Showing 6001 words to 9000 words out of 105161 words
Chapter 3 - CIRANIN AMANA BOOK COMPLETE BY Asma Baffa .pdf
haka,gata Christian,
Harara ya kuma watsawa Amana,ka Adana Harararka malam kar nayi fushi wlh zan iya ma
dukan tsiya na jefarka a hanya,banda mutunci,dankwalin kanta ta cire ta zaro pcap dinta
tsohuwa ta saka,
Kamar Handsome yayi dariya ya maze,aswakinta ta dakko a jaka sabo ta fara dirzar
bakinta,yayinda motocin suka dau hanyar lagos gaba daya guda 10 a Jere suke tafiya,sai satar
kallon Amana yakeyi yanda take dirzar hakoranta da aswaki,sanda ta zaro harshenta ta fara yi
har can ciki har kakarin Amai takeyi,ita kadai nan ma yaso yin dariya,
Amana dai akwai tsafta sai dai kayan jikinta sun ji jiki da yawa,sai da ta kusa kwashe 1hr tana
aswaki,sannan ta gama,tace Baaba dan miko min ruwa kuma ka sauke glass,ko kulata baiyi
ba,turancinta tayi am talking to u Mr Man,guard dinsa dake gaban motane ya mika mata ruwan
roba, tare da sauke mata Glass,ta kuskure bakinta tare da shan ruwan ta jefar da robar cike da
takama,
Mudubi ta dakko karami ta dinga duba hakoran nata sai da ta gama tace perfect,itafa turancin
lagos ta fara tun yanzu,kasa kasa me kyau yake kallonta,sanyin ac ne ya fara gigitata, Jakarta
ta duba ta dakko wani dan towel light blue sabone Baba ya siya mata shi,har turare ta fesa
masa na tafiya lagos, Ware towel din tayi tare da rufe jikinta da kafafunta da sanyi ya ratsasu,kamshi kawai me
kyau yaji,ya dan bigeshi ba laifi kuma turaren da dadin kamshi,minti 2 ta fara bacci baji ba
gani,a nutse takeyin baccinta,
Magazine yake dubawa sanye da wani glass fari kal siriri a fuskarsa ko kallon Amana bai
kara yi ba,yana duba jaridarsa yana kora ruwan juice,tafiya sukeyi tare da sheka gudu,Driver
me kyau ne ya kauce hanya tare da kasa control din motar,nan suka kafa tangal tangal a
titi,kafin kace me ya daki motar gabansa ta baya ma ta dakeshi,Allah yasa duk motocin tawagar
me kyau ne,nan take Amana ta farka firgigit,amma ko a jikinta bare ta razana,me kyau ya gama
firgita amma yaga Amana tsaki taja tare da cewa kai malam parker mortar nan ka bani tukin,ba
shiri driver ya gangare kasa suma sauran motocin haka sukayi,saida suka duba lafiyar motocin
me kyau sannan driver cike da girmamawa yace Sir a bata key din,
Me kyau kuwa dan ya kure Amana yace a bata ta tukashi,yasan bata iya mota ba,inda take
talaka haka ina suka ga motar da zata koyi mota,da gani ma bata da iyaye karuwan tasha ce,
Karbar key tayi tare da fita da karfi ta zauna a mazaunin Driver tacewa driver koma wata
motar kar hanjinka yayo waje bana saurarawa a hanya nikam,ai kuwa a cikin motocin ya shiga
daya,guard daya dake gaba ya gama tsurewa karfa yarinya bata iya mota ba ta kashesu a
hanya.
