Showing 21001 words to 24000 words out of 106121 words

Chapter 8 - kanin Ajali Book Complete by Zee Makawa .txt

Advertisement

01 Jan 2025

8058

hadiza hakkuri zamuyi don Allah daya bamu ita ya karbi abinshi .
Baba nace da karfi sai kuma na koma fadin inna lillahi wa,inna alaihim rajiun sai naje su a gurin na somay masu ban san inda nake ba don halin da na shiga.
Sai farfadowa nayi na ganni a hannun umma tana shafa min ruwa a fuskana budan baki na nace mama da karfi tayi saurin rufe min baki da hannun ta.
Baba bai iya fadin komai ba don shima kuka yakeyi a lokacin ga kanne na da suke kuka wiwi a kaina suma.
Umma rana naga taushi a gurin ta don ita ta koma tana lalashi kamar yadda mama zatayi min ta koma min makwafin mahaifiya a gareni.
Banci ban sha don damuwan da nake ciki bazan iya fada ma mai karatu ba sai wanda ya taba shiga irin halin da nake ciki a lokacin yasan irin rayuwan dana riska a lokacin.
Baba yana lalashin mu yana nan nan damu baya son yaga ran mu ya baci ko kadan sai dai duk wanan ban gani nidai muradina mahaifiyar mu ta dawo gare mu.
Da kyat suka shawo kaina na fara dan walwala da kannena da nasiha da fada da komai hankalina ya fara kwantawa.
Sai daga bayane nake jin labarin mutuwan mahaifiyar Jamil wurin kanne na na tausaya muna sosai dani dashi don irin halin da muka riski kan mu a ciki na rashin magaifiya da mukayi.
A cikin wanan yanayi na bakin ciki ne hutun mu ya kare haka aka mayar dani school ba tare da na gama warwarewa ba.
Wanan time din na dai koma school din ne ba don zan aiwatar da komai ba na fannin karatuna haka din ne kuwa don tunanen mahaifiyata ya hananu shakat a raina.
Sannu a hankali na fara sakewa ina dan walwala a makaranta duk da ba wani yi nake kamar a baya don ba zan iya shafe rashin mahaifiya a zuciyana ba.




ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
5/18/21, 11:49 PM - 🤔🤔🤔: 🙆🏼‍♂️ KANIN AJALI 🙆🏼‍♂️


8️⃣


ZAINAB IDRIS MAKAWA

FATAN ALHERI DA CIKAWA DA IMANI GARE KU MASOYANA ALLAH YA SA MU FI KARFIN ZUKATAN YABA MU IKON BAUTA MASHI, BAUTA TSARKAKAKIYA ALLAHU MA AMIN YA ALLLAH 👏👏👏👏




