Showing 1 words to 3000 words out of 105161 words

Chapter 1 - CIRANIN AMANA BOOK COMPLETE BY Asma Baffa .pdf

22 Mar 2025

13413

Compiled by Umar Dalha Funtua.


✳CIRANIN AMANA✳


1-5



By
AsmaBaffa




BISMILLAHI



INA MIKA GODIYATA GA DUBBAN MASOYANA ,DA FATAN ZA KUJI DADIN WANNAN
NOVEL KAMAR YANDA KUKA JI A MA'AIKACIYAR GOMNATI READERS,ALLAH SA A FARA
LAFIYA MU GAMA LAFIYA.




Sanye take cikin wata jemammiyar rigar atamfa ko kugu bata kai ba,ga wani wandon yadi
ja ajijinta dogo,ta nannade kafa daya iya gwiwarta,wata dagargajajjiyar p cap ce a kanta,tafiya
take tana bouncing har wani dinginsa kafa daya takeyi,irin tafiyar nigogi maza takeyi tana shan
kamshi tare da dauke kai sama tana hura hanci,tafiya takeyi tare da sa hannayenta a aljihunta
tana bouncing tare da yin doro tana kwobarewa hadi da budawa.

Bata kula kowa kawai kwana take sha,wata dandazon majalisa ta maza tazo,tana zuwa aka
fara ihu da tafi sai Amana,kallonsu tayi tare da kara kwobarewa tace sai Baba,sa'a dai sa'a dai
tayi Gaba bata kara yin magana ba tafiya kawai takeyi,wani yaro taci karo dashi,sai da ya buya
a lungu yace Maza Mazaje Cike da bala'i ta dago kanta aifa sai ta hango yaron,da gudu yaron
ya zura,ta bishi itama sai da ta kure masa gudu har cikin gidansu yaron ta kamoshi a gaban
Uwarsa ta hau jibgarsa kamar Allah ya aikota,mutane sun taru amma ba Wanda ya riketa
saboda kowa yasan halinta,in tayi fushi ba a iya tsaidata,suna ji suna gani ta farfasawa yaron
nan jiki sannan ta gyara p cap dinta sosai ta da kyar take gani tsabar janyo hular da tayi, gaba
tayi tare da bouncing,ta kusa zuwa kofar fita daga gidan tayi tsalle tayi ball da wani baho da ta
gani a hanyar kofar fita daga gidan sai da bahon yayi raga raga,sai da ta fita ta bar gidan

sannan mutane suka sami bakin tsine mata tare da Allah wadai da zuriyar Gidan baki gaba
dayansu,kowa da abinda yake fada akan wannan matashiya da sauran yan uwata tare da
iyayensu.

Har kofar wani gidan kasa tazo kato da alama shine gidansu,Babanta ta gani a waje tare da
mutane a kofar gidan Sallama tayi musu tare da cewa Allah barmana Baba,sai me gida wlh,tayi
cikin gida,da wani gurjejen namiji ta hadu da gani katon dan Wiwi ne,lips dinsa sun nuna da
tafin hannunsa,cije baki yayi tare da karkace shi gefe,ke dan Uwarki daga Ina haka?hannayenta
biyu a Aljihunta tana hura hanci tare da ja baya,ta kara yin doro tace kafa ja girmanka
Hamza,dan zan iya takeshi kasan da wa kake magana dan tsab zan Zagi Amarya
uwarka,kasan Halina ko?

Jinjina kai Hamza yayi tare da cewa zan tattakaki in bakiyi hankali ba,bani da mutunci,to ni
din an fada ma mutuncin gareni cewar Wacce aka Kira da Amana.tsaki taja tare da banke
Hamza tayi cikin gida,tana shiga Ashar ce take tashi a gidan ana ta dambe tsakanin yan mata
gidan, Iyayensu ma sai dirko ashar sukewa junansu,ruwan Ashariya kala kala ce ke tashi a
gidan,nan take ran Amana ya baci ko kallonsu batayi ba ta wuce cikin dagargajejen
dakinsu,Wanda yake daf da ruftowa.

