Showing 87001 words to 90000 words out of 106121 words

Chapter 30 - kanin Ajali Book Complete by Zee Makawa .txt

Advertisement

01 Jan 2025

8072

zuwa wani gari neman kudi.
Ko lalura zai rage min a gidan don na gane nisa da nisa dashi yanzu ya fiye min dadi da idan yana gari bai yi tafiya ba.




ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
5/18/21, 11:57 PM - 🤔🤔🤔: Sannu sanu zance ke zuwa min ban yarda akan jamil da dadiron shi wai basu rabu ba sun canza gari ne har yanzu ya tare da ita.
Da farko wanan zancen ya tayar min da hankali sosai don har yangida mu naji zancen a gurin su sai ban yarda da su ba.
Sai dai abinda ke daure min kai kuma shine yanzu zaman may yake a gida hakan ya kara ban kwarin gwiwan rashin yarda da zancen.
Karshe dai na kasa hakkuri na tunkare shi da maganan da nake jin din a bakuna da yawa na mutane.
Nan ya shiga fada yana zagi sai na fada mashi wanda ya fada min don kotu zai kai mai shi kara hankalina ya tashi yadda naga yana fadan nayi ta bashi hakkuri.
Yace daga karshe idan na sake kawo mai wana magana ni zaiyi karan bata mai suna inyaso zan fitar da wanda ya fada min din.
Hakan yasa na yarda dashi na basar da zancen duk wanda ya tare ni da maganan sai i nuna mai ba gaskiya bane wanan magana .
Gani ban iya boyo ba don har gidan mu naje na fada masu yadda muka kwashe dashi din kan maganan.
Nan sukai min caaa a kaina suna fadin yasan su suka fada yasa yace hakan da in kyale shi yai karan nasu daga wanan lokacin suka kara daukana shasha wace dai bata san abinda takeyi ba ma.
Kowa ya kawo ido yasa mun a kan zancen ga gaskiya ana gani aka kyale ni dashi mu tafi a hakan .
Kunci da talauci ya isheni babu sauran inda zan tafi in kai kukana kuma a tausaya min don ansa ko an bani shi zai karbe.
Yasa yanzu babu sauran dan uwa da ke tausaya ma al, amarina kuma sai dai irin su baba kabir dana zama ma kamar dolen shi.
Don abinda yake muna bai ko yiwa "ya"ya cikin shi gaskiya don yana matukar tausaya muna sosai a rayuwa .
Ba dai yadda zaiyi ne mun riga da mun zabi mazajen mu dasu yasa suka saka muna ido sai dai taimakawa idan suna da halin yin hakan.
Ga yanzu abin na baba kabir yaja baya sosai do yanayin da kowa na kasan nan ya shiga yanzu shima ba samu yake kamar can baya ba.
Babu sauran abin kwarai da yarage min a daki sai kujerun dake falona kawai kula na kwarai da idan nayi baki ko na Jamil banda na fita kunya a gidana.
Haka nake ta manejin rayuwa a wahalce don rashin da yai min katutu a gidana kamar ni kadai ce iyayyena suka fara mutuwa a duniya su barni.
Yau ma ina kwance saman dogon kujeran falona tun safe nake aikin sakawa ina warwara a zuciyana don rashin samun mafita gashi ko kudin sayen garin kwaki banda shi.
Balle shika ko wani abinci da zamu sarrafa a gidan.
Shawara na yake a karshe in sayar da da gadona daya saura min a dakin wands shi kadai na saura dashi daga cikin kayan da akai min tun gida.
Duk da ina fargaban hakan a raina amma kuma shine kawai mafita a gareni yanzu don in rufawa kaina asiri a gidana.
Tunda ba kowa ke shiga min dakina ba dama iyakar bakona falo don ko banza ina jin kunyan a shigo aga dakin hakana ba katifan kwarai a dakin.
Ya shigo nake fada mai shawaran dana yanke sai washe baki yayi yana fadin tuntuni naso in baki wanan shawaran ina gudun ki ce wani abu.
Yanzu ki samu mai sayen gadon ne nace a,a dama kai nake jira ja shigo in fada ma idan ka yarda sai In nemi mai saye din.
Yace kiyi ki shirya to ko za a samu ya shiga a lokaci nace ban samu abinda na dan dafa muna ba yau gaba daya ma ban karya ba tun safe.
