban zuwa gidajen nasu da sunan yin zumuci.
Wahala yakai min wahala dole na nufi gidan mu dan samun mafita a kaina bayan an gama saurare na.
Anty tace to hadiza ke ce da abin haushi duk abinda akai maku a baya baku gani ba an taimaka maki kin kwashe kin bashi.
An maki fada kin kwashe kin fada mashi abinda kowa ya fada maki gamay yana kallon kowa a hankade don kin gama zubarwa yan uwanki da mutunci a gaban shi.
Ina zaune ina hawaye banda bakin magana don duk abinda take fadi haka akayi babu karya a cikin shi.
Muryan ta ne ya katse ni tana fadin ko yanzu aka taimaka maki kara bashi zakiyi don dawowa zaiyi ya lalabe ki ya kwashe abinda kika tara.
Da sauri nace aa wallahi anty ai yanzu nayi wayau wallahi, tsuki taja bata bari naci gaba ba take fadin.
Dama duk wanda ya danki na miji a matsiyin uba itako zata mutu maraya a duniya.
Don namiji bai da tabbas baka daukan amana ka mikawa namiji hundred pacent kun nuna dan uwan mahaifin ku ya cuce ku yana cin amanan ku kan dan abinda aka bar maku a duniya.
Idon ku ya rufe mazajen ku sun maku huduban shedan kun haye kunyibwa kowa cin mutunci duk mu nan kuna muna kallon mayaudaran ku .
Abinda aka baku muke so muci daga gare ku hakan yasa kuka jaye daga wuri mu dama sun shirya hakan ne do su samu kafan yaudaran ku ba tare da kowa ya saka maku ido ba.
Don ku zauna daga ku sai su suci karen su babu babbaka ko gashi sun kuma ci tunda wawaye kuke.
Nasan ko waye jamil fiye da sanin ku na karanci wanan yaron tun yana karami nasa ko shi waye bake yake so ba hadiza tun farko abinku yake so.
Ya kuma ci yanzu ma abinda baki sani ba shine ni zuciyana bai kwanta da wanan tafiyan daya ce yayi ba na zuwa wai neman kudi.
Kaina na dago da sauri ina kallon ta da mamaki don ina tsoron kalamin anty don kamar mai baki take da wuya ta fadi bai faru ba.
Da sauri na tare ta ina fadin wallahi anty yana abuja abokin shi ma da suke can tare ya fada muna tare suke.
Na tare na hanata magana sai naga tayi murmushi tare da mikewa ta dauko dubu biyar tace shi zata iya bani a yanzu inyi hakkuri.
Idan baba ya dawa zata fada mai halin da ake ciki don a samu abinda aka taimaka min dashi din ina kuka nayi mata godiya na koma gida.
Ga dai anty tana nuna muna tankar ita ta haife mu amma mu har lokacin son mazajen mu ya rufe muna ido.
Bamu yarda su sakamu a hanya da zaran an dauko zancen mazajen namu yanzun ne zamu nuna bacin ran mu gun mutum.
Dama ita kadai ce mai fada muna gaskiya mu kyale ta itama din dai bata da zuciyane irin abinda muke mata tana shanyewa.
Nayi iya bakin kokarina i bar fada mai zancen yan uwana akanshi sai dai dadin hira bai bari na daina ba do ban sani sanda za kwashe in fada mashi komai.
Ba laifi baba ya dawo sai ga sako abinci harda kudi da sauran tarkace an kawo min naji dadin wanan sako don an samu banda komai a gidan dama.
Ranan da naje godiya a gurin baba na samu anty ta dawo daga aiki take ce min hadiza zuciyana yana ban mijin ki yana tare da wanan matar daya musuluntar har yanzu.
Ina dariya nace Anty ita da take nan jahar shi da yake abuja zaune ba tare suke ba gaskiya tace to Allah yasa .
Ban dade ba na bar gidan don raina ya baci da zancen sosai sai hakkuri na shanye har zuwa lokacin da ya dawo garin.
