Showing 78001 words to 81000 words out of 105161 words
Chapter 27 - CIRANIN AMANA BOOK COMPLETE BY Asma Baffa .pdf
da cijewa,kuma sunyi mukus
suna ta faman ture turen juna,haka suka dingayi sai kallonsu yan biki keyi suna dariya,mitsini
Alim ya kwanyawa Amana a cinya da sauri ta sosa waje tasa kafa ta take masa kafa tare da
murzawa,Alim yaji Zafi amma ya cije, hannu yasa ya yakusheta a wuya har wajen yayi danja
kadan,Mama tace wai me kukeyi haka Ku tashi ku barmin Palo iya shege a cikin bakina sai ture
ture kukeyi da yakushe yakushe, Ku fice Ku karata can,mikewa sukayi gaba daya Amana fuska
ba rahama Alim ma haka,Asiya dariya ta cika mata ciki wannan soyayya haka.
Suna fita tsakar gida Alim ya taho da sauri Amana ta matsa gefe amma saida yazo ya
bangajeta ya fara tafiya,da gudu Amana Ido cike da kwalla ta bishi tare da cafko hannunsa ta
ganya masa cizo da karfi kamar kura tayi hanyar part din yan mata,
Alim sai da ya saki kara,a fili yace sai na balla yarinyarcan ina wasa da itane,ina ruwana da
ita zanyi maganinta.
Amana kuwa daki ta fada tana ai wlh kana min zan rama kaji mutum ina ruwana dashi
saboda yana neman na masa rashin kunya ya ci min mutunci shi yasa yake tsokanata to ni
kuwa bazan kyaleshi ba sai na rama karma yace tsoron sa nakeyi.
Ana ta shirin dinner Amare sunsha kyau,yan mata da samari kowa walkiya yakeyi,ana ta iba
ana tafiya can,Amana ma ta shirya cikin tsadajjen lace light blue da red,gogoronta red,jaka da
takalmi red,jambaki red,sarka dan kunne agogo duk red,pose dinta ma red,tasha kyau na
gaske,dinkin fitted gown fadin kyan da Amana tayi bata bakine,
Har wajen kaka tsohuwa taje har an shirya Aabid,kowa yaba irin kyan da Amana tayi akeyi da
wanda ya Santa da wanda Bai Santa ba,Aabid na Jin muryarta ya dago kansa da sauri tare da
rugowa da gudu ya daka tsalle ya dane ta,dagashi sama tayi suna ta dariya,Momy ina kika tafi
bana ganinki? Amana tace unguwa naje nan suka dinga surutu tare,sai ji tayi gaba daya har an
tafi tana nan,Aabid ta dauka tayiwa tsohuwa sallama,tana fita Alim ma ya fito cikin shiga ta
alfarma kamar wani dan sarki,yasha kyau sai kallon juna sukeyi kowa na yaba shigar dan
uwansa,Alim cikin shadda Fara kal yake komai fari yayi kyau na gaske,suma taci kudi,kamshi
da kyalline kawai ke tashi,
Tunawa Alim yayi ai sunyi fada da Amana basa shiri da sauri ya dauke kai ya juya,Itama
Amana a hankali tace au jaka ni kamar muna shiri na wani kalleshi,to wanne ma kyau yayi shi
din me, me ya hadani dashi tsaki taja ta wuce motarta ta bude tare da sa Aabid a gaba,Aabid
ya fito fit yace Momy ga Daddy can motarsa tafi kyau muje a tasa,Aabid ya kwalawa Alim kira
Daddy ka jiramu muje a taka,Amana tace to bazan shiga motarsa ba dalla wuce muje,Alim ma
yaji me Amana ta fada shima magana yayi da dan daga murya yanda zata jishi ko kinzo ba
daukanki zanyi a motata ba,ko kinji nace zan daukeki dama,da masifa Amana tace oho ko kace
ma ba shiga zanyi ba ehe,kuma a daina kallona za a cinye min kurwa to tawa daci gareta
kurwata kurrrr ta karasa tana huci,.