Sallamar megidan sukaji da alama shine babansu,shima Ashariya ya Shiga dannawa yaran
tare da iyayen su hade da kallon wata yar yarinya bata wuce 7yrs tana gatsine da harara yace
tafi can shegiya da kai kamar kuda,kallon sauran matan nasa yayi da yaransa maza da mata
yace wacce bata fasa ba taci ubanta shegu tsinannu,tambadaddu,bakin da aka sauka a gidan
ne suka fito daga masaukin da aka basu suna bada hakuri,
Matan ne sukayo kan bakin da masifa kamar zasu cinyesu da zagi na tashin hankali.

Me gidan ne yayi tsalle ya dire yace kar tsinanniyar data kara zagar min bakina,bakin
Alkhairi,dole kuma na dinga saukar baki a gidana,wlh babu yar wata katuwa da ta isa ta taka
min birki.
Wata ce a cikin matan nasa tace tambadadden dan iska dama dole kace haka
munafuki,Allah ya isa duk ka tarwatsa mana yara,ka lalatasu,dayar ma tace an dai ji kunya
kwarton Banza,wata tsohuwa ce tukuf itama ta fito tana ba kwarto bane yaro na,kar ku kara
zagar min da shegu jarababbu,haihuwar Asara. Watace ta zaburo itama a cikin matan ta nuna me gidan,tace ga tsohon haihuwar asara
kwarto maci amana.Amana ce ta fito daga dakin tana budawa tare yiwa mutan gidan kallon
banza,tace kuna yawa fa,kuna da matsala,dan Allah ku rufe mana baki wlh ko yanzu ayi abin
kunya a nan wajen nan ko Baku gane bane eh?
Me gidan yace yawa Yar Amanata kiyi maganinsu,sai Baba kaima fa Baba kana da Matsala
fa,ka dinga kiyayewa duk kabi ka jona mana masifa da irin abinda kakeyi a gari.

Baba ne ya kalleta zaki ci Ubanki kema shegiya me suffar maza,jibi yanda kikeyi, wa zaki

samu ya aureki haka? Shi yasa baki da mashinshini,kinyi kwantai anyiwa kannenki aure ke kina
shirme a gari,
Cike da takaici ta kalli kanta tare da sa hannu daya a Aljihu tare da cewa Baba ni ba gudun
maganarka nakeyi ba,bana tsoronku ku kanku kun sani,kawai biyayya nake ma amma dole a
fadama gaskiya ka gane Tsoho kana yawa wlh,wannan abin da kakeyi ba me kyau bane,shi
yasa muka lalace,dole na fada ma gaskiya,ka gyara badan mu ba ko dan Allah kaji tsoronsa. Rufe min baki shashasha ubanki nakeyi? Hmmm Allah baka Hakuri Baba nasan yanzu zaka
iya tsine min.
Ta inda kikafi yan uwanki hankali kenan akwai biyayya ga iyaye,ga sallah akan lokaci,cewar
Baba Dariya amana tayi kadan tare da fadin Allah barmana Baba,ammafa Baba Allah shirya
mana kai.ki kiyayeni Amana cewar Baba,sorry Baba Amana ta fadi,
Baba yau ba dan tsire ne?cewar Amana, Babane ya watsa mata harara tare da cewa
ubanwa zai sai miki tsire maganin me kike min a gidan nan,ke ba saurayi ba bare nasa rai zan
samu kudi,tafi kiban waje shashasha.bouncing ta kama yi tare da kwobarewa tana kunkuni,wofi
banza da baki kamar gidan tsutsa cewar Baffa.Anayin kiran sallar Magriba Amanace ta Riga
kowa yin Alwala da Sallah a gidan.

