Showing 24001 words to 27000 words out of 105161 words

Chapter 9 - CIRANIN AMANA BOOK COMPLETE BY Asma Baffa .pdf

22 Mar 2025

13428



Godiya me tarin yawa gareku fans dina.



AsmaBaffa
[6/27, 9:25 PM] +234 808 968 1079: ✳CIRANIN AMANA✳


50-55



By
AsmaBaffa





Wurin wani hadadden park Amana ta kai Aabid wuraren wasan yara,sosai Aabid yaji dadi
sai murna yakeyi tare da zubawa Anty Amana surutu, hadadden resturant ta kaisu sukayi ciye
ciyensu,ko ina Amana ta gifta sai an kalli motar,
Ga wani hadadden tuki da takeyi,shopping mall ta shiga Aabid ta kwasarwa kayan zaki,da
wasu kayan sport,schl bag new design,dasu canvas da tarkacen dai makaranta,wasu panties
Na maza 3qtrs da riguna duk ta siyawa Aabid, Wasu singlet ta gani na maza latest masu tsadar
gaske da boxers,Kudin ta ebo dungurugun ta siyawa Alim boxers guda biyar singlet biyar,ita
kuwa kayan make up ta siya da turaruka masu saukin kudi,

Sai takalmi guda biyu da ta siya,da wasu sabuwar pcap guda biyu, ice cream ta jidar musu
sannan ta je can wurin da Alim ke siyo nama,wato wajen manager inda ta taba yin aiki,sai
mamaki sukeyi yanda suka ga Amana ta kara gogewa ta kara haske da kiba,ga wata shegiyar
mota da tazo da ita,sun zata Amana ce tayi kudi,nama ta siya ta wuce gida,8pm suka shigo

gidan,ko kayan basu ebo ba ta ja Aabid room dinta sallah sukayi da wanka suka canja kaya
marasa nauyi,sannan ta riko hannun Aabid suka kwaso kayan gaba daya har part din
Alim,lokacin 8:30pm suka sami Alim a Palo yana zaman jiransu da tunanin ina suka tafi haka
tun 5pm,
Ganinsu yayi da kaya niki Niki,a gabansa suka ajiye komai,a hankali yace dama kun Dade
da dawowa?Aabid yace Daddy wanka mukayi da sallah,

Kayan Amana ta fara budewa ta nunawa Alim kayan Aabid gaskiya shi kanshi sun birgeshi
ta iya zaben kaya,jawo wata ledar tayi ta nuna masa nata,sai yayi mamaki nata ko kayan make
up din ma ba masu tsada bane,ba wani abu special da ta siyawa kanta,daya ledar kuwa mika
wa Alim tayi Master kalli naka,Alim yaso gwasaleta amma yayi tunanin hakan ba dadi ayi ma
abin kirki kaki yabawa,karba yayi ya duba,komai size dinsa kuma ta siyi masu tsada,
Gasu best Color nasa komai white,

Thnx ya furta a hankali,ledarta ya kalla yace amma wannan shirme kika kwasowa kanki kika
dawo,next time ki kiyaye in ba haka ba baza ki kara zuwa ba,ok master cewar Amana.
Alim yace aransa jibeta kamar ta kirki yanzu kaji ana dambe da ita,kayan zakinsu ta diba tace
Aabid baka shan wannan yau sai watarana watarana,idan ana shan zaki hakora mutuwa sukeyi
su fara ciwo,mata iyaye a kiyaye za kuga yanzu yaro zaije schl sai a sa masa lemon kwali da
biscuit a jaka kayan break,ba kudi bane,ba birgewa bace,ba kuma gata da tarbiya bace,saboda
illa zai masa hakoransa su mutu da wuri,ko ya fara ciwon hakori tun yana yaro,gwara ki bashi
ashirin ya siyi aya,ko taura,tsamiyar biri etc yanda akeyi da,ko ki dafa musu abinci me kyau yafi
wannan kayan zakin.a kiyaye pls.

