Showing 18001 words to 21000 words out of 105161 words
dole big girl kar a rainata.
Dan Uzuri har bakin mota ya raka Amana yana hawayen karya,yana to 'yata ga number ta a
dinga tunawa da mu,ki tsare mutuncinki kamar yanda Na sanki da kamila,nutsatsiya,a
yafemana Amana yar albarka ya karafashewa da kukan maula, driver kuwa Jan motar yayi ya
dauki hanyar Gidan Alim,Amana kamar anyi mata bushara da gidan Aljanna saboda murna. A lagos dinma wata tsantsararriyar GRA suka shiga wacce kaf lagos ba kamarta a kyau sai
ka cika me Naira za ka Gina gida cikinta, yawanci turawa ne da sauran jar fata suke zama a
cikinta,saboda komai nata tsarin turai ne,gidan da ya fi kowanne kyau,girma da tsaruwa suka
nufa,wani gate katon gaske suka nufa wani remote driver ya matsa sai ga gate yayi sama ya
dage kansa,abin fa ya bawa Amana mamaki da alajabi tunda take rayuwa bata taba sanin
wannan unguwar ba,da badan ita bata da tsoro ba to da tuni ta fara kuka za a yankata,
Cikin harabar gidan kuwa ma'aikata da masu tsaro birjik,wasu sun hau tsani suna goge
glasses Na windows,wasu Na bayin flowers wasu kuwa motoci suke gogewa dukkansu sanye
da Uniform dark blue wando da riga fara,motoci ne birjik gasu nan sai ka rasa wacce zaka zaba,
Wani new design Na sweeming pool kamar kogi haka yake yabi ta wani lungu ya mike sosai
ruwan garai garai blue shar dashi,
Driver ne yace fito hajia,Jakarta ya ja har ciki suka shiga,kalle kalle kawai Amana keyi,kofar
ma wasu numbers akayi dialing,sanyi da kamshi ya bigeta,ga wasu kujeru a palon ko a film bata
taba ganinsu ba,
Wata TV a jikin bango kusan Rabin bango,sai wasu manyan flowers suna walwal da haske
tiririn kamshi Na fita daga jikinsu,sai wani center table Na glass,wanda shima matsa wani abu
akeyi a jiki yana juyawa a hankaki,
Center carpet kuwa dake palon idan ka taka sai ka zata nutsewa zaiyi dakai cikin kasa,tana
nan zaune tana baza ido wata dattijuwa ta kawo mata abinci saida ta cika gabanta da kayan ci
da sha,
Amana da maza ta saba bata Hulda da mata hannu ta dagawa dattijuwar nan tace ai sai Iya
Allah dai ya saka,kallo dattijuwa tabi Amana dashi tunda ga shigar Amana matar a ranta tace
wai wa kuma Alhaji ya kwaso mana me kama da maza haka,
A mazan ma yan jagaliya,wani matsiyacin kallon matar tayiwa Amana tare da tabe baki taja
tsaki tayi gaba,Amana wacce zuciyarta ke tafasa game da matar nan taso daukan mataki sai
kawai ta shareta tare da Dora hannunta a kahon zuciyarta ta danne tana lallashin kanta tare da
cewar sorry Amana calm Down be patients a fili takeyin maganar,Amana duk kayan dake jikinta
ganinsu takeyi masu tsada Na yan gayu amma tana shigowa gidan Alim sai ta raina kanta gaba
daya.
Top din data Dora saman rigarta ta cire ta Dora saman kujera ta gyara zamanta a kasa kan
tiles ita Amana bata son zama ko kwanciya a kan laushi kujera ko bed
Shi yasa ta baje a kasa tare da jawo tiren abinci ta fara ci ba tsayawa hannu biyu ta jefar da
cokular a kasa tasa hannu dayan hannun tana yagar kaza daya kuma ta dauki Apple ta balla,ta
dauki kankakana,ta gutsiri waina ta dangwali miya,ta yagi kaza ta kora lemo ko ruwa ta ebo
fried rice ta watsa a bakinta.
