Showing 39001 words to 42000 words out of 106121 words

Chapter 14 - kanin Ajali Book Complete by Zee Makawa .txt

Advertisement

01 Jan 2025

8134

dai dakin baiyi mashi ba.
Ban fito ba sai da gari ya dan haska zuwa gaida iyayyen shi dake cikin gidan inda na zube daga kofan su ina gaida su da kwana ban san jamil yana dakin zaune ba tare da mahaifi nasa.
Jin muryana mahaifin nasa yace in shigo daga ciki yana fadin ashe kuma haka mayaudaran ubannen ki sukai maki ya tabbata ke nan sun cinye maku gadon ku ko ?
Nace baba basu cinye ba har yanzu kudin bai fito bane na baba yace sunciye mana waye bai san wanan maganan ba ya ta.
Yanzun dai kuyi hakkuri da dan abinda suka kawo maku din tunda kin shigo cikin mu komai zaizo da sauki don ba zamu saka ido muga ana cutan ku ba haka ai.
Nayi maki alkawarin zamu tsaya maki akan komai dake da yan uwan ki muddin muka samay ki a yadda muke son ki mai biyayya a gare mu.
Nace insha Allahu baba mun gode yadai dan muna fadan zama tare da nusar dani akan saurin yarda da iyayyen nawa da nakeyi.
Nayi godiya na bar sashen nasu don tsakanin mu dasu ba wani nisa bane kusan ma dakunan a hade suke sauran yan hayan da ba a tayar ba suna a dayan bangeren su uku.
Ya ganin amarya suna ta zuwa daga gidan mu wasu kuma suna zuwa yi min sallama don komawa gidajen su an bude dayan buhun shimkafan da iyayyenba suka kawo na gara a gidan suna dafa ma yan uwan su da suka zo gurin buki.
Sai dai abinda ke ban mamaki duk wanda yazo yana yaba kyawon dakin nawa in ka debe daidaikun yan uwan jamil dake tabe bakin su.
Dangin mahaifiyar shi da suka zo buki a wurin su nake jin ashe su suka zo da turamay nan da aka kai gidan mu ke nan, nan iyayyen shi su basu kashe mai komai ba kenan.
Ranan dai wuni nayi ina taron baki a gidan sai dai yakan shigo jefi jefi yana wani cika yana batsewa na rasa gane kan shi a gidan ga baki daya.
Zaman sati dayan da mukayi kullun a cikin korafi yake akan shi shirin dakin bai mai ba har dai na hakkura na tambaye shi yanzu yaya kake son ayi ke nan yace yanzun kikai magana dai.
Abinda nake so shine mu sayar da wanan kayan a sai wasu wanda ya dace damu a dakin ina ganin haka zaifi bada ma,ana sosai nace kana ganin haka zai yuyu tun ban kai wata daya da aure ba ace na sayar da kayan dakina.
Baka ganin zasu ga na rena da abinda sukai min a baya yin hakan zai kawo wani rigima a tsakanin mu nan gaba a hasale ya furta ina ruwan su dake yanzu ina sun sauke nauyin su da ke kansu suke gani da wanan abin da sukai maki suna ganin burgewa ne a gurin su.
Yanzu muke da ikon ki basu ba don nauyin ki ya dawo gare mu ke nan ba ruwan su da abinda zamuyi maki anan kuma yanzu.
Nace to shike nan yace da kaina zan kai kayan nan can kauyen mahaifiyana a sayar muna dashi muzo mu cika kudi a sai maki na zamani wanda ake yayi.
Nace idan kana ganin haka zaifi a kai a sayar din na kuma gode da kaunar da kake mun din dani da yan uwa na ya saki wani shu,umin murmushi a fuskan shi.
Bai bar dakin ba nan ya zauna muna hiran yan uwan mahaifina na zage ina fadin karya da gaskiya ga irin rikon da suke muna a gidan baba kabiru din.
Yana ta faman zugani ina hawa ina ganin gaskiya yake fada min don banda masoyi bayan shi a duniyan nan kaf baki daya.