Kwashe kayan tayi ta boye icecream biyu da nama da drinks kawai ta bari,kitchen ta koma ta
dauko su plate etc ta bude ta ebi nata Dana Aabid ta zubawa Alim shima

Alim a ransa yace to yau abincinmu kenan,ci yayi sosai yana kora drink yasha icecream
kadan ya mika musu abinsu yana kallonsu suna ta cin nasu suma.

News Alim ke ta kalla Amana ta matsu a canja tashar ball amma shuru gajiya tayi tacewa
Aabid tashi muje muyi baccinmu,ko kallonsu Alim baiyi ba har suka sauka suka bacewa
ganinsa,
Washe gari Sunday da 9pm Alim ya kira Amana ya mika mata schl Uniform irin Na
makarantar su Aabid green and white,ba hijab sai hula da mata ke sawa,Riga da skert,skert din
irin da kadan ya wuce gwiwa abinka da lagos,
Kayan har kala biyar,sandal dasu canvas,schl bags,littafai komai ya mika mata,yace kuma Ss1
suka baki ba ss2 ba,
Murna wajen Amana ba a magana hakan ma Na gode master,Allah ya biya bukatunka ya kara
buda maka,
Gobe sai kiyi shiri idan kinje office din pc zakije,wani card ya mika mata yace ki bashi wannan
cewar Alim,karba Amana tayi tana ta murna.

Washe gari kuwa da sassafe ta shirya ta shirya Aabid cikin uniform ba karamin kyau
Amana tayi ba, already ta hada breakfast,cin nasu sukayi suka barwa Alim nasa, brush suka
karayi suka gyara sannan suka je wajen Alim dake zaune a palonsa,

Gaisar dashi sukayi sai kallon Amana yakeyi yanda ta hade a uniform,key din mota ya mika
mata gashi kin iya driving ai no need driver ya tukaku,ki kiyaye ban son ayi tukin ganganci da
Aabid dina.
Murmushi kawai Amana tayi ta rike hannun Aabid suka fito compound,ba motar jiya da ta
tuka bace,wata motarce har tafi ta jiya kyau da tsada,
Ma'aikata kamar idonsu zai fado ganin Amana a uniform wato matsayinta har oga ya sata a
schl,kuma a schl dinma me tsadar gaske irin ta dansa,ga motoci ko wacce hawa takeyi,mazan
gaba daya murna suke taya Amana,matan kuwa bakin ciki kamar su kasheta haka sukaji,

Amana tana kallonsu suna shiga motar tayi wani tuki Na yan tasha ta fice daga gidan,Alim
yana kallonta ta window,bai San sanda ya saki murmushi ba,tare da furta yarinyar nan bata ji ko
Kadan

Tunda Amana ta cinna hancin motar schl ake ta faman kallonsu,an zata yar gidan wani
shegen me kudice tazo da kaninta,kowa driver ke kawo su amma Amana ita ke tukin gasu daga
Amana har Aabid masu kyau ne,kalar naira da Hutu,saida takai Aabid har class sannan ta wuce
office din PC ta bashi card, ya kaita har ss1A tafiyar da Amana takeyi cike da gadara da takama
tana cin magani an dauka Naira ce ta hudata,basu San Amana tun tana kauye haka take ba.
Kafin kace me duk mazan Ajin sun saba da Amana,matan kuwa ko kallonsu bata yi,break aka
kada anje restaurant Na schl cin abinci,Amana duk yan aji maza da mata sai da ta raba musu
maltina kowa daya daya,nan da nan schl ta dauka wata yar gidan wani kusace Amana

Har class din su Aabid taje ta daukoshi ta bashi abinci da kanta Amana tana mugun kaunar
Aabid bata son abinda zai bata masa rai,Aabid kuwa yanzu ya daina tsokana da ciwa mutane
mutunci ya nutsu sosai,gashi Aabid yafi ma Alim haske ka rantse baturene,shi yasa yake da
farin jini. Amana har malamai take kaiwa drinks kyauta,kwananta 3 da fara schl amma har ta zama
popular, kuma ba laifi tana da kokarinta,amma Amana tafi iya mathts duk wani abu Na
calculation to Amana ta sanshi ta iya gifted ce,

Matan schl din tsinewa Amana sukeyi bata da mutunci bata kula kowa sai maza,guda dayace
yar ajin su Amana wata Rufaida ita kadai ce suke magana da Amana sabo da Rufaida tana son
Amana haka kawai,shi yasa ta nacewa Amana tun bata kulata har ta fara kulata.

