Showing 99001 words to 102000 words out of 106121 words
Chapter 34 - kanin Ajali Book Complete by Zee Makawa .txt
abin na samu zuwan kudin nan yasa min yarinyata babba makarantan ana biyan dubu uku da dari biyar niko sai yake hakori nake yarinya ta tana pravert school ai idan an tambaya.
Gane sana,ata da kowa yayi bai hanani samun alheri daga ciki ba don ina samu gwargwado hali na sai yan tunkiya guda biyu na aika kauye a min kiwon su don kar Jamil ya gane ya batar dasu idan yazo.
Abinci yanzu banda matsalan shi tunda kudi na zuwa min yadda ya dace sai dai tun ina boyo har na kai gidan mu sun gane ina wanan sana, an.
Ba wanda yayi yunkurin hanani shikan shikafa da nake ina sayar da tsakin buntun daga cikin yan uwana tunda sun gane ina samu daga cikin sanaa,an .
Sai fadi suke yadda nake wahala wata kila yanzun zan koyi tanadi in dinga boye kudi idan na samuwa jamil din.
Ko ga yadda nake yawan nunawa mutane cewa ai yanzu nayi hankali na koyi darasi sosai na duniya.
Sai mutum ya dauka lalle duniya ta koya min hankali sosai yanzu don na kare ga shikan butun shimkafa ina sayar ma masu karamin karfi irina ina samun alheri daga ciki nima.
Da yake ban saba da aikin wahala irin haka ba sai abin ya fara fita mun rai duk da ina samu daga ciki ina rufawa kaina asiri da wanan sana,an shikan da nakeyi din.
Yan uwana da saura abokan arziki suna ban shawaran in dan samu in dinka sutura ko yaya ne daga cikin dan abinda nake samu din daga sana, an.
Sai dai kasssh ban saba ba don haka ban iya cire kudi in dinka wa kaina tufafi dashi sai dai muna ciwa ran mu mai dadi dani da yarana gaskiya.
A haka nayi ta juya rayuwana har zuwa lokacin da Jamil ya waiwayo mu ya dawo gida bayan yaci zaman shi a garin da yake.
Wanda izuwa yanzu kowa ya gama gane karyan da yake sharawa na zuwa neman kudin da yakeyi kamar yadda yake fadi idan zai tafi.
Sai dai a wurina ne ban gane hakan ba saboda dan albashinshi da yakan tara ya dawo dashi mu cinye a cikin kwana biyu sai ya koma cin wanda na dan tanada muna nida yara anan.
Tunda ta dawo nake boye mai wanan sana,an nawa da nakeyi yanzu ina samun rufin asiri ta wanan hanyan.
Sai dai abin bai boyu min agareshi ba saboda mutane dake yawan zuwa tambayan ko akwai tsakin shimkafa din.
Har dai na daure na fada mai abinda nake a bayan shi a zatona zaiyi fadan haka din.
Don sana,an kaskantantu ne a gurin wasu da suke ganin shi aikin wahala ne da kaskantar da kai.
Amma sai nayi mamakin jin baiyi fada ba illa fadin da yayi idan ana samu sai in rike sana,an da kyau in dinga yi.
Nan naji dadi na shiga fada mai irin alherin da nake samu ta wanan sabon sana,an dana rike yanzu yana ta bugun cikina ta hayab nuna min jin dadin hakan da nakeyi.
Sai da ya gama jin komai ya nuna kamar bai damu ba da yake ya iya sallon yaudara kala kala har yakai shike zuwa nema min butun shimkafa da kan shi.
Hakan yasa na kara yarda dashi tunda ya nuna min kauna da yaudaran shi ashe kwanto yayi min a hakan.
Sati biyu yazo min da dadin bakin ya samu kifi mai saukin kudi sosai da zai samu kudi ya saya zai samu karuwa sosai ba zai dade ba zai dawo ya kara saran wani.
Ba tare sa wani shawara da zuciyana ko wani ba na yanke shawaran kulla kudade na tunda duk karuwan mune hakan nace ya bari zan hada in bashi sai mu gwada.
Murmushin gefen fuska ya sakar min tare da shiga zuka min albarka da fatan alheri gamin da yabon halina na kirki a gare shi.
Nan na fara fadi tashi har na hada mai dubu hamsin ya dukula ya tafi ya barni da fadi tashin hada wasu kudin kuma.