Wanan time din haka na kare shi babu dadin rayuwa a tare dani don sam hankali baya ga karatu don tunanen mahaifiya na da yai min yawa a raina.
Na dawo gida na samu har lokacin umma tana gidan zaune da kanne na kamar kada in dawo sai umma ta tayar da hankalinta akan tana son zuwa gida ta duba su can.
Wanan abin ya daga hankalin mahaifin mu sosai da ya rasa yadda zaiyi damu gashi hutu akeyi sai ya shirya har damu zata tafi muyi hutu a can.
Da yake dogon zango ne muka fara murna zamu gida muga yan uwan mu sai dai ina gani kamar idan munje zanga mama acan a raina.
Mun zama yan matasa yanzu don haka muka fito fes damu a gurin baba kabiru muka fara yadda zango da muka iso zamu dan kwana biyu a gurin shi kafin mu karasa gida.
Matan shi suka shiga ina aka saka damu suna yi muna kokari mun fi sakewa da matar shi ta biyu a gurin ta muka sauka inda umma ta sauka gurin uwargidan shi.
Bamu da wani damuwa dan zaman sati dayan da mukayi da iyalin shi sai dawainiya yake damu yana nuna diyan dan uwan shi ne mu tankar diyan cikin shi muma muke a gurin shi.
Muka kare sati dayan mu muka wuce kauyen mu, yan uwa na ganin mu sai sharan hawaye sukeyi don tunawa da mahaifiyar mu da sukayi.
Muma dai kukan muka dauka tundai ni dake da wayau a cikin mu nafi kowa shiga tashin hankali sai da kyat da fada da komai umma ta samu na dakatar da kukan da nake yi.
Washe gari da rana muka shirya zuwa gidan kakannin mu na fanin mahaifiyar mu kai mata ziyara don muna jin dadin kasancewa da ita fiye da umma da take mahaifiyar mahaifinmu.
A can ma mun taba kukan saidai da ta rarashe mu mukai hakkuri duk firan mu na ranan kan ciwon mama ne da yadda muke maraicin ta.
Sai dare muka koma gida bayan tayi muna abinci mun ci mun dawo umma ta cika fam kan dadewan namu da mukayi a gidan kakan mu mahaifiyar maman mu din.
Ba wanda ya tanka ta muka shige dakin mahaifiyar mu inda anan muka sauka tunda muka iso don dakin umma ba fili kaya sunyi yawa.
Ina kokarin cire kayan jikina ne hafsa ta shigo tana rada min Jamil yana waje yana son ganina nace hafsa kin san ba abinda zai yuyu bane don yanzu umma ta gama muna fada munyi dare a gidan Auta don haka ake kiran kakan namu dashi.
Kije kice yayi hakkuri tunda muna nan watarana zamu hadu ai wanan ranan bamu hadu ba dashi haka ya juya ya tafi .
Ba tare da ya ganni ba sai dai banji dadin hakan ba don mun dade bamu hadu ba dashi ba zance ga ranan da muka hadu dashi last ba.
Gama shiri nayi na samu wuri na kwanta har na fara barci nake jin umma tana kwala min kira daga kofan dakin ta na amsa a sanyaye tare da mikewa zuwa wurin ta ina fadin umma gani.
Bazaku ci abinci bane har wanan lokacin baku dauka ba nace umma a koshe muke don mun ci abinci a gidan Auta kafin mu dawo gida.
Salati ta saka tare da fadin yaran nan kun iya sai da hali yanzun zuwa kukayi kuka nuna mata muna barin ku da yunwa ko may ?
Da sauri na dago ina girgiza kai tare da fadin ba hakana bane umma ba wanda ya nuna hakan a cikin mu wallahi rufa min baki munafukan banza kawai.
Gobe in Allah ya kaimu zanje gidan inji abinda yasa ta girka maku abinci a gidan ta kallon mamaki nayiwa umma din kamar ta manta da Auta ma kakan mu ne kamar yadda take kakan mu itama.
Nidai naja kafana na barta nan tana surfa muna zagi dani da kanne na akan zuwa gidan kakan mu ta uwa da mukayi muka kai dare.
Washegari tun fitowan mu dakin na gaida umma ban kara fitowa ba ina dakin mama ina aikin tunane rayuwan mun yadda muka koma abin tausayi duk da dai bamu da tausayi don mahaifin mu yana tsaye a kan mu.
Dama yan uwan shi kowa na nuna kulawan shi akan mu a matsayin su na yan uwan mahaifin mu din a gare mu.
Saidai mu bamu ganin hakan da suke muna dan abu kadan zamu dauka don mahaifiyar mu bata da raine ake muna wani abin da bai dace ba.
Yinin ranan haka nayi shi a dakin ba wani walwala a tare dani sai ma gyaran dakin da na tsiri yi tankar mahaifiyar mu tana nan a cikin sa ne kamar yadda naga tana yi idan munzo tare da ita garin.
Sai yama lis na watsa ruwa a jikina kofan umma na dawo na zauna muna hira da yan uwana a gurin ta fito daga daki tana fadin kin ga dama kin fito ke nan don maganan da nayi maki jiya kike fan fushi haka yau.