Wanan karon ba laifin irin yadda yake yi tun a waya yasa nasa zai dawo muna da abin arziki irin tambayan yara shi tsaraba da suke so ba kamar wancan karon ba da ya dawo da karya yan fashi.
Na san da zuwa shi don haka nayi kwalliya kamar yadda mata keyi idan mijin su yayi tafiya zai dawo gida.
Irin su kitso kumshi da gyaran daki da gida duk nayi shi kafin ya dawo daga tafiyan.
A cikin dare ya sauka muna don haka ba kowa ne yasa da zuwan shi garin ba irin yadda ya shigo muna ana shigo da katon ghana most go yasa ni jin dadi a raina.
Ga doya da manja da yashigo dashi duk da ba wani mai yawa bane sosai hakan dai yayi min dadi sai da nakai mai ruwa yayi wanka kafin ya bude jakkar bayan ya gama cin abinci.
Kowan mu ya samu tsaraba dagani har yaran dadi ya kashe ni nan nake fadin dama ance mahakurci mawadaci da ace na dauki zuga da yanzu nine a ciki.
Da sauri ya tambaya zuga akan may sai nayi shiru ban iya fada mai komai ba don na fara hankali da halin shi.
Yanzu idan na furta mai sai ya sani a gaba dole na fada mai wanda ya fadi maganan yasa nayi shiru da bakina don ban son ince anty ce ke hasashe ba can yaje ba wai.
Dadi dadi muke sai dadi muke ci kwana biyu har yan haya suna gulma idan ya kwanta bai tashi tun barcin dare sai karfe daya ko biyu na rana.
Babu zancen sallah ga al,amarin shi don ko nayi mai magana ma bai sallah don haka na kawo ido na saka mai.
Idan yayi wanka suna da wani daba a unguwar dake kallon titi ana suke zama har dare na dauka tafiyan da yayi ya sa ya canza rayuwan shi ne akan yawon banza.
Ashe abin ba haka bane kudine baida ya kawo hakan ya dawo ya lafe min a gida niko ina ganin yadawo da kudade masu yawa yadda naga yana muna tunda neman kudi yaje.
Ashe ban sani ba adashe yayi da albashin shi ya dan tara yadawo dasu yana muna karyan yaje nema a nan ba gaskiya bane.
Mutane sun sani nice dai sakaran ban sani ba lokacin nake yarda da karyan shi idan ya sharara min sai in hau in zauna kan abinda ya fada min din.
Haka muke zaman duk in yazo baifi yai wata daya ba ko sati uku ya koma inda ya fito da sunan neman kudi yake a abuja.
Ana son fada min gaskiya sai dai ana gudun surutuna wajen shi injawa mutum magana akai yasa kowa yayi shiru da bakin shi aka zuba muna ido aga iya gudun mu.
Sana,a kan ina dan yi don in samu kwabon kashi da diyana kar mu gani a gurin mutane musanman abinci do ban yarda suje daukan ido gurin yan hayan gidan mu.
Wanan zuwa ya dade bai koma ba muna zaune dashi a gida tunda yazo yayi sallah tare damu yake zaune a gida.
Bai komai sai dan buga buga a cikin gari mukeyi har ni don rufawa kan mu asiri a gari ba laifi tunda albashin shi yana zuwa duk wata.
Dashi muke samu muna karyan ci bashin da yake turani in samo muna wani abin don bukatan mu na gida damu da yarad mu.
Akwai wani lokaci da akai albashi ya nuna min ba kudi gashi yasa naciwo muna bashin shinkafa a guri makwaciyar mu har mudu goma.
Gashi dajin anyi albashi ta fara aiko min da sako in bata kudin ta shi kuma ya nuna min ba kudin sai dai tayi hakkuri har wani wata.
Cikin dare ina barci nake jin hayaniyar mace a kofan mu da sauri na mike ina saurare ashe bayeraban dake sai da kayan sanyi nasha ne a unguwar mu tazo bin bashi itama take wanan hayaniyar dashi haka.