Ummanta tana zaune tana tace gasarar kokon siyarwa na safe,bata da niyyar tashi tayi
Sallah,Amana ta kalleta a hankali sannan tace Ummammu Anyi fa Sallah ni halina dake kenan
wlh anata ta Sallah ke baki da Niyyar tashi,
Wacce aka kira da Umma ce ta daure fuska ke jarababbiya sauraramin,niba uwarki bace zaki
dinga gaya min magana inda kika ga dama?,ko ni sa'ar ubankice,har ni zakiyiwa wa'azi kamar
kanwar uwarki,sai da safe ki taso sakalo sakalo na sammiki koko,kin dauki aikin banza a
kanki,kin rasa me sonki tallanma kinki yi kince ke boko zakiyi ayi mugani ai duniya ce, Haba Umma daga cewa kiyi sallah shine kike min baki?kin San ma'anar duniya ce,ku gidan
nan Baku da aiki sai zage zage,duk kun gama kwashe mana Albarka,taya zamu samu
miji,kuma boko tun daga primary waye yake daukan nauyina?itacen kara nake yowa a kauyen
nan haka gashi har ina ss2,ai abin ku jinjina minne amm kullum kunfi so kuga na shiga duniya
dan na samo muku kudi haba Umma,ya kike haka ai gwara idan bake kika haifeni ba ki fada
min nasan matsayana tun wuri.
Ke tashi ki bani waje jakar banza.wani bakin cikine ya cika zuciyar Amana,Sam basuyi dacen
iyaye ba,yo ni da za a dinga min fada wani ciyar dani akeyi?sutura ake min ko sabulun wanki
bare na wanka ba ayi mana a gidan nan,kuma sai a bimu da zagi nifa bazan dauka ba cewar
Amana tare da ficewa daga gidan.
kowa a gidansu babu na gari a cikinsu,gaskiya Allah kawo min sanadiyar tafiya Cirani na yi
wajen kudu,na huta kawai da bala'in gidan nan,Allah sa Baba ya turani cirani nima irin su
Hamza na tafi na huta da masifar gidan nan.

Wannan wanne gidane kenan,da alama babu me tarbiyya a gidan kaf. bari muji tarihinsa.


GIDAN BAKI kenan gidane Wanda me Gidan yake saukar mutane Baki idan sunzo gari suna

Neman masauki sai ya saukesu amma iya mata banda maza,baya saukar maza a
gidansa,shine dalilin da ake kiran da gidan Gidan Baki.
Gidane Wanda yake cike Da mata da maza.da yan gidan da kuma baki iya mata amma.

Baba me gidan shine Sulemanu Harka dan Asalin kauyen Albasune LGA ne dake Kano
state,Amma aikin gini yasa ya koma garin Wudil da zama,Babar Sulemanu Harka wato Ille ta
haifi yara kanne da Yayyen Sulemanu harka amma duk su nutsatsune suna zaune a can
kauyen Albasu lafiya da iyalensu yayinda Sulemanu ya dauke Uwarsu wato Ille,saboda tana
sana'ar soya kosai sai wayo yake mata tana ciyar masa gida da kudin da take nema,.

Ille ita kanta tasan Sulemanu Harka ba mutumin kirki bane amma ba yanda ta iya dashi,haka
take Sana'a tana ciyar masa da iyalensa,
Sulemanu Harka matansa 4 Haule itace ta farko ana ce mata Goggo,yaranta 10 Maza 4 mata
6 Safiyya itace Babar Amana suna kiranta Umma, yaranta Uku maza 2 mace 1 Amana.
Laure Hajiya kenan ta uku yaranta 5 Maza 3mata ,
Sai Raliya Amarya tana da yara 8 maza manya 4 sai mata ma 4.gaba daya yaransa 25 kusan
mata 4 kacal akayiwa aure, matan suna gidajen mazajensu a kauyen Albasu wasu a garin
Albasun,
Saura mata da yawa suna a gidan ciki harda Amana,maza kuwa ba wanda yayi aure cikinsu
kawai iya shege sukeyi a garin, Sulemanu Harka sana'ar gini yakeyi sosai tun yana da kuriciya
har ya girma yayi yara magina.baya taimakawa iyalansa da kwandala sai matan banza,Sai
kuma yaci me kyau a waje yasha me kyau,ga sutura me kyau,sai ka Rantse Sulemanu ba a
gidan kasa yake kwana ba,
Yaransa duk ba munana suna da kyansu,Amana tafi kowa kyau a gidan sai dai wasu su fita
haske shima da kadan don itama fara ce Amana.

