Showing 69001 words to 72000 words out of 105161 words
Chapter 24 - CIRANIN AMANA BOOK COMPLETE BY Asma Baffa .pdf
hawaye na tunowa da Baba,Umman Amana kuwa wani uban tsaki
taja tare da cewa aikin banza akan wannan ya bata lokacin to wlh ni yola state zan koma cikin
city wajen yan uwana su rikeni mahaifina,duk kun hanani ci gaba a garin nan.
Dan haka wanda yaga yana da kudin siyen dakina ya siya ya bani ko na kira wani a waje
bare ya siya,
Amana hawaye da takaici ya isheta,tace Umma zan siya,Umma saida tayiwa Amana kallon
banza sannan taja tsaki tace naji dumus,Kb Amana ta kira gefe tace kb ku samu a siyi dakin
nan banda kudi hanuna kun san komai dai,kb yace akwai ragowar kudin gidan ki a hannuna ina
ga zai siyi gidan,
Amana ta dawo cike da Ladabi tace Umma nawa kudin dakin? Umma tace sannu azagwai uwar
Iya, wa ya sani ko da gaskene abinda kika aikata nasan ubanki kika gada shi kwarto ke kuma fa
?ai dole ayi gadon tsiya,wannan mijin naki yaron kirki Amana amma sai da kika nuna hali ya
sako ki gaki ga gidan nan ai ki zauna,
Muna zaman lfy yaro na mana kyauta kika watsa kanki ya sakoki ga ciki dan Allah baki ji
kunya ba?
To ko kin sayi dakina dan ubanki dole ki bini mu tafi yola na dinga dora miki talla,mene
amfaninki wai ku masu Uba ko?
Amana dai bala'in da take ciki kadai ya isheta ta saba da hali Ummansu tunda yanzu bata da
kudi,
Shi yasa Amana kamar ba ita ba duk tayi laushi tubus ta gama karaya da lamarin duniya,cike
da ladabi tace to Umma amma Baba yace in ba aure ba kar mu rabu da yan Uwa, da karfi
Umma tace iyyeeeeeee to wlh sai kin bini,sana'a za muyi mene amfaninki,
Nan Umma tayi kudin daki Amana ta siya sannan Umma tace dauko kaya mu tafi,kowa dake
gidan yaji ba Dadi,nan Mutuwar Baba ta dawo musu sabuwa kowa kuka,
Musamman Badriyya da suka shaku da Amana ga bikin Badriyya da Huzaifa ya kusa,domin
Huzaifa ma har tallafi yake kawo musu idan yazo sai Badriyya tace suna tare da Alim a lagos ita
kuma Amana ta boye kanta,Sakina da Badriyya rana daya za ayi bikinsu saboda mazajensu
masu hali ne sunce sun dauki nauyin komai na biki.
Amana bata so bin Uwarta ba amma gudun bijirewa iyaye dan kar ta maimaita yanda ta
bijirewa Baba ta bar gidan da ita da Alim duk da cewa iyayen sune masu laifin amma duk da
haka saida masifa ta afka musu shi yasa taji tsoron bijirewa Ummanta
Duk yan gidan ne suka taushi Amana suna ta kwantar mata da hankali,Badriyya da Haladu
harda kuka yanda Amana ta fita daga hayyacinta gaba daya,
Haka tana ji tana gani tare da sharbar kuka ta hada kayanta tas tabi Ummanta,amma abin
mamaki Umma ta bar kannen Amana wajen su gwaggo wai su rikesu Amana tallafa mata za
tayi da talla.
Tun a tasha,Amana kuka kawai take shike nan an kara nesantata da Alim,kuka kamar ta
kashe kanta,Umma tace kiyi kukan jini ma ke kika jawa kanki,
A mota ma kuka takeyi ana ta kallonsu,to Amana ko wa zai taimaka miki oho.yanzu ba kudi
basu Hamza ba Alim baki da kowa sai Allah.
