Showing 15001 words to 18000 words out of 105161 words

Chapter 6 - CIRANIN AMANA BOOK COMPLETE BY Asma Baffa .pdf

22 Mar 2025

13655

lagos banyi aboki ko da me Mota ba,amma
wannan me suffar mazan gashi tayi masu motoci ma,ko da yake mace ce suna kwashe zumar
ta dole haka ta faru.
Wajen Amana ya kara ta watsa masa masa wani matsiyacin kallon da ya sa Dan Uzuri ya
bar wajen ba shiri tare da cewa yarinya duniyace bariki ce kici kema watarana ta cinyeki.ni dai
ina fada miki kar ji jawo mana abin kunya a gida ato.
Share shi Amana tayi ta dauki Aabid suka shiga zaga gari,sai wasa sukeyi,sai kallon Aabid
mutane keyi sunga bature dan Madara,gida suka dawo tayi musu girki suka ci suka sha sai
bacci,bayan sun tashi daga bacci,daukansa tayi suka shiga wani boutique na yara,ta siyawa
Aabid wata farar Riga Armless da jean black 3qutr na yara a kantin ta gwada masa dai dai
shi,sweets dasu biscuits ta siya masa da yawa sannan ta kaishi wajen aski dan kansa ba
gyara,nan Amana tasa akayi masa wani arnen aski na yan gayu,na samari masu ji da
Kansu,yaron sai yayi masifar kyau,bayan sun gama gida suka dawo ta cire masa kayan jikinsa
ta wankesu fes ta shanya,abinci suka kara ci sannan tayi wanka shima yaron tayi masa,
Vaseline ta shafa masa hannu da kafa,gashin nan ta shafawa man gashin da take amfani
dashi ta kara gyara masa gyaran gashin da akayi masa,

Turare ta fesa a kayan yaron da ta siyo masa sannan ta sa masa,sosai ta shiryashi yayi
kyau,itama shiryawa tayi cikin wandon jean pencil dogo Red,rigarta T-shirt siririya amma
doguwa har gwiwa tasa fara,ta fesa turaruka sosai,sannan ta dauko siririn gyale Red yafa sai
tayi kyau sosai, Sai kamshi sukeyi,karatun qurani ta fara Koya masa suna yi dama Amana tana son Bawa
yaro tarbiyar karatu,nan da nan yaro ya iya suratul Iklassi,sai wasansu sukeyi har magrib tayi
sukayi Sallah da Azkar,

Kayansa data wanke sun bushe kwasosu tayi ta linke tare da zubawa cikin leda wata me
kyau irin ta gift,bayan Sunyi Sallar Isha ta kara fesa turare ta fesawa Aabid shima sai dariya
yakeyi yana tsokanarta,
Karatun da Amana ta koya masa Aabid yake ta faman nanatawa yana jin dadi,suna Haka Dan
Uzuri ya fado dakin jiki na bari tare da cewa kiyi sauri ki kaiwa masu kudi dansu yana waje yace
kuje.
Tsaki Amana ta ja tare da gallawa Dan Uzuri Harara ta dauki Aabid yana New Anty ci goyani
pls,goyashi tayi a bayanta tare da daukan ledoji biyu a hannunta suka yi waje.

