Showing 9001 words to 12000 words out of 105161 words

Chapter 4 - CIRANIN AMANA BOOK COMPLETE BY Asma Baffa .pdf

22 Mar 2025

13645


Hausa girl How far noooo?tsaki taja tare da riko hantsar wandonta tace a dey woooo bro
Steven ,how u na?am fine,wani yorubane ya shigo Frnd din manager shima yasan Amana nan
ma suka tafa yana up my girl,u r shining beb,murmushi tayi me kyau wanda ya sumar da
mutanen wajen,that's my man cewar Amana,taci gaba man I need a job here,life no easy my
man,u know everything Sir,u know how things work,murmushi manager yayi never mind my
Frnd u don't have problem with that.nan manager ya bawa Amana aikin me kawowa mutane
Abinci,

Za a dinga biyanta 10k duk wata,tayi murna da godiya sosai,a ranar Amana ta fara aiki
sabida dama ma'aikata basa sa Uniform,dan danan mutane suka saba da ita amma iya maza
dan ita bata kula mata sai maza
Tsakaninta da mata hi hi kawai.yau duk Wanda yazo wajen suya meat dinan da nishadin
Amana yake tafiya,dole ta baka dariya,tunda Amana ta fara aiki anan basu sami Matsala da
kowa ba,aikinta takeyi,sosai suke jin dadin aiki da Amana a wajen,sun kara samun customers a
wajen sosai dalilin Amana Amana tayi 3wks a wajen wannan suya Meat kamar kullum duty yamma takeyi 5-10pm
sanye take cikin Riga fara kal yau ma iya Gwiwa me rubutu da manyan baki Golden a jiki,rigar
me hannun singlet din mazace amma ta mata,sai ta Dora wata yar top iya kirjinta ta tsaya
amma me budadden gabace top din Golden color, Wandonta blue jean,da dan karamin takalminta kamar canvas amma dan siriri me kyau
Golden shima,p-cap Golden,ga wata doguwar sarka har Rabin cikinta da wata karama da yar
wata a makale a wuyanta,a takaice sarka Uku ce a wuyanta duk wasu yan sirara kamar zaren
Sarkar Gold haka suke sunyi bala'in mata kyau,powder da pink lipstick kamar kullum su ta sa, Manager ne ya zo wajen Amana jiki na bari,kiyi Sauri za a hada take away a kaiwa master
mota,wanne master kuma Amana ta tambaya?baza ki gane ba shine Wanda yafi kowa a kudi a
masu zuwa wajen nan,ke kaf lagos kafin ki samu Wanda ya fisu kudi sai kin tona,zaki dinga
jinsu a news.jiya ya dawo daga America,cikin harshen turanci suke maganar.
Baya shigowa yana mota,watace a cikin ma'aikata ta shigo a guje tana manager kaga ga Sir
can kaga cars dinsa sun kai 12 wasu kala da babu irinsu,tabe baki Amana tayi tana kallonsu
yanda suka haukace akan sunga me kudi, kafin kace me masu hada suya meat sun hada me
uban yawan gaske diff colors,Amana ce ta karba tana budawa tare da takama da isa tana
bouncing,ta isa wajen jerin motocin nan,ita kanta ta firgita da ganin hadaddun cars din,
Wacce tafi ko wacce kyau ta nufa kafin ta karasa guards sun tarbeta a hanya tare da karba

Can gaban motocin Amana ta ga ana fada mata da maza,wajen ta karasa tana zaginsu da

turanci,kafin kace me Amana ta siye fadan,ta zagesu sannan ta juyo zata koma cikin wajen
aikinsu yayinda motocin Master suka taso suna garawa a titi a hankali,
Juyawa tayi ta kalli motar ai kuwa sukayi ido hudu da me kyau Wanda ta taba taimakawa da
yan fashi suka taresu,Amana bata taba jin tana tsoron wani ba sai wannan me kyau din,mugun
kwarjini yake mata,
Ya ganeta tsab amma sai ya dauke kai kamar bai taba ganinta ba,itama Amana hakan tayi
don bata son raini.