Key Amana tayiwa motar tare da bata wuta sosai,har wani jiny jiny tayi sannan ta take motar
tare da hawa titi,ta fara tafiya a nutse da mitar a cikin nutsuwa na gaba tayiwa Alama su tsaya a
baya itace a gaba coz gudu zata sharara,
Ai kuwa ta fara tuki gashi gudu take tsulawa me uban yawa sosai tare da over taking da
takewa motoci,amma kai baka is a kace gudu takeyi,irin tuki ne na kwararru,manyan drivers ba
kowa ya iya irin tukin Amana ba sai babban kwaro,kamar ka hau jirgi ba wani gargada a titi
haka take tuki suuuuuuuuu kawai kake ji,haka takeyin tukin,kafin kace me tayiwa sauran
motocin tazara sosai basa hango motarsa duk da suma gudun sukeyi kamar zasu tashi sama,
Amana wucewa takeyi yuuuut yuuut,vol ta karo na kida ta cika motar har stiyari take duka
idan kida yayi dadi,kadan Kadan take kallon me kyau ta mudubi,
Ga shegiyar pcap dinta kamar zata rufe mata ido,kara kallon mudubi tayi ai kuwa carab
suka hada ido da me kyau,Wanda yake cike da mamakin wannan Aljanar yarinya kamar namiji
har ma tafi mazan,
A cikin motocin tayiwa daya Alama da ta shiga gabansu ta nuna mata hanya,saboda sun kusa
shiga garin Lagos,me kyau ya gama cika da mamakin Amana,suna shiga lagos Amana ta ciro
wata yar wayarta Nokia 1110 da Baba ya siya mata second sabo da kira,number abokin Baba ta
kira bugu daya ya dauka ta sanar masa ta iso,
Yace to ki shiga taxi kice ta kaiki mytwelve,parker motar tayi tacewa me kyau na kawoka iya
nan zan wuce ni ka gane?
Wani driver ne ya karbi tukin,shi kuma me kyau Wanda tunda suka hadu sai yanzu ya kara
kare mata kallon ba tare da yayi magana ba ya Mika bundles na 1k guda biyu
Ganin bata da kudi yasa tace sabo da bani da kudi zan karba amma ka kiyaye ko dan gaba
bana son taimako,bana son a dinga taimakamin ni ka gane ko,harda zare masa ido,kai man ko
kurmane?idan baka jin Hausa ka fada min na iya English dina,har ta gama surutunta bai yi
magana ba,kawai da hannu yayiwa driver alama dasu tafi,kudinta ta boye a jaka zata tafi ta
hango ana fada a gefen titi,da Sauri ta karasa wajen su,Wanda suke fadan kawai Amana ta
fesawa ko wanne cikinsu mari daya tace Wanda yaji zafi ya rama dan Ubansa,
Ai kuwa yarabawa bata sani ba duk basa jin Hausa nan take suka rufeta da duka,sai da
sukayiwa Amana jina jina,da kyar wasu suka taimaka mata suka janyeta gefe,amma saboda da
taurin rai irin na Amana ko hawaye batayi ba,Jakarta ta duba ta tare da zaro yar kudigar
wayarta ta kira wayar abokin Baba tare da fada masa inda take yazo ya dauketa wai an mata
duka.
Masifa ya farayi tare da cewar bazai zo ba idan bazaki hau taxi ba ki shekara a wajen,nan
lagos ce fa ditt ya kashe wayarsa,ba shiri ta mike da kyar ta fada taxi tare da fada masa
unguwar da mutumin yace mata.
Har mytwelve ya kai Amana basu san Layin ba sai da ta kara kiran wayar sa sannan ya ce
Aisha 12 street,sai da suka isa can sannan ta biya driver kudinsa ta dauki jakarta da kyar.