Talakane na karshen karshe,saboda ko ya samu baya tsinana komai ga iyalinsa,sai dai yaci
tsire da kudin,domin kullum yana gaban tukubar me nama,gidansa kuwa ko masara ya kasa
siya musu ko wacce Sana'a takeyi tana ci da kanta da yaranta,Sulemanu Harka gawurtaccen
dan Neman matane,kaf kauyen da wasu garuruwan sun sanshi,shi yasa idan yaji baki mata to
shi zai basu masauki yana zagawa wajensu.

Bashi da Amana,ko yarinya ka kawota gidansa riko sai ya ci amana ya lalata ta karfi,haka
baki wasu su gudu wasu su tsaya su sha harka,yaransa ma sunsha kama Baba da
mata,matansa har fakonsa sukeyi idan dare yayi,sabo da ko yar uwar matansa ne sukazo sai
ya zaga wajensu ya kwashi Harka, Bashi da abokin da ya wuce limamin garin domin halinsu daya,
Sulemanu Harka ko yarsa kaje nema idan baka da kudi to bazai baka yarsa ba,kuma idan
kana zuwa zance wurin yarsa to sai ya dinga rokonka kudi,haka gaba daya sai Allah ya bashi
yara gaba daya tantirai,Amana ce ta gari a hakan lol kaf gidan babu me nutsuwar Amana a
hakan. Mazan gaba daya wasu barayine,wasu yan wiwi,wasu yan Neman mata, domin suma suna
lallabawa wajen baki masu sauka,na gidan aure ma ko wacce da rashin mutuncin da take

shukawa a gidan mijinta,kullum a kawo kara da Sulhun yaran Sulemanu Harka ake,babu na ciki
babu ga na wajen,kowa da halinsa,
Su Kansu yaran sun San basuyi dacen iyaye ba,su kuma iyayensu mata matsalarsu rowa,
zagi da tsinuwa kala kala,sun gama raina mijinsu saboda ya zubar da mutuncinsa.a cikin labari
zaku ci gaba da jin Halin kowa a Gidan Baki.

Amana kyakyawar yarinyace ta kwatance fara ce Amma ba kar ba,doguwace ga shape,duk
inda kake neman diri to kazo wajen Amana, shekarunta 18 going to 19, gashine da ita ya wuce
kafada kadan baki wuluk,gata da idanu dara dara masu tsananin kyau,gashin gira dumbul
dashi,dan bakin nan cut,lips light pink,hancinta dan dai dai bai cika tsini ba kuma ba gajere
ba,ga dimple idan tana magana bare tazo yin dariya,hakora yar yar dasu kar kar,saboda kullum
cikin yin aswaki take ko yaushe,skin dinta me laushin gaske, gata da tsafta ba laifi.

Amana yarinyace me son al'adun maza,haka take tun tana karama rayuwarta da maza
takeyi,shi yasa kaf garin wudil bata da kawa mace ko daya, sai Maza,bata da mutunci ko kadan
idan ka shiga safgarta,ko uban waye komai girmansa,macece me karfi da zafin nama,ga juriya
da taurin rai,idan fada ya hadaku tofa sai dai a mutu bata ji ba ta gani,idan ta fara dukan mutum
sai ta gaji da kanta,kowa daya Santa tsoronta akeji ko a gidansu Amana sarauniyace dan ko
waye bai is a ba,iyayenta kawai take dagawa kafa,
Ba wani abu na nafeela takeyi ba amma duk farilla tana cikawa,Sallah bata wuceta duk inda
take,gata da son ilmi,gidansu ba a sasu a islamiyya bare boko amma har gona take zuwa tayo
ciyawa ko kara ts siyar ta sayi littafan schl,haka ta gama primary yanzu tana ss2 a wata
government schl ta garin,duk da ba wani turanci ta iya ba amma tana iya karantawa,haka
islamiyya ma,tana da haddar izu 30 ga wasu littatafan tayi,duk gidan ita kadaice take zuwa
schl,har yaran gidan sabo da tsoron Amana da sukeji take korasu makarantar Allo dolensu suke
zuwa,