Amana zaman lagos yasa ta fara zuwa wata hadaddiyar football stadium,manager ne yake
daukanta a motarsa ta rakashi haka wuraren hutawa na manya Steven yake kaita,manager
steven ma akwai kudi ba laifi ga son jin dadi da hutawa,
Shi yasa tunda Amana ta zama best Frnd dinsa take jin dadi, yana kashe mata kudi ya siya
mata irin kayan da take sawa masu tsada,abinci taci me kyau har saloon yake kaita.

In kaga Amana yanzu zakace wata mawakiyar raps ce tazo daga turai,gashi motocin
manager tana driving dinsa yanda take so,Amana ta iya mota both auto an manual tun a
garinsu ta koya wajen maza Frnd dinta yan tasha direbobin Mota,
Shi yasa ta iya tuki sosai,haka tukin machine ta iya,keke,ta iya sweeming sosai shi yasa ma
take zuwa beach na lagos,karambani ne da Amana shi yasa tun a kauyensu ta iya abubuwa da
yawan gaske na rayuwa.

Yau ma manager yace taje gida ta shirya zasuje gym,kamar kullum yauma cikin shigarta take
Riga light blue me dogon hannu har gwiwa,da wandon jean dark brown pencil ,takalminta
Brown tasha sarka guda daya siririya kamar azurfa ta kai har cikinta,
Yau gyale dark brown ta dan Nada a kanta Wanda yasha acuci maza,sai kamshi takeyi,
Wurin aikinsu ta dawo wajen Manager su,yau kamar tafi kullum kyau sai kallonta akeyi,shi
kanshi manager sai da ya kasa dauke idonsa a kanta,yana wow u look so cute,murmushi take
yayin da dimple dinta ya lotsa abin birgewa tare da cewa tnx,haka abokan aikinta ma suke ta
yabawa,manager ne ya karaso suka fito da niyyar fita,wasu kalar Jerin motocin ne suka tsaya
guda biyar ne yau,jikin manager ne ya kama rawa da sauri ya isa wajen motocin nan ya kyale
Amana tsaye.

Glass din aka sauke kasa suuuuuuu da hannu kawai akayiwa manager magana nan ya
gane me master yake nufi, da sauri ya koma wajen Amana tare da riko hannunta, master ne
yace a baki suya meat dinsa ki kai masa,hmm kuma sai ni kadai zan kai?haka yace to,nifa bai
taba yi min ko da daga hannu ba guards dinsa ne suke min bayani sai yau da kansa ya min
magana amma Da hannu ya kwatanta min kuma na gane.
Ita dai Amana shuru tayi nan aka hada mata suyar masters ta fito har motar da taga an zuge
glass kasa ta karasa,ta window ta mika wa me kyau suya meat dinsa shikam kare mata kallo
yayi a ransa yana dariyar wannan yarinya kamar namiji,wani tunani ne ya fado masa a ransa
amma sai ya barshi,kallonsa tayi tana jira taga ko zai mata magana amma shuru sai ma gira
daya dage daya irin lfy? A rude ta tsorata tare da matsawa daga jikin motar,manager ne ya cillo
mata key din motarsa yace let's go,cafe key dayi tare da shigewa motar manager shima ya

