Showing 102001 words to 105000 words out of 105161 words
Chapter 35 - CIRANIN AMANA BOOK COMPLETE BY Asma Baffa .pdf
ita sai abinda takeso
Wata ranar talata Amana ta fara Jin ciwo kadan kadan ta fadawa Alim honey kamar fa
nakuda nakeyifa wlh daurewa nakeyi kawai ciwon yayi yawa.
Da gudu Alim ya hada komai suka tafi asibiti,ya fadawa Mum tazo da Hajja me aikin Mum
wata dattijuwa,
Amana ana dubata akace haihuwa ce,Abin mamaki tsabar juriyar Amana ko hawaye
babu,yatsina fuska kawai takeyi idan ciwon ya motsa mata,
Alim ya kasa zaune ya kasa tsaye sai zirga zirga yakeyi baji ba gani.
Kamar shine me nakudar,
Amana kuwa daurewa kawai takeyi bata taba Jin ciwo irin wannan ba,amma bata ko ehem,ko
Mum ta jinjina mata har dai yau bata haihu ba sai wahala da take Sha sosai ta fita a hayyacinta.
Alim ya rasa yanda zai saka kansa,Amanarsa kawai yake tunani da tausayi,gashi an hanashi
shiga ciki.
Alim harda hawaye ganin doctor tace har yau bata haihu ba.
AsmaBaffa
✳CIRANIN AMANA✳
205-210
Official
By
AsmaBaffa
FINAL
Amana ta dan Dade kadan sannan Allah ya taimaketa ta santalo danta Namiji katon
gaske,kyakyawa fari kwal kamar bature,readers yaron dake jikin poster din Ciranin Amana ba
Aabid din farko bane wanda ya rasu,Aabid din Amana ne da ta haifa yanzu.
Alim murna kamar ya Haukace ganin Amanansa lafiya lau da ita,
Mum cewa tayi gidanta zasu koma da Amana baza ta koma gidan Alim ba sai tayi arba'in,
Alim baiyi musu ba amma yace dashi za a koma gaba daya ai nan ma gidane ba matsala tunda
gyara masa headquarter za ayi b a damuwa.
Dungumawa sukayi gaba daya gidan Mum, Alim yaki tafiya wai shine zai mata wankan,Mum
ta koreshi,sai dare ya dawo tare da haurawa saman Bed yace honey ina ma yan uku kika haifo
min,Amana ta Galla masa harara,tace dayan ma na gode akace uku zan haifo ai na shiga
uku,ashe dana ke neman yan uku ganganci nakeyi wai wannan wahala haka,na zata mutuwa
ce.murmushi Alim yayi yace na matsu kiyi arba'in na koma Ango,murmushi tayi tace me za a
fasa mutuwa ko hisabi,ai Harka zamu koma sabuwa dal,
Tafa mata Alim yayi yace sai Amanata tawan ba sanya, juriyar nan taki tana birgeni,da watace
gudun mijinta zata fara yi akan wuyar da ta Sha,ko kar ta samu ciki da wuri,sai kiga haihuwa
daya ana fada tsakaninsu,
Fari Amana tayi da Ido tare da cewa ni da muka Dade bamu haihu ba,yaci ace kana da yara
Uku yanzu kaga dole na bude mahaifa nayi ta haifowa idan nayi Uku sai na huta ko?
Alim yace good haka kuwa,Mum ce ta shigo tace tashi ka tafi dakinka Malam,
Haba Mum Alim ya fara shagwaba,Mum tace anan zan kwana,Alim ya bude baki kai Mum
dan Allah ki tafi dakinki Abba yana gari fa,
Kunnensa Mum ta murde Amana tana dariya tace Mum kyaleshi dan Allah kin San halinsa
da kafiya wlh idan ba haka ba aure zai fara nemowa kyaleshi ya kwanta,Alim yace gwara da
kika samawa kanki lafiya dama wata ta manne min sai na nemota,Amana kamar zatayi kuka
tace Mum kinji ko kyaleshi kawai, Mum tace kinji kunya wlh kina tsoron kishiya ki zauna ya rainaki yana miki barazana da
kishiya,
Sosa kai Amana tayi Mum baifa ce zaiyi ba nice dai nake tsoro kuma wlh idan yace zaiyi Allah
saina ballata harda shi ma, murmushi Mum tayi tace ai nasan zaki iya aike kishiya ta shiga uku
a hannunki,gwara karma mutum yayi domin korarta zakiyi da muguntarki kala kala,
Shagwaba Amana ta fara haba Mum ni Allah,Mum tace sai dai ki gayawa wani amma nice