Tana dubawa ta ga motocin sa sai taga wata Azazababbiyar mota guda daya sabuwa gal
me shegen kyau a kalla ta ba million 30 baya,horn ya danna musu nan ta gane yau a mota
daya yazo,karasawa sukayi wajen motar,Aabid sai faman washe baki yake yana rera karatunsa,
Mazaunin baya ta bude tare da saka ledojin a baya,sannan ta bude gaba ta zaunar da Aabid
dake ta faman yin karatunsa,kan Aabid ta shafa tare da manna masa kiss a kumatu good night
my Boy,murmushi kawai yaron yayi tare da fafin Anty Jan kwana da ke,kijo muje jidanmu,zanzo
da kaina Boy never mind ok,kai kawai ya daga mata amma Baiji dadi ba yaso ta bisu sunyi
bacci tare,
Alim Wanda ke a mazaunin Driver tsayawa yayi tsam yana ta kallon Aabid dinsa da Anty
Amana,gashi har karatu yaji a bakin Aabid,gashi ta kaishi aski,ta sa masa sabon kaya abin sai
ya birgeshi shar shar dasu,dubanta ta kai wajen Alim taga sanye da 3qtr da wata black T-shirt
yayi kyau,ga wani kida na tashi a motar me ratsa zuciya,
Amana hannunta biyu cikin aljihu tacewa Aabid bye shima yace bye ta wuce abinta tana
bouncing ba tare da ta yiwa Alim magana ba shima bai mata ba.
Motarsa ya ja ya bar unguwar a nutse,yayinda Amana ta juya ta shiga gidansu cike da
Mamakin halin Alim baya magana ko kadan kuma shi ba kurma ba,ko dan yana da kudi ne oho.
Alim kuwa mamakin yanda yaga Aabid yake neat dashi gashi ta gyarashi harda sabon kaya
ga abinda yafi birgeshi shine karatun da yaji a bakin Aabid yanzu dama wannan yarinyar tasan
addini yana ganinta me kamameceniya da maza Jahila Ashe tasan addini
Tunani ya Shiga sosai akanta.

Dole ya dauketa ta kula da yaronsa kuma shima dole ya gyara mata zama ta daina
abubuwan maza,nan tunaninsa Alim ya tsaya cak.
Kwance Amana take kan tabarmarta tana tunanin gidansu da halayen yan Uwansu nan kewa

ta cika mata zuciya tana so taje gida taga yan Uwanta,da iyayenta amma sabo da halayensu
Sam bata marmarin ta koma,nan take hawaye ya fara kwaranya a idanunta tana tausayawa
Kanta,gasu da iyaye amma ba gata,ba a damu dasu da rayuwarsu ba su dai kawai an haifesu
ne gasu nan a zube a duniya.
Gidan Baki kuwa Baba har yau yaki kai Maryam makaranta tunda aka bashi Amanarta yaki
yarda ya kaita,so yake ya cimma Burinsa,kamar kullum yau cikin dare ya lallaba dakin Goggo
Uwar gida inda Budurwar take,suna cikin bacci ya lallaba ya fara shafa kafar maryam yana
murzawa a hankali,yarinya tana ta baccinta,nan ya kara kaimi ya koma kirjinta ya shiga shafa
boobs dinta a hankali yana lumshe ido,sosai yake washe baki yana latsawa tare da
murzawa,kamar a mafarki Maryam ta mike zumbur tare kwala ihu,Goggo ce ta mike cike da
mamakin Ganin Baba yana ta aikin shafa boobs din yarinya,
Goggo ce tayi tsalle tare da make masa hannu tana zaginsa tsohon banza wlh kayi asara yar
cikinka yar Abokinka Yar Amana kake Neman lalatawa rayuwa,wlh nayi Nadaman
Aureka,matsiyaci mazinaci,fasikin banza kuka ta saki da karfi nan take matan gidan suka fito
dama sun San haka zata faru ba wata wata suka fara zagin Sulemanu Harka shima yana
zaginsu,Maryam sai kuka takeyi,su kuwa ashar ce kawai ke tashi a gidan,
Da kyar Goggo ta lallashi maryam, washe gari da sassafe Goggo tasa Maryan ta shirya da
kanta ta dauketa ta kai ta makarantar kwana tayi mata komai daya dace.
Ko da Sulemanu Harka yaji labari an kai Maryan schl Ashariya da tsinuwa ba wacce baiwa
Goggo ba da sauran matan gaba daya.