Don na koma banda ko hari yanzu da zanjuya wurin sayen buhuhunan butun da nakeyi inzo in sheke su koma min tsakin shimkafa masu karamin karfi su saya a wurina su samu saukin sayen abinci a yadda kasa ta koma yanzu.
Sai na tura kauye a sayar min da tumakan da na saya na turawa yar mahaifiyar mu a can a kiwata min su har su dan tasa in sayar.
Sai ga sako yazo min wai ai tumakan sun dade da bacewa fada min daine basuyi ba amma zata kokarta ta saya mi wasu..
Jin haka hankalina ta kara tashi sosai gashi shi har wata biyu na neman rufewa bai dawo inda muke ba tunda ya tafi da sunan sati biyu kawai zaiyi a can.
Gashi yanzu mutane sungane sana,an ana samu sosai gare shi mutane sun raja,a ga sayen shi don sauki da yake dashi a gurin jamma,a yanzu.
Sai ya kasance butun yana wuyan samu gare mu haka zamuyi ta yawo a ckin rana muna neman shi don mu sarrafa wa masaya su samu su saya suma.
Wahala yayi min yawa sosai a cikin haka na fahinci ina da shigan ciki a tare dani kuma sai abin ya zamo min sabo ga wahala ya taru yai min yawa lokaci daya.
Haka nake ta fama da rayuwana ko yaushe don neman abinda zanci ba zancen yin sutura ko wani abu a gare ni kuma yanzu na karuwa.
A haka ya dawo ya samay ni cikin wanan halin ba wani karuwa ko kadan daga gare shi sai buga bugan rayuwa da mukeyi a gidan yanzu har shi.
Ba laifi duk da hakan da nake yan uwana diyan baba kabir suna kokarin su dani sosai don da matar nan yar haya ta matsa min da fitana a gida.
Da taimakon yaran wurin baba kabiru na samu salama har ta bar gidan don suma kamar yadda ta tayar min da hankali haka sukazo suka tayar mata da hankali sosai.
Sai data firgita ta tattara tabar muna gida ba shiri suka canza gida na samu yarbawa na saka a dakin ta sai dai Jamil din ya karyata matar akan wai sheri take mashi.
Zaman da ya danyi tare damu na matsine sosai don banda halin tambayan shi komai na girki yanzu za a jimu yana cika yana batsewa.
Sai in ya ga dama yake kawowa ayi in bai kawo ba dole inyi dabaran abinda zamu ci da yara don zama da yunwa bai yuyuwa gare mu.
Dan sabon da nayi da rike kudi sai yanzu na koma wata kala can dani don rashin kudin dake shigo min a hannu na dana saba kwana biyu dayi ina taimakawa kaina dashi.
Har yakai an fahinci halin da nake ciki don yawan ragga da ya baibaye ni har yarana bamu da sutura don ko na fita bamu dashi.
Ni dai dama bukata muci musha tunda na saba da rashin sutura kamar yadda ya biyar dani a gidan shi tun shiga na ba zance ya kashe min kudi akan sutura ba ko yayane don duk wanda yake muna a cikin kudina ko jiki na yake yayabo muna su a wullakance.
Ban baku labari ba can baya har maciji ya sare ni a gidan Allah ya taimaka yana garin lokacin da abin ya faru dani da kanwata tana gari sunzo a lokacin.
Naga gata a wurin dangina kaf lokacin don sun nuna min suna kaunan mu don anty da kanta tazo gidan ta sa a toshe duk wani kafa dake gidan.
Anan suke wuni tare dani da aka sallamoni daga asibiti ana hadawa dana gargajiya don kada ya taso min kamar yadda kace wai yana yi bayan duk shekara idan ya zagayo.
Ba laifi lokacin ya nuna masu shi na miji na don ya tsaya ya kula dani sosai da fannin maganin da ake bayarwa anayi din .
Kuma yana sayo min abinda zai gyara min jini na akai akai sai yabon shi ake tayi ana saka mai albarka kan namijin kokarin da yakeyi dani lokacin.
Wanan dalili yasa na rike yan uwana yanzu sosai na fahinci mutum baiyi saida yan uwa shi na jini a rayuwan shi.
Sabanin nida na rike yan uwan miji wanda hakan ke ba kowa nawa haushi irin yadda na ba yan uwan miji amana dari bisa dari na watsar da nawa sai wutin wahala nake nemo su.