A fili cikin santi tace banza ta fadi Allah sakawa me gidan nan da Aljanna,wuyanta ta Sosa
tace me bamu Allah ka bashi,Wanda bazai bamu ba Allah Bamu tare
Sai da taci tayi bamkam kadan ta rage,Karambanin Amana inda taga matar ta shiga nan ta
mike ta fara lallabawa zata ga mene a ciki,handle din kofar ta murda a hankali sai ta ganta a
wani daki ya gaji da haduwa,wata kofar ta bude ta cikin dakin sai ta ganta a wata doguwar Palo
ya gaji da haduwa yasha kayan alatu,kara mikewa tayi sai taga wata kofar Budewa tayi sai kawai ta ganta a wani makeken kitchen,hade da store,kofar baya kuma ta
kitchen zaka fito compound,
Komawa tayi ta kara shiga kitchen nan fa ta kwashi kallo,fridge ta bude tare da dauko wata
fura bowl guda dan karami tayi sanyi,a tsaye ta shanye furar tas ta ajiye bowl din ta dawo palon
da take,
Wani cycle steps ta gani daga palon yayi sama,ga wata kofa opposite din wacce tabi
dazu,nan ma kara budewa tayi bed room ne da toilet ciki,ta kara bude wata kofar sai ta kara
ganinta a compound amma tana hango wasu part guda biyu a gidan da har can taje taga Ashe
daya part din Na yan aiki mazane daya kuma part din Na baki ne da mata yan aiki,
Baki ta tabe tare da cewar ni dai bazan zauna a bangaren can ba wannan part Din da Alama
shine Na Alim dan haka a nan zan zauna yafi haduwa kajifa Amana,har magrib tayi tana
palon,cycle steps din nan ta fara takawa har ta haura sama,
Wow......nan Amana taga aljannar duniya kiri kiri,wakeken Palo ne yasha kujeru Na garari,ga
dinning can gefe,wata tafkekiyar plasma TV,da wasu manyan speakers,flowers manya, sai
tafkeken hoton Alim a manne,
Jikin bangon kansa abin kallon me,komai Na saman fari kal ne,Na kasan kuma peach
color,yan aiki kuwa light brown ne nasu,
Amana fa ta gama rudewa da kallon haduwar gidan,wani kofa ta gani a cikin Palon guda
biyu,daya ta nufa ta bude a hankali,wani tangamemen bed ne da sip zureriya,sai madubi,har
bedsheet komai fari kal neat,
Ko ina gidan kamshin dadi da sanyin ac, daya room din ta bude subhannallah ta firta a fili
komai fari shima yafi ko ina kyau da tsaruwa, komai Na dabanne,
Alim ta hango zaune kan sallaya yana Sallah, Aabid Na jikin gado a zaune yana game.
