Showing 54001 words to 57000 words out of 105161 words
Chapter 19 - CIRANIN AMANA BOOK COMPLETE BY Asma Baffa .pdf
da wani auren dolen da Mum zata yi min ba,Nura yace
hmmm ai na rasa wanne haline da Umma zuciya ba Imani,Asiya tace ai ni shi yasa na koma
wajen Abban su Huzaifa kusa da masoyina ni kam bazan yarda ba wlh.
Alim wanda magana bata dameshi ba,yace Ku kenan nifa fisabilillah Ku duba komai a kaina
ya kare,aure nawa tayi min.
Yanzufa Amaryace Dani Amarya pls kuji fa ta hanani sakewa na rasa yanda zanyi yanzu taje
duba babanta ba lfy amma Mum ta hanani zuwa cike da shagwaba ya karasa zancen kuma wlh
ni dai I need my wife firewood ne ni ko rock Amaryafa guda,
Dariya sukayi Autan Mum yace hhhhh bros mun ganoka dama ai kai kawai son ehhh...
Zan mareka ban son iskanci ni sa'anka ne,Nura yace kyaleshi bro shi ai Bai San dawar garin
bane.
Tsaki Alim yaja to ni dai a bani shawara guys body fa ba dutse bane,Mum ce ta katsesu
Body yaci kutmar ubansa duk naji me kuke cewa kuma wlh Ku kiyayeni babu dan iskan daya
isa ya ja Dani,ni na tsuguna na haifeku banzaye,ke kuma Asiya kyaleki nayi kika zauna a Kano
wajen wancan tsinannun wlh ki kiyayeni dakikiya. Huzaifa dake gefe yayi kus baice komai ba dan ya gama shiri gobe yakeso ya bar gidan nan
ya gaji da jarabar Mum ta safe daban ta rana daban haka ta dare ma.
Dan Auta ne ya fara kunkuni yana turo baki Bai aune ba yaji Mum ta zuba masa rankwashi
a kai.
Mikewa Alim yayi cike da bacin rai ya koma gidansa shi da Huzaifa suna shirye shiryen yanda
zasu bullowa Mum ayi mata wayo Alim yaje wajen Amana
Domin ko ya fadawa Abba to tsine masa Mum zatayi.
Amana da Badriyya zaune gaban Babansu sai kuka sukeyi yanda suka babansu raga faga
komai sai dai ayi masa kafafinsa a karye hannunsa daya ma a balle,jikinsa duk raunuka an
canja masa kamanni,
Cikin rauni Baba yace Yayana kunga yanda Allah yayi dani ko?
Nasan wanda ya min abin nan Amma bazan fada ba sai nan gaba idan Allah yaja
kwanana,na jawowa kaina wayyo duniya oh.....Amanata na dauko ruwan dafa kaina, lallashin
Baba sukeyi,Baba yace kayya yara ni na siyo da kudina,Amma Amanata kinfi kowa a wajena ke
kadai zan fadawa wanda suka sassarani haka. Da dare daga Sulemanu sai Amana nan ya fara magana Amanata ina so ki sani bake ba
komawa lagos Allah tsinewa lagos,tir da halina na turaki Cirani na amfana dashi ta wanni fannin
na jawowa kaina masifa,inaso ki sani duk son kudina yau na hakura naga duniya,don haka
baza ki koma lagos ba,ba aure ba ko tattabarace ke karewar aure na yankeshi Tari Harka yayi yace Allah kawo mijinki wallahi sai ya sakeki bake ba komawa hannunsa,
Idan kika koma lagos to ban yafe miki ba duniya da lahira gaban Amana ne ya yanke ya fadi
nan take sai hawaye takeyi,yace Uwar mijinki ita ta zo da yan daba tasa sukayi min haka,duk
kuma nasan irin ukubar da take gana miki,
To aure anyi kenan na dauka yan mutuncine shi yasa na basu ke Ashe shegiyace.
To bari mijinki yazo sai ya sakeki,
Amana tace Baba ya akayi kasan itace?
Baba yace tare da yan fashin suka shigo dakina da ita,ta rufe fuskarta da zasu tafi ta budemin
fuskarta na ganta kiri kiri harsai da ta tabbatar na ganeta sannan ta tafi cikin mota.
Amana taji wani bakin ciki amma tasan ba laifin Mijinta bane,
Amana tace Baba ina son mijina kayi hakura za a daukar maka fansa,Baba dake kwance
rashe rashe ko ina a daure a jikinsa,yace kaji wofi banza da gadamar daukan fansa nayi da tuni
ban fadawa su Hamza ba sunwa shegiya fata fata,yo Allah na tuba ko ke nasa ai nasan sai kin
mata rugu rugu kin ramamin,
Amana cikin kuka tace Baba wlh ina son mijina ni dai,Baba yace soyayya taci ubanta,uban
soyayyar tattabara ma taci uwarta.