Shi kanshi Alim dadi yakeji yanda yaga Amana Na kula da Aabid,ga Aabid sai kiba yakeyi
yanzu kuma yayi hankali sosai.dan haka Amana ta kara daraja da kima a idonsa,Amana kuwa a
schl kullum sai anyi fada da ita a schl,gashi ba a daukan mataki a kanta sabo da ta siye kowa
da kyaututtukanta.

Kamar kullum Amana ta fito da mota ita da Aabid zasu je schl ta ware mota tana fella
gudu,wata rantsantsiyar mota ta gani ta parker wata kyakyawar dattijuwa ajin farko ta fito daga
bayan motar tana yanga da takama tazo zata tsallaka titi tana ganin mota amma sabo da
takama irin ta wannan dattijuwa kawai ta hau titi tana tsaida wata mata,Amana ta Riga ta kawo
da mota da kyar ta iya take birki amma duk da haka sai da ta bigi dattijuwar nan kadan a
kafa,matar ta fadi wanwar,Amana da sauri ta gangare tazo tana yiwa matar sannu tana bata
hakuri,matar ta rigada ta rude sosai bata gane wace kawai murya takeji,
Masifa ta fara yiwa Amana dalla matsa dabba yar talakawa matsiyata,sai faman ashar matar
nan takeyi Amana Na bata hakuri amma matar nan cewa take wlh iyayenki ma sai sunyi
nadamar haihuwar ki,sai Na batar dasu.

Amana haushi taji kawai ta take motar ta suka tafi schl,ta bar matar nata masifa da zage
zage,da kyar driver da wannan kawar tata da take kokarin zuwa wajenta suka sata a mota suka
kaita asibiti aka dan duba lfyrta suka dawo gida,matar kawai tunani takeyi a ina zata ga yarin
yar nan da ta kadeta taci ubanta har iyayenta,gashi ko ta ganta baza ta gane ta ba tana rude
bata ga fuskar yarinyar ba,amma zata gane muryar,motar ta tuna sai taga kamar tasan
motar,kamar motar Alim danta,amma me zai kawo wata ta hau kai ba ta Alim bace amma taci
alwashin nemo Amana dan ubanta,wannan dattijuwa ba kowa bace face Mum din Alim.
Amana kuwa mamakin irin masifar matar takeyi,bayan sun tashi daga schl saloon ta wuce
aka gyara mata gashinta wannan karan kasan gashin tasa aka canjawa kala y koma yellow fari
fari,sama kuma baki,kaji turawa an waye a lagos.

Aabid ma anma masa wani kala ya kalli sama ka rantse bature ne,dama Aabid gashin
turawa gareshi yellow ba black ba,
Amana har islamiyya Saturday Sunday tana zuwa yanzu,Alim tunda yaga gyaran gashin
Amana yake mamakinta kamar wata baturiya wayewar tayi yawa,na Aabid kuwa ai kasa
magana ma yayi ya rabu dasu kawai,.
Suna zaune a palon kasa, Baban Amana ya kirata a waya,dagawa tayi da sauri tare da cewa
Allah bar mana me gida sai Baba,ya kowa da kowa,alhmdlh cewar Baban Amana sannan yaci
gaba bakya nemanmu ko, haba Baba ka daina irin wannan kasan ina ji dai kai fa cewar Amana,
Baba a gaishe da Umma kace gobe zan kirata pls,Baba hope dai ka daina abin nan da kakeyi
?Allah Baba shi yasa naki zuwa Na ganku ga kudi ina samu.