Maman Alim ce zaune a kujera sai Huci takeyi tare da tabbatarwa kanta Alim bai isa ya auri
wata ba koda zata mutu sai zabinta,gashi ta rasa inda zata shawo kan Abban Alim,tunani ta
shiga kan taje wajen kawarta Hajiya Talatuwa suyi shawara yanda zasu bullowa abin,tana
zaune wata yar Aikinta cikin ma'aikatan tazo tare da ajiye mata juice tazo tsiyayawa jikinta Na
rawa sabo da tsoro ta zubar da kadan a kasa,kafin ta dago da kanta Mum ta kwada mata wani
mahaukacin Mari kafin tayi wani yunkuri Mum tasa kafa ta daketa nan wannan dattijuwa ta Daki
jikin kujera tare da zubewa kasa wanwar,
Mum kuwa mikewa tayi ta hau sama dalaf dalaf tare da Jan tsaki sunfi goma tare da cewa
shashashai talakawan banza matsiyata.

Alim da jerin motocinsa ne sukayi parking a gidansu,bayan an bude masa kofa ya fito cike da
tafiyar nan tasa ta izza da kasaita sanye yake cikin wata farin yadi kal dinkin fitted ya amsheshi
yasha kyau hannunsa dauke da wayoyinsa guda biyu yana latsawa,cike da yanga kamar
bazaiyi magana ba yayi sallama a palon Abbansa,nan ya samu Abba yana shan fruits,har kasa
ya gaishe da Abbansa,Asiya kanwar Alim ce ta shigo cikin shiga ta alfarma,wata shadda ce
maroon a jikinta tasha aiki,laaa Ya Alim sannu da zuwa kallonta Alim yayi ke kuma yaushe kika
dawo daga kano?jiya Na dawo,bro ina Aabid? Yana schl mana,ya Alim Ya Nura yace ya kiraka
wayarka a kashe,zan kirashi later, ok ,Ya Alim? Tsawa ya buga mata ke kin dameni ban son
surutu,shidai Abba yana jinsu har Mum ta Shigo,
Harara ta zabgawa Alim wato da ban shigo ba Abbanka kawai zaka gaisar ka wuce ko?am
sorry Mum tsaki taja, nan Abba yace sarkin kishi aikinki kenan kishi.

Shuru tayi daga bisani tace dama haka zakace mana tunda sun nuna sunfi sonka, kallon
Alim tayi tare da cewa Ina jikana? Murmushi yayi tare da cewa yana nan lfy yana schl.
Hirar Nura dake Finland suka farayi Mum kuwa daure fuska tayi bata kaunar ayi mata zancen
Nura saboda ya gudu da matarsa yana Nuna mata so,sun kwace mata yaro suna cin kudinsa a
banza ya daina sonta.

Alim shikam halayen Mum dinsu mamaki ke bashi,Asiya ma Sam bata kaunar halayen
Mum dinsu,
Yau Sunday yaune Alim ya shirya domin kai Aabid wajen Amana saboda ya dameshi kan
yaje wurin Antynsa.
Amana kuwa yau bala'i ya sameta sunyi fada da wani Igbo yayan manager sosai sukayi fada
akan ya shafa mata wuyanta,
Zaginsa ta farayi Wanda ya fusata ya cafki boobs dinta a taron mutane,nan take Amana ta
dauki kujera ta kwada masa a kai,sai jini tako ina,

Ba tare da Manager yayi tunani ba ya fesawa Amana mari har Uku tare da korarta daga
wajen aiki. Ita Amana ba korar ce ta sata zub da hawaye ba illa irin yadda bro din manager ya
shafa mata breast agaban mutane Wanda ba a taba kwatanta mata hakan ba,

Tun Saturday da yamma tana gida tayi kuka ta gaji har yau Sunday idan ta tuna Babansu
Sulemanu Harka shi ya ja musu sai kaga Hawaye Na sintiri akan fuskarta idonta ya kumbura
yayi jajir bata da wani kuzari,gashi wani marar Imani yana binta bashin dubu sittin 60 gashi
kudin hayarta ya kare Dan Uzuri ba mutunci,abincinta saura kadan ya kare dama da aikin ta
laru zata biya wasu don Dashi take son shiga dama sai ta samu ta rage wasu to gashi aikin da
ta dogara ma dashi an koreta.