Wato so yasa kin canja ko kin Zama lusara ina alfahari dake ashe kin lalace.
To mijin naki zaizo ya sameni dan ubansa tashi ki ban waje.
Cikin kunkuni Amana ta fito.
Yau kwanan su Amana 3 a garinsu yaune kuma Iyya kakarsu ta fara Amai da gudawa cholera
zuwa magriba Iyya tace ga garinku nan,sunyi bakin ciki sabo da zaman tare ba wasa ba amma
basuyi kuka ba domin sunce ai Iyya taci duniya dama ya kamata ta wulla.
Ana zaman makoki su Hamza sune kan gaba,kwana daya kacal Hamza yace an rufe zaman
makoki ai Iyya ta cancanci ta wuce.
Badriyya tace wlh amma kalli Baba da rashin godiyar Allah wai harda kuka Ummansa ta
mutu,Haladu yace ke rabu dashi da Allah tsufane eh...
Amana tace su Iyya yanzu tuni nasan walakiri ya mata guduma daya,don fa Iyya ko sallah
bata iya ba, kb yace ai Iyya ta wuce guduma sai dai a kafa mata Kusa Allah wlh.
Amana ce ta janyo jaka ta zaro kudi ta mikawa kb gashi Baabaa ayo mana cefane,Haladu
yace easy wlh Anty Yau dan Allah a bani 3k zanwa my one and Only hidima,Amana tace sai Bro
ai mu inde akan har kar Love ne to gwara jari ya karye don mun San darajarsa ga 5k ayi
manage.
Haka suke ta abinsu Amana ta canja sosai Amma haka take biye musu tana raha da tuna
baya ana har kar eh..aha..da ita hakan ba karamin nishadi sukeyi ba.
Alim ya je ya kokawa Abba amma kar ya fadawa Mum domin tsine mishi zatayi, dan haka
Abba yace Alim ya tura Adamawa zai masa wani aiki Huzaifa kuma zai koma Kano,har Mota
Mum ta raka Alim tana masa addua,Huzaifa ya mata sallama amma a wulakance ta amsa ta
wuce. Alim da Huzaifa jirgin kano suka hau sai kano,
Suna sauka gidan su Huzaifa suka huta, washe gari da safe da wuri ko Amana bai fadawa ba
tsabar zumudi suka dau wanka shi da Huzaifa Sai garin su Amana.
Huzaifa ke driving,
Alim waya suke da Amana amma bai fada mata ba cewar suna hanya ba har suka gama
soyewa a waya.Mum da Abba da yan uwansa duk sunyi waya suna yi masa ya Adamawa kawai
sai yace lfy shi da Abba ne kadai suka San inda Alim ya tafi.
AsmaBaffa
A dinga yi ana sharhi readers yana kara kwarin gwiwa fiye da tnx etc.love u all.
✳CIRANIN AMANA✳
135-140
Official
By
AsmaBaffa
WANNAN PAGE DIN NA SADAUKAR MIKI MARCYCOOL ALLAH YA BAR ZUMUNCI
Suna kan hanyar garinsu Amana yau Alim cikin nishadi yake kamar yayi tsuntsu ya afka
garin shuuut,sai nishadi yake,
A kofar gidan Sulemanu Harka suka gyara parking din jibgegiyar motarsu hadaddiyar gaske.
Haladu tun a majalisa yace wannan irin motar sai dai bakin Amana,dan kaf unguwarsu itace
me harkalla da masu kudi shi yasa ma suna parking shima ya kara so wajensu، tun daga
takalmansu da suka zuro kafafu waje kasan sai kusoshin Nigeria,
Tun kafin Alim ya fito bude motar kawai kamshinsa ya cika layin,
Haladu sanye da 3qtr da armless yayi kyau hannu ya mikawa su Alim suka kashe cike da
mutuntawa saboda kaf yan gidan su Amana babu me duhun kai,kowa ya waye saboda suna fita
wasu state din,ko wankansu irin na yan birni sukeyi musamman yanzu da Alim ya musu hanyar
samun kudi da ilmi.
Palon baki Haladu ya kaisu palon yasha kujerun da Alim yasa musu,su Sakina sun gyara
shi tsab sai kamshin turaren wuta yakeyi me dadi haka gidanma ko Ina fes fes yana kyalli.