Asmabaffa
✳CIRANIN AMANA✳
40-45
By
AsmaBaffa
Murmushi Amana ta saki kana ta kutsa kai cikin dakin da sallama, a gigice Aabid ya waigo
tare da kwala ihu ya rugo a guje wajen Amana tare da daka tsalle ya daneta yana oyoyo new
Antyna I miss u,
Dariya Amana ta saki tare da kankame Aabid suna ta murna tana shafa masa kai,my sweet
boy I really miss u,yau tare zamu kwana,za muyi wasanmu cewar Amana,shi kuwa Aabid Jan
Amana yayi har Bed din Alim yana nuna mata game dinsa,
Amana kuwa ta manta da wani Alim dake zaune kan sallaya yana Azkhar,kan gadon ta haura
tare da Aabid suka fara wasa ba ji ba gani sai dariya sukeyi,kafin kace me sunyi waja waja da
bed din Alim,pillows duk a kasa rabin bedsheet dinma yana kasa,
Alim kuwa ba shiri ya daina azkhar tsananin mamakin me suffar maza ya rufeshi,idan banda
rashin tarbiya taya zata shigo musu gida har bed room ta hau kan bed ko gaisuwa babu ba
komai,in hakane ai tafi Aabid ma rashin tarbiya,ina bazai iya zama da wannan ba,
Rashin tarbiyarta yayi yawa da kuruciya da hauka,ran Alim yayi matukar baci kan abinda
Amana tayi yanzu,wata razananniyar tsawa ya daka musu,wanda suka gigice gaba
dayansu,musamman Aabid nan take ya fashe da kuka saboda ya tsorata sosai,
Cikin tsananin fushi Alim yace ke baki da hankali?baki da tarbiya?dabbar inace ke?dakikiya
jahila wacce bata san me takeyi ba,jakace ke?wa ya baki damar shigowa har part dina,kuma
bedroom har bed dina,zaki shafa min cuta a bedsheet,dakikiya dan Na daukeki aiki ba dama Na
baki da zaki zo ki min halin mahaukata ba, Da karfi yace get out now,Amana wacce mamaki da bakin ciki suka taru suka cunkushewa a
zuciya,idonta ya kada yayi jajir tabbas yau da badan Alim bane Wanda Allah ya sa mata
tsoronsa,kunyarsa da kwarjinin da yake mata to da wani ne yau sai dai a dauki gawarta ko
tasa,amma Alim ne tsoronsa takeji amma duk da haka Amana sakkowa tayi daga bed din tana
kumbura tare da cijewa,tace hey Baabaa control mana ya kake yawa,hannuna tasa biyu a aljihu
tana tafiyar gadara,wannan ai yawa ne master eh idan dan Na hau Bed dinkane ai sai kace na
sauka,ya zaka dinga zagina,
Bed din ta nuna masa idan akan wannan bed din ne easy master ni laushi bai dameni ba ko
a kujera bana zama bare bed a dalilin danka Na hau,amma ka sani bed dasu kujeru basa
birgeni,kaci sa a Kaine ka zageni haka,cije lips tayi jajir dashi gwanin sha'awa tace a kiyaye
master tayi gaba abinta ta dawo palon kasa Wanda aka ajiyeta tun farko.
Alim kuwa mamaki ya gama kamashi yayi mutuwar tsaye,Aabid kuwa kuka ya sa an yiwa
new Anty fada,kukan ne ya dami Alim,ba shiri ya figi hannun Aabid ya sauko dashi palon kasa
wajen Amana,Amana ta bararraje tayi mala mala a kan tiles tana tunanin duniya,kawai tuna irin
zagin da Alim ya mata takeyi, Idonta ya tara kwalla du duniya babu Wanda ya taba zaginta haka sai me kyau,sabo da
bakin ciki kawai kuka Amana ta fara babu damar ramawa.
Yana zuwa da Aabid ya ganta haka kallo daya yayi mata ya dauke kai Aabid ya jefa a kan
cikinta,a firgice ta mike ba tare da tace komai ba tsaki taji ya ja tare da ficewa daga gidan gaba
daya tare da escort dinsa.
Sai lokacin Amana ta sauke ajiyar zuciya tare da saurin kallon Aabid tace kai yaro Daddynka
masifaffe ne wlh,idan Na gaji guduwa zanyi,Aabid kuwa dariya yayi kamar me hankali yace Anty
me kirkine Daddyna,zai daina fushin fa.