A, a ina ko da dari biyar barin baki ku samu abinda kukaci tunda ga kudi zasu dan shigo ya sa hannu a aljihu yana kumbiya kumbiyan ciro kudin kada in gani na tabe bakina tare da kawar da kai gefe daya.
Ya ciro kudin yana miko min duk da lankwashe kudin da yayi alama ya nuna ba shi kadai bane a aljihun shi.
Ni dai na karba tare da daukan hijjabina zan fita don samo muna abinda zamu sarrafa muci da rana don yanzun safiya ya wuce.
Inda na barshi zaune nan na dawo na samay shi yana zaman jiran in dawo ina shigo yake ce min wai nace ai ya kamata a kwabe gadon kada tazo ta samay shi a kafe tace yana da wani bakasu kuma.
Nace hakane kuma fa yanzun dai girki zan dora idan nagama sai in kwabe kafi in tafi yace bari dai in tayaki kwabewa zaifi sauki don in rage maki aiki.
Na fita ya shiga aikin kwabe gadon kafin in gama hada abinci har ya gama ya fitar da gadkn wajen gidan ya jingine su.
Arzikina daya ta kofan baya ya aje kayan gadon ba tare da yan haya gidana sun sani ba balle abin yazama abin magana.
Bata na gama aikina muna zaune muna cin abinci yake fadin idan sauran kudin ku sunzo sai ki samu gado na zamani mai kyau na yayi ki saye.
Ina mamakin Jamil ba wanan ne karo na farko da yake cika min baki kan kudin mu idan ya fito ba sai dai idon kufin sun fito kuma sai abi wani hanya dasu da ban sani ba.
Na samu wata dillaliya mai saye tana sayarwa na kayan daki muka shirya da ita zata zo taga kayan sai tai mashi kudi idan zamu shirya.
Kamar yadda tace din tazo taga gado tace kuma yayi mata nan muka fara cinikin kayan gado da ita.
Dubu talatin ta saye da kyat ta karamin dubu uku sama nace ta kawo kudin an sayar mata take a gurin ta lale mun kudina ta bani ta fita neman wanda zai kwashe matasu
Har aka fitar ba wanda ya sani a gidan shine rufin asirina saidai mai washe gari ina karyawa da safe sai gashi ya fito falon .
Ya samu wuri ya zauna yana fuskanta na nasa yana da magana ke nan si kuwa bamu fi minti ralatin ba ya kawo zancen kudin.
Yana fadin may kika yanke zaKiyi da kudin gadon nan dago kai nayi ina kallon shi nace.
Sana,a nake son yi da wanan kudin ya gyara zama yans fadin sai nake ganin da zaki ban in fita garin nan zuwa wani gari da zaifi.
Dago kai nayi tare da dakatar da abincin da nakeci ina kallon shi ya wani gyara zama yana fadin ko baki yarda dani bane .
Abinda mutane ke fadi zaki dauka ni ba komai yasa nace hakan ba kinga ni wanan zaman da nake haka ya isheni.
Gashi na saba yanzu da sana,a kinga in na fita na juya muna su ba,a san iya albarkan da zasu koma muna ba ai .
Nan dai ya dinga kawo min dadin baki irin nasa yana tsarani har na yarda inda yace wanan karon ba Abuja zai tafi ba zai canza gurine.
Zuwa bakin boarder ance sana yana daukuwa can sosai kamar may kin ga zama haka bazai yuyuba gare mu yanzu ga yaran nan suna tasawa.
Amira na ina son idan na dawo mu sakata makarantar boko ta fara zuwa yakare tare da fadin ko may kikace ga shawarana.
Dan shiru nayi ina nazarin sa sai naga maganar shi kuma gaskiyace idan ya fita din zaifi sana,an da zanyi a nan din samu.
Sai na buda baki nace hakan za ayi sai kaje da kudin mu gani ko Allah zai sa muna albarka a cikin al,amarin.
Wani shu,umin dariya yayi yana cabe yar karamar yar mu tare da fadin mamana babakin ya samu mafita ku tayani da addua, don ance addu,an yara tana kamu sosai.
Tun ranan ya fara shiri kwana daya kawai yayi a tare dani ya kammala kudin shi ya bar garin ya barmu a cikin wani sabon wahala kuma.
Sai da ya tafi naga wautana daga baya na yarda dashi danayi na bashi kudin yanzun gashi ya tafi ya barmu a cikin wahala nida yara.