A bakin wani shago taga tsohon mutumin abokin Babanta,
Har gidan da yake ya kaita amma da alama gidan karuwai ne saboda ko ina dakuna ne gashi
duk mata arna da musulmai,
A tsakar gidan yace ke yan mata lagos ba a aikin banza kawo kudin dakinki,murmushi
Amana tayi tare da yin wani yar jijjiga tana doro,ta zura hannaye a Aljihu tace Tsoho kenan da
Alama baka sanni ba,amma ni da ka ganni bana Neman sauki da rangwame a wajen
mutum,sannan bana son a dinga taimakamin,da kudina nake harkata,ka Bini a hankali ka gane
ko,tsohon bariki na fika iya shege,mamaki ne ya kama dattijon nan dan ko a karuwai bai taba
saukar irin Amana ba,
Kaga tsohon banza yi min kudin dakina naji,dubu Dari a shekara kudin dakinki,dattijon banza
harda dariyar mugunta irin ya San Amana bata da kudi,nan take yaga ta karkace ta Ciro bundle
daya na 1k sababbi kar kar ta mika masa,tace oya karba iya kudina iya shagalina,
Na biya na shekara guda kar kuma ka dawo ka takura min zan iya ballaka a gidan nan.
Key din dakinta ya bata ta shiga harda toilet,ko ciwon raunin da yarabawa suka ji mata bata
ji,wanka tayi a toilet din room dinta,ta sa wata rigar atamfa da wani falkeken jean blue,ta fito har
wajen tsohon nan,tace Man tashi maza ka rakani kasuwa,yanda yaga Amana a dire gata komai
da jikinta takeyi ba wani lako lako,tsorata yayi ya sata a gaba har kasuwa,ta siyo tabarma,da
risho da kayan girki,Tsoho yace ke da zaki siyo katifa yan mata,
Tsoho kenan ka gane Neman kudi nazo ba jin dadi ba,shi kuwa Tsoho sai kallon Amana
yake yana lashe baki,a ransa yace dole na dandana wannan yar chamai mai din.
Har tukunya Amana ta siyo guda biyu,komai biyu ko daya take siya har ta gama suka koma
gida,yau baza ta fara girki ba,a kasuwar ta samu wata me saida doya da miya,nan ta siya taci a
wajen,ta siyawa tsohon ma,harda shan lemon kwalba,
Wani me shayi da kwai ta gani tace ayi min hadin kauri,ta manta yanda zata fada da turanci
sai tace thick thick tare da gwadawa da hannu 2 cups harda Tsoho,saida suka koshi sannan ta
ga wani bahaushe me gashin kaza taje ta siyo biyu manya ta dauki tata ta bawa tsoho
tasa,sannan suka Shiga Taxi har gida, Tsoho dai sai mamaki yakeyi,tare da jin dadi ya samu budurwa me kudi,zai like mata ta zama
kawarsa.
Dakinta ta shirya tsab sannan ta fara zaga gidan sannan ta dan leka waje ta kai 1hr a waje
amma kafin kace duk ta fara sabawa da mazan layin nasu,ganin kudin da me kyau ya bata
suna da yawa har wasu ta siya abinci suka ci,wasu lemo ta siya musu,duk majalisar data je ko
shago sai ta raba musu lemuka sunsha hira,kullum haka takeyi har ta kwashe 2wks a lagos,duk
ta saba da mutane amma iya maza,dan bata saurarar mata ita,
Yanzu da kaje Layin kace Amana kowa ya Santa,gata dama da karambani,ko mai ta gani sai
ta koya kuma ta iyashi,har yau bata samu aikin yi ba,yayin da kudin me kyau daya bata suka
kusa karewa,abin na damunta gashi tsohon nan yaki nemo mata aikin,
Amana tana ganin rayuwa kala kala a lagos gasu da Neman mata kamar yan akuya,ita kanta
duk abin ya isheta,ko wanne yace zai kawo mata hari,baren ma tsohon daya bata masauki ya
dameta da zuwar mata cikin dare wai sai ta yarda sunyi xxx ita kuma baya tsarinta tana tsoron