Alim shi dariya ma ta bashi da birgeshi,kinga na kallekine?baki kyau ba dai,ga masu kyau
can sun tafi party,Da masifa Amana ta hayayyako me zasuci da kai ragowar mata,woooo
ragowar mata an gama da kai sai ragowa zasu samu,mata nawa ka aura me auri saki,ina fada
ma watarana wata sai ta harbeka kowa ya huta, Dariya ta kusa kwacewa Alim sai ya kara mazewa ya tamke fuska yace haka na gani shi yasa
kike bin abokaina kina fada musu su bani hakuri na dawo dake,
Kugu Amana ta rike tace kalleni tsaf na wuce ajinka Malam ai kai na gama da shafinka na
jefa a shara masu kwashe shara sunzo sun kwashe ka an zubaka a katon rami.sai yanzu ma
nakejin haushi kaina na auri Kazami yan... yan... yan.....tana yatsina fuska ta kara da cewa ko
kyau babu,yanzu ma da kasan munin da kayi da baka je dinner ba ta tsaya tare da murguda
baki,
Alim dariya fa yake tayi a zuciya ya samu abinda yakeso,da sauri yace wannan kuma karya
kikeyi yarinya,kuka ne ya tahowa Amana tayi sauri ta maida shi tare da jan kwafa ta shige
mota,Aabid Bai San me sukeyi ba har ya gaji da jira,kowanne ya figi mota ya hau titi suna tafiya
idan Alim ya figi mota ya wuce Amana sai Amana ta cisga ta wuceshi itama, Idan masifa ta ciyosu sai kowa ya danna mugun horn,yanzu Alim zai wuce Amana ya sauke
glass kasa ya zo saitinta da mota ya fara mata gwalo,itama kuwa ta tako da karfi ta masa gwalo
wullo wai dan ta tura masa haushi da yawa ta dallaro harshenta ta barshi a haka,tana kaga
kaga suna hada Ido ta glass tace nafi karfinka baza ka iya Dani ba,na Riga na maka nisa na
wuce ajinka,ta ce woooo wulluuuuuu, ta zuge glass tana haki cike da masifa tace nayi
maganinsa ai Bai isa na kyaleshi ba,bazai ja Dani ba,
Alim kuwa yana rufe glass ya dinga dariya kamar me har suka karasa wajen dinner.tare suka
tsaya Amana da Bala'i ta fito wai irin kar Alim ya rainata.
Alim kuwa ya shirya me zai taokaneta dashi.
AsmaBaffa
✳CIRANIN AMANA✳
170-175
Official
By
AsmaBaffa
MARCYCOOL JINJINA GAREKI,
DUK MASU SHARHI WANNAN PAGE NAKUNE,SANNUNKU DA KOKARI INA MATUKAR
JIN DADI,KUNA KARA MIN KARFIN GWIWA.
Amana rike da hannun Aabid sauri tayi ta shige wurin da ake event din,wow wuri ya hadu
sosai Dinner Baban Ishaq angon Sakina ce yau nasa da ya hada musu aka fara yi,Amare
zaune da angwaye sunsha kyau,wurin ya cika da mata da samari dangin Amare da
Angwaye,ga kawaye da abokai,wanka iya wanka,mata iya mata maza iya maza a wajen nan ba
a magana.