Nace ba haka na bane aikin dakin mu nayi don yayi kura da yawa sosai ta tace ke dai kika sani idan kin sa kanki a damuwa haka ma yan uwan ki ba zasu sake ba don basu ga kina walwala ba .
Shiru nayi ina fadin a raina walwala ai ya kare a gurin mu umma tunda mun rasa mahaufiyar mu ko a duniya.
Maganan ta ne ya dawo dani ga tunanen da nakeyi tana fadin idan ba zamu iyacin abincin da akayi ba a gidan mu dafa taliya muci da dare.
Don mahaifin mu bai barmu munzo hakana ba garin sai da ya sawo muna duk wani cimar daya san muna amfani dashi a can muka zo dashi gida.
Tambayan kanne na nayi idan zasu ci da sauri suka amsa min haka yasa na tashi don in dafa muna taliyan tunda suna son ci na sani dolene kawai yasa suke cin abincin gari.
Mungama muka taru a gurin umma din nan mukaci taliyan sai dai itako kallo bai ishe ta ba tuwon ta da aka kawo muna taci.
Bamu wani dade ba muka kwanta don dare yayi a lokacin sai dai ni ba barci ne nayi ba na dai kwanta ne ina tunanen duniya a lokacin.
Tunda muka zo ko hanya bai hadani da jamilu ba har yakai satin mu daya da zuwa garin duk ko shima yana cikin garin a lokacin.
Yau ya kama kasuwan kauyen mu ne kowa sai hada hadan sana,ar shi yakeyi don fita dashi gurin yan kasuwa in ka debe mu da bamu komai sai dai mu wanke mu saka don yanayin mu daya dan banbanta dana yan gari.
Sai dai duk da haka ba,a barmu a baya ba don muma munyi kwalliya mun saka kaya masu kyau don muna da muradin shiga kasuwan mu dan zagaya.
Saboda akwai kudi a hannun mu bayan wanda baba ya ba umma don lalurar mu na yau da kullun da wani matsala daka taso a gare mu a gidan.
Kamar yadda tsoho keda naci a kudi haka ma yaro yake da kunata akan kudi don su sauran basu san baba ya bamu kudin ba a hannu na.
Mun gama shiri muka sallami umma don abokai na da suka shigo don mu fita sai dai ni abinda ke ban mamaki shi su hafsa kawana ba karatun sukeyi ba kuma su ba aure sukayi ba har yanzu.
Mun fita mun dan zaga abin marmari na sayo muna da kannen na don mun dade bamu ci ba a can mun juyo zamu dawo gidane muka hade da su jamil da kungiyar su.
Ashe sun saka ido a kan mu suga fitowan mu take dan leken asirin su ya sheda masu mun fito garin muna zagawa a kasuwan sai gasu sun sha kwaliyan su zakace ba yan kauye bane su.
Kallon juna mukayi na sada kaina kasa don kunya su a dole ga samarin da suka ga yan mata suka zo da guntun turancin su don su burge mu saboda mun fito birni musan sun iya turanci.
Da sumaiya kawanta suke turancin sai kanne na maza da muke tare suke buga turanci dasu suna jin dadin yadda yaran ke amsa su.
Na dago yana fadin baby ya kike ne kwana biyu bamu hadu ba ya mukaji da hakkurin rashin mama kuma sai lokacin naji wani iri a raina.
Don haka nake da an min maganan mama hankalina sai ya tashi sosai mutuwan ya dawo min sabo a raina.
Mun dan dade a gurin tsaye dasu suka rokeni da dare in basu lokaci su samay ni a gida mu kara gaisawa don nan ido yayi muna yawa akan mu.
Na matsu in bar gurin haka yasa mukai sallama dasu muka wuce zuwa gida inda kannena maza suka bisu kamar yadda suka bukata suyi.
Yalon da muka sayo kasuwa ne nake wankewa a bakin kwatan shiyan umma kanne na suka shigo da leda shake da abin motsa baki suna fadin cikin murna Jamil ne ya saya masu.
Ina kokarin fadin su rage murya kada umma ta jiyo su sai ko gata tafito but daga dakin tana fada cikin hasala wani jamilun din badai na gidan babbaku ba danayi mashi iyaka daku ?
Wanan yaron kamar jikan mayu da bakin naci haka na fada mai na mashi iyaka daku a garin nan Baffa kanina yace umma mu hadiza ne da za a hanamu fita gurin shi.
Dakuwa tayi mai da hannu tana zagin shi tace dama zubin arnan da gare ka dan nema mara kunya ya juya zuwa dakin mu yana bata rai da zagin da tayi mashi din.
Ko kafin in zo dakin na samu ya fitar da kayan yana ci fada na fara mai don may suka karbo mai kayan shi yanzu gashi sun sa umma fada damu haka.
Yace idan ke baki ci ki barmu muci ai ba rokon shi mukayi ba ko tun ina jin haushi har na dauki gwangwanin maltina daya na bude ina kurbawa.