Nan sabon fadi tashi ya dawo min ina nema abinda zamu ci don ko na omo da sabulu ya ishe ni fama yanzu.
Ance anbin duniya baya boyuwa koda ko kai kadai kayi shi ban san inda yan uwana sukaji wai na sayar da gado na ba.
Sai ranan da na shiga wurin kanwata yar gurin baba kabiru muna ckin hira ta jefo min zance da cewa ke anty may ya kaiki sayar da gadon kwancin ki kiba namiji kudi yayi tafiya.
Mutuwan zaune nayi don ban taba zaton wani yasan da wanan maganan ba sai ni sai shi muka sanda wanan maganan.
Gashi yanzu magana ya fito fili har an sani wani irin bata rai nayi tare da faman rantsewa ni ban sayar da gado na bashi kudi ba.
Nan dai ta dinga min nasiha akan namiji tana nuna min illolin dake cikin sakar, wa mijin bakin aljihun ka.
Banji dadin da akaji wanan zancen ba dukda na nuna mata ba komai a haka ban bashi kudin bani.
Dama mukan danje gurin ta mu cika cikin mu ne faman da abinci dagani har yaran sai mun koshi mu dan taba hira mu dawo gida.
Amma yau wannan maganan data fito min dashi yasa naji raina ya baci da ita sosai ban ko tsaya yaran sun gama cin abinci ba nace da ita mu zamu tafi.
Duk da ta gane nufina sai batai min magana ba a lokacin ta kyale ni na fice hakanan tunda ta fahinci rainane ya baci kan maganan da ta fito min dashi din.
Niko damuwa da bakin cikina bai wuce ace yan gidan mu sun san da wanan maganan ba a gida tunda ko ita ta sani ke nan kowa ya gama sani a cikin dangin mu.
Waima yaya akayi wanan maganan har ya fito fili akaji shi shine tambayan da nakewa kaina har na iso gida ina wanan tambayan a raina.
Ga Jamil din tunda ya tafi wata biyu ke nan yanzu da tafiyan shi ko waya bai kiramu ba balle sakon shi ya iso gare mu.
Gashi na dauke kafana ga kowa nawa don gudun wanan maganan kada in je inji takaici a raina don nasan nice banda gaskiya.
Tunda munyi da anty cewa idan ya sake sayar min da wani abu da zafizafi in zo gida in fadi a dauki mataki a kan shi.
Balle wanan din da dakaina na yanke shawaran sayarwa don sama wa kaina sallama sai ban mori kudin ba shi ya karbe abinshi ya tafi.
Ga kuryan dakina ko dakin gwauro ya fishi dadin gani yanzu don babu komai a cikin shi sai tsohuwar katifana dake yashe a kasa da tsumakaran mu da ke gefe daya.
Don hatta akwatunan auren da baba yayi min da gidan su Jamil basuyi min ba na sayar nayi lalura da kudin lokacin da naga ya sai min sabbi na haiwan karamar yata.
Yanzu ko babu su tunda ya sace ya fita dasu basu dawo gidan ba har wanan lokacin, tundai ina saka damuwa a raina har yakai na hakkura na ci gaba da gudanar da rayuwana yadda na saba a baya cikin hakkuri.
Mu ke nan ko yaushe cikin cin taliya ko garin kwaki don shinafi karfi a gidan yanzu.
Duk da ba lalaifi indai shi zai sayo muna abinci abinda zamuci musan munci mai kyau yake sawo muna aci gaskiya..
Idan ina ba yan gida mu labari irin yadda nake baku yanzu sukan ce a cikin kudina muke cin dadin da yake sayo muna din ai.
Ranan na gama abinda zanyi na kwanta barci da rana sai nayi mafalkin wai gashi tare sa wata mata da yaran su biyu wai nasa ne.
Muna fada sosai dasu a cikin mafalki na falka daga barcin sai naga duk na jike da zufa jikina sai kyarma nakeyi kamar nayi fada a fili da wani.
Nan na fara tunane a raina har tsawon wani lokaci ina zaune a gurin dana kwanta din ban iya tashi ba sai faman tunane nake kala kala a raina kan wanan mafalki da nayi dashi.
Ina maimaitawa a cikin raina yara biyu fa a yadda na ganshi da yaran mace da namiji sai mafalkin yayi matukar tsaya mun a raina sosai.
