Showing 18001 words to 21000 words out of 106121 words
Chapter 7 - kanin Ajali Book Complete by Zee Makawa .txt
hankalina ga karatuna sosai.
Idan na gama zai kaini inyi kararun likita nan gaba kada in sa wasa in bata kurciyana ga banza har sai da nayi hawaye ba tare da ya sani ba.
Lokacin vistinga da yayi ina saka idon zuwan yan gidan mu sai naga sabanin hakan sai babane yazo shi kadai wai sun tafi gida su.
Banji dadin hakan ba amma sai na dake ina addu,an Allah ya dawo dasu lafiya ba karamin sayayya baba yai min ba a lokacin.
Nasan duk cikin tsigar lalashine yasa yai min sayayya haka mai yawa bai jima a gurina ba ya wuce sai dana koma hostel ne nayi kukan tafiyan da sukayi wanan karon ba tare dani ba gida don ban san lokacin da zan tafi ba kuma.
Mun dan jima wanan karon don candy da zamuyi na jinor waec sai da muka gama na dawo gida da kaina don yanzu ina da wayo na zan iya kai kaina gida da school din.
Nayi murna da na samu sun dawo gida suna ta ban labarin gida da wuraren da sukaje ina son in tambaye su labarin Jamil babu daman in tambaya don mama dake falon tare damu.
Da dare na ina shirin kwanciya baffa ya ban takarda wai inji Jamil yace ya kawo min tare da fadin bai bari kowa ya ga takardan ba ya boye min.
Naji dadi sosai ga labarin shi da yake ban yace yanzu yana final year ne a inda yake karatun shi.
Sai dana gama komai mun shige na fito da takardan na karanta gaisuwa ne tare da jaddada min irin kaunar da yake min din naji dadi sosai har cikin raina na samu wuri na boye takarda.
Duk da takardan ya dade a wurin baffa kafin in dawo gida amma bai hana shi kamshin turaren daya zuba a jikin takardan ba daya rubuta.
Na mayar da takardan abin dabe min kewa do duk dare idan zan kwanta zan dauko in karanta in mayar in nuke a inda nake adanawa kada wani ya gani a cikin iyayyena.
Haka rayuwa ya dinga gudana muna jin dadi sosai a gurin mahaifan mu don duk wani abinjin dadi suna muna shi na nuna so da kauna gare mu.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
5/18/21, 11:49 PM - 🤔🤔🤔: 🙆🏼♂️ KANIN AJALI 🙆🏼♂️
7️⃣
ASSALAMU ALAIKUM YAN UWA MUSULMAI DA FATAN MUN WAYI GARI LAFIYA, YAN UWANA LITTAFIN KUDI NE MUJI TSORON SHIGA HAKKIN JUNAN MU DON ALLAH.
MAI FAHINTA ZATA GANE MAI NAKE NUFI ALLAH YASA MU DACE YA KARE MU DAGA DUK WANI ABINKI DAGA SHERIN SHEDAN AMIN ALLAH TA BAMU WUNI MAI ALBARKA, , ,
Wanan dawowa gida ne danayi na samu mahaifina yana gina gida a garin abuja bayan wancan daya gina a garin mu wanda na samu yan gidan mu na ta dokin sabon gidan namu da zamu tare a ciki idan an kare ginan shi .
Yau baba bai fita aiki don haka yana gida bai fito ba tun da safe sai mama ne takan fito jefi jefi ta duba aikin da mukeyi ni da kanwana dake secondry na jeka ka dawo don ita bata je bording school ba.
Acewan mahaifin tayi karama sosai da zuwa makarantar kwana a shekaru ta gama yadda duniya ta koma yanzu babu yarda ta kowani fanni.
Sai wuraren shadaya ya fito daga dakin kwanan shi muna falo muna kallo muka shiga gaidashi da kwana yana amsa muna tare da tambayan mu dalilin rashin zuwan mu islamiya yau.
Nice na bashi amsa da fadin baba ka manta ance mu dinka uniform din makaranta idan bamu dinka ba kada muzo.
Ya juya gurin mahaifiyar mu yana fadin may yasa baki tuna min ba na manta da zancen maganan uniform din nan gaba daya hankalina yana wurin aikin nan yanzu.
Mama tace na tuna maka ai sai dai idan ka mantane amma ko shekaran jiya sai da na tuna ma ai kace kaji.
Yace yana zama saman daya daga cikin kujerun falon yau insha Allahu idan na fita zan biya in saya maku ban son zancen rashin zuwa islamiya sam.