Washe gari ya bude kofan falona ta baya ashe tare da motar daukan kaya yake ina ji ina gani Jamil da wasu mutane suka kwashe kayan falon nan kaf suka fice dashi a gidan.
Sai da yai kwana biyu bai dawo ba a cikin kwana na uku ne ya dawo garin fuska a daure ya shigo min ina jin muryan shi yana gaisawa da iyayyen shi bayan ya gama dasu ne ya shigo yana kara sha min kanshi.
Ba daman in tambaye shi zancen kayan don banga fuskan haka ba a gurin shi abinda ban sani ba ashe ya fita yaje gidan wata dillaliya ya juye mata kayan ta bashi kudin shi ya biya bashin da ake bin shi na party bikin daya hada sai sutura na alfarma da turararuka daya kara saye.
Sauran kuma ya hole da yan matan shi sai da kudin suka kare ya dawo gidan a lokacin shine yake cika yana batewa don kada inga fuska shi in tambaye shi yadda akayi da kudin kayan.
Sai da yaga ban tambaye shi zancen kayan ba wanda ni a zahiri tsoron haka nake ji yasa ban tambaye shi ba amma zancen kaya yana a raina.
Don ina jin kunyan mutane suna shigowa suna ganin dakin haka ba komai a cikin sa alhalin kowa gari yasan amin kayan daki na alfarma.
Matsalan farko dana fara fuskanta shine akan ibada sam Jamil baya sallah ko wani iri da safe sai sha dayan rana zai tashi daga barcin jiya da muka kwanta yayi wanka ya shirya ba maganan yin sallah.
Idan nayi mai magana sai ya hauni da fada yana fadin kin san ni bansan Allah ba sai kin koya min may zaki nuna min akan addini kin dai san na fiki sanin hakan.
Ni da na tashi a gida cikin hausawa yan uwana kuma musulmai na san Al,Qurani nasan hadisi don haka bake zaki nuna min yin sallah ba inda yake shiga ba nan yake fita ba.
Ni dai na samu gefen gado nayi tagumi ina kallon shi sai ruwan bala,i yake min kan kawai nace dashi ya tashi rana nayi yayi sallah.
Har ta gaji ya mike ya dauki buta ya kurkure bakin sa ya dawo yana tambayana idan na gama abin karyawa in kawo mashi fita zaiyi.
Na mike jiki ba karfi na fita na dauko mai kayar karyawan shi da na aje mai ya zauna sai da yayi kat ya fice daga gidan.
Mikewa nayi na kwashe kaya raina ba dadi ina tunanen maganan umma a karo na farko a raina ashe abinda take hango min ke nan wanda na kaaa hangowa kaina shi.
Tun ba,a je ko ina ba zaman ya fara ban tsoro da Jamil don babu wani dadin auren da zance naji wanda amare suke ji idan anyi aure a farkon aure.
Ga tsoro shi da yake kokarin cusawa a zuciyana dan abu kadan zanyi yanzu ya hauni da fada na fitan arziki yana zagi iya son ranshi ni dai babu zancen wani amarci a gurina sam.
Iyayyen shi kuma da muke zama dasu da akace wai zasu zauna ne don barin iya mu yara a gidan baiyi ba shine suka ga dacewan zaman mu tare dasu din.
Ni dai banga wani amfanin su ba a gidan asalima kamar tsoron dan nasu suma suke ji don har su yakewa wanan tsare gidan nashi da yake min sai dan jefi jefi zakaji yana hira da mahaifin nasa.
Ko idan yana min fada mahaifin nasa ya karbe ya goyi bayan dan nasa kirikiri yana fadin nice banda gaskiya banda mutunci.
Sai dai idan sunga yana cikin dadin rai da nine nake samun sakewa dasu a gidan har zamu dan zauna muyi hira da matan amaryan baban nasa da muke zaune a tare.
Duk wanan baya damu na nidai buri na inga munyi zaman lafiya a tsakanin mu dashi kamar na sauran ma,aurata don sam banda wani walwala balle har in dan fara cikan daki da akeyi idan anyi aure.