Kuma idan baka kawo mata haddar karatun ba sai ta farfasawa yaro jiki,ba ruwanta don kaninta
har kashi ta tsaga masa garin duka bai iya karatu ba,har yayyenta tsoronta sukeyi sun san
karfin Amana,ba mutunci ba daga kafa,shi yasa a gidan ita kadai ce take sa doka kuma dole abi
dokar,
duk masifar Amana bata yi a schl tunda wani malami ya kusa korarta daga schl din gaba daya
sai ta daina komai da take musu,sai kadan kadan takeyi, domin tunda ta fara schl take jibgar
dalibai,tare da karya kafafun yaran mutane,domin har malami cin kwalarsa takeyi ta fesa masa
mari, Gata da kokari da tsafta,shi yasa aka bata head girl,tunda aka bata mukami idan yaro yayi late
sukaganta a gate juyawa sukeyi gida sabo da sun San dole sai ta fasa ma jiki,ta gagari
malaman bare abi wa yaro hakkinsa,

Amana yar rigima ce sosai,tunda aka haifeta Ummanta ta zabi wannan suna Amana aka
radawa yarta,wajen aiki kuwa ta iya girki kala kala domin Amana har wajen wata Bilkisa me
tuwo tuwo take zuwa tana tayata girki ta bata kudi,dasu take biyan bukatunta da dama,

Amana Ummanta bata da halin kirki,ga son kudi,bata iya taimakawa yaranta da ko
kwandala,kowa yaro da babba dake gidan Sulemanu Harka Neman na kansa yakeyi,kowa ta
kansa yakeyi babu me taimakon wani da ko kwandala,gwara Amana tana bawa babanta wani
abun idan ya rasa,har su Hamza takan sai musu kokon safe watarana,sabo da Amana ta fisu
zafin nema,ba ruwanta kullum cikin Neman hanyar samu take,kuma in taje neman aiki wajenka
tofa dole ne ka bata aiki tayi ma,kuma sai ka biyata dai dai da guminta, sauran yan matan da
basuyi aure ba maza suke damfara da yaudara su sami kudin sabulu da sauran kayan sawa,shi
yasa suka fi Amana sutura da yawa,sabo da Amana bata da saurayi sai abokai,bata da kayan
sawa,atamfarta kodaddu kala 2ne sai tsimmokaran da take sawa,suma wasu wandon duk na su
Hamza ne da kannenta,take dauka idan zasu jefar sai ta karba ta wanke taci gaba da sawa
tana hadawa da rigar atamfa,Ummanta tana Sana'a tana samun kudi amma sisi bata iya bawa
Amana,hatta kokon Safe sai dai Amana ta siya, idan ba kudi ta tafi wajen abokanta maza ta
samu,amma tana bawa kannen Amana Maza,basa shiri da Amana da Ummanta sabo da
Umman Amana tafiso Amana ta dinga damfarar maza tana samo musu kudi,amma Amana taki
yarda kuma bata da me sonta.

Shi yasa Amana tace abokai maza sunfi mata muhimmanci,ga kyauta,gashi basu fiye gulma
da hassada irin ta mata ba,Namiji ko ya kuke mutunci zaka moreshi,sabanin mata da yawa sai
su dinga yi ma hassada ma,idan sunga ka fisu sai gulma da bakin ciki.
Yawan Hulda da Maza yasa Amana takeyin acting din maza, sauran yan uwanta duk Suna
Neman mata,matan ma sabo da son kudi Neman maza sukeyi,Amana ce kadai cikinsu Bata ma
da saurayi bare ma ya taba jikinta,kuma mazan da take Hulda dasu tsoron jarabar Amana
sukeyi ko yatsanta basa rikewa.
Ci gaban labari

Amana ce ta tashi da asuba tayi Sallah sannan ta fito wajen Ummanta dake gaban murhu
zata dama kokon siyarwa,naira ashirin Amana ta mika mata ba wata gaisuwa ba komai,duk
dama gidansu haka suke ba a gaishe da kowa,ungo wannan kudin Umma a bani koko damun
farko nake bukata kuma yaji gaya a dauraye masa kai da gasara sosai,karba Umman tayi ba
kunya tace kawo robarki,tana kwobarewa da takama ta mika mata,koko na a

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login