Showing 63001 words to 66000 words out of 105161 words

Chapter 22 - CIRANIN AMANA BOOK COMPLETE BY Asma Baffa .pdf

Advertisement

22 Mar 2025

13730

bata kulasu,Matar Nura ke Kula da Aabid sosai.Mum
kuwa kullum kuka takeyi harda Jin haushin Abbansu Alim shi ya cuceta ya tura mata da yaro
aiki wani state.

Amana na kallon yanda Iklima yar Sa'adatu take kallonsa ta faki idon kowa ta dallawa Iklima
harara,radawa Alim tayi tashi mu tafi tare da tamke fuska wai haushi,a hankali yace mu dan
zauna ayi hira ko ma Saba dasu,Amana tace pls kaga ni Bana son wani sabo,mu kadai zamu
dinga rayuwarmu. Me za
Muyi a wajensu dama mutuncin makwaftaka yasa muka shiga,
Sa'adatu ce ta fito dauke da lemo da ruwa amma Amana tace sun koshi tafiya
zasuyi,Sa'adatu tace da kun zauna munsha hira?Amana tace zamu dawo watarana ai,Alim
yace to Mene mu zauna mana Amana cikin Jin haushinsa tace ko second Biyar bazan kara ba
tashi mu tafi kawai ai yawo zamuje.muje to ya Mike sukawa matar sallama Amana tasa Alim a
gaba kamar danta,suna fita Iklima tace Mama wlh wannan matar tasa masifaffiyace kuma
kamar itace mijin yanda take abu ta gama mallake bawan Allah, wa ya sani ko asiri ta masa da
ganin Alama,Sa'adatu cikin fada tace ina ruwanki dasu ki iya bakinki,Iklima tace ai naga ta
gama mallakeshi wlh har ya bani tausayi.

Alim suna fita Amana tace Allah ya taimaki yarinya watarana ta gwada min hauka kamar yau
ta gane shayi ruwane da kanta kamar kwallon kwakwa,Alim yayi murmushi ke ki kwantar da
hankalin ki ke kadai ce ba Kari don ta kalleni sai me ni kinga na kalleta ne?to me yasa zaka ce
mu zauna?nufina mu dinga zumunci,to bazamuyi dasu ba karma ka jawo na koresu daga gidan
nan.
Sorry sarkin zuciya ni dai ki huce kar mu koma gidan ki hanani Harka,da wasa Amana ta
dalla masa harara sunan Babane fa Harka,sorry na manta I swear
Dariya Amana tayi tare da rungumeshi tsam haba dai ai kome zaka min bazan hanaka komai
ba,ba wannan shirmen ai sai kace yarinya marar tunani,idan ana Jan fada haka ai aure baya
lasting duk fadan da zakuyi da mutum matukar baza Ku raba makwanci ba to dole a shirya da
wuri bare har ya kai ga saki,kiss ya manna mata tare da shafa wuyanta a rungume da juna suke Suna tsaye sai ga Baba tsoho yana takawa da kyar ya dawo daga masallaci ya kara biyowa
ta wannan lungun me duhu,wannan karan tsohon masifa yakeyi a hanya sosai,Alim yace laaa
ga tsohon nan na ranar nan mun ga ta kanmu

Tsoho Ashe yaji me Alim yace yace bakuga ta kanku ba sai Allah ya damkeku da kansa,
Yau ba ta Ku nakeyi ba domin kun Zama Bala'i sai sadaka,
Amana tace Malam me aka maka yau kake fada?yace kedai bari karuwai wlh wasu yarane
suka bata min tsoho ya fara basu Labari wai wasu Samari ne a masallaci kullum sai sun
dagashi bayan an idar da sallah saboda bashi da karfi da kyar yake tashi ma,
Kawai sai rannan matarsa ta haihu gobe suna shine ya bada Sanarwa a masallaci gobe za a
rada suna matarsa ta haihu samarin nan suna jin haka suka saki dariya tare da cewa ah....tsoho
Ashe kana da karfi yanzu har matarka ta samu ciki ta haihu ta wlh baza su kara dagashi ba sai
dai idan ya kasa tashi ya kwana cikin masallaci tunda har yasan zai iya wata ciki,ai kuwa su
Alim suka dinga dariya,Amana tace Baba dai dai sukayi wlh gwara haka,
Tsoho yace ai gwarani ba dan iska bane irinku,karuwai shedanu,Amana tace wlh Tsoho muna
da aurenmu fa,yace ban yarda ba ko sama da kasa zata hade bazan yarda ba kuna da auren