sheda,ni indai ina raye bazan bari ma ya miki kishiya ba,nasan ma bazai miki ba yanda yake
Sonki,
Dadi Amana taji tace na gode Mum,koreshi ya tafi dakinsa,bige bakinta Alim yayi kadan ta
kwalla kara,
Mum tace kwaji dashi can kunfi kusa,sai da safenku tare da kallon Alim tace ka kiyaye kaji na
fada ma,ina ganin ba dai dai ba sai ka bar gidan nan ka koma gidanka,
Wannan yaro yana Shan kulawa wajen Amana,kullum yana hannunta ta hana kowa,da an
karba zata dinga mika wuya tana lekensa,
Idan yarane ba manya ba Baza ta basu danta ba kar su jefar dashi ya fadi kasa wai,daga
yayi uhum Amana dama kadan take jira zatace mikoshi na bashi ya sha ta karbe abinta,
Ko Alim masifa take masa wai yana shilla mata yaro zaiyi zazzabi,
Asiya dasu Badriyya kuwa da suka zo suna dauka kadan zata dan jira mintina kadan tace
bani dana,har tsiya ake mata Amma Amana ko a jikinta,
Har ranar suna tayi dangi da abokan arziki ansha suna,yaro yaci sunan Aabid,Aabid ake ce
masa,
An gama komai kowa ya koma gidansa,Mum kuwa da sauran dangi suna ta faman gyara
Amana kamar sabuwar Amarya,
Alim dan albarka yayi dauriya da hakuri bai takurawa Amana ba sam,
Amma da kyar yake daurewa har sai da ya daina kwana gidan Mum saboda tashin hankali
yake shiga yanda Yake kallon Amana tana kashe kala,gashi sai kara kyau da girma takeyi har
akayi arba'in Aabid yayi wayo sosai gwanin sha'awa
Ranar kuwa da ta cika arba'in ranar Alim zuwansa gidan Mum yafi Goma yana jira yaga
Amana ta Zama ready su tafi gida,Amma sai yaji Mum tace kano zasu tafi tare da Amana su
zaga dangi,
Da bacin rai ya koma gida,Saida Amana suka gama zaga dangin lagos sannan suka wuce
kano kwanansu 4 suka dawo lagos,washe gari Mum tace shirya maza na kaiki gidanki,wannan
mijin naki kamar zai dakemu kina gani da kyar ya gaishe ni.
Amana ma tayi missing mijinta,har gida Mum ta kaita da yamma misalin 5pm,
Nan Alim ya fara fushi yana shagwaba,da kyar Amana ta lallashi abinta, yana dawowa daga
Sallar magrib,yasa Amana ta kara bawa Aabid Nono ya koshi ya tattarashi ya kaishi wajen
hajja,
Amana tace idan yayi kuka fa?,Alim ya ce can da matsalarsa yazo ya kankane komai ya
barni cikin wahala,
Ranar Amana taga ta kanta a hannun Alim,ya gurjeta son ransa,
Sunji dadinsu sosai,Alim kara nutsewa yayi akan so da kaunar Amanarsa,
Kullum yana manne da ita ba sauki ba daga kafa,itama Amana hakan take irinsu daya.
Saida Alim yayi Hutu na 2wks sannan ya koma aiki,
Wata yarinya ce wacce sukayi university da Alim a london Teema take matukar son
Alim,kullum sai tazo office dinsa kan ita sai ya aureta,Alim Amanarsa ta isheshi,bazai iya mata
kishiya ba Sam,
Yanda yake mutuwar son matarsa me zai ci da wata,yayiwa Teema bayani amma taki
yarda,shi kuma Bai son wulakanta dan Adam musamman yanda sukayi schl daya,yana ganin
mutuncinta.
Yauma kamar kullum tana office dinsa,dabara ce ta fado masa yace Baza ki iya kishi da
matata ba,Teema tace haba dai ai ni nafi karfin ko wacce kucaka, ka kirata mu hadu kaga
yanda za ayi sai abinda nace dole ma ta hakura,
Murmushi Alim yayi,Teema da kuri tace kirata mana tazo na fada mata amma da sharadi idan
ta yarda dole ka aureni,Alim yace kwarai kuwa.
Amana ya kira a waya tana jikin mirror tana sheka kwalliya ta daga,Alim yace kizo Office
yanzu wata tana son ganinki wai zata aureni zata iya kishi dake shine nace kinfi karfinta ni mijin
tace ne amma taki ji,wai sai ta ganki.
