Showing 33001 words to 36000 words out of 105161 words
Chapter 12 - CIRANIN AMANA BOOK COMPLETE BY Asma Baffa .pdf
70-75
By
AsmaBaffa
Amana bata gama shan mamaki ba sai da taga Babanta ya fito daga gida dauke da Alawa
goro da chewgum Na daurin aure domin a kauyen haka akeyi,
Hangame baki Amana tayi domin ganin su Haladu da Hamza tare da sauran yayyenta duk
sunzo daga garin da suke Cirani,mamakin Amana shine ganinsu cikin shiga me Kyan
gaske,gaba daya sun canja,kyansu ya fito,sunyi fresh,to me ya faru haka,amma ai suna waya
dasu Baba me yasa basu bata labarin komai ba,cikin motar da take ta kalla kawai sai taga
wayam ba kowa Ashe angwaye duk sun fice an barta a ciki,su Alim ta hango sai hada hada
sukeyi,musamman yanda taga Alim da danginta sai wasa da dariya sukeyi,mutumin da ba ya
magana shine yake ta wasa da dariya haka.
Ana haka aka fara hudubar daurin aure,Amana sauke glass din window motar tayi dai dai
da lokacin da taji ance an daura auren ALIM USMAN MUSA da AMANA SULEMAN HARKA kan
sadaki naira million daya.
Amana poster tayi ta kame waje daya tare da hangame baki,shi kuwa Alim ya rasa me yake ji
a ransa sai congrat akeyi masa da fatan alkhairi,
Baban Amana baki har kunne sai rabon alawa da goro yakeyi ana masa Allah sanya
Alkhairi,Amana kuwa ta matsu mazan su watse ta shiga cikin gidansu taji wannan wanne irin
abune,za a min aure ban sani ba,
Wani bangaren kuma wani nishadin dadi ta tsinci kanta ciki,tana ta tunanin duniya bata sani ba
har mutane sun waste,angwaye kadai suka rage a kofar gidan su Amana,
A rude Amana ta gyara gyalenta siriri shara shara da ta yana a kanta bata daura dankwaliba
sai acuci da tayi,gashi shaddar da tasha kowa ya ganta zaice Amarya ce,
Fitowa tayi daga motar kamar zata tashi sama ta wuce cikin gida ko bangaren angwaye bata
kalla ba,Amana doluwa ta zama data shiga hadadden gidansu,kamar a birni,ko ina yasha tiles
kofofi da windows masu kyau,cikin dakuna sun sha furniture masu kyau,
Komai Na gidan Na yan gayu,dakuna ta duba bedrooms gasu nan na maza Dana
mata,Dana baki,da Na Babansu Palo da bedroom,
Dakin iyayensu ma Palo da bedroom ko wacce,kakarsu ma haka.gida ya kai gida ba jin
kunya,mamakinta waye yayi gidan haka,
Yan biki mata sai kallon Amana yar gayu akeyi,ana guda,shewa,tare da tsokanar
Amarya,Amana sabo da tsabar gulma dan kar ace tana so sai ta fashe da kuka tare da kallon
Badariya tace ke dan uwarki ina dakin Umma,nuna mata badariya tayi ta fada ciki da kuka,
Babane ya shigo dakin shima,Amana cikin kuka tace Baba ya zaka yi min haka,ayi min aure
ban sani ba,ko a waya ai ka fada min,Baba yace haba Amana ta ki yafewa Babanki kinji,uwar
mijinki ce tace kar Na fada maki sabo da tana kaunarki tafi so tayi abinda zai saki nishadi,kinga
gidan nan mijinki shi ya Gina min,kinga kowa Na gidan nan ya basu jari me tsoka,kannenki duk
ya biya musu kudin makaranta,kudi da abinci da sutura duk shi ya aiko mana sosai har
yayyenki da suke Abuja da cross river yayi musu komai,ta dalilinsa gidan nan an ci gaba,ga ilmi
ana samu,
Ga shi kowa yana da aikinyi,yanzu duk iskancin da jahilcin da ake tafkawa a gidan nan Nawa
ya fara raguwa, Iyayenku sun fara daina zage zage sabo da islamiyyar da kika ce su shiga,haka
duk maza da mata masu shaye shaye da sata da matan ma masu mugun hali ta sanadiyyar
makaranta da aikinyi da suka samu duk sun daina sai abinda ba a rasa ba, Ki duba da kanki ki gani su Hamza duk sunyi hankali,nima yanzu alhmdllh Ina ciyar da
iyalaina,to Baba kaifa ka daina daya halin naka?cewar Amana,
Jan numfashi Baba yayi yace kuci gaba da min addua Amana Na kusa dainawa,kuka Amana
tasa haba Baba yanzu so kake yayanmu su gajeka,mu gaskiya kana jawo mana abin kunya,
To Amanata sai hakuri ai inji Baba,shi yasa alherin da mutanen nan sukayi mana dole Amana
nayi musu abinda suka bukata,amma gaskiya uwar yaron nan mijinki da Babansa mutanen kirki
ne,kinyi dace,yanda suka nuna mana kauna gamu talakawa amma suka iya hada zuriya damu
ai sai dai Allah ya saka,Allah sa Albarka cewar Umman Amana dake zaune bakin gado,Amana
tace nidai kawai ba a kyauta min ba,
Kudin sadakinta Baba ya mika mata dubu dari shida ta dauka haladu yaje banki ya sa mata a
accnt dinta Dari hudu kuma ta rabawa iyayenta da danginta,
Gidan su Amana suna da tsafta sosai saboda shi Baba Allah yayoshi me tsamtsami,shi yasa
dole kowacce ta zama me tsafta a ko ina,saboda yana ganin kazanta zai iya sakin mace.