Ranan da yan gidan mu suka zo gani na na rasa yadda zanyi akan rashin kayan dakin da babu dakina wanda akai min daga gida da Jamil ya sayar din.
Suna shiga dakin maganan farko da sukai min shine anty hadiza ina kayan dakin ki nace ku zauna mana in fada maku komai a tsanake.
Zama sukayi suna saurarona don jin abinda zance din bayan sun zauna ne muka gaisa nake fada masu sai da aka jera min kayan naga basu min kyau ba na bayar a hurhura min ne za a kawo min wani sati in Allah ya yarda.
Badon sun yarda da magana ta ba don yarda naga suna min wani irin kallon na tuhuma a ransu sai da mukai hirane zasu tafi nake rokon su akan don Allah su rufa min asiri kada su fada a gida sai idan an kawo min kayan zanje in fada a gida.
Sukai min alkawarin ba zasu fadi ba kuma hakan ne don naji shiru ya tabbatar min da basu fadi din ba a gida don banga kowa yazo min da maganan ba.
Jin shirun yayi yawa ne kan kayan yasa ranan na tambaye shi labarin kayan fada ya fara yi abinda yasan ban so ke nan fada yana fadin idan ta ban ai zan kawo maki tunda kin nuna min banda iko a kan abinki yanzu.
Da har zaki bude baki kina tambayana kayan ki kamar wanda baki yarda dashi ba ya fice yana fada kamar yadda ya saba yi idan zaiyi yaudaran nasa a gurina.
Tun ranan da nai maganan kayan ya shiga fushi dani sai ya shigo fuska a murtuke yayi abinda zaiyi a dakin ya fice daga gidan idan ya gama.
Da abin ya ishe gani ban iya gaba ba a rayuwana ranan dai na kudirta a raina zan mashi magana idan yashigo gidan don mu fahinci juna dashi.
Dama ni tsoro na kada yan gidan mu su sanda wanan zancen a dauki mataki a kaina shine kawai damuwa na a lokacin.
Can cikin dare ina barci ya shigo dakin ina jin motsin shi na bude idanuwa ina kallon shi filo ya dauka ba tare da yai min magana ba zai nufi falo dashi da sauran abinda yake bukata a dakin.
Sannu da dawowa nayi mai bai amsa min ba sai kokarin fita yakeyi a dakin zuwa falo na mike na bishi falon yana kokarin kwanci a saman dogon kujera don kujera kawai ya bar min a dakin sai ledan kasa a lokacin.
Zama nayi a dayan kujeran dake kusa dashi ina fadin haba my may ya faru da zafi haka kake fushi dani kan dan magana kankani.
Ya juyo a fusace yana fadin oh baki ma san abinda kikai min ba ke nan har kina daukan maganan dan kankani a gurin ki ko ?
Nace ni banga abindana fada mai zafi ba daga tambayan kaya sai ka hau fushi dani haka kawai yace eh tunda kin nuna min kayan ki kayan ki ne ni banda iko dasu ke nan.
Na marairaice murya ina fadin ni ba haka nake nufi ba my ka sani wanan ba halina bane amma idan maganan ya bata maka rai kayi hakkuri don Allah.
Sai hawaye ya zubo min wanda ban san ko na may ye ba a lokacin ya dago kai yana kallona tare da fadin mayye kuma na kuka yanzu daga magana.
Nace naga maganan ya bata maka rai ne sosai don kawai na tambayi ba,asin kayan dakina daka kwashe da sunan hurhura min su.
Yace baki yarda ba dani ke nan kika kasa hakkuri har kiga iya guduna a kan kayan na kara marairaicewa nace ni dama tsoro nake ji azo daga gida a samu babu kayan a dakin nan.
Yace idan sun zo sunyi magana ki fada masu abinda na fada maki a baya, ina kin gane yanzu na gyada mai kai a hankali wanan ne yasa muka shirya ya bar fushin da yake yi din dani da farko.




ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
5/18/21, 11:55 PM - 🤔🤔🤔: 🙆🏼‍♂️ KANIN AJALI 🙆🏼‍♂️




1️⃣5️⃣




ZAINAB IDRIS MAKAWA




A fanin girki ba iyawa nayi sosai ba ranan da suka sakar min girki da kaina don farkon zuwa uwar miji ke girkawa sai dana cika wata daya a gidan tace in karbi girki in dinga yi.
Ranan tabara zalla a gurina don tun a gida muke kwasan rikici da anty akan girki sai kanwa tace mai yin girki da duk wani aiki daya shafi kitchen a gida don ni ba iyawa nayi ba ko nayi girki bai dadi.
Anty kance dani sai nayi aure zan san illan yin hakan da nakeyi don cutar kaina nakeyi ince wai ban iya girki ba ni sai gashi yau maganan ta ya zama gaskiya a gare ni.
Idea yazo min bayan na soya makarde na zunbuda maggi star ina jin uban mijina har da santin girkin yakeyi da aka kai mashi nace a raina nagode ma kafanin maggi star don sun fitar dani wanan kunyan.
Tuwo dai ne ban iyaba ba musanman na gari ga uban mijina bai cin shinkafa da dare sai tuwo yake so ko wani abu mai nauyi haka.
Sau biyu ina tuka tuwo yana ruwa ya sake don yadda nakeyi ashe ba haka akeyi ba don sai na kwaba garin da zantuka da ruwa nake tuka shi ban kuma bari talgi ya nuna nake tukawa sai tuwan ya sake baya kwana da safe ya sake sai dai a zubar.
A nan muka fara samun matsala dasu sai uban mijin nawa ya hau zage zage ina ji shi har dakina yana fada akan ban iya tuka tuwo ba kamana.
Dole uwar mijin nawa ta shiga koya min yadda zan tuka tuwon don barnan da nake ja masu din na hasaran garin kamar yadda sukace inayi masu.
Shi dai zancen kayana yabi ruwa ke nan don babu halin in magana akan shi yanzu fada da gaba zai shiga tsakanina da Jamil din.
Ina jin sarakuwa tana gulma da matan hayan gidan mu wai ban iya komai ba sai aukin kwanciya da miji suna min dariya.
Ta dauka barci nake nan suka saka faifaina sukaci har suka gaji ina ji su ban kuma fito ba daga dakin har suka watse a gurin haka yasa na dauki niyar gyarawa da kaina.
Da yamma na fito zan dora girki tace in jirata idan ruwa ya tafasa tazo ta duba min ruwa na tafasa nayi yadda ta koya min sai Allah ya taimake ni nayi a cikin sa,a don tuwon ya tuku da kyau baiyi ruwa ba.
Ina gamawa na ta fito da taji shiru ta samu har na tuka tuwon har ta hau fada wai don may ban kirata tazo ta duba min ba.
Shiko surkina da muke cewa malam yana ji ya fara fada tana bude tukunya taga tuwon yana tafasa ya tuku da kyau bata dai yi magana ba sai tabe baki da tayi ta juya ta tafi.
Sauran yan hayan gidan sun kafa kujerun su a tsakar gida suna jiran suji yadda zamu kwashe da ita da ta fito sai sukaji ba ai magana ba haka yasa suka fara tashi daya bayan daya suna shigewa dakunan su mai zuwa yin aikin gabata kuma ta shiga yi.
A kwaini da nauyin aiki idan na fara aiki daya sai ya kaini wani lokaci ban karasa ba yanzun ma wanke wanke na tattaro zanyi sarakuwa na tana fitowa ta hau fada wai wanke wanken da yakakata inyi da farko shije sai yanzu zanyi in sa masu abinci karnin kwano yana tashi zuciyar su ya kama tashi idan sun ci abincin.
Na dai gama na kife ba tare dana ce da ita kanzil ba ga uban mijina daga daki yana karba mata don shi mutum ne da baya fita ko ina iyakan shi gida kullun sai dai akwashi da son cin dadi sosai.
Don gaskiya fannin abinci baida wasa ko kadan muna cin mai lafiya mu sha mai lafiya sai mun koshi zaman nawa dasu dai da dadine ba dadi gamu nan dai ne zaune.
Don ma ban cika shiga shirgin su ba idan na gama aiki ina cikin dakina sai ko idan yan uwa suka zo gurina zakaji murya na a gidan.
Daga cikin matan hayan gida akwai wata jamila da jinin mu ya dan zo daya da ita itace ke fada min wata rana da muka dan kebe a gurin wanke wanke take ce min.
Wanan sarakuwan bata son ki hadiza suruka haka komai kakeyi idon ta yana sama ni dai da nice ke bazan bari tasan komai nawa ba gaskiya ko dai don ba itace ta haifi mijin ki ba yasa take maki haka ne.
Ni dai murmushi nayi mata tare da fadin kin san zama da manya sai hakkuri tunda suna koya muna gyara ne ai ban yarda na fadi wani maganan da zata kaini gaba ba a gaban ta.
Fadin haka da wanan matar tayi yasa na shiga rufe sirina ga kowa dama shi kan shi Jamil din haka yake so bai son ina hurda da kowa bama a gidan kawai ba harda yan uwa na ga baki daya.
Niko ina da dabi,an in nayi bako sai na cika mashi ciki ya koshi sosai kafin ya tafi sai hakan ya shiga bata ma uwar mijina rai kuma.
Sai ta tsiru da dabian idan na

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login