Aabid kuwa da gudu ya tafi wajen Nura da matarsa da yarsu,Amana ana tafiya kwas kwas
sai kallonta ake ta faman yi musamman maza,
Ta wuce zata zauna Ashe Alim yana bayanta duk inda tasa kafa sai yasa,sabo da kida bata
ji tafiyarsa ba,Amare harda dagowa Amana Hanu suna zaune,Badriyya ta dagawa Alim babban
yatsa shima ya daga mata tare da murmushi,Sakina ta masa inkiya da Ido,nan take Alim ya bar
kusa da Amana wajen Asiya yaje tana zaune ita da Ahmad yayan Huzaifa ,Alim fuska ba wani
walwala ya furta Asiya tashi ki janye min wancen Ku zauna tare,
Dariya Asiya tayi tace yaya Da Alama Allah laifi kayi mata shi yasa kabi ka nacewa mata ka
kyaleta ta huta pls,
Zan mareki kije kiyi abinda nace,Ahmad yace kai masifaffe mufa ka ishe mu da wannan
matartaka tunda tazo yanzu duk gidan biki gulmarku akeyi iskancinka gaban kowa yi kakeyi Ayu
kawai.
Kana surikin nawa? ai an kusa bikinka idan naga dama sai na hanaka kanwata ka rufawa
kanka asiri cewar Alim, Asiya kuwa tuni ta cika Umarnin Alim zaune ita da Amana dan auta ma
wajensu ya dawo yana fadawa Amana wai ga wata can dan Allah taje ta hadasu ko zata
soshi,Amana tace dan yaro dakai to ba Dani ba,dariya sukayi,Alim yana kallonsu yana ta Jin
dadi.
Amarya Badriyya da Huzaifa MC ya kira su fito fili ana bukatarsu,Amana ce ta fara mikewa ta
shiga fili, Amana bata rawa bata taba yin rawa ba saboda kar a rainata wai hee baya ga haka
ma bata iya ba.
Yan Dari Dari ta fara lika musu, cikin takun isa da birgewa sai ga Alim yazo ya fara likawa
Amarya da Ango yan Dubu Dubu shima yana liki
Kallon Amana yake yi idonsa na kanta suna hada Ido sai ya maka mata harara itama kafin
kace me ta rama harda murguda baki,
mutane ne suka zo yuuuu mata da maza suka lullube wajen kowa liki yakeyi,wani Namiji ya fara
likawa Amana kudi sosai,Alim takaici ya kama shi,Amana juyawa tayi ta dinga likawa Saurayin
nan kudinta,Alim kamar ya hadiyi zuciya ya sheka lahira,
Kafin kace me ransa yayi bakinkirin,har idonsa ya canja color tsabar bala'in da yakeji,
Yana ta likinsa Bai fasa ba cikin zafin nama ya samu ya shige tsakiyar Amana da saurayi ya
musu kerere a tsakiya tare da ci gaba da yiwa Amare likin Naira.
Amana Jin kamshin turaren Alim yasata lumshe Ido nan take ta fada tunanin rayuwarsu sanda
suna tare yana nannadeta cikin kirjinsa ta shaki kamshinsa da dumin jikinsa son ranta
Matsowa yayi yanda zata ji shi cikin bacin rai muryarsa har rawa takeyi nace ki fita bana so
me kikeyi haka kinawa kato liki for God sake, ko kallonsa Amana batayi ba,cikin karajin da
Amana ce kadai zata ji ya furta zan yi maganinki ki bar ganin Ina wasa dake akan wannan
bazan miki da sauki ba.
Amana ba walwala ta furta sannu Ubana Sulemanu kai awa?mene hadina da kai ta fada tana
Balla masa uwar harara,haka kikace?cewar Alim,Amana ta kalleshi up and down tana fari da
Ido tace wacce grass ce kai ko nace wanne weed ne? Wanne ruwan kwatar ne?wacce shara
ce? Me likawa Amana kudi tuni kudinsa suka kare yayi waje kuma yana jin fadan da sukeyi da
Alim a ransa yace saurayi kayi asarar budurwa sai dai ka koma wajen Bazawara Amma wannan
Budurwar yar dagwas gwas ni zan kwaceta.