zaku dinga bin lungun masu shegen duhu ba kunya ba komai,
Da Allah kar Ku kara min takaici wai yanzu ace yaronka Bai jawo ma magana ba wasu a titi
na kwararo su dinga sawa zuciyarka na tafasa.
Dariya suka karayi tsoho yace kwayi da wani marasa mutunci.
Alim ne ya zaro kudi masu yawa ya mikawa tsohon Baba ga wannan ka siyi rago ko
tsoho yace wuuu...rufani ka sayani dannan niiiiii na karba kudinku na haramci inma cin hanci
ka bani wato dan na dinga rufa muku asiri kuna shekewa to ni Bana karbar cin hanci,bazan rufa
muku asiri ba,zan karba na gode kuma amma kar kusa rai zaku zauna lafiya a unguwar nan sai
na sa me gidan ya koreku,tsoho ya karbe kudinsa yana godiya,wata mata tazo wucewa Ashe
tasan Amana nan suka gaisa sosai,tsohon nan har ya fara tafiya ya dawo yace Delu wato ke
kike daure musu gindi ko har gaisawa kukeyi?Delu tace kaji tsoho da sa Ido to har duwaiwai na
hada na daure musu karewarta,tsoho yace Bana ja'in ja da matar wani yayi tafiyarsa yana
masifa wlh sai ya tonawa su Amana Asirinsu.

Delu tace tsohon nan sai hakuri ta wuce,su Alim suka tafi yawonsu sosai suke Jin dadin
yanayin.

Saude ce zaune a wani rubabben dakinta dake kauyensu tana waya tana faman sheka
dariya,ba a Jin me suke fada sai dariya r Saude kawai kake ji.
Alim da Amana sun Dade suna zaga garin har 10 na dare sannan suka dawo gida hannunsu
rike da ledar da suka siyo gashashiyar kaza da yogourt.
Suna shiga cikin gidan Amana tace ayi rige rigen zuwa Palo,ai kuwa Alim yace 1,2,3 go suka
zura da gudu Amma Alim ya Dade da shiga Palo sannan Amana ta karaso ciki tana nishi tare
da kukan shagwaba ni... ban yarda ba Allah,dariya sukayi gaba daya suna ta faman haki,ta fara
masa rigimar sai ya goyata,haka ya goyata har saida ta fara bacci a bayansa sannan ya samu
lfy,
Dole ya tasheta suka ci namansu da wanka sai bacci,
2:30 Alim ya farka da rigima ya fara tashin Amanarsa Babyna Baby,cike da maganar bacci
tace naam mene?cikin kulawa tayi magana tana mayen bacci ruwa zaka Sha?yace ae Mikewa
tayi zaune zata bar kan bed ta kawo masa ruwa,cike da sha'awa yace honey naki nakeso
fa,dukan wasa ta kai masa sukayi murmushi nan suka karashe Daren suna ta faman raya sunna.




AsmaBaffa


Ina godiya masu sharhi kune nawa.

✳CIRANIN AMANA✳

150-155



Official




By
AsmaBaffa





ZAUREN QUEEN MERMU DA TASKAR FIDDAUSI SODANGI WANNAN PAGE NAKUNE.
TNX ALL.