Addua takeyi sosai da nafeela kan Allah ya kawo mata mafita a wannan Al'amari,11am tana
zaune a dakinta tayi tagumi hawaye Na zuba Dan Uzuri ya rufto dakin ko lura da Kukan da
takeyi baiyi ba yace ke yar chakwaskwas kizo inji masu lokaci me kudin nan yana waje ya bar
dakin da sauri kamar zai kifa.
Fuska Amana ta wanke idon nan a kumbure jajir dashi ta fito, Wanda ke binta bashi taci karo
dashi,yana busa sigari yace ke yayane?kwana 2?ina kudin ne? Fuska a daure Amana tace
kasan bazan ci ma kudi ba dama lalura tasa Na karba, ke yarinya naga kina wani masifa ne,mu
zakiwa Jan ido dan me cin uwarki yanzu Na makeki kuma wlh gobe ba mutunci dole
kibiyani,dalla ware banza, Amana yau dan tana cikin Bakin ciki ne da tuni an kwashi yan
kallon,Alim dake mota sauran jerin motocin suna bayansa yana kallon Abinda ke faruwa, kuma
da Alama fada sukeyi.

Tunda ta taho yake kare mata kallo yau salab salab take tafiya fuskarta ba annuri, ido ya
kumbura Jajir haka ta karaso jikin motar kanta a kasa tana wasa da zoben azurfarta me
matukar kyau.

AsmaBaffa
✳CIRANIN AMANA✳


35-40



By
AsmaBaffa




Ina ganin sakonninku ta ko ina readers ina godiya sosai.





Tun kafin a bude motar Aabid ya fara ihu da murna yana kiran New Anty,idonta cike da
kwalla ta daga masa hannu,ganin zata iya fara kuka yasa ta yi saurin bude motar tare da
daukan Aabid ta juya cikin sauri ta bar wajen,Alim kuwa yasan tabbas da gani tana cikin
damuwa ba haka ya saba ganinta ba. Motocinsu suka juya suka wuce direct office ya nufa,ita kuwa Amana yini sukayi da Aabid
yana debe mata kewa,bakin cikinta ya yaye sai dai in ta tuna sai kaga tayi shuru kwalla Na
Neman zubo mata,karfinta ya gaza,mace me raunice tunda ta taso cikin wahala take tunda ita
ke ciyar da kanta,Sana'a kala kala da rayuwa duk tayi,gashi yanzu ba uwa ba uba ba wani
Wanda zai taimaka mata ko tana kusa dasu baza su amfana mata komai ba,sai bacin rai da
bakin cikin halayyar su,a rayuwa ta ya mace ace babu Wanda ya dau nauyinta,ita kewa kanta
komai ,dole yanzu ta gaza kuma dole ta shiga wani yanayi.

Wajen magrib sukayi wanka ta shirya Aabid ta mayar masa da kayansa da yazo dasu tare
da fesa musu turare,wani cornflakes ta hada musu ita da Aabid suka sha suka koshi,sunayin
Sallar Isha wani ya shigo tare da sanar da ita ana kiranta a waje,

Aabid ta goya suka fita dan tasan bazai wuce Daddynsa ba,tana fita ta hango wata bakar
mota me shegen kyau da tsada guda daya,da alama shi ya kawo kansa,wajen ta karasa yana
zaune a mazaunin driver cikin shiga ta alfarma,kamshi da kyalli yakeyi,ba bata lokaci ta bude
gaban motar ta zaunar da Aabid Wanda ke kuka shi wajenta zai kwana,da kyar ta

lallabashi,haka kawai taji bakin cikin dake damunta ya dawo sabo dal,nan take ta fada tunanin
rayuwarta bata da wani plan,bata ma San inda ta nufa ba,ita ba karatu ba,ita ba aure ba to
waye ma zai aureta a haka,ga shi bata ma gaban iyayenta su Burunsu ta nemo musu kudi,ba
ruwansu da halin da zata shiga, Nan take zuciyarta ta kara karyewa ita waye ma zai so ta a haka yanda take kamar
namiji,wani hawaye masu dumi da zafi ne suka shiga ambaliya a fuskarta,sheshekar kuka ta
farayi ba shiri ta rungume Aabid kam kamar zata Fasa masa kashi taci gaba da kukanta a
hankali,duk inda taso danne hawayenta da zuciyarta abin yaci tura,
Shuru kakejin motar babu Wanda yace ko ehem,kukanta kawai ne ke fita kadan.
Alim kuwa wani tausayinta ne ya lullubeshi da alama akwai Matsala babba tare da ita,bai ce
mata komai ba illa bundle Na 1k dubu Dari kenan ya mika mata,Aabid kuwa shima kukan ya
fara,yana Anty wane ya dakeki?