Suna zaune suna kallon cartoon wannan matar ta dazu ta dawo tana watsawa Amana kallon
Banza tace taso ki dauko jakarki Na kaiki dakinki,Amana bata ce komai ba ta dauki Jakarta
hannunta rike Dana Aabid har part din yan aiki mata aka kaita,mata birjik kowacce da uniform
dark blue skert da Riga me cola da dogon hannu fara kal,sai gyale dan siriri fari. Ko wacce bin Amana take da kallo,sun ganta kyakyawar budurwa ajin farko,ga shigar niggogi
tayi abin dariya,ko ina matan dariya sukeyi suna gulmarta,
Bata kulasu ba amma sun ga dan gidan Oga Alim a hannunta,wannan ya nuna me renon
dansa ya dauko,
Tunda suka ga haka sai suka tsani Amana suna jin haushinta tare da yi mata hassada tazo ta
fisu fada wajen me me gidan gashi ita CE me renon dansa,sunga irin matan daya dauko a baya
sun sami kudi da fada a part dinsa ma suke zama amma kwana kadan ake korarsu da wannan
suka kwantar da hankalinsu cewar Amana ma korarta za ayi kwanan nan zasu ji abin tsiyarta,
Ko wacce da abinda take fadi kan Amana,har aka kaita wani daki lafiyayye,dan gado karami
sai sip karama da madubi da toilet dinta ba sharing, kamar dakin dai yan mata,komai
yaji,kayanta ta ajiye sannan tayi wanka sukayi sallah tare da Aabid, sannan tayi masa wanka
tare da shafa masa mai sai kamshi sukeyi towel daure a kugunsa,suna ta hirarsu tana koya
masa karatu har 9:30 Na dare sannan Alim ya dawo,ya duba ko ina baiga Aabid da Amana
ba,da sauri ya kira wannan dattijuwar shugabar ma'aikata mata na gidan wato Saude,
Tana zuwa Alim yace Aabid da wannan yarinyar fa?soshe soshe Saude ta kama sannan tace
Na kaita part din yan aiki suna tare da shi a can,harara Alim ya watsawa Saude yace ni nace ki
kaita wani waje har yarona za akai wajen yan aiki?how dear u ko kin taba ganin me kula da
Aabid a part din masu aiki maza ki kawo min su nan,
Da sauri Saude tace ayi hakuri Ahaji hakan baza ta faru ba insha'allah,jiki Na bari cike da jin
haushin Amana ta fada dakin bako sallama,to uwar iya kizo inji Alhaji yana part dinsa ki dauki
kayanki da Aabid can zaki zauna,munafuka saura ayi dan hali muna nan muna zuba ido
kwanan nan za a koreki,kar kice zaki mike kafa matsiyaciya.
Amana ta dau Aniyar cin uban su saude sai nan da yan kwanaki,
Aabid ta nade cikin towel sosai fuskarsa kadai ake gani,goyashi tayi ta kinkimi akwatinta ta tafi
part din Alim zuciyarta cike da tsoro,
Ta rasa dalilin da yasa take jin tsoron Alim,a palon kasa ta sameshi yana kallon
News,sallama dauke a bakinta ta shiga,taga bakinsa ya motsa amma Sam bata ji muryarsa ba.
Aabid ta sauke cikin towel yayi fresh dashi,ba tare da Alim yayi magana ba ya mika mata
uniform dinta,karba tayi tana budawa taga skert, a ranta tace yaufa akeyinta,a fili kuwa cike da
tsoro tace master....master ban iya sa skert ba pls ka bani uniform me wando,
Ko kallon inda take baiyi ba kuma baice komai ba,shuru Amana tayi can tace to Master a
bani kayan Aabid zan sa masa,sannan ka nuna min dakina zan je Na kwanta.
Sai da ya dauki 15mnt sannan ya mike yace biyoni ki karbi kayansa,a hankali ta bishi har
bedroom dinsa ya nuna mata Sip wani part shake da kayan Aabid,akwati ta cika guda da kayan
sawar Aabid har uniform din schl dinsa sanannan Alim ya gwada mata address din
dakinta,godiya sannan ta sauka kasa dakin da ta fara shiga da farko me kofa biyu,daya kofar
wacce zata kaita kitchen,bedroom din ya gaji da haduwa kamar Na Amarya,
Aabid ta shirya cikin kayan bacci itama tasa nata ta sukayi Addua suka kwanta tare,Aabid ya
makalkaleta ya rungumeta sai kamshi sukeyi bacci me dadi ya kwashesu.