shiga gaba,nan fa Amana ta fara tuki cikin kwarewa da bajinta,

Motocin me kyau tayiwa over take ta wucesu fiiiiii, bayan sati daya yau suna wajen da
manyan masu kudi suke zuwa domin wasanni,wasu ball,wasu table tennis,handball,bolly
ball,wasu keke suke tukawa etc kowa da abinda yakeyi a wajen,wajene kamar a england,wajen
manyan masu kudi tsabar son jin dadi irin na manager ya dauki Amana suka je wajen suma,
Amana dama ta iya table tennis da football ba laifi,dan haka wani dan yaro ta gani me
matukar kyau fari kar dashi,yana gefe yana buga ball dinsa shi kadai,manager yana can zasu
fara handball da wasu,
Amana zama tayi shuru ita daya,wajen yaron nan ta nufa tace let's play nan suka fara buga
ball dinsu sosai,sai nishadi sukeyi kamar wani danta,sai yi sukeyi abin birgewa shi kanshi yaron
yaga Amana ta iya ball,suna ta dariya,me kyau ne a tsaye a bayansu ya jingina da wata bishiya
ya harde hannaye a kirji yana ta kallonsu, sai murmushi yakeyi.
Amana ce take ta cinye dan yaron nan da bai wuce 3yrs ba,haushi yaron yaji tare da kwace
ball dinsa ya kwadawa Amana a jiki,ya dauki juice din dake kusa dashi ya watsa mata,tare da
rufeta da duka,
Amana a ranta ta tabbatar wannan yaron bashi da kunya bashi da tarbiya,sai zagin Amana
yakeyi,nan fa ran Amana ya mugun baci da wannan sangantarcen yaron marar tarbiya,tun yana
dan haka amma yake irin wannan abu na cin mutunci,cinci (kinci) uwarki tayaka(talaka) kawai
wannan yaron yace da Amana, Amanafa ta gama kulewa ba imani ba tausayi ta sa kafa tayi short da yaron nan,nan yaron ya
fadi can Tim bakinsa ya fashe sai jini,har wajensa taje ta mikar dashi ta fesa masa maruka har
biyu,fuskarsa ta kumbura,dagashi tayi sama da hannu daya yana kuka yana am shory(sorry)
Anty,bajan kayaba,zare masa ido tayi baka da kunya kana zagin manya,ko Baka da
tarbiya?idan ka kara zagin wani na kamaka sai na ballaka na yankaka,

Jikin yaro na tsuma da karkarwar tsoro,ga baki na jini fuska ta kumbura,yace bajan kayaba
promise u Anty.
Saukeshi tayi kasa ta zaro wani farin handkerchief ta goge masa bakinsa da fuskarsa,sannan
ta bashi ruwan roba yasha,harda wanke masa fuska,tare da goge masa kayan ball din daya
sa,bayanta ta juya tare da cewa sorry my boy Kaine u r too stubborn boy,gashi ka jawo zan ma
illa,shoyi(sorry) Anty,ya haye bayanta tare da sakalo hannayensa ta wuyanta yana wasa da
sarkarta,keke taje biya kudi tare da cewa yaron little rikeni kam zamu tuka keke,
Dariya yaron ya kamayi yana murna ya riketa kam kam,ta hau keken dashi a bayanta. Ta
dinga tuki liiiii liiii iska na kadasu,yaron sai dariya yakeyi,

Bayan ta gama ta kara karbar hayar machine Lifan nan ma yana bayanta ta dinga tukasu.
Bayan sun gama yana gadon bayanta suna zaga wajen yayi bacci a bayanta.

AsmaBaffa
✳CIRANIN AMANA✳


20-25



By
AsmaBaffa





Wajen jakarta ta koma ta dauko wani dogon towel karami a ciki ta Goya yaron dashi a
bayanta ta daureshi tam tam,ta koma cikin bishiyoyin dake wajen tana ta dan yawo dashi tana
jijjigashi,tana jin son yaron a ranta tana inama danta ne wannan yaron, wajen table tennis ta
koma duk table din a kwai mutanen da sukeyi wani table ne guda daya taga mutum daya ne a
wajen securities sun zagayeshi suna bashi tsaro,yana ta buga tennis dinsa a nutse,wajen ta
karasa tare da cewa Hello guys,juyowa mutumin yayi sai taga Ashe me kyau ne a wajen,
Guards din yayiwa umarni su dan matsa gefe ba tare da yayi magana ba,a ranta tana ko dai
kurma ne mutumin nan,Allah sarki na tausaya masa,ga kudi ga kyau sai Allah bai bashi kunnen
ji ba,Allahu Akbar,ita kadai take zancen zucinta ta,
Maganar kurame tayiwa me kyau da hannu wai tazo su buga game,a ransa yayi dariya wato
ta zata shi kurma ne gashi har maganar kurame take yi masa,