Bayan 3months Mum Alim ta shiga damuwa,zuciyarta dankare da bakin ciki,haka
Sulemanu Harka komai sai dai ayi masa baya iya komai ya rame yayi baki ya tashi daga
aiki,gashi Bai yiwa yaransa abinda ya kamata ace iyaye sunwa yayansu ba,bai sauke hakkinsu
ba,ya gama zubar da mutuncinsa duk da cewar suna masa komai da ya dace amma basu
damu dashi ba ko ya mutu ko yayi rai harkokinsu sukeyi domin mazan ma sun koma state din
da suke business wasu kuma sun dawo Kano da kasuwanci duk cikin tallafin Alim gashi Hamza
Babban yaya da kb sun samo matan aure a city har an musu engage,
Badriya ma maganarta da Huzaifa tana tabbata sai karfi takeyi,

Alim ne yayi shiri da safe da wuri yace zaije banki ya curo musu kudi,cikin shadda dakakkiya
yake dinkin fited yasha kyau har bakin titi Amana ta rakashi ya shiga taxi drop ya wuce
Ta dawo ta gama komai na gidan tana Jin zazzabi kadan kadan har ta kwanta tana tunanin
rayuwarsu ita da mijinta,
Gaba daya jinta take bata da lafiya kawai hijab dinta tasa ta tafi hospital sabi da ta tsorata
this mnth bata ga period ba,kuma Alim yace mata indai unguwa ta kama da lalura to ko baya
nan taje kawai ya yarje mata,
Karamin asibiti taje a cikin garin saboda yana da girma garin nasu,ana aunata ciki ya bayyana
a jikinta wata daya,magungunan da aka rubu ta mata ta siya ta wuce da result a hannunta tana

ta murna,ta matsu Alim ya dawo ta bashi labari,
Kasa hakura tayi tun a hanya ta danna masa kira a waya cike da nishadi shauki na kwasarta
tace my Man yaushe zaka dawo? Alim yace nan da 3-4hrs na biya ta wani waje,
Amana ta saki murmushi tare da furta Allah dawo min da kai lfy,murmushi Alim yayi cike da
zallar
Kauna ta gaske sannan a hankali yace Ameen sai na zo me zan kawo miki?anything kawai
cewar gogar,sallama sukayi ta koma gida tare da bajewa a 3seater.
Alim Bai dawo ba sai 9pm ya kwankwasawa yayi tare da murda handle,Amana ta fito daga
kitchen tasha kyau da sauri ya jawota jikinsa yayi hugging dinta yana murmushi sannan ya mika
mata ledar hannunsa,

Wani dan kyakyawan saurayine ya fito fit daga bed room din su Amana yana sweetheart kin
barni ina t faman jiranki kiyi sauri muyi abinda za muyi kafin dare yayi nisa ina da aikin yi
....kamar gaske saurayin nan ya tsaya cak yana hangame baki yace dama cutata kikeyi kin San
kina da aure kika ce nazo, Da gudu saurayin nan ya nufo Amana tare da kwasheta da wawan mari yace kin cuceni
Allah ya isa ban yafe ba nayi tarayya da matar aure.
Ya bude kofa ya fice fit,Yana barin gidan wata dalleliyar mota ta tsaya gabansa ya shige
suka bar garin gaba daya.
Alim kamar gunki haka ya tsaya yayi poster sai hawaye da suke ta bulbula kamar famfo
daga idonsa,Amana kuwa da ledar da Alim ya mika mata da result na ciki na hospital ta saki a
kasa,
Kafin kace me ta sume sharab a wajen,
Alim kuwa innalillahi kawai yake maimaitawa sannan ya shige bedroom ya tattara nasa ya
nasa kaf,ya fito ganin Amana har yau a sume sharab a kasa kallo daya ya mata ya tsugunna
tare da daukan result din hospital dinta ya duba hawayensa ne suka karu kamar ba Namiji ba
ya zauna ya dinga rusa kuka, Yana why....why.....na bar yan uwana da iyayena duk sabo dake,Mum dina ban San wannan
Hali suke ba,sai yanzu Alim ya gane kuskuren biyewa shawarar Amana da yayi sabo da so ya
rufe masa Ido,Mum dinsa tana can cikin bakin cikin rashinsa har cuta tayi sabo da son da take
masa,ta dauki cikinsa,ta raineshi amma yanzu ya gujeta duk da Mum Nada babban laifi amma
uwa uwa ce baza ka biyasu abunda suka maka ba,sune sular zuwanka duniya Harka hadu da
wata,
Amma yayi fushi da Mum dinsa ya barta saboda matarsa kuma yasan dole tana cikin wani
hali tunda duk tafi kaunar Alim cikin yaranta,
Kuka sosai Alim yakeyi,ashe Amana dai Amanarsa take ci,yana ta shirme akanta yana biye
mata,bai taba zatan zata aaikata haka ba,tunani yayi sosai da karfi ya furta
no.no...nooooo...baza tayi haka ba,
Amma Sam zuciyarsa ta hanashi tunani bare wani bincike,ji yayi ya tsani Amana gaba daya
baya kaunar ya bude Ido ya ganta,sambatu yakeyi sosai idonsa jajir jijiyoyinsa sun tashi rada
rada ji yake kamar ya kashe Amana ya huta,
Ya yarda a gaban ko waye zai iya zubar da mutuncinsa kan Amana domin ya faranta mata,
A titi,a lungu,a kwararo,a bainar jama'a duk saboda yayi proving dinta yanda yake sonta,dan