Baffa ne yace da baba din baba idan zaka wurin ginan ka yau zakaje dani daga inda nake nace nima baba ina son zuwa inga wurun ban taba zuwa ba.
Zanje daku yace amma ba yau ba don yau ba zan leka wurin akwai inda zan tafi idan na fita abinci yaci ya gama ya fita inda na mike na kwashe kayan na kai kitchen.
Mama ne na gani zaune tayi shiru yasa na mayar da hankalina wuri ta tare da tambayanta abinda ya samay ta tace dani babu komai .
Ashe aure mahaifin mu ya tarkato zai kara don yanzu ba zai iya zama da mahaifiyar mu ita kadai ba yana ganin yana a cikin lokacin shi.
Kudi yana shigo mai ta ko ina akoda yaushe yadda mukaji labari wai wata yar uwarsu dake kaduna ne tayi mashi hanyar kanwar mijin ta zai aura.
Aure rigirigi har yakai wani lokaci a dan zaman gidan da nakeyi baba ya kwashe mu har mama sai kaduna wai su sada zumunci da matar.
Ran mama ya baci sai dai ba yadda ta iya don kalman zumunci daya fada zasuyi da yar uwarshi din yasa ta hade abinda ke ranta ta biye mashi akaje lafiya aka dawo lafiya.
Ba a dauki wani lokaci ba muka ji labarin ashe har baba ya hade lefe kudi yaba wanan yar uwar tashi ta hada mashi lefe a can.
Shine dalilin saurin ginan da yakeyi don ya samu kafin buki su tare da sabuwar amarya a ciki da yake mama mace ce mai hakkuri duk wanan abin bata yarda ta tada hankalin ta ba akan auren da zai kara din.
Duk dako abin yana taba mata zuciya sosai sai take ganin kamar don yanzu ya samu ne yake son ya kara mata kishiya kamar yadda wasu maza da yawa keyiwa mace.
Don wasu mazan sai su wahala da mace da zaran samu da yalwa yazo masu wanan matar da aka wahala da ita ta zama banza a gare su.
A lokacin zasu fara neman wata wace zasu ji dadin rayuwa a morewa juna ke ko kin zama yar bi sai yadda akayi dake duk da tasan mahaifin mu yana kokari ta fannin kyautata ma iyalin shi din.
Sai da fargaban ta shine bata san sauyin da hakan zai kawo a tsakanin su ba don anyi sau dayawa tana ganin yadda matar gida take komawa sai anyi dace da wace ta san Allah ake zaman lafiya yanzu.
Duk wanan zancen auren da baba keda niyar karawa ba wanda ya sani a cikin yan uwan shi don haka bayan ya hada laifen shi ne.
Yayi shirin zuwa gida don ya sanarwa umma da yan uwanshi zancen auren da yake son ya kara din nan bada jimawa ba.
Umma ta nuna mai rashin jin dadin ta duk ko da yawan fitinan ta da mahaifiyar mu din anan kan umma ta nuna ma mahaifiyar mu gata don tas tayiwa mahaifin mu din.
Sai da ya fadakar da ita abinda yake nufi da auren da yake son ya kara din sannan hankalin umma ya kwanta tayiwa mama nasiha ta kwantar da hankalinta indai tana raye bazata bari a cuta mata ba insha Allahu.
Da haka hankalin mahaifiyar mu ya dan kara kwantawa don umma din data tsaya mata kan zancen tasan abinda ta fada haka yake don diyanta basu fi karfinta har lokacin.
Da haka muka juyo muka dawo sai dai wanan tafiyan banji dasin shi ba don a cikin kwana biyu kawai da mukaje mukayi a gidan.
Gashi ban samu ganin Jamil ba lokacin yana makaranta suna jerabawan karshe na fita secondry school ke nan
Nikan damu da halin da nakan ga mahaifiyar mu a ciki na damuwa wanda nima yakan sani in damu a lokacin har nakan yi tunanen ko laifi mahaifiyar mu tayi mashi da zai kara aure kuma.
Ranan dai sai da yakai na tambaye ta ko laifi mukayi wa baba zai kara aure mama ta dago ta kalle ni raci gaba da ninke kayan wankin da mukayi na kwaso muna a waje.
Tace ba laifi mukai mashi ba ra,ayin shine kawai haka yanzu yaga lokaci yayi da zai kara ne don haka kibar wanan tunanen don ba naki bane a yanzu.