Kamar an watsa mata ruwan Zafi haka Amana ta mike, gyale ta figa a hannunta ko yafawa
bata yi ba,Aabid dama yana wajen Hajja,motar da tafi ko wacce tsada da kyau a gidan ta shige
tare da fisgarta sai office din Alim,Teema kuwa harda fitowa waje tana jiran Amana,
Alim sai dariyar mugunta yakeyi yasan yau Teema ko mari daya ne sai tasha a hannun
Amana,
Motar Amana ce ta Parker tun daga parking kasan ba lafiya,tana fitowa Teema ta sume a
tsaye ganin Amana,tunaninta Amana ba wata me kyau ko hadaddiya bace tunda tasan Mum
kewa Alim aure,
Tun kafin Amana ta karaso daga yanda Amana take tafiyar gadara da takama gashi kana
ganin idanunta kasan a bushe suke sun goge da duniya,
Duk wajen ya dauki kamshin Amana,shigarta kanta abin kallo ne wajen tsada da haduwa,
Alim ya fito waje yana ta faman murmushi da Ido ya nunawa Amana Teemace me son zama
kishiyarta,Teema kuwa ta maza tayi,tare da hade rai wai itama shegiya ce,wajen Alim ta matsa
tana masa wani kallo,
Hannu ta daga wai zata rike hannun Alim,dan Amana ta gani tasan suna soyayya.
Kafin ta ruko hannun Alim,Alim yayiwa Amana magana da Ido wai kullum haka take takura
masa a Office,shi wlh ya gaji zai aureta,Amana da hannu ta yanka wuyanta wai sai ta
yankashi,murmushi yayi,Teema kuwa taje tana hada hanunta dana Alim wai zata rike, Amana ta
fincikota baya tare da kifa mata maruka har uku, Tare da shake Teema ke karamar yar Iska kin sanni kuwa,Teema Ido ya firfito sai
hawaye,sakinta Amana tayi tare da ja baya tana, bana Cece kuce da mutum na wuce nan,Dalla
ja rubabben bakinki dake yar kauye zaki taba mijina da kazamin Hanunki kwartuwa ana zubar
da aji ana bin maza,nafi karfin kishi dake, Warning na miki kika kara zuwa Office din mijina sai nayi daga daga dake, Alim munafuki harda
cewa sorry Teema kinga abinda nake fada miki gashi fuskarki ta kumbura kika ki yarda,ba
laifina bane,
Teema share kwalla tayi tace amma Alim kayi asarar halinka wlh,sam bansan haka ka Zama
lusari sakarai ba,kai da kake dodon mata amma mace yarinya karama jibi yanda ta ke Baka
Umarni,Alim yace uhm wlh kuwa ganemin hanya Teema aini a kanta na gama lalacewa,ta
shanyeni na shanyeta idan ba ita rayuwata Baza ta yuwu ba,kinganta to bana jin yaren kowa sai
na Honey ta,
Teema fuska kumbure tace Allah yaji kanka Alim,wlh ka haukace aikin banza kayi asara
dai,kuma marin da tamin Allah ya Isa wlh Bazan yafe ba,
Alim yace taba mata miji da kikayi bata ce miki Allah ya Isa ba sai ke dan ta dan
mareki,hukunci ta miki a duniya kafin Allah ya miki nasa,karki sake ki zagi mata ta wlh a nan
zansa a tara miki gajiya uban waye ya kawoki Office din mijinta,
Amana tace a bar mana Office yanzu ehe, Baby muje gida an tashi a Office yau Baza ka
zauna ba sai gobe kuma,
Alim yace an gama ranki ya dade,ya kwaso wayoyinsa ya rufe Office yabi Amana,yace
Securities su kai motocinsa gida Madam tace a tashi a Office haka,
Amana harda jin dadi Alim yabi maganarta,abinda idan yaga dama idan ta yi ba dai dai ba sai
ta gane kurenta ba wani mijin tace.
Teema kuwa motarta ta shiga tace Amma na maru wlh,wannan jarabace da ace na kulata
Dukan tsiya zata min,ga shegen iya mari,hannunta laushin tsiya Amma idan ta dakeka sai kaji
ajikinka,
Kamar namijine ya mareni,yaje ya zauna da jarabar matarsa,mijin tace shege,dan
iska,tsinanne ta dakeni Amma ko a jikinsa koma ya mata fada.wannan Alim ai shine dan iskan
marar mutunci suje can su karaci jarabarsu ko kallonsa wlh Bazan kara ba tunda bashi da
mutunci haka Teema ta dinga zage zage har ta koma gida.
A ranar ta nemo tsohon saurayinta me sonta da take masa wulakanci suka shirya zai turo ya
kwashi tsohuwa Teema..domin Teema Sa'ar Aleem ce 33years itama.