Yanda Amana take wannan halin haka Alim ya shiga sanadiyyar rashin Amana kusa dashi ya
yarda itace rayuwarsa,shima ya rame sosai da kyar yake fita ma,yan uwansa da iyayensa sun
rasa gane kansa,yayin da Mum ta Nemo masa wata yar kawarta Zainab wai Abba yayi masa
aure ko zai samu nutsuwa,Abba kuwa ganin halin da Alim ke ciki sai ya yarda, Har zance Mum tace sai yaje wlh,Alim yana zuwa yaga Zainab wata tambadaddiya marar
tarbiyya nan take yaci mutuncinta tun daga sama har kasa yayi tafiyarsa,wannan dalilin yasa
aka dage biki sai nan da 6mnths,
Saude kuwa ana can Ana Wainar siyarwa tare da ci gaba da kulle kullen tsiya.
Ranar da Amana tabi Umma suka tafi ranar da yamma Alim yazo gidan shi da Huzaifa,dalili
kuwa ranar kawai yaji ba abinda yake so ya gani a duniya irin Amana,
Waya yayiwa Huzaifa wai yana so ya gaisar da iyayen Amana mata yayi musu alherin
saboda yanzu basu da miji,ai kuwa Umma bata da rabo Alim Mota guda yasa aka kawo gidan
ta kayan abinci,sai kallon yan gidan yakeyi,sai ya faki ido ya share Hawaye,gaba daya suma
sunga ya rame,inda Su Hamza suka birgeni ba wanda yayiwa Alim maganar Amana ko kadan,sai Baza ido yakeyi
yaga Inda Amanansa zata bullo yayi tozali da ita ko bai mata magana ba zaiji sanyi kuma zai
rage radadin sonta da yake daminsa,
Amma duk da haka yana cike da bakin cikin Amana taci Amanarsa ta zalinceshi gashi yana
sonta Amma dole ya hakura da ita,maybe ma ta manta dashi tana ta rayuwarta cikin Jin dadi,a
hankali ya furta Allah sarki ni..a fili .
To Alim dai yana ta baza idanu Ba Amana ba labarinta,tunowa yayi da Badriyya mutuniyarsa
me handling case dinsa,
Komawa yayi wajensu ita da Huzaifa yace sorry frnd zanyi magana da kanwata for some few
minutes,
Sun kebe waje daya shi da Badriyya Alim yace Sis wannan yarinyar fa? Badriyya tace wa
kenan a hankali yace Aman...kasa karasawa yayi saboda yanda zuciyarsa ta kare,takaici yake
son taso masa haka ya daure,
Badriyya ta lura da hakan sai tace oh...Amana ai sun bar gidan na....kafin ta karasa Alim yace
Badai aure tayi kan aure na ba?Badriyya tayi dariya kamar bata San komai ba tace haba aure
ba aure ba kawai Ummanta ce ta takura mata sai sun tafi Yola garinsu tayi mata talla.
Talla?Alim ya kwala da karfi yace to wlh bazai yiwu ba Sam,nan ya fara fada ni nake da iko da
abata,
Badriyya batace komai ba sai tace ai na tausaya mata in ka ganta baza ka ganeta ba ta rame
sosai kullum cikin kuka take tace wai sharri akayi mata aka rabaku gashi tana da ciki har ya fara
girma,kasan me Baka ga bakar wahalar da take Sha da cikin nan ba,yanzu Amana ko maganar
kirki ta daina sai da dalili, Fiya fiya fiya Alim ya kama fyalla sauri kamar zai tashi sama,mota ya bude tare da fadawa ciki
ya dinga bakin ciki da share kwalla na tausayin Amana har ya gaji yace ko mene ke kika
jawo,ke kika jefa mu cikin masifa...nan take zazzabi ya rufeshi da ciwon kai mai tsanani cikin
motar ya kudundune saida Huzaifa ya kaishi asibiti sannan suka koma gidansu Kano kenan.