Sai satar kallon yaron da ta Goya a bayanta da towel yakeyi Wanda yake bacci hankali
kwance,da hannu ya tambayeta wannan dan natane?ai kuwa tace ae tare da murmushi tana
kara jijjigashi,shareta yayi still tana tsaye a wajen sai buga game dinsa yake
cike da nishadi ko wannensu,gashi ta gama kasheshi da dariya kamar wata namiji yanda
takeyin abu,a ransa yana gata me kyau she need to change her character wa zai aureta a haka,
Yaron dake bayanta Wanda take cewa little boy shine ya farka daga bacci,
Ido 4 sukayi da me kyau da yaron nan yaron ya buga kara tare da cewa Daddyna kayyi(kalli)
nayi new Anty tace na daina zagin mutane,ta hau dani keke,da yifan(Lifan) har ma zaneni tayi
Dana jageka(zageta), murmushi me kyau yayi Wanda ya jawo hankalin Amana kansa ta kura
masa ido tare da jinjina kyau irin na wannan mutumi. Yaron dake bayanta ta kwance ta saukeshi,da gudu ya tafi wurin me kyau,me kyau kuwa sai
kallon yaron yakeyi yanda Amana ta fasa masa Baki tare da kumbura masa fuska,
Da sauri Amana tace my boy ina zuwa Jakarta ta dauko ta zaro wasu chocolate masu dadi
guda 4 da sweet ta mikawa yaron,sai murna yaron yakeyi yana new Anty zakijo
jidanmu?murmushi tayi tace yes,yace mu dinga kwana taye kina kaini cukul(SCHl) OK my Boy

zanzo insha'allah,bye Amana ta dagawa yaron hannu tayi tafiyarta gabanta sai faduwa yake
sakamakon me kyau da take gani kusa da ita,sai da ta bar wajen ta samu saukin zuciyarta ta
daina bugawa.

Wurin Manager ta koma shima ya gama game dinsa suka wuce take away ya siya itama
Amana ya siya mata ya sauketa a gida kana ya wuce. Shi kuwa me kyau securities ya wa
Umarnin su zo akai yaronsa hospital a dubashi, ana ta jin labarin me kyau,
waye me kyau?

Me kyau dai Amana ce ta sa masa suna amma asalin sunansa ALIM USMAN
MUSA,Babansa USMAN MUSA DA MAHAIFIYARSA FATIMA asalinsu yan Ethiopia ne,shi yasa
idan ka gansu kamar wasu larabawa don a Ethiopia ma su daban ne kalar nasu kyau ya wuce
na kasar Ethiopia, Gaba daya dangin Fatima da iyayenta du suna kasar Ethiopia,

yayin da family Usman na jini suke a Nigeria,sabo da su dama su Usman Baban Alim da
kannensa su Biyu a kano aka haifesu,anan suka taso suka girma har Sukayi karatun degree
suka gama,dukiyar su ta gado ce tun asali su masu kudi,sun gaji dukiya,basa aikin Gomnati sai
zallar business,Usman duk yafi yan uwansa kudi nesa ba kusa ba,sabo da yafi yan uwansa
neman kudi,
Babar Usman wato kakar Alim,da kannen Usman Haj Sameera da Alhj Ishaq da iyalansu
suke zaune a birnin kano cikin shahararriyar g.r.a shi kuwa yayansu Usman Musa sabo da
harkokin tafiye tafiye da business ya koma Lagos da zama tare da matarsa da yaransa, Haj
sameera tana auren wani engnr da yaranta maza uku mata biyu, sai Alhj Ishaq yaransa bakwai
maza 5 manyan samari sai mata biyu,ko wannensu mata daya daya garesu,babu me
biyu,kuma alhmdllh suna zaune lfy suna zumunci cikin so da kaunar juna,kasancewar matar
Ishaq yar kano ce basa shiri da fatima matar Usman,