Nan dai mukaci gaba da harkokin mu irin na yara ba tare dana kara bi ta kanta ba kuma, sai dai duk a cikin kwanakin haka nake ganin ta bata walwala idan na tambaye ta sai tace min ba komai.
Na gama girkin rana tana daki na samay ta ina fada mata kai kawai ta gyada min har na juya zan tafi na juyo ina fadin in debo maki ne mama ?
Tace bari idan na fito zanci kidai dibarwa kannen ki suci na amsa mata da to, na fice daga dakin ina kiran kanne na su zo suci abincin.
Bayan na zuba masu ne sai sumaiya ta dawo tana fadin wai na zuba mata miya kadan sai ta kara nace ba zata kara ba.
Muna cikin rikici da ita sai ga mahaifiyar mu fito daga daki tana fadin wai yaya haka ne mai ke faruwa daku ne wai ?
A hasale nake mayar mata da abinda ke faruwa tsakanin mu kallo na tayi tana fadin yar kabiru ki zama mai hakkuri da kannen ki mana.
Ki kara mata mana maye a ciki idan kin kara mata miyan ba akwai sauran miyan a cikin tukunyar ba, kara mata don Allah.
Bayan na kara mata miyan na dawo na zauna ina hasalan dariyan da kaunan nawa take min muryan mamane yasa na dago kai ina kallon ta.
Don cewa tayi keda zaki zama uwar su wata rana tun yanzu, kina nuna masu haka yaushe zasu girmama ki nan gaba kin riga da kin bari sun raina ki ko.
Ki dinga binsu a hankali ki dauki girman ki gare su sai kiga sun koma jin tsoron ki suna daukan maganan ki da muhinmanci sosai ba raini a tsakanin ku.
Nace nagode mama tace ba komai don Allah ki koyi hakkuri da yan uwanki don watan watarana kece dai babban su.
Ta juya gurin da sumaiya ke cin abinci ta fara mata fada mai kamar nasiha ita ma ta nuna mata amfanin girmama na gaba gare ka.
Ba tare da taci abincin ba ta mike don kiran sallah da ake zata je tayi sallah a lokacin na sake fadin mama abincin fa kada yai sanyi kuma ?
Ta juyo a cikin yanayin rashin jin dadi tana fadin barin idar da sallah zan fito inci ta shige daki na bita da kallon tausayawa don na fara fahintar bata da lafiya ne.
Sai dai tana daurewa kada mu fahinci halin da take ciki a lokacin abin yarinta sai ban mai da hankalina ba ga alamarin.
Wasa wasa har yakai mama ga kwanciya asibiti ashe ciki ta samu yake mata wasa bai zauna ba shine take wanan wahalan haka.
Ta sha jiki sosai da kyat ta sha wanan karon jikin bai gama warke mata ba na koma makaranta don jerabawan mu da ya fito sai dai na koma ba a dade ba don na dan jima ban koma ba akao hutu muka dawo gida .
Abinda ya ban mamaki shine tunda na koma ba wanda ya lekoni a gidan mu har dan visting din da mahaifina yakan kawo mun na bazara wanan karon ba wanda ya leko ni .
Sai dai ina shiga gida na samu tashin hankali don na samu mahaifiyata a cikin jin jiki sosai har yafi wanda tayi da farko wahala hankalin mahaifina yana a tashe shine dalilin rashin ganin shi da banyi ba.
Wanan halin da mahaifiyar mu take ciki ya tayar muna da hankali sosai duk da yara kanana ne mu amma mun san mahaifiyar mu tana cikin wani hali mai muni a lokacin.
Nafi kowa shiga tashin hankali a cikin mu don nafi sauran wayau don nice tunda na dawo na koma jinyar mama din don da makwabta da abokan arzikine ke jinyar ta.
Dawowana sai komai ya dawo kaina nice girki nice kula da mahaifiyar mu din ga laluran kanne na wani lokaci nice maiyi masu wani abin.
Da mahaifin mu yaga abin ba sauki sai na Allah dole ya buga waya yana sheda ma baba kabiru halin da mahaifiyata take ciki.
Kwana biyu sai ga baba kabiru da umma da daya daga cikin matan shi sun iso garin hankalin su ya tashi sosai ganin yadda mama ta koma a dan kankanin lokacin.
Sunyi jinyar ta a cikin ikon Allah zuwan su ta dan samu sauki sosai ta dan warke haka yasa na fara shirin komawa makaranta don an koma da dadewa .