Amana sun sauka lfy,wani gida suka shiga da Alama nan ne gidan su Umma,gidan Bulo ne
ko siminti babu,daki biyu ne rak,ba mace a gidan iya Baban Umma ne kawai wato kakan
Amana kenan,shi kadai yake rayuwa saboda tsabar masifar tsohon,masifaffe ne number
daya,sabo da haka mata basa Zama da shi,haka Umma ta masa bayanin Amana da ita,zasuyi
Sana'a,
Malam Nuhu yace to gwara da kukace zakuyi Sana'a ni dai kwandalata bazan kashe muku
ba,gida dai gashi nan Ku zauna a waccen dakin baya Ga wannan ba zan yi muku abun sisi ba,
Amana dai tunda ta gaisheshi kala batace ba,tana rakube a bango kamar marainiya,tana
tunanin Umma Babanta ta gado, Umma ce ta dan sai musu abinci har Malam Nuhu sukaci dan
kadan dashi baifi mutum daya ba,
Amana kuwa bata cin shinkafa da miya amai takeyi da tashin zuciya amma Umma tace
iskancine wlh baza ta sai mata komai ba,ga yunwa tana ji gashi bata da ko sisi,haka taci abincin
tana ci ta fara Amai sosai Ai kuwa Malam Nuhu ya fara sauke Bala'i wannan iskanci ne
wannan?yanzu haka ma cikin shege ne kuka gudo min nan za a cuceni, Umman Amana tace
Haba Baffa da kai fa aka daura mata aure.
Amana ta ebu ruwa zata kuskure baki ta wanke hannu datt
ijon yace karki bata min gida kimin asarar ruwa ubanki ne ya sai min?kai gaskiya ubanku ya
Sha wahala daku to wlh baza a zo a hanani walawa ba a gidana,
Amana kwalla ta share tare da tsugunawa tace kayi hakuri,kallonta yayi tsab yace iyye ke
baiwar Allah yaushe kika daina harkar niganci da jagaliyar ne?Allah da iko yaushe haka ta
faru?amma wanda ya aureki kamata yayi a bashi kyautar sarkin hakuri,yo ni da nine
yausheeeeee tabbb,badan halin ki ba ebi ruwan kadan amma ki shiga bayi ki wanke hannu da
baki ba a tsakar gidana ba bar ganin gidan ba siminti ba a lalata min gida,hakan Amana tayi ba
tare da tacewa Malam kala ba,saboda tasan ma idan tayi magana to bakar magana zatayi
domin ta kai wuya saboda halin da take ciki ga duniya ta bata darasi shi yasa bata cewa
komai,kun San shi karatun duniya dole sai ka jishi,kuma ba iya kunne ne ke ji ba duk gangar jiki
ce ke karba sosai.Amana sarkin zuciya ji take kamar tayi ta dukan Malam har ya suma,dan
darajar Umma ta kyaleshi amma da sai ta nuna masa ita wace
Washe gari Umman Amana ta siyo gero ta fara kunun siyarwa ba na markade ba na daka su
surfa ita da Amana su daka ayi Amana ta dauki katon botikin paint a kanta ta fita can wata
majalisa,bata so gudun fushin Umma ta hakura, Amana kar A manta fa,dama can ta Saba da
sana'a talla ne kawai bata taba yi ba amma duk aikin wahala tayishi kuma gata da zafin nama
ba bata lokaci tunda tasan dole tayi ko dan abinda zasu sa a bakin salati bare ma ta San Umma
ba kyaleta za tayi ba kuma bata son yi mata musu heeeee su Amana anji jiki fa da dane na
tabbata Umma baza ta iya juya Amana ba,sai gashi yau Amana har mamakin wai ita Amana
akewa abinda aka ga dama,da ace da dane har Baban Umma Malam Nuhu zata ci Ubansa.
duniya kenan.