Allah,
Amana zuwanta lagos ta kara wayewa da gogewa fatarta ta kara haske sosai ta kara yin
smooth,ta zubar da kayan da tazo dasu daga kano ta siyi wasu wajen 10 amma fa duk ba skert
ko doguwar Riga,gaba daya wando dogone pencil da 3qtr maka maka kamar yar
America,kamar ta hada dangi da lilwayne wizzy yanda take Burma wanduna manya ga T-shirt
dinta har gwiwa suke kawo mata wai shigar kamala takeyi sabo da masu kawo hari hh, p cap
kuwa ta siyi kala Uku masu dan kyau,
Har inner wear ta dan siyi abunta,always pad ma da yawa ta siya ta ajiye,Amana har ta fara
koyon yarubanci,ga broken English, ga grammar ma tana karuwa sosai yayinda kudinta suke
barazanar karewa.ta fara Shiga wani hali
AsmaBaffa
✳CIRANIN AMANA✳
15-20
By
AsmaBaffa
Amana tana haki tare da addua ta koma gida,Dan Uzuri me gidansu ta gani a tsakar gida
suna ta fada da karuwan gidan,sai bin Amana yakeyi da kallo yana lashe baki,yanda yaga
zaman lagos yasa Amana ta kara fari sosai tayi yar kiba ga uban hips da breast masu matukar
birgewa,yau ya kashi takobin dolene ta bashi zumarta ya sha,ya gaji da hakuri,kuma Dan uzuri
gani yakeyi Amana yar iska ce itama karuwa ce duba ga yanda take Hulda da maza da
abubuwan da takeyi tare da yanayin shigarta,kai kana kallon Amana zaka San cikakkiyar
wayayya ce,
Sai dai zargi da zato ya jawo ya fassara Amana bai bai,domin Amana babu namijin daya taba
koda rike mata hannu da niyyar iskanci,ko saurayi bata da shi,har so take taga Wanda zaice
yana sonta zai iya aurenta a suffarta,gashi tasan babu me sonta,ta cire a ranta baza ta taba
aure ba saboda babu me sonta a haka,itama har so take ta ganta ta dawo kamar mata masu aji
da birgewa amma ta kasa.
Da dare misalin 2am tana bacci akan yar tabarmarta,ji tayi kamar ana shafata a hankali
dama ita bata da nauyin bacci,firgigit ta farka,mutum ta gani kwance a jikinta touch light ta
haska sai ga Dan Uzuri makale a jikinta,Tsoho dashi ko kunya baya ji dan ya girmi babanta ma
Mikewa tayi tare da cewa tsohon banza fitar min a daki wlh iya kwadayinka baza ka sameni
ba dakiki,zama Dan uzuri yayi yana mata magiya kan ta amince masa,ka tashi ka fita kafin na
kar Karyaka,haba tawan Amana ta,nifa abokin Babanki ne ko dan wannan kya
taimakamin,nasan ma kin San komai da ganin Alama kema yar gari ce cikin harkar zumar nan,a
fusace Amana ta suri Tsoho Dan uzuri ta bugashi da kasa tare da daga kafafunsa ta lankwasa
su saura Kadan su balle kana ta daukeshi ta jefashi waje ai kuwa Dan Uzuri ya saki kara da
kuka,
ji kake garam ta kulle kofar ta tare da cewa dan iska ragowar wiwi,ko karfi babu dan kwaya duk
ya tsiyace kwanjalallen banza,wannan in banda cuta me zai shafawa mutum,shi da Baba duk
together Allah shiryesu,
Ta kwanta tana tunanin halin babansu duk shi ya ja musu,sai ga hawaye idon Amana sharrrr
sabo da tuna yan uwanta da gidansu da tayi da mamanta,tare da halayen family nasu,gasu
kowa ya tarwatse a gidan babu wani na gari.
Bata marmarin ta koma gida Sam ko kadan,mikewa tayi ta daura Alwala ta fara nafeela
ganin bacci ya gagareta,ga tunanin yanzu bata da wani aikin sunyi fada dame shayi,dole gobe
ta fita Neman wani.