Saboda ciwon mama yasa ni ban koma ba do baba yaje ya daukan min permition a makaranta don kada aga na makara da yawa saboda suna daukan mataki sosai.
Bayan tafiyana da sati daya Allah ya karbi ran mama ta tafi da cikin dake jikin ta su umma sun ga tashi hankali don mahaifin mu ya birkice masu shima gaba daya don mutuwan ya taba shi sosai.
Abin mamaki a ranan ne kuma mahaifiyar Jamil ta rasu a can gida sai waya suka samu Allah yayi mata rasuwa itama da yammacin ranan a gida don ita ma tayi dan jiya sai dai ba a sa ran rashinta ba don zazzabi ne tayi na dan kwanaki yazo da ajali.
Ina school ban san wainar da ake toyawa a gida don nasa ran mama taji sauki har su umma kila sun koma gida a lokacin.
Ashe mama bata duniya ta tafi gurin da ba a dawo sai rabon a hadu gobe kiyama idan da rabon haduwa din gare mu Allah yasa mu cika dakyau da imanin ubangijin mu a ran mu Amin.
Nasan wanan shafin zai taba zukatan makaranta da dama don akwai zafi irin wanan mutuwan ka rasa mahaifiya a lokacin da kafi kowa bukatan ta a duniya.
Mama ta tafi tabar baba da nauyin rikon iyalin data bari shine kalman da mahaifin mu ke fada ko wani lokaci yana kuka da hawayen shi na rashinta a tare damu.
Har sunje gida anyi zaman makoki sun kwana biyu a gida suka dawo duk banda labari saboda makaranta da ya boyeni a lokacin.
Mahaifina ya kawo min ziyar sai dai duk da karancin shekaruna naga sauyi a tare dashi don ya ramay yayi baki sosai babu walwala a tare dashi.
Cikin farin ciki da kaguwa na tambaye shi mahaifiyar mu yace taji sauki sosai tana gaishe ni umma fa na tambaya sun koma ne baba ?
Yace umma nanan zaune gida zata kwana biyu a wurin mu kafin ta koma sai dai maman mu ta tafi gida a can zata haihu yace dani.
Ina ta murna maman mu zata haihu ya bani abinda zai bani ya tafi bai dade a gurina ba kamar yana sauri ashe kuka ne yazo mashi a lokacin.
Ina ta fadama abokaina mahaifiyata zata haihu zan gyaiyace buki suna ban address din su tare da layin wayan su idan ta haihu in fada masu.
Har akai hutu baba yazo da kanshi ya dauke ni na isa gida da murna na ko zan samu mama ta haihu a lokacin.
Sai dai ba mama a gidan sai umma da kanne na a gidan suma yanayin su ba dadi a yadda na samay su sai umma ce mai karfin halin taro na da zuwa.
Ni a zatona tunda nace umma mama har yanzu tana gida bata haihu ba naga bata dawo ba sai cewa tayi da sauran lokaci zata dade a can kafin ta dawo.
Na dauka idan ta haihy zamu tafi gida ayi bukin suna damu acan tana ganin ina murna ta shige daki tana kuka tunda nace Allah yasa mama ta haifi mace wanan karon.
Maimakon in ga murna da doki a fuskan kanne na sai bata rai danaga sunayi idan na shiga daki su biyo ni sai umma ta kwala muna kira dole mu fito daga dakin.
Ashe umma bata son su fada min halin da ake cikine sai washe garine bayan mun karya naga mahaifina bai fita aiki ba sai na dauka yana up ne aikin dare zai fita.
Kira ya kwala min ina daki ina gyara na fito da sauri yake ce min tare da nuna min wuri in zauna bayan na samu wuri na zauna ne ya kira sunana.
Na dago kai a hankali na amsa mashi da na,am baba yace magana zamuyi dake ina son ki fahince don ke musulmane ko.
Na daga mashi kai a hankali yace kin san rayuwan mu a gurin Allah yake ko nace eh baba ya ce dakyau yace kin san ko yanzu ko anjima Allah zai iya kiranmu mu koma gare shi ko ?
Sai lokacin na fara jin tashin hankali yana ziyara na don ban son ai min maganan mutuwa ko kadan sai naga umma tana share hawaye da gefen hijjab din ta.
Baba yace kin san kin wuce kin bar mahaifiyar ki bata da lafiya ko da sauri na dago ina fadin eh baba nasani yace to