Amana kam yau satinsu Biyu da zuwa Yola,suna zuwa har gidajen sauran yan Uwan su
Umma suna zumunci,
Amana tana zaune da waya a hannunta zata kira Hamza Umma ta kwace wayar kawo siyarta
zanyi na kara jari,Amana shuru tayi ta zare sim dinta ta mikawa Umma dalleliyar wayarta
sannan ta fashe da kuka sabo da wayar taka rage zafi da ita wajen kallon hotunansu tare da
Alim sai taji sanyi a ranta ta samu nishadi to yau Umma ta kwace wayar ma amma duk da haka
ba iya sim ta cire ba komai na wayar ta mayar kan Memory ta zare Memorynta ta hade ta daure
a Leda tasa a bag dinta,
A banza Umma ta siyar da wayar Amana duk tsadarta,yayi dai dai da Alim wanda ya kasa
hakura da Amana,ya shiga matsanancin Hali kullum sai ya Sha maganin bacci yake iya bacci
kawai ya yanke shawarar kiran Amana ko muryarta zaiji ya rage zafi,canja new Sim yayi tare da
dan nawa Amana kira amma ya makara wayar bata shiga,Badriyya ya kira itama ta gwada bata
zuwa,yace Badriyya pls bani Address din inda suke a Adamawa,Badriyya tace wlh duk gidan
basu sani ba amma dai gwaggo tasan sunan local government da suke a can da unguwar
amma bata San wanne gida bane,tsaki Alim yaja yace kinga Illar rashin Zumunci wannan ba
zumunci bane yanzu idan wani abu ya sameta kuma baza Ku sani ba، ya kamata ace ko
kishiyoyi a dinga zumunci ana sanin asalin inda kowanne ke zaune Sabo da irin wannan. yanzu
wannan me yake nufi kenan kuna Uba daya baku san inda yar uwarku take ba ku bakwa shiga
harkar kowa gashi abin har yan Uwa na jini ma wannan ba dai dai bane,
Haka Alim ya dage ya dinga bala'in da masifa ya dinga saukewa Badriyya kwando kwando
yana ta nuna mata illar rashin zumunci wasu kuma zumuncinsu ma sai suna Uwa daya Uba
daya da iya su suke zumunci.Sai da ya gama yana huci kana yace hadani da gwaggo ta fada
min Unguwar da lg din, Bayan an fadawa Alim komai sai kuma ya fara jin dadi da nishadi kamar wanda akace masa ga
Amana a gabansa,
Amana ce suke ta daka geron kunu,sanye take cikin kayan da ta saba dasu wata falkekiyar
riga tshirt saboda cikinta ya dan fito sai jean trouser fari tayi kyau ba laifi Sabo da yanzu yawan
addua yasa ta dan rage damuwa duk da cewar kullum sai tayi Kukan rashin Alim,amma yanzu
ta danyi kiba kadan Sabo da cikin ya sata yar kiba da kyau yanzu,
Yanzu ma tana dakan geron ta tuno Alim sai hawaye tana yi Hawaye na bin kuncin ta,Malam
Nuhu dake gefe yana jin radio ya mike yau ga kwarzababbiyar yarinya yar iska ke zan koreki fa
daga gidana kullum cikin kunci da kuka ko uwarki aka yimiki iyeeee nace Ubanki aka miki? Ke
kenan a gidana kullum cikin shigar yan iska kike kina nuna tsaraici,shi yasa ma ga badayanki
zubin karuwa shaddar kasuwa ce dake wannan anya jikata tace ba musaya akayi ba,Umma
dake wajen Murhu haushin Babanta taji yana zagin yarta sai taji tausayin Amana kuma,mikewa
tayi tace ajiye dakan muje ciki muyi magana ba musu Amana ta shige daki tsoho ya dauki Salati
yace Hauleeeee Hauleeeee yau ni Ubanki zaki nunawa kin haihu niiiiiiiiii....sai ya saki kuka.