yasa taji duk duniya ba kamarta tafi kowa sa'ar miji,har ana ce masa kwarto sabo da ita,
Abinda watsatsun yan mata keyi a boye a titi yayiwa Amana shi tana matarsa amma duk
wannan Bai hanata neman maza ba,
Ashe makaryaciyace,ta yaudareshi,mikewa yayi da niyar tafiya

Amana ta ja dogon numfashi ta farfado,zumbur ta Mike tare da rike rigarsa tana kuka wiwi
kamar ranta zai fita,da kyar tace pls....ka...sau...rareni...dan Allah wallahii ban sanshi ba,kayi
tunani da bincike sharri aka mana kasan muna da makiya,hannu biyu Alim yasa yaci kwalar
Amana tare da girgizata da karfi ya makata jikin bango ya shaketa sosai tana ta kakari,...
sannan yace ohhh makiya ko......da karfi yace makiya Mum ce makiya ko?Amana ta kasa
magana sai hawaye nan Alim ya jefar ta kasa ta zube rigip,juyawa yayi tare da cewa kar ki sake
ki nemeni,kar naga kafarki a gidanmu bana son ganinki na tsaneki,
Inda kika San zamu hadu kar kibi ta layin coz idan na ganki cikin karaji ya karasa I will kill u.
Result din ciki kuma ki haihu ayi DNA test idan har nawa ne zan karba.ya bude kofa baram ya
kara makota ya bar gidan,
Direct airport Alim ya wuce ya bi flight sai Lagos inda akafi wayo.