Ni dai ban kula ba don haka ban ma fito ba tunda ba maganata bace nima tawa ta isheni dashi ai.
Sai da suka gama ya bata hakkuri bayan yayi mata alkawarin zai samu abinda ya rage mata bashin dashi.
Da ya shigo gidan ne nake mashi magana kan abinda yake baida kyau tunda anyi biya ya biya mutane kudin su kawai zaifi.
Fada ya hauni dashi waini zan koya mai abinda zaiyi ko may ko nafishi sanin duniyane inda yake shiga ba nan yake fita ba.
Dole na kyaleshi na kwanta raina babu dadi ga wanan halin na Jamil ace mutum baya tsoron bashi har wurin mata yake cin bashi a waje.
Fitina bai kare ba da safe ina shirin dora wutan abin karyawa sai ga mai kudin shikafa da kanta ta wai ala dole kudi ta take so a lokacin tunda anyi biya taji.
Na rasa abinda zan ce mata ga matan gidan mu sunyi shiru da mazajen su suna sauraren mu don haka na fada daki na samay shi.
Nasan ba barci yakeyi ba yadai lafe ne kwance nake fada mai mata mai shin kafane ta shigo ya ce yaya nake son yayi da ita shi.
Daga waje kuma ina jin tana fadin ke nake jira fa don akwai inda zan tafi daga nan din ban samu kulawa daga gare shi ba dole na fito na bata hakkuri zan kawo mata zuwa anjima ta tafi.
Ina aikin da nakeyi ina tunane a raina inda zan samo kudi in biyata tunda ni ta sani , har na gama ban samo mafita a raina.
Ina gamawa nayi wanka na shirya lokacin shi har ya karya yayi sakkon fita daga gidan ya barni a zato shima neman kudin ya fita yi don mu biya bashin.
Nima dai ban zauna ba fita nayi zuwa gidan yar uwata yar gurin baba kabir don bamu da nisa nida ita can naje na fada mata halin da nake ciki da kudin mutane.
Sai da tayi min kwakwazon don may nasan halin mijina zan yarda in biye mashi inje ci mai bashi duk nassn ai ba biyana zaiyi ba .
Da kyat da lalami ta aramin dubu biyar bayan nayi mata alkawarin zan biyata a cikin sati biyu abinka da dan uwa ganin yadda nake kuka ta tausaya min ta bani aro ban ko shiga gida ba da kudin naje nakaiwa matar kudin ta saura kuma nadan sayo abin bukatan gida dashi.
Shiko bai shigo ba don yasan ba abinda zamu dafa da rana don haka bai damu ba ko yaya zanyi da yarana.
Sai dare sosai ya shigo gidan yana wani cin magani dani nima ban kula shi ba hakana na kwanta na kyale shi.
Ko tashin zancen kudin matar bai min ba ga kwanakin da na dauki alkawari wa yar uwata yana karasowa na bata kudin ta.
Hankalina ya tashi sosai don haka na yanke shawaran zuwa gidan mu wurin anty don ta rokan min kanne na su bani wani abu in samu in biyata kudin ta.
Da naje gidan kunya da nauyi ya hana in mata magana kamar yadda nayi niya sai ma itace taga damuwa a tare dani take tambayana ?
Ko lafiya ta ganni a haka nake cewa ganinan dai anty sai kuma na fashe mata da kuka don ban san ta inda zan fara mata bayanin abinda ke tafe dani.
Hakkuri ta shiga bani tana fadin hakkuri zakiyi hadiza matsalan mijin ki kin saba dashi nace cikin kuka anty bashi yasa naje naci yaki biya.
Nan dai na kwashe komai na fada mata muna cikin magana ne sai ga kanni ya shigo dakin kallo daya yai min ya kawar da kan shi gareni.
Don yanzu haushina suke ji suma ga shi sun gane Jamil yayi amfani damu mun saba da iyayyen mu masu kaunan mu tsakani da Allah.