Baban Amana yaji Amana tace tayi kudi sai murna ta kamashi bai damu da abinda Amana
tace ba kawai ya fara haba yar Amanata yaushe zakizo Na ganki yanzu Allah ya kusa shiryata
ai Amanata,zan hadaki da Ummanki,Umman Amana dake gefe taji ance Amana tayi kudi caraf
ta kwace tace Amana yata yaushe zan ganki dan Allah kizo mu ganki,ki siyo min doya da
manja,ki taho min da garin kwaki dan lagos,ki tahowa da kannenki kwakwar manja,da ashobe
Na yarabawa zan dinga zuwa biki,
Baba ne ya kwace wayar daga hannu Umma yana harararta tare da cewa matsa banza
kwadayayya,yace Amanata Nima ki siyo min leshi dinkin buba zanyi Na yarabawa maza,ki siyo
wa Haladu 3qutr Na maza,ga kannenki su Badariya ko T-shirt ki siyo musu kinji,

Matan gidan da yara duk sun rude kowa yana Anty Amana ki kawo min ayaba da lemo,wasu
suce naman kaza,wasu suce yohourt,Badariya yan mata kanwar Amana me ji da kanta da
tashen fitsara ita ta fisge wayar daga hannun Baba tace ke Amana ni Apple zaki siyo min kin
San ni ba kalar kauye bace,amma Baba yana wani wai ki kawo min T-shirt yo Allah Na tuba
T-shirt ko ta su Badaru ai Na sa,kin San Baba dan kauye ne wlh,

Zanci Uwarki Badariya Jakar banza dan Ubanki Babane dan kauyen?mahaifinkine fa Allah
ya kamaki shegu marasa tarbiya cewar Amana,Badariya ma ta cikin waya tace Badai ni ba kece
shegiya wlh,su iyayen namu da kike tarewa Ubanme suka tsinana ma,komai mu mukewa
kanmu,ba makaranta hattana sabulun wanki mu ke siya,sannan kuma muyi musu
biyayya,Amana tace ke Iyayenmune fa dole mu duba darajarsu garemu,kuma dole mu bisu ko
me sukayi mana,iyaye iyayene wlh amma Badariya kodai kina Jan hayakine?
Tun yaushe kuma Amana ai har wiwi ja nakeyi cewar Badariya,shuru Amana tayi.

Badariya tace ke Amana anfa kama Isa yana police station ya saci akuyar gidan shehu me
alewa,Zahrau kuma ta cirewa wani yatsa daya ana ta rigima,Goggo uwar gida ita ta karbi wayar
tace Amana ni ayabar da ake soyawa zaki kawo min,Amana tace oh Goggo plantain? Eh
yawwa inji goggo.to shike nan sai mun kara magana kitt Amana ta kashe waya tare da dafe kai
tana maida numfashi.

Sun dameta da surutu kowa nata shirme,tsaki taja a fili tace gidanmu gidanmu baza su taba
canjawa ba,hannu ta daga sama tace ya Rab gamu gareka,
Kyalkyalkyal taji dariyar Alim da Aabid har sun tuntsuro kasa sabo da dariyar kauyancin yan
gidan su Amana,juyowa Amana tayi taga yanda Alim yake sheka dariya sosai dimple dinshi sun
lotsa yayi mugun kyau,
Sakin baki tayi tana kallonsu,ita ta manta Alim yana wajen gashi wayar a handsfree ta sata,
Tsayawa tayi ta shagala tana ta faman kallon dan bakin Alim da hakoransa yar yar ga dariyar
tayi masa mugun kyau,

Saida suka gaji da dariyar suka tsaya Alim yace no wonder kike haka,Ashe a hakan kamar
ma kece wayayya nutsatsiya a gidanku,wlh Na kusa zuwa kano kece driver komai za a siya
musu kar ki damu,nan ya kara sakin dariya,