Yanzun ko na san dadin su sosai don ba a kwana a wuni basu shigo sun duba lafiyana ba duk da ba komai nake basu ba idan sunzo wurina din.
A haka nake dan bubugawa ina samun rufin asiri a guri Allah muna ci muna sha nida ke dauko buhu goma sha bakwai har ashirin sai gashi na koma da kyat nake samun buhu daya in gyara a ciki zamuci na sayar da saura muyi lalurar mu dashi.
Da Jamil ya fahinci ciki ne dani ya fasa tsiro min da wasu halaye wai shi haihuwana yayi yawa akan lokaci har yaushe da zan tara yara haka a gida.
Wanan maganan ya tsaya min a rai naji na kara tsanar cikin da na samu yanzu dashi don nasan nike da wahala a karshe na cikin ke nan.
Tunda dama ba komai yake tsinanawa idan na haihu din ba don nasan wanan tunane shima yake yasa ya fara aibanta cikin jikina din .
Ya fara shirin komawa inda ya fito inda yake ta fadi tashin neman kudin motan da zai koma inda yace yake da zama.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
5/18/21, 11:57 PM - 🤔🤔🤔: Narasa inda zan sa kaina da rikicin Jamil akan kudin nan daya kwallafa ranshi gare su.
Gashini bako ganin kudin nayi bawa a idona va do Baffa ya rike ya hanani komai daga cikin kudin.
Gashi shi kuma Jamil har yana kirarin zai iya sakina idan na hanashi wana kudi do baiga amfnin zama dani va tunda zan iya samu in hanashi yanzu.
Wai da sani na aikai komai na rike kudina a gidan mu don ai va haka aka saba yi ba a baya cn da yanzu za a kirkiro mai da wani sallon kanina ya rike kudina.
Da abin ya ishe ni na aika akira min kanwata dake aure yar gurin baba kabir a kusa damu do ya hanani fita ko ina inga kowa nawa lokacj saboda baki rai da yakeyi dani a gida daga ni sai shi sai yan hayan mu dake gefe daya a gidan da ba wani shiri mm nake dasu ba sosai.
Wanda duk sherin shi ne hakan ya hanani zaman lafiya da kowa a gidan don ba halin ya gano ina shiri da daya daga ciki matan gidan yanzu zai fara sukan mai shi har sai naji na tsaneta a raina.
Mu bar shiri hankalin shi zai kwanta wasa wasa sai da yasa na kore duk hausawan dake gida suna haya ya zuba matan yare a gida sai bahausa daya ta saura muke zama da ita.
Ko ita do tana matar abokin shine da suke shiri shi kuma mijin ba mazauni gari bane dama sai lokaci lokaci yake zuwa gurin iyalin shi yayi yan kwanaki ya koma.
Abin da na kula dashi shine matar da muna zaman lafiya kasancewar mu hausawa a gidan dani da ita sai yanzu naga canjin fuska a gare ta kuma har da diyana.
Abu kadan sai taso fada ya hada ni da ita sai dai ban biye mata nakan share ta idan naga tana jin fitina dani lokacin nakan fita batun ta sai ta sauka da kanta zamu shirya.
Sai na fahinci na wanan lokacin yafi tsananta don magana take dashi a bakin ta da take son samun kafa ta fada min shi a cikin fada.
Rashin kulata da banyi ba yasa ban ji ko may take da niyar fada min ba a lokacin wanan ke nan.
Bayan kanwata tazo nake fada mata halin da muke ciki da jamil da abinda yake fada min a yanzu bata ko bari nakai ayaba ta karbe zancen da fadin shiko Jamil dai.
Duk irin halarcin da kikai mashi da kudin ki da farko bai gani ba sai wanan da baida wani yawa kuma shine na karshe.
Tace a fusace ki fita batun shi duk abinda zaiyi yaje yayi kawai kudi daine suna hannun baffa a yanzu bai iya kwatar su kuma.
Watau shi ya saba cin banza yanzu ya sa rai a wayan nan yaga sunzo basu shiga hannun shi ba shine yake jin haushin akan hakan.
Ki ma godewa Allah da akai dabaran yin hakan gareki don kila wanan a samu a sai maki abin kwarai dashi.
Kinga ko ba zai so haka ba shi don yasan kece da karuwa a kan hakan da za ai maki din nan gaba, surutu take zubawa.