Amana a mota sai faman dariya sukeyi da Alim yanda Teema tayi,Amana tace sai ni wlh har
aja Dani ko wacce shegiya ce, tana driving Alim ya mika mata hannu ta rike tare da hadewa da
sitiyari tana tukinta,
Tana Driving Alim na tabe tabensa a jikinta,yana dora hannunsa a kirjinta Amana tayi slow
da mota ta kara fincikar motar,yana kara tabawa Amana ta gangare kasa tace zo ka karbi
driving bazan iya ba ai sai kasa muyi hatsari ai,
Dariya Alim yayi tare da cewa na gaji ban iyawa,na daaina tabaki muje pls,
Driving taci gaba har gida,
Wannan shekarar Amana da Alim sukaje aikin Hajji again suka koma umrah tare da Aabid
dinsu,Amana na zuwa schl tana karatunta sosai yanzu tana final year,
Salma ta gidan Deeni kwaro tana dauke da ciki haka matan su Hamza ma,
Shekarar Aabid biyu a duniya Amana ta samu ciki za ayiwa Aabid kani ko kanwa,
Murna sukeyi sosai,tana gama degree dinta da wata biyu ta santalo Danta Namiji shima,
Ranar suna aka sa masa sunan Baban Amana Sulaiman suna ce masa Irfan,
Aabid an girma an zama dan saurayi,
Amana tana jin dadinta suna zamansu lafiya ita da Alim da yaranta,
Sai abinda sukeso, har ansa Aabid a schl, Amana ba abinda bata Yiwa Alim don ta faranta
masa,sai abinda yakeso,kullum Amana cikin gyaran jiki da kwalliya a haka take kara susuta
Alim,ya gama matowa a kanta,akan Amana sai dai a mutu,
Ga tsananin biyayyar da Amana ke masa,uwa uba ga iya kwanciyar aure,ta gama da Alim
gaba daya, baya ganin kowa a gabansa sai Amana.
Kullum cikin soyewa suke basa iya zama ba tare da juna ba,
Bayan bikin Ameer dan Autan Mum da Amaryarsa Minat.
Alim yace Amana taje tayi masters,haka ya kara biya mata private schl ta fara masters,
Tana gama masters ta kara samun cikin na Uku,
Wata tara ta haifo yarta mace zukekiyar gaske me kama da Alim,Daga nan Alim yace ta huta
haka da haihuwa sai nan gaba an dan dade.
Yaran su dagwas dagwas dasu gwanin sha'awa su uku, Aabid kullum baya fara'a cikin
muzurai yake da kaninsa Irfan ya masa Abu ko Mufeeda kanwarsa zai samu ya zanesu,baya
daukan raini kamar Babban mutum haka yake,
Yanzu ya daki mutum ba ruwansa,mugune Aabid na karshe,baya wasa da Yara,ko cikin Yara
ya shiga yan uwansa sai dai kaji Kukan Yara ya bubbugesu ba ruwansa,kannensa ma tsoronsa
sukeyi,
Mugun tsoron Amana sukeyi yaran nata don sun San idan sukayi laifi ba ruwanta zata
hukuntasu,shi yasa suka taso masu hankali nutsatsu ko ina suka je zaka gansu cif a nutse,kallo
Idan Amana ta musu sun San me take nufin.
Alim ne ke shagwaba su ma baya son ana taba su.
Alim ne kwance a bedroom dinsa Amana na gefensa,Mufeeda ta kwankwasa kofa
Dad...Dad....ta kwalawa Alim kira, Alim ya mike tare da bude kofa,lfy Mufeeda? Ni a wajenka
zan kwana Ya Aabid dukana yakeyi,wai muyi bacci,
Amana ce tazo wajensu tace Baza ki kwana ba Mufee ki koma Bed dinki,me ya kaiki wajensu
ke dana ce ki je dakin Hajja ki kwana,
Kuka Mufeeda ta fara ni...ni bana son wajen Ajja.
Alim ya kalli Amana tare da yin magana kasa kasa yace yarinyar zata hanani sakewa yau,kin
kuma san Bazan iya jure rashinki ba,
Amanace ta riko Mufee tana lallashinta ta maidata dakin Su Irfan ta dorata a Bed dinta,Aabid
sai fushi yakeyi su baza su kwana da mace daki daya ba,
Momy pls mu baza ta kwana a room dinmu ba.
Amana tace zan taka wuyanka Aabid ka rufe min baki,kunyi karatu kuwa yau kaida Irfan?yes
Momy cewar Irfan,gobe zan duba na gani ai Amana ta furta.
Shuru Aabid yayi Irfan yace sorry Mum zan kula da ita,
Hararar Aabid Amana tayi tare da cewa idan naji kukan yarinyar nan Aabid saina karyaka.
Shuru sukayi Amana ta dinka masifa ta kashe musu light tare da rufawa kowa blanket ta rufe
musu kofar ta koma wajen mijinta, suka fara baje Harkar da suka saba ta sunna..wajen Sunna
basa sanya.
ALHAMDULILLAH
Ina matukar farin ciki da godiya ga Allah daya bani ikon kammala wannan littafin CIRANIN
AMANA.
Godiya da jinjina gareku readers,masu sharhi,godiya etc,masu yin Document,masu kirana a
waya