Amana kuka takeyi tana salati sallah tayi tayi addua sosai hawaye kuwa yaki tsayawa a idon
Amana,bata San wannan tsinanne ne ya hada mata wannan sharri ba.
Tattara nata ya nata tayi itama cikin dare tana zabga kuka ta bar gidan ko su Sa'adatu bata
yiwa sallama ba,tana fita ta fara tafiya a kasa wani Almajirin kusa da gidansu ya biyota yana
dan Allah Anty ki bani sadaka dare yayi banci komai ba,wani takaici ne ya kara kama Amana ta
kara harzuka ta hayayyakowa Almajiri da masifa cikin kuka kai dalla karka dameni ka kyaleni
naji da matsalata,da wannan matsalar dana shiga gwara na kwana 3 banci komai ba,dallah
matsa ta furta tare da tallafewa Almajiri keyarsa ta jefa masa Dari Biyar,
Tana yin gaba ta hadu da karamar kanwarsu Zaliha ta siyo sugar a kanti na gobe da
safe,Zaliha tace Amana kece da dare yau me ya sameki Baba yana ta nemanki har ya rasu ma
naga su ya Haladu suna ta kuka da Umma,ai Amana kafa tasa tayi short da Zaliha,
Ta kara gaba,Zaliha ta gama kukanta ta bi bayan Amana suka shiga gida,tun daga tsakar
gida taji kukan su Haladu da gudu ta fada dakin Baba,Baba ne a kwance yana ta suma yana
farfadowa ya suma yafi sau saba'in gashi yace Baza a kaishi asibiti ba,an tafi dashi yace duk
wanda ya kaishi asibiti Bai yafe masa ba,haka aka dawo dashi, Amana kan Baba tayi tana kuka ta cakumeshi tana Baba dan Allah karka tafi ka barmu muna
sonka Baba,
Farfadowa Baba yayi tare da damke hannun Amana ya fara magana da kyar Amana...ta....da
yan uwanki Ku yafe min ban muku tarbiyar kirki ba na sabawa Allah da yawa kin min Wa'azi
naki ji ga yanda duniya tayi min juyin wainar Asabe,ki rokar min matana iyayenku su yafe
min,gwaggo uwar gidan Baba tana sheka kuka tace mun yafe maka Allah Baka lfy,
Sauran matan ma suka ce sun yafe suma ya yafe musu domin irin zagin da tsinewa
Sulemanu mijinsu da suka dingayi kullum a maimakon suyi masa addua,
Tari Baba yayi yace Amanata ki koma dakin mijinki na yafe miki ki yafe min kin Sha wahalar
rayuwa na turaki Cirani saboda kina min Wa'azi kaico na,

Badriyya tace Baba mun yafe maka dan Allah kar tafi ka barmu muna sonka,muma munyi
maka laifi sosai bamuyi ma biyayya ba,Sakina cikin kuka tace Baba wa zaimin kayan daki idan
ka tafi wayyo gashi na samu miji gatana ya kare bango ya fadi,kayan daki Baba gashi ko
secondary ban gama ba,Sadiya wacce ke Aure a Gaya lg tace Baba gashi su Hamza sun fara
kudi Amana ta auri me kudi karka tafi baka dangwali dadi ba Baba,

Kb ne yace baku da hankali Ku ta abin duniya kukeyi ko,Baba ne ya fara tari ba ji ba gani
sannan ya lafa,Amana ya damko yace ga Amana nan na daura mata nauyinku gaba daya
saboda nayi Imani duk abinda zan muku Amana zatayi muku shi domin tafi kowa
hankali,kyauta,da son zumunci,Amana ke ce wakiliyata ki rike min Iyalina ki maye gurbina,ga
yayyenki Maza da sauran Ku hadu kuyi zumunci Ku tallafi juna,ku Manyan maza abinda Allah
ya hore muku Ku tallafi yan uwanku Ku hade kanku babu yan Ubanci duk da nasan dama
bakwa nuna yan Ubanci Ku kara akan Nada,
Ku Zama masu hakuri,juriya,hankali da nutsuwa duk fitinar da kukeyi da kuyi kokari Ku daina
saboda nasan kun daina Amma a kara jajircewa duniya ba matabbata bace,hakuri da yafiya
shine komai Ku rike wannan komai akayi muku banda daukan fansa Ku Zama masu yafiya da
kawaici,a tsare mutunci, amma kar Ku bari a rainaku ko ubanye Ku taka masa birki.
Baba ya kara Suma ya farfado ya Dora da nasan Amana da saurin zuciya kike dan Allah ki
dinga salalawa ga maza nan zasu tayaki Ku Kula da kanku,ga takaddun dukiyata nan nayi
rubutu na fitarwa da kowa gadonsa yana nan rubuce a cikin littafin nan,Amana nafi yarda da ke
me adalci ce dauki ki rike a hannunki,Amana dai sai kuka kawai Baba sai nauyi yake Dora mata
Bai San ma

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login