Wanda ni ba haka naso daga gare taba don kiranta nayi ta ban shawaran yadda zan karbo kudina hannun baffa in bawa jamil nake so ba wanan dogon sharhin da take min ba a yanzu.
Ta fahinci maganan bai mun dadi a raina yadda taga ina bata fuskana kamar zancen ya isheni ji hakana sai ta dawo fadin yanzun dai shawara ya rage gare ki .
Idan kinga zaki karba ki bashi ne don kada ku samu matsala sai kiwa baffa magana ya baki ki bashi a zauna lafiya.
Sai lokacin na iya magana tunda ta fara magana nace nima dai haka naga yafi sauki ya bani kudin in bashi a zauna lafiya idan ya kashe sai kwadan shi ya fada.
Wani kallo tayi min tare da mikewa tana gyara goyon yarta dake bayan ta tare da fadin ni zan tafi Allah ya sauwa ka.
Saurin tare ta nayi ina fadin yanzu in turo maki Baffa din gidan ki ki masa magana ko zai yarda ya bani kudin na fada cikin yanayin son ta taimakeni din.
Tace ba matsala indai zai yarda ya bada kudin ai ta bafa cikin son ta bar gidana a gagauce don ko bata fada ba ranta ya baci dani sosai don bata samu hadin kai a gurina ba.
Kamar yadda tace zata kira baffa din gidan ta haka ta aika yazo suka zauna sukai min tas kan rashin sanin ciwon kaina da banyi ba.
Karshe dai baffa din yace ta barshi da Jamil din yasan hanyan da zai bullo mashi akan maganan kudin .
Washe gari sai gashi ya sallama gidan namu da safe na tare shi a cikin daure fuska muka gaisa sama sama dashi yace dani bayan mun gama gaisawa.
Naji sakon ki gurin anty sai dai ki sani na riga da nayi maki amfani da kudin ki kamar yadda nace zanyi
Raina ya baci kafin ya gama magana nace kudin wai ko nawa nace kaban abina inyi yadda nake so da abina zaka kawo min wani magana yanzu kuma.
Mikewa tsaye yayi yana fadin kiyi duk abinda zakiyi kudi dai ne na hana bazan bayar ba kiyi abinda zakiyi dake da mijin naki yana fadin haka ya fice daga gidan rai bace.
Nima na bishi da zagi na fitan arziki har ya bace min a gidan na zauna ina huci sai ga jamil din ya fito daga daki don yana ciki kwace.
Dama nasan da gaiyya akai min wanan abin don wanan ba shawaran baffa bane shi kadai da munafukar nan anty suka hada baki a karbe kudin nan.
Suci, su rike zasu ga abinda zanyi nan gaba wallahi don kowa ai ya iya iskanci shi karami dashi zai kawowa mutane rainin wayo don ya raina mutane.
In akwai abinda nake tsoro shine Jamil ya furta zai sakeni a duniyan nan don irin son da nake mashi a raina ba na wasa bane.
Wanda mutane suke min kallon tababba ko mara wayo don ban san ciwon kaina ba dole na shirya zuwa gidan kanwata again don ta kara lalasan min Baffa din ya bani kudin in bashi .
Don ban son iyayyen mu su san da wanan zancen ga kudin da aka bani in ba yan uwa daya karbe ya zama min fitina sai zargina da zagi yan uwa keyi kan an basu kudi na cinye.
A gidan ta baffa yazo ya samay mu inda da kyat yace sai dai indan shi zai arawa Jamil din kudin shi inya yarda suyi aggrement a rubuce .
Don kudina ya riga ya juya min su kamar yadda yace min da farko dole na yarda da wanan shawaran don nasan su suna da kudin ko nawane a hannun su.
Da wanan shawaran na dawo gida sai zuwa hudu na yamma Jamil din ya shigo yana wani cicika dani na fada mai cikin daurewa abinda Baffa din ya ce min.
Kamar maye don na dauka zaiyi fushi yace bai karba sai naji yace idan haka yaga zaiyi ai ba matsala .
Shi a zato shi zai dai ci kudin ko ta halin kaka don haka ya dai samu su shigo hannun shi din shike nan yadai ci kudin ke nan.
Ba musu ko wani zance yace sai baffa din yazo zuwa yamma ko sai gashi gidan