Daidai lokacin umma ta dago labulen dakin tana fadin watau ma bakuji maganata ba ko in kuce kwadai ne ai wurin shi zaku mutu.
An fada maku kauye ana haka ne a banza idan yasa maki asiri a ciki fa garin bakin kwadai ki bishi kamar karya kuwa.
Dan maltinan dana fara sha ne nake kokarin amayarwa don abinda naji umma ta fadi don ina tsoron asiri kamar yadda umma din ta fada.
Kanina yace humm, abin da a gaban mu ya sai muna wani magani zai sa a ciki kuma ni dai tsoron maganan umma ya kamani don haka naki cin komai a cikin kayan suka cinye shi tas suna santi.
Kamar yadda mukai alkawari da su da dare sai gasu sun aiko inzo da yake mai wayau suka aiko sai umma bata san na fita ba har na dawo bata sani ba .
Daddan kalaman shi gare ni sunyi tasiri sosai a raina tun daga wanan ranan muke haduwa duk dare ba tare da kowa ya san da haka ba cikin iyayyena har umma din.
Sai ranan ne ta gane hakan aiko mun sha masifa dan gaba dayan mu ta hade tayi muna tas tare da alkawarin sai ta fada ma mahaifin mu wanan maganan.
Tsoron kada ta fadi yasa na kama kaina kwana biyu don ina matukar tsoron mahaifin mu din tunda ya muna warning akan hakan da dadewa.
Sai dai dadadan kalaman jamil suna min yawo har yanzu a zuciyana sun ki fita min a raina sai nake ganin duk duniya babu mai kaunata da yan uwana irin shi.
Haka yasa alamarin shi yaki fita a raina sam hakana nake samun in dan kebe dashi mu danyi hira sama sama dashi ba tare da an fahunci hakan ba a gida.
Don ita umma tana ganin na fita batun shi a yadda nake nunawa a gabanta gashi dogon hutu muka samu zamu share wurin wata biyu a gida kafin mu koma lokacin ana bada hutu yadda ya kamata ba irin yanzu ba don damana ne.
Jamil dai dan kauye ne amma ya banbanta da mutanen kauyen mu wuein iya tsara kwaliyan shi da shigashin daban yake shi sai dai gajere ne baida wani tsayi sosai irin na wasu maza.
Zan iya cewa ko mu dake abuja bamu fishi iya kwaliya ba don haka yake kamar mace wurin tsara ado da shiga kamar dan wasu manyan mutane can.
Niko irin matan nan ne daba wani kyau gare ni ba can ina dai tsaka tsakiya ne kawai don banda abinda za a zuzuta a gare ni sai dai ilimin kawai da Allah ya bani.
Baba kabiru ya kawo muna ziyara a dan zaman mu na kauyen da mukeyin hutun mu tare da wasu kayan da zamuyu amfani dashi irin sabulun wanka su omo da man shafi sai taliya da idomie daya zo muna dashi.
Kwanan shi daya a tare damu ya koma tare da fadin idan lokacin komawan mu ya matso umma ta sheda mashi da wuri.
Munji dadin kayan dama wanda mahaifin mu ya sai muna ya kusa karewa sai maneji mukeyi dasu kawai gashi bai kara bi ta kan mu ba tunda ya turo mu kauyen.
Kanne na na yawan maganan shi akoda yaushe sai ince dasu aiki ne yayi mashi yawa sun san yadda aikin su yake.
Hakan kan sa su manta da zancen don ko kadan ban bari su shiga damuwa a garin koda yaushe ina tare dasu sai mazab dakan dan fita yawo duk da muma ba wani shamaki akai muna da fita ba kowani lokaci.
Ban san yadda akayi umma tasan da wanan zancen ba na ina kebewa da Jamil ranan ta haukace muna sosai tace ko mutuwa zanyi ba zan auri jamil ba wahal da kaina kawai nakeyi a banza.
Kuma ko bayan ranta mukai aure dashi sai ta taso muna fatalwa ta hana mu zaman lafiya wanan zancen nata ne ya kara tsoratani.
Sai ma na matsu mu koma abuja mu bar garin don samun salama a raina da saukin komai don fitinan ta ya isheni har muka kusa komawa schoool muka fara shirye shiryen komawa abuja.
Duk da muna sa rai zamu koma da umma ne tunda ita ke zaune damu a can dama tun bayan rasuwan mama.
Ashe abin ba haka yake ba don umma ta tace bazata koma wanan gari ba sai dai mahaifin mu ya barmu a nan mu zauna tare da ita din.
Ranan sai ganin baba kabiru mukayi yazo garin sun dade daki da umma dasu baba yushau da baba musa suna tattaunawa akan zancen mu ne ashe.
Bamu dai san yadda akayi ba baba kabiru ya fice da bacin rai yakai dare a garin mun dauka a nan zai kwana sai da yazo sallaman mune yake fada muna tare da wata gwagon mu zamu tafi don haka mu shirya nan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login