Amana takaici ya kamata za a raina mata dangi da iyaye a masifance tace don't go there pls
dan billahillazi ka zagi iyayena sai nayi butar malam da kai,kai akan iyayena zan iya karyaka,ka
San me zaka fada min bana daukan wulakanci gwara ka koreni,dan kana da kudi muma haka
Allah yaso ganinmu ehe, Aabid ne ya matso kusa da ita zai riketa da sauri ta hankadashi baya ya fadi tim,ta zare masa
ido kai ni zaka yiwa dariya a haife Na haifeka takalminta ta cire ta Zane duwawun Aabid dashi,

Sai kuka yakeyi yana bata hakuri,Alim yana gefe yana kallonsu yace kinji kunya your Boy kike
duka yau,da sauri ta jefar da takalmin ta rungume Aabid tana lallashi,Mum Alim wacce ke labe

jikin kofa tana kallon komai akan idonta,banko kofar dakin tayi da karfin gaske.


AsmaBaffa
[6/27, 9:25 PM] +234 808 968 1079: ✳CIRANIN AMANA✳



55-60




By
AsmaBaffa





Mum Alim tana muzurai zata fara masifa tare da bin Amana da wani mugun kallon
tsana,amma shigar Amana ta bata mamaki,domin Amana bata sa uniform din yan aikin Alim
ba,kayan sawarta ne Na swagg a jikinta,Wani tunanin mugunta ne ya darsu a zuciyar Mum Alim
nan take ta saki fuska da fara'a tace Alim wannan yarinyar fa? Alim yace Mum me kula da
Aabid ce,ya ban ganta da uniform ba? Yanzu ta cire Mum,Aabid kuma me yayi mata take
dukansa?tsokanarta yayi Mum,hmm ba a haka yarinya me raino da hakuri akasanshi,
Alim ne ya kyaftawa Amana ido wai ta gaisar da Mum,da sauri Amana tace Mum An yini
lfy?hmm haka ake gaisar da manya a garinku?Baki da tarbiya ne? Amana tana zumburo baki
tace sorry fa Ina kwana,
Mum ce tace hmm yanzu ai yamma ce,to ina yini?lfy cewar Mum tare da tabe baki,

Amana kuwa sarai ta gane masifaffiyar matar da ta kade ce a titi,itama Mum ta gane Amanace
ta kade ta,shi yasa ta kulla mugunta a ranta,
A fili tace ke yarinya ya sunanki,sunana Amana,wanne gari? Kano state a garin
wudil.murmushi Mum tayi tace good tare da cewa Alim dama Aabid nazo gani ni Na tafi gida,
Haba Mum ki zauna mana,murmushin mugunta tayi tace abinda nazo wajenka zan nemo Na
samu cikin sauki shiken nan bye ta yi waje cike da shirya mugunta,

Mum murna take taga yarinyar da tafi tsana a duniya,ga laifin ta dukar mata jikanta,gata a
gidan danta tana cin arzikinsa,lallai Amana zata ci Ubanta.
Ita kuwa Amana bata kawo komai ba a ranta,Hannun Aabid ta kama take ta faman
lallashinsa tare da cewa master pls ka tayani lallashi,tabe baki Alim yayi yace kunfi kusa Amana
keda ur Boy.

Bacci Aabid yayi a jikin Amana,kallon Alim tayi dake latsa waya tare da cewa Daddyn Alim
wannan dama Mum dinka ce? Itace wacce nake fada maka Na kusa bigeta a mota tana ta
fada,Kinyi sa'a da ta iya kyaleki haka ki godewa Allah,shuru Amana tayi tana tunani.bayan sati
daya Alim ya samu kiran gaggawa daga wajen Mum, 5pm ya dawo gida cikin tsananin kunci da
bacin rai ba a San wacce Magana sukayi da Mum dinsa ba

Amana suna palonsa ita da Aabid sunga lallai Alim yana cikin damuwa,shi kanshi Alim so
yake ya samu abin nishadi abinda zai sanyaya masa rai,wayar sa ya dauko tare da mikawa
Amana wayar take this kira Daddynki kuyi hira da su Ummanki,da sauran yan gidanku,
Amana cike da mamaki ta kalli Alim tace rannan fa munyi waya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login