Don yanzu shekaru sun kora sun yi wayau fahintar wani abu daga iyayyen namu don haka suke jin haushi har dani baki daya.
Anty ce ta iya mai magana akan abinda ke faruwa dani da Jamil din yace cikin tsaki anty bar wanan da kike gani ko yanzu ta samu kudi kara bashi zatayi wallahi.
Ai tasan halin mijinta take biye mashi tasan mayaudari ne macuci tunda anyi daya anyi biyu yanzu jira yake na uku yazo ya cinye shike nan ya korata.
Naji haushi maganan shi don ina neman abu a gurin su ban tsaya ya fada min maganan banza ba nan na haushi nima don ban son mutum yai min zancen mutuwan aure na ko kadan.
Tunda nasan kowa hakkuri yake da auren shi kowa kuma da irin kaddaran da yake gani ga rayuwan shi ni da wanan na dogara na bashi amsa.
Anty ce ta katse ni da fadin in bi a sannu tunda nema abu muke a hannun shi dole na sassauta harshena gareshi.
Da kyat da sudin goshi ya yarda zai bani amma da sunan aro idan na samu zan biya shi abinshi sai bayan ya yarda ne ya kawo maganan kudin hayan da Jamil din ke cunyewa yanzu.
Don lokaci ya kusa na biyan kudin yan hayan gidan mu don ba zasu yarda ina cinye kudi ko wani shekara ba da mijina mu kadai.
Yace karshen shi ma ba nike cin kudin ba shine mai cinyewa ya kyale kowa ranan dai kanina ya fada min magana iya son ran shi sai da anty ta taushe ni.
Na yace in tafi idan ya ciro kudin zai kawo min har gida da yamma ina komawa gida na samu Jamil yana cika yana batsewa wai na fita yawo na bar gida ba kowa.
Kyaleshi nayi ban fada mai abinda naje yi ba don in har ya sani sai yasan yadda yayi yaci wani abu a cikin dubu goman da za a aramin din nan.
Do haka naja bakina nayi shiru inda nayi sa, a koda kani yazo ya dan fita har ya bani kudin na boye bai gidan.
Sai dai kafin ya tafi ya shigo ya samay mu muna hira ya zauna suka gaisa a cikin hiran ne yake tambayan wai yaushe ne sauran kudin mu zai fito har yanzu shiru.
Amsan da Baffa di ya bashi ni kaina naji mamaki don cewa yayi dashi kudi tunda suna nan ko yaushe sukazo daidai ne.
Don masu kudin ma basu damu kanar masu son cin banza ba ai yana fadi haka ya tashi yace zai tafi nayi mai sallama shi bai tanka shi ba.
Yana fita Jamil din yace naga yanzu yaron nan yana son ya raina ni ko don yaga na damu da damuwan ku ne ko yana ganin yanzu ya kawo karfi ne shi ?
Ni dai ban bashi amsa ba na share shi yaci gaba da fadin ni zai cewa masu son banza ke nan mune masu jira muci banza ke nan ko ?
Ni abu ya damay ni ban tsaya bin ta nasa ba don tunanen maganan yaron kan kudin hayan da yayiwa anty ya damay ni a raina sosai .
Tunda yace basu yafe min ba tunda ba ni kadai keda gadon kudin ba balle mijina yai ta karbewa yana ci shi kadai.
Don haka wanan shekaran shi zai karbi kudin da kanshi gurin yan hayan nako san akwai tsiya da Jamil ke nan tunda ba kunya ke gare shi ba kan kudi da kowa yana ja tunda shi ya zama cima zaune.
Ina samu kudin nan washe gari naje na kaiwa yar uwata kudin ta nan ta dorani ga sana,an da zanyi da sauran canji na daya rage min cikin dubu goman da akace an ara min ne.
Na fara juyawa a hankali tunda banda komai ya karbe duk dan wanda nake juyawa a baya .
Dan zaman ma da yake yanzu a gida sai ya gundure ni na kwammace ace ya fita din da yake yi yanzu

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login