Sameera ma kanwar Usman basa shiri da matar Usman saboda da bata kaunar dangin mijinta
kaf,Fatima bata son kowa ya rabesu har Babar Usman wato Haj khadija,suna kiranta Hajja,
Usman zuwansa ethiopia wajen sauran danginsu a nan Allah ya hadashi da Fatima kyakyawar
mace ya aureta har Allah ya azurtasu da yara.
NURA shine na farko 38yrs yake yana da mata zainab da yara biyu mace da namiji,yana zaune
a Finland can yake aiki tare da iyalansa, sai ALIM me kyau yaro da kudi yafi kowa kyau a
gidansu,ga dukiya da Allah ya azurtashi dasu,yayi degree da masters nasa a harkar kasuwanci
a Germany, 31yrs yake, ASIYA 25yrs take wata uku kenan da gama degree dinta a London, sai
Ameer Wanda yake Finland wajen Nura yana karatunsa yana level 2,21yrs yake kuma shine
auta.

Ranar da yan fashi suka tare Alim kano yaje wajen danginsu ya dawo yan fashi suka taresu
har Amana ta taimakeshi,
USMAN MUSA Baban Alim dattijon arziki ne,me hakuri da kyauta tare da son talaka,duk inda

ake Neman mutumin kirki to azo wajen Usman Musa,
HAJ FATIMA kuwa Sam bata da mutunci ko kadan,bata son talaka,bata kauna wani ya rabi
yaranta musamman Alim da yake me kudin gaske,
Bata kauna taga yaranta maza suna son wata mace don kar ma ta kwace mata yara,kishi
takeyi sosai da matan yayanta maza,Nura ita ta zabo masa mata yar gidan wani kusa a Nigeria,
bata kauna taga Nura na nunawa matarsa soyayya wai zata kwace mata yaro,sai ta dinga
kishi,da farko da ta sa Nura ya auri Zainab sai murna takeyi ganin Nura bai son
Zainab,kasancewar zainab ta gari ce sai ta sace zuciyar Nura,ganin Nura na nunawa zainab so
tace lallai sai ya saketa,Nura kuwa yaki yarda haka Abbansu ya nemawa Nura aiki a Finland ya
turashi can da iyalinsa,sai bakin ciki Mum Fatima takeyi,

Amma tace duk ranar da Nura ya dawo Nigeria dole ya saki matarsa Zainab,shi yasa Nura
yaki dawowa Nigeria,yana son zuwa amma halin Mahaifiyarsu bazai barsu ba,Abbansu ma ya
ce kar ya dawo,shi kanshi halin Fatima matarsa na damunsa,yanda take wulakanta danginsa da
Wanda ya rabesu gashi yana kaunar matarsa,addua kawai yake mata Allah shiryeta.
Alim yaro da kudi,babban dan kasuwa ne na gaske,sosai yake neman na kansa,bai dogara da
kayan wani ba,da kudinsa yake harka,me kwazone da basira tare da zafin nema,ya mallaki
dukiya da kadarori masu matukar yawa tun yana 17yrs yake Neman nasa yana karatu yana
business.dan Jari Abbansu ya bashi me yawan gaske ya fara juyawa,kafin kace me Allah ya
albarkaci abin.

Kyakyawan gaske ne na karshe,fari ne sosai sai kace dangin turawa,idanunsa ma dara dara
masu kyau wasu Golden kamar irin kalar na mage shi ba na mage ba,irin dai na
turawa,gashinsa kuwa baki ne sosai me santsi da kyalli,girarsa kuwa wow har hadewa
takeyi,hancinsa siriri ba sosai ba,normal hanci me matukar kyau,bakinsa karami da shi red,
habarsa yar doguwa,dauke da siririn saje da dan gemu kadan,sumar kansa ya tarata da dan
yawa gyaran gashin sa ma abin kallo ne,

jikinsa me yar kiba ba ramamme ba kuma ba me kiba ba,gashi karkarfa da damatsa,kirjinsa me
fadi sumul dashi,gashi dan dogo dashi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login