Da kyat na iya tashi na dan watsa ruwa a jikina sai ba samu na danji shakat a raina, sai dai na kasa cire zancen mafalkin a zuciya sai faman maimaita maganan nake har a fili kamar wata zautata dani.
Bayan kwana biyu na fita zuwa gidan wanan kanwar tawa inda na samu aron waya na kirashi don abokin shi ya bamu lamban shi ranan.
Kira biyu ya daga don baisan ko waye ya kirashi ba don nasan da yasan nice kila ba zai dauka ba ma ban sani ba.
Yana dauka tare da fadin hello nace sallamu Alaikum baban Amira don haka yanzu nafi kiranshi dashi, yana jin muryana yace .
Hadiza ce a ina kika samu layina wayan wa kika samu kika kirani dashi wani amsa zan bashi daga cikin don ko gaisawa bai bari munyi ba ya hauni da wanan tambayan haka a jere.
Babu boyo nace na safiya ce kanwata yace kinje gidan ta ke nan ko nace eh yanzu nazo gidan ta don ta ara min waya in kiraka.
Ya sauke ajiyan zuciya yana fadin to yaya gida ya yaran kunji kwana biyu shiru ko nace shiyasa ma na nemi layin ka don muji ko lafiya shiru haka ?
Yace lafiya abubuwa ne suka dan cije min kwana biyu yasa ban kiraku ba ban turo maku sako ba har yanzu.
Nace yanzu baba Amira don abubuwa sun tsaya sai ka kasa turo muna dan kudin da zamuci abinci dashi ka san fa baka barmu da komai ba ka tafi.
Yace a hasale wanan wani irin magana ne haka ni ban fiki sanin halin da na barku a ciki bane gidan ke may yasa baki da fahinta ne wai hadiza ?
Inda yake shiga ba nan yake fita ba idan da dane hakkuri zan bashi da yake fadan nan sai yaji har ya gama ban tanka shi ba sai da naji ya gama nace.
Ni yanzu dai ka samu kudi ka turo min ko abinci mu samu mu saye ko ka turo min kudina idan ka samu mu sai abinci.
Dan shiru yayi kamar mai nazarin magana na sai can naji muryan shi yana fadin naji zan turo idan na samu ya kashe wayan.
Kallon juna mukayi dani da yar uwata kai kawai ta gyada tare da murmushi niko mamaki da takaici ya hanani magana.
Hakkuri ta dinga bani inda ta hada min dan kayan abinci inzo dashi gida mu dan dafa da yara sai kwalla ya zubo min daga idona.
Hawaye shar shar wani na bin wani a fuskana inda na kasa yin magana a lokacin saboda kunci da takaicin da ke cin zuciyata kamar ta fado min nake ji a lokacin.
Na kasa fadin komai gare ta haka na mike zuwa gida sai Amira ne ta dauko dan kullin kayan da ta hadda min a cikin leda ta biyo bayana dashi zuwa gida.
Ko da na shiga gida na dade zaune a falo na ina sakawa da kwancewa a zuciyata sai dai na rasa mafita a kan hakan.
Ni, banga kudina, banga gadona, yanzun na tashi a tutar babu, ya yaudareni, ya cuce ni ya raba nida komai nawa na gado da wanda iyayyena dake raye sukai min na aure .
Jamma,a ni haka tawa kaddaran tazo min da aure mayaudarin namiji wanda baida tausayi ko imani akan iyalin shi kanshi kawai ya sani a rayuwu.
Nasan masu karatu duk kuna ganin laifi a wanan labarin sai dai ku sani Jamil ya yaudari mahaifin shi ya yaudari wasu maza yan uwan shi balle ni mace, macen ma kuma matar shi da yake ma kallon sakarai




ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
5/18/21, 11:57 PM - 🤔🤔🤔: Yau da gabe muna zaman jiran kudin mu kin san yadda alamarin kudin suke yau zamu gansu gobe zasu fito shiru har wata uku da maganan da baba kabir yayi min yanzu babu labarin kudi.
Ga bubuwa sun taru sun min yawa a kaina zuwa yanzun duk da Jamil din bai faye zama damu a gari ba yanzu.
Sai yaje ya share wata uku hudu har shidda yanayi ba tare da mu ba a can na ramay nayi baki na lalace babu mai taimaka min a cikin dangina

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login