Umma daki ta samu Amana kwance bisa tabarma tana sharbar Kukan takaici tayi rashin Uba
da miji yanzu da Ubansu ya na raye duk Lalacewarsa ai gidansa zata zauna,a da suna ganin
Baba bai musu rana ba bashi da amfani a garesu sai gashi tun ba a je ko ina ba mutuwarsa
tasa sun ga rashin Uba babban wani abune a rayuwa,
Da da Mahaifa sai Allah Umma ce ke lallashin Amana tace kiyi hakuri kinji tashi ki siyo
abunda kike so yau kici kinji,Amana bata ce komai ba,Umma ta rasa abinda zata cewa Amana
ta sata nishadi Umma gani take yau kudi zata kashewa Amana sai tace Amanan Baba ko za
kici mitimis?saida Amana tayi murmushi,Umma taci gaba zan kashe miki kudi ko mene fadi
kinji,shuru Amana tayi tare da goge hawaye,Umma tace Aya fa? Dan
tamatsitsi?dabino?awara?gurasa?ko dan silif zaki siyo flour kiyi? Amana tace ni kaza nake
sha'awa dan Allah Umma ki sai min a ribar da muka samu,Hangame baki Umma tayi tace yo
ina kudin kaza yake ke Amana wannan ai zalincine da mugunta har Kaza fa?
So kike ki karya jari canja wani kinji yar Baba,Amana kuma a duniya kazar take son ci,haka
tasan Umma ba siya mata zata yi ba,sai ta hakura tace Umma to ki siya min kasar calabar da
Aya.
Umma tace ko kefa zauna da kaina zan siyo miki ma,A mana insha'allah sai mijinki Alim ya
dawo da kafarsa ya nemeki har ki ja masa aji da yanga ko?kyalkyal Amana ta kyalkyale da
dariyar Jin dadi tare da furta ai Sai Umma,Amana sai nishadi Umma bata taba birgeta ba irin
yau,tunda Umma ta ambaci Alim ta gamawa Amana komai a duniya. Umma kuwa mamakin Yarta takeyi yanda take matukar son Alim haka,
Umma tace tab Amana ni kuwa me Alim yake miki ne kike sonsa haka?ko kanki bakya so
haka,Amana cike da fara'ar da ta Dade rabonta da yin irin ta ta fara magana Umma baza ki
gane ba komai Alim yi min yake Umma komai da kika sani,Umma tace komai? Amana tace
komai Umma bazai fadu ba ina fada miki Umma Mijina karshene a komai da kika sani wasu
suka rab....sai kuka wiwi Amana ta fara,sannan tana murmushi sosai ga hawaye tace Umma
Allah uban giji ya daidaita ni da mijina,Umma Alim mutum ne,Mijina yayi Umma nayi
dace,hawaye ya kwararo mata taci gaba da sambatu Umma Alim abin so ne dan ina Jin kunya
ne da kullum sai na dinga baki labarinsa abubuwan da yake min.
Umma harda kwalla tace kullum zan dinga tayaki da addua yata.
Fita tayi da kanta ta siyowa Amana Aya da calabar harda Rabin kaza gashashiya sai da Umma
ta siyo mata,Amana bata zata ba Allah sarki Uwa me tausayin yayanta.
Nan Amana ta zauna a tabarma ta dinga Garza,
Umma na kallon ta da tausayi.
Kusa da gidan da Amana suke makwaftansu akwai wani Deeni kwaro tantirin dan iskan gari
ne,tunda yaga Amana ta fita tallan kunu yaji a duniya Bai taba sha'awar mace ba irin Amana,a
ransa yace ko hannun Amana ya shafa sosai to ko ranar ma dan ta shi ya mutu,
Sabo da haka duk unguwar ake ce masa na me Kunu ko hannunta ka shafa sai ya karasa
musu da ko yau namutu.
An fara Zafi sosai a Adamawa nan su Amana suka dawo suna kwana a tsakar gida,Amana
tana can karshen gidan kan tabarma ta shige cikin net dinta sabo da sauro
Umman Amana ma tana tsakar gidan farkon gidan cikin Net,haka Malam kuwa yana can cikin
daki,
Cikin tsakar dare Deeni kwaro ya taka katangar gidan