Washe gari kuwa haka ta dan sha tea dinta tare da siyo kosai tayi Karin safe,ta yi wanka
hade da shiryawa cikin wata farar T-shirt fara kal kal siririya dai dai jikinta amma me tsayin
gaske ta kai gwiwarta gaban rigar da hoton mace me gashi pink,wandon jean tasa black da fari
fari a cinya yayin da wani aka yanka gwiwoyinsa crazy jean dai shi ba 3qtr kuma ba dogo ba
gashi birmeme irin nasu wizzy,jikinsa duk aljihuna,wata farar p cap tasa gashinta ya wuce
kafada ta tufkeshi ta cusa a cikin hular amma dole ya fito,takalmi tasa black flat me igiya
baki,tayi kyau,bata fiye sa dankunne ba,powder kawai da lipstick ta shafa ta fesa body spray
dinta me dadin kamshi sai shining takeyi ta fito,amma matsalar bouncing takeyi tare da
kobarewa tasa hannu biyu a aljihu,
Tana fitowa tayi ido hudu da Dan Uzuri ya zura mata ido tare da marairaicewa yana mata
shagwaba pls babyna aji tausayina mana,wani kallon banza ta watsa masa,sauran karuwan
dake gidan su suka kalleta tare da tabe baki,
Ta fara tafiya suka kyalkyale mata da dariya,dawowa tayi a fusace dama haushinsu take
ji,wani ruwa ta gani cikin bucket a wajen pampo dauka tayi cak tare da juye musu shi a jiki,ta
fara ball da botikin robar saida ta ragargazashi sannan tace ugly prostitute with ur big mouth tayi
waje,arnan karuwan nan sun tsorata da bahaushiya Amana mukus sukayi.
Duk inda Amana ta ratsa a lagos gaisuwa ake kaiwa wajenta,saboda girman kai irin na
Amana bata taba nuna talaucinta,bata wulakanta kanta,da ta roki wani kudi gwara ta kwana da
yunwa, bata harkar karanta shi yasa kayanta masu yar tsada take siya,
Da ace a kauyensu ne to da sai tayi shigarta ko wacce iri tunda kowa yasan asalinta kuma ga
talauci bata samun kudi sai yan dabaru,amma yanzu alhmdllh tana samu dole ta kankaro
girmanta da mutuncinta, ba raini bata son a rainata shi yasa kullum ake ganinta kamar me
kudice.
Direct wani lafiyayyen wajen suya ta nufa wajen masu kudi ne da manyan yara su ke zuwa
wajen.manyan guys both christains da musulmai suna zaune a kujerun dake wajen wasu na cin
abinci wasu suna jiran take away,
Da ganin wajen Kasan bana talaka bane,a me kudi ma sai ka isa zaka shiga wajen,shiga ciki
Amana tayi tana bouncing tare da sa hannu daya a aljihu daya kuma tana danna karmar
wayarta touch screen amma yar karama da ita.
Chewgum take taunawa a hankali bakin yake motsawa sai ka kula sosai zaka gane tana cin
chewgum, duk da masu kudin gaske ne a ciki kuma manyan yara babu ruwan wani da wani,ba
Wanda zai kalleka ma kowa harkar gabansa yakeyi,amma Amana tana shiga wajen duk Wanda
yayi tozali da ita bazai so yayi missing kallonta ba,sabo da ko iya tafiyar ta yanda take gadara
kamar yar wani shugaban kasa,tana budawa,ga tafiyarta kanta a mazanma sai manyan shegu
su keyin irin tafiyar da Amana keyi,ga p-cap dinta yanda ta wani kusa rufe mata ido,Riga har
gwiwa ga creazy wizzy jean habawa ai kowa kallonta yakeyi,gata yar fara me kyau sai shining
takeyi ga shape,sai ta birge wasu yayin da wasu ta basu dariya,
Kowa dake wajen maza da mata dariyar Amana yakeyi,ita kuwa ko a jikinta,
Manager wajen ta kira a waya sai gashi ya fito wani katon Igbo Arne,yasan Amana ta taba
taimaka masa sanda wani yazo zai yankeshi da wuka,ita ce ta taimaka masa,dan haka ya fito
da fara'a dauke da murmushi a fuskarsa,yana zuwa ya mika hannu tas suka tafa,da karfi yace