Ki fadawa Daddy ya fadawa sojoji,murmushin yake Amana ta farayi ga hawaye Na zubar
mata har ta samu saukin zuciyarta,ba tare da ta kalli Alim ba cikin rawar muryar me kuka tace
Na gode Allah kara budi ta juya tare da barin wajen tana share Hawaye.Alim yayi tunanin bai
kamata yanda take kula da dansa ba ya kyaleta haka iya kudi kawai ya bata bai ji matsalarta
ba,

Horn ya danna mata Wanda ba shiri ta juyo a firgice tare da dawowa wajen motar budewa
Alim yayi tare da kiranta ta side din kofar sa,ya kai 5mnt tana tsaye gabansa ba tare da yayi
magana ba,da kyar ya furta what's wrong with u?meke damunki?da kyar ta kalleshi kadan
sannan tace ba komai Na tuna iyayena ne,suna ina parent din naki?ko sun rasu Alim ya
tambaya.
Hawaye ne ya zubo mata sannan tace suna kano state, CIRANI aka turo ni lagos Neman
kudi,
Da Sauri Alim ya zaro ido waje Ci...ra...ni? Kai ta daga masa tare da cewa yes,mamaki da
alajabi ne suka cika Alim,yace aikin da kikeyi fa yau naje bakya zuwa?ae an koreni munyi fada
da wani yana son taba min jiki that's y.

Tausayinta Alim yaji tare da cewa wannan Unguwar da kike a lagos bata mutanen kirki
musulmai bace,gidan da kike zama Na karuwai nai,hmmmm aini na jawowa kaina tunda da
yarda Babanmu ya kawoni cirani, Amana tace tayi shuru.

Damace tazowa Alim dan haka yace ko zaki Bini gidana Na baki aikin kular min da
Aabid?matarkafa?cewar Amana,ta Dade da rasuwa,eyya Allah ji kanta, ameen cewar Alim,jeki
gobe zan turo driver ya daukeki kiyi shiri.OK tnx Allah kaimu.
Nan ta wuce shima ya bar unguwar cike da mamaki.

Amana tana komawa dakinta tsalle, rawa,sannan tayi nafeela ta godewa Allah cike da murna
ta fice kudin da Alim ya bata ta je a Daren ta biya bashin da ake binta,
Bayan ta dawo gida Dan Uzuri tayiwa bayani sannan ta bashi kyautar dubu goma sai murna

yakeyi.

Washe gari da wuri Amana tayi shirin komai iya kayan sawa Dana kwalliya ta dauka kawai ta
zuba a wata trolley da Manager ya siya mata kafin suyi fada,kayan girki etc kuwa duk ta bawa
Dan Uzuri su.

Har kayan sawa ta bayar da wasu iya sababbi ta eba,har boutique taje ta kara siyo inner
wears da wasu kayan ta shirya komai irin zata koma gidan yan gayu masu kudi.

Yau Abincin da Amana taci ma me tsada ne,tun 3pm take jiran azo a dauketa amma shuru
har tayi la'asar shuru,sai wurin 5:30pm sannan wani driver da motarsa daya me kyan gaske
yazo Duk Wanda Amana ta sani dake unguwar sai da tayi musu sallama,da ance unguwa zaki
canja da zama? Sai ta yatsine fuska tana yanga sannan tace wlh kuwa Na gaji da zama a nan
unguwar tayi min kauye da yawa,Na samu babban aiki a company, haka Amana ta dinga
sambada karya kala kala ita

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login