Haladu exotic da malt sai holandia da ruwan roba duk ya cika musu a gabansu، Alim wanda
ya matsu ya ga matarsa yace Ina wife Dina first,murmushi Haladu yayi yace na tura a kirata wai
taje gidan wani frnd zata gaisar da Mum dinsa makwafta ne ana mutunci da iyaye sosai,
Nan take mood din Alim ya canja,kishi ya cikashi Mum din frnd ba ma mace ba Mum din wani
ba Mum din wata ba,
Kasa Zama yayi ya jawo waya yana danna Kira yace Ina zuwa ya fita can waje,kofar gida
yana huci tare da Jan tsaki zai kirata a waya.
Rashin sa'a bata shiga,minti kadan ya hango ruhinsa Amana ita da kanwarsu Sakina suna
tahowa ta wani lungu, tsananin kyan da yaga Amana ta kara yi shi ya ja hankalinsa tare da
kafeta da Ido,
Arabian gaunt ne jikinta tayi rolling dankwalinta black and pink.
Tun daga nesa Amana ta hango sahibinta,wani farinciki ya mamaye zuciyarta,cike da
nishadi take karasowa,kishi yakeyi maza na kallar masa murmushin matarsa,gashin kansa ya
shafa,
Wani wajen da ake charging a jikin gidan su Amana su ne suke kunna DJ kida na tashi me
matukar dadi wakar Hausa kamar a taka rawa,
Nan ya kara musu wani nishadi Amana tun daga nesa ta kashe Alim da mugun kallon kauna
tana aika masa da wasu sakkoni,
Alim ya kasa dauke Ido,
Tana zuwa kusa dashi sai ji tayi ya rungumeta tsam so tight,
Kunya taji kar a ga rashin kunyarta a fili
Kafin kace me yara sun zagayesu ana ta kallansu wasu na cewa yan iska ne....yan iska ne,
Wasu kuma suka ce yan film ne....laaaa Alquran ga yan film,harda masu leke ta saman
katanga
Da kyar Amana ta kwance kanta cikin dabara don taga Alim kiss yake shirin manna mata ga
shi sun kwashi yan kallo,Allah yasa an San yan gidan Sulemanu Harka ba mutunci garesu ba
shi yasa ake tsoronsu sun wuce raini.
Hannun sa ta ja har cikin gidan ya gaisar da su Ummansu sannan yaran gida suka gaisa
sosai,ya musu ya jikin Baba da ta'aziyar Iyya,su Baba an tafi Hospital sai wurin magrib zasu
dawo sai sun jira. ya Dade cikin gidan wajen yan uwan Amana ana ta hira dashi shi kam yasha
dariya sosai, Huzaifa kuwa yana can da Badriyya suna hirarsu, Amana dakinta ta ja Alim da yake gidansu ba wani kunya ko wani sa'ido musamman ga
mata da miji
Suna shiga Alim ya jawota jikinsa,daga nan ya fara lalubar bakinta yana ta tsotsa,tana shafa
wuyansa ta baya domin hannunta na sakale a wuyansa,
Kallonsa tayi cike da shagwaba tace I missed u,kan bed suka zauna sannan ta dan zamo
kadan ta risina Ina kwana,ya hanya,
Sai sannan ya balla mata harara bana amsawa Ina kikaje?
Narkewa tayi lalle fa naje kalli ma ta miko masa hannayen da kafar,
Sai kuma na biya gidan Maman na Marsiyya muka gaisa domin ta tallafamin lokacin da
banda shi,magana take amma hankalin Alim yana kan kirjinta, yana kallon yanda suka kara
cikowa, waye kuma Na Marsiyya?Alim ya tambaya,tace makwafta ana gaisawa da Babarsu
kuma tana so na ta karasa zancen tana
Kallon sa, ta kalli inda Alim yake kallo wato boobs dinta kunya taji tace kai yaya Alim Mene
haka?
hannayenta ya rike yana kissing din lallen da aka mata
Kinyi kyau my wife I love u.
Kansa Amana ta kamo a hankali ta kwantar a saman cinyarta tare da shafa sumarsa tace
Husband karka damu trust me kasan bazanyi wani abu Bad ba ko Ina naje naga kamar ranka
ya baci.
Cikin shagwaba ya furta ni dai pls ki daina fita ko kofar gida idan kina son farin cikina.