Alim da ya tuno me yayi sai ya tuna fada sukeyi ba kishinta yakeyi ba ina ruwansa,
Sai ya canja magana da cewa taimaka miki nakeyi saboda bakiyi kyau ba abin kunyane aga
ana miki liki ke baki ga dariya ake miki ba,Amana taci gaba da masifa Alim kake ko wa?ka sakar
min mara nayi fitsari pls nace bana yinka kaje ka nemi irinka yanzu nafi karfinka ehe yawwa
asakar min mara nayi fitsari,, murmushi Alim ya saki wanda ke kara masa kyau, Amana a ranta
tace mijina me kyau, Alim ne ya katse mata tunani da cewa idan naki fa?
Itama ta fara magana kasan ni ai kasan Halina ko na gwada ma? ni da kake gani na ba
mutuncine dani ba,ni abin kunya idan ya ganni to guduwa yakeyi saboda uwar gidansa tazo
Amana ta furta cikin fushi kamar bata taba dariya ba,Alim yace hmm wanda kikewa ne suke
kyaleki yarinya,Amana ta maida martani gaka nan Babban yaro brolas kajin gidan gona girman
dare daya.
Gadan gadan ya nufi wajenta da niyyar damkota amma Amana da sauri ta sauka kasa tace
idan yau za a kwashi wani zuwa hospital yazo ya biyoni ya gani, masu rawa da liki suka ci gaba
da yi,
Amana tsakaninta Da Allah fada akeyi gagarimi, yanda take jin haushin Alim sosai ba
mutunci,shima Alim haushin Amana yakeji baiga ciki jikinta ba,sannan ta wani manta dashi ta
kara kibarta da kyau,da aurensa a kanta tana ta yawo inda taga dama.
Alim yaga Amana da gaske takeyi karta kunya tashi a mutane sai ya fasa ya koma ya zauna
Amana taci gaba da shagalin bikinta,har aka zo cin abinci inda kowa zai tashi yawa kansa
serving abinda yakeso,ana ta karbowa,Amana ta ebowa Aabid,little Zaliha,da Ikkram din Nura,
Komawa tayi zatayi serving kanta fara Eba tayi Alim yazo ya wani faffake wajen,Amana bata
kulashi ba ta samu ta matsa, kara faffakewa yayi, lekawa tayi tana dogon wuya zata ebo ta
wani cokalo bakin masifa,duk inda ta nufa da niyyar ebowa sai Alim yaje yayi blocking wajen,
Alim haushinta yakeji yanda ake kallonta ana yaba surarta, cokali me yatsu tasa tare da yakuso
hannun Alim ai kuwa fatar hanun ta kwarzabe kamar yakushin damusa, ta eba tayi gaba.
Dinner tayi kyau da dadi,bayan an tashi duk an watse gida,su Mama sun tafi da Aabid,Alim
ya fito ya hango Amana zata shiga Mota shima zai shiga tasa ya murde mata kunne sosai
ya,Amana haushi ya isheta ta sai kawai ta shareshi ta shiga Mota ta figa ta hau titi,Alim ma
haka,
Gani tayi Alim zai wuce ta tayi masa Over taking tare da sauke glass tana masifeshi dan
jagaliya baka iya tuki ba ka koma ka koyi mata,Alim ma ya leko ya kwalla da karfi idan na raina
kasuwa ko sautun Cincin bazan yi ba,
Amana tace dan kauyeeeeee,Alim yace daga birni nazo nazo ai,wai yayiwa Amana gori,
Nafi karfinka dai ni na wayar da kai,
Alim yace ai kin iya daurin dankwali yanzu,Amana tace ance maka da can iyawa kayi? ,Alim
yayi maganar yan daba yace kya nuna mana Zara,ai mune Zara yar nan,
Ni ba karamin tantirin dan iska bane,Amana ta kwallo itama da karfi tace ai kuwa nima ba
karamar tantiriyar yar iska bace kai dukkan mu ba kananan tantirai bane,Maganar ta irin ta
nigogi tayi Baaaaba kana yawa,Alim yace motar aroceee,Amana tace dan mafiya me kudin
tsafiiiii motar da ka siya da kan dan jariri.