Washe gari da asubar fari Amana ta tashi Aabid sukayi sallah abinda Aabid bai taba yi ba
sallar Asuba amma yau Amana ta sa yayi har azkhar ta fara koya masa,ita Amana fa yanzu
bata da burin da ya wuce taga yaro me tarbiya,tana sha'awan hakan saboda gidansu kaf babu
me tarbiya,shi yasa ma ta ke son koyawa yaro tarbiya duk da cewa ita bata da ita,ta sani amma
tana so ta koyawa wani,shi yasa take koyawa Alim tofa kaji su Amana.
Wanka da brush tayiwa Alim sannan ta shiryashi cikin uniform din schl dinsa,ta yi wanka
itama tare da tsaftace lungu da sako Na jikinta sannan ta fara shiri,uniform din Ma'aikata da
Alim ya bata Riga da skert su ta ebo,tana kunkuni tasa pant da wani tight iya gwiwa,sannan
tasa skert din,Amana kwai diri da sura,kamar an gwada ta skert din das a jikinta,sannan tasa
rigar,gyalenta ba fari Alim ya bata ba kalar skert ne dark blue,Amana gaba daya ji take a takure
take ta dabaibaye,ita da wando ta saba,
Gyalen maimakon ta yafa sai ta daura kawai a kanta ta gyaran room din tas,sannan ta fesa
turarenta ta fesawa Aabid ma,7am ta riko hannun Aabid suka haura saman Alim,
Aabid da gudu ya shige bedroom Alim yana cikin bacci yaji Aabid Na tashinsa Daddy ina
kwana Anty ce tace Na dinga Ce maka ina kwana,
Alim a hankali ya mike tare da shafa kan Alim yana morning son har kayi shirin schl,ae Daddy
Anty tana jirana zanci abinci ta kaini schl,maza to jeka kace tazo ina nemanta,
Da gudu Aabid ya koma wajen Amana yace Anty Daddy yace kizo,gabanta ne yayi mugun
faduwa kamar kwai ya fashe mata a ciki haka ta shiga dakin tana tafiya bata saba da sa skert
ba,kawai garin tafiyar niggoginta skert ya hardeta ji kake rim ta fadi a kasan tiles Na dakin
Alim,Alim dake kwance nade cikin bargo yana kallonta,ko sannu bai mata ba,haka ta mike tana
Sosa kanta,tunda Alim yake bai taba sanin uniform din ma'aikatansa Na da kyau ba sai a jikin
Amana,a ransa sai ayyana irin kyanta da kyan diri irin Na Amana amma take cutar kanta kullum
abubuwan maza takeyi.
Ko gaisuwa Amana bata yi ba kawai sallama takeyi ita bata saba da gaida mutane ba,shima
Alim bai damu ba yace kije kitchen ki hadawa Aabid abinci, kece kullum zaki Na dafa masa
abinci,ki kaishi schl ki daukoshi ke da driver,
To kawai Amana ta furta tare da fadawa tunanin family dinta,jibi gata da son karatu, amma su
iyayensu Sam ba ruwansu da ilimin yaransu,gashi suna son karatu ba dama,a fili kuwa cewa
tayi master dan Allah ka sani a makarantar Aabid kaga ni a ss2 Na tsaya sai mu dinga zuwa
muna dawowa tare,
Bazan saki ba cewar Alim,kafin ya rufe baki Amana tace master lada zaka samu Ina fada
ma taimakon irinmu zai iya jefaka a aljanna,Fice min da gani cewar Alim, baki ta zumbura tare
da ficewa tana kunkuni.Alim a ransa yace lallai yarinyar nan bata da kunya karshe,zan gyarata
very soon. Kitchen Amana ta shiga Wanda ke part din Alim,Dattijuwa Saude