An gama ya Alim,me kake son ci? Tuwo nake so idan akwai idan babu ma kiyi min wani.babu
sai dai na yi maka,
Ok ayi min to zanci kallonsa tayi tare da yi masa kiss a goshi ka fiye shagwaba Allah ya Alim,
har kafi mace kamar dan jariri haka kake.jawota yayi jikinsa sosai yana murmushinsa me sa
Amana Sandarewa saboda kauna,ya shiga mirza boobs dinta yana wani shidewa itakam
lumshe Ido tayi tana jinsa kasa hanashi tayi suka shiga romancing gani tayi Alim zai wuce gona
da iri murya can kasa ta rada masa a kunne tare da shafo cikinsa tace bari nama girki ko?
Uhmmmmm ya furta tare da tura kansa cikin wuyanta yana shakar kamshinta amma dai ke zaki
dafa min da kanki nayi missing girkinki
Fari tayi da Ido tare da yin wata Mika me Jan hankalin da Namiji ta furta wa zan bari ta dafa
ma abinci,wannan hakkinane Ina kissing kaci girkin wata mikewa tayi tare da barin dakin,
A bed din Amana ya kwanta nan take bacci me dadi da nishadi ya kwasheshi.
Amana ana kitchen duk mutan gidan kallonta sukeyi suna mamakin Kula da miji irin na
Amana,
Sakina ce ta shigo tana kuka sosai ta samu gaba daya yan gidan suna zaune a katon
palonsu banda Baba da Badriyya,Baba na asibiti Badriyya na wajen Huzaifa
Sakina ta rushe da kara rushe musu da kuka,Amana cikin hasala tace dallah malama yi
mana shuru wlh ko naci Ubanki banza doluwa katuwa dake kina wani mana kuka kin Zama
budurwa fa,
Kb ne cikin takaici yace Amana Mene haka halina dake hauka da saurin fushi baza ki
tambayi dalili ba,
Amana da masifa tace rufemin baki kb wlh kasan halina bani da mutunci yanzu dan nayi
laushi ne da Baka isa ka fada min haka ba,kar fa kaga ka girmeni wlh ba ruwana bazan raga
maka ba,kana jinta tana kuka mijina yana bacci idan ta tasar min shi fa,Isa da dariya yace yaro
ne shi eh an tasheshi din,Haladu dan zamani yace kin birgeni ki Kula da abinki, Amana tace to
dan Allah ma yanzu wlh da kyar na samu na lallabashi yayi bacci idan ya tashi rigima zai min ta
karasa da shagwaba,
Hhhhhhhh kowa dake gidan ya kyakyace da dariya harda Sakina me kuka.
Hamza yace ke kikeyin Abin wlh amma ni nakejin kunyar abin,ke yanzu ko yar kunya babu
ko?
Umman Amana tace ai banzace wai ita a dole yar birni ta waye,Gwaggo tace. Munji labari har
rungumeshi tayi a bainar nasi.
Hamza ya kalli Sakina uban waye ya taba mana ke fada min wlh ya gane kurensa yau,
Sakina kuka taci gaba dayi harda shidewa Amana a fusace ta make bakinta har sai da ya
fashe tace ohhh zaki tace Babyna wlh kika sake ya tashi ban gama masa abinci ba sai na
tattakaki a gidan nan.
Sakina dafe da baki sai Hawaye takeyi,
Hamza yace ki bita a hankali mana ke fada mana Mene?
Sakina tace saurayinane Mohd mukayi fada yace ya fasa aurena wai na fiye masifa ta kara
fashewa da kuka kuma wlh Ina sonsa wayyo....karshena yazo...ni mutuwa zanyi.
Yaya Isa dan Allah tunda abokinkane ka bashi hakuri ko gidansu can cikin Kano city ka je ka
bashi hakuri,
Ke.....ke...ke....hold there abeg wanne irin in bashi hakuri sai kace dole ki kyaleshi Allah ya
baki wani ai sai ma ya raina mu yaga kamar andamu dole ya aura karshe kisha wulakanci,c
cikin kuka tace dan Allah ya Isa,
Isa yace ke zan kwada miki mari wlh kinma rainani sau nawa Ina zaunar dake ina baki
shawara cewar idan kin San kina son Mohd ki rikeshi sosai ki gyara wannan masifar taki kika ji
ke a dole budurwa dole ya so ki ko ai gashi na kinwa kanki.
Kuka taci gaba da yi ,Amana wacce ta fito daga kitchen rike da wani bowl tace a'a ke tashi ki
tafi can kofar gida wlh ko ki koma dakin uwarki kiyi ta kukanki ya dan iskanci zaki tasar min
Baby yana bacci,
Shuru Sakina tayi tana kunkuni.Badriyya ce tayi sallami tabi Sakina da kallo