Suna karasowa cikin gidan kowa ya Parker tare da fitowa zata wuce part dinsu,Alim ya kama
yatsanta ya lankwasosu baya ta kwalla kara ta kwala masa jakarta,tana haki tace azzalumin
mutum ni ba wasa nake da kai ba
Tafiya Alim yayi ya kyaleta yace yarinyar nan da gaske take amma na kyaleta daga yau ya
furta cikin fushi.
Amana kuwa ciki ta shiga tayi wanka ta canja kayan bacci ta kwanta gefen Sakina da
Badriyya.
Badriyya ce ta Mike ta fara magana Anty Amana ina kika tsaya haka kin San har 2am yanzu
fa,banza Amana ta mata,Badriyya tace dama tambayarki zanyi dan Allah first night da
Zafi?Allah tsoro nakeji,
Amana tayi dariya tace sanda kika dinga zuga Alim kina hadamu daki ki kulle kin nemi
shawarata?
Ki kyaleni naji da abinda ya dameni pls,
Juya baya Amana tayi ta fara tunanin Alim yanda zata daina kulashi ko yayi magana ta daina
kulashi,ita zai rainawa hankali ya mata laifi ko yayi tunanin lallashinta saima wani hade mata
fuska da yakeyi tare da gwada mata mungunta.
Washe gari bayan Anyi sallar Asuba rana ta fito kadan kowa ya koma baccin safe,12pm
Amana ta tashi daga bacci wanka tayi ta shirya cikin doguwar Rigar material Golding color tayi
kyau Sosai kamar a sace ta,Amare da kawaye duk sun dau wanka anci ansha,Amana bata ci
komai ba ta wuce wajen Maman Huzaifa tare da gaisheta da sauran dangi,Aabid ne yazo tare
da makaleta,cike da kunya Amana tace Mama abinci nazo nema,Mama tace ke duk kowa yaci
yasha sai yanzu kika fito ana jira a kawo lunch duk an wanke komai tare da gyarawa,shiga
kitchen ki hadawa kanki,
Kitchen ta shiga ta dafo indomie da kwanta ta dawo Palo kusa da Mama zata fara ci Alim ya
fito cikin 3qtr da Riga T-shirt yana kamshi,Mama tace girman lagos aikinka kenan yawo cikin
Mata kaine nan kaine can ga shigar arna, Amana sau daya ta kalleshi ta dauke kanta gefe,
Matsowa yayi tare da gaisar da Mama kana ya kurawa Amana Ido tana cin Indomie Aabid
yana gaida Alim ya zura da gudu ya bar wajen ya hango yara na wasa,
Alim kuma ya tsuguna ya dauke plate din Amana yayi tafiyarsa da abincin,Mama ta saki baki
tace Alim zan bata maka wlh dawo mata da abincinta,Alim yace Mama yunwa nakeji fa,to ita
kuma fa?Sai ta dafa wata Mama tace sai dai ka dawo kuci tare sai ta kara dafa muku wata Ku
kara, Amana tace ni na koshi kyaleshi,a'a baki isa ba cewar Mama spoon biyu kikayi fa, Mama ni
bazan ci dashi ba Kazami ne fa Amana ta fada da azababbiyar shagwaba wacce tayi sanadin
zukewar numfashin Alim, ajiye Alim kuci cewar Mama, cikin yan uwa duk suna palon,Alim ya
jawo sallaya ya zauna yana masifa yacewa Amana sai ki sakko kasa ai kamar wasu yara,
Amana gudun kar tayiwa Mama musu ga dangi za a gane basa shiri kawai ta sakko kasa ta
zauna Mama harda mika mata pillow ta zauna tana hade rai,
Mama tace Asiya ta je ta dafa musu wata kafin su cinye wannan,
Asiya taso a kyaleta itama taga fadan su Alim amma haka ta wuce kitchen,
Fork spoon dayane Alim ya fisge a hannun Amana ya dinga cin indomie da sauri da sauri
wai dan yafi ci da yawa Amana ta rasa ,Amana ta finciko cokalin a bakinsa