Badariya ce ta kawowa Amana wainar fulawa da yaji me dadin gaske,ta kawo mata waina
da miya ta bikinta,tuwon shinkafa miyar ganye,ummanta kuma ta kawo mata danwake me zafi,
Tun anan Amana taga canji,da Dane yaushe Badariya zata wani girmamata haka,gashi abin
farin ciki Badariya ta daina zuka hayakin sigari,Umma ma da ace da ce yaushe ma zata wani
saurareta idan ba kudi Amana ta bayar ba gaskiya Alim da iyayensa sun taimaka musu,ko sabo
da wannan dalilin ta yiwa mijinta biyayya.
Ta fara cin danwakenta kenan Badariya ta kara shigowa Anty Amana kinga booth din motar
angwaye kuwa abincine irin Na hotel da kaji,da ruwan jarka ke harda lemuka sun bude a irin
abin take away suna ta ci in fada miki gaskiya yan gayu ne,amma angonki bai ci ba
shi,Badariya tace kinga wannan Huzaifan ya bani da yawa Na kawowa su umma,
Anty Amana wai dan Allah nima ina da kyau?kinji wannan Huzaifan sai yace ni me
kyauce,nace ai kin fimu kyau yace bai yarda ba Badriya ke ta faman surutu,Amana cike da
masifa tace karki dameni dallah,
Sallamar Alim sukaji Umma dake waje tace shiga mana tana ciki ai an zama daya,tana cin
danwakenta Alim ya shigo ya zauna a daya daga cikin kujerun palon.
Kwanikan gaban Amana ya shiga Budawa wainar fulawa ya gani tana ta tiriri,dama shi yana
son wainar fulawa,gabansa yaja kawai ya fara ci,saida yaci ya koshi ya mike yace ki gama ki
fito mu tafi ina jiranki,OK kawai tace da kyar,
Saida ya fita sannan ta sauke ajiyar zuciya tare da shakar kamshinsa,
Saida taci ta koshi sannan ta mike tace Umma zamu tafi, hhhh dariya akayi sosai amarya da
ango sunzo daurin aurensu tare sun koma tare,ba a taba ganin irin wannan aure ba,Amarya
kamar bata da gatan dangi,
Umma wata katuwar Leda ta mikawa Amana tare da fadin Badriya ta rubuta komai a
jiki,wajen Baba Amana taje sukayi sallama,Baba yace to Amana in kayi da kyau kaga da
kyau,kibi Allah kibi mijinki Idan kika tsaya wuru wuru ki gani a allonki, muna kallo za a watsaki a
jahannama,gidana ba a yaji,idan miji ya sakoki to ki nemi wani gidan ba gidana ba,Amana dai
aranta tace wannan ai ba nasiha bace ta kirki,kai Allah shiryi su Baba,a hakanma gwara Baba
ya kamanta,Umma ba wata nasiha sai wasu kwalabe manya ta wani bani a Leda,ko mene oho,
A fili kuwa kallon Baba tayi tace ai billahillazi ya sakoni ko nayi yaji dole gidanmu zan taho, ina
kakeso naje,Baba ma yace aikuwa kinyi karya in kina wasa ki gwada ki gani,Baba no...zanci
Ubanki Amana karki ga ina lallabaki Na fiki iya shege,Amana tace Baba Allah baka
hakuri,yawwa tashi maza kuje Allah bada zaman lafiya,
Baba yanzu baza a kaini a matsayin Amarya ba?ke ya isheki Amana tafi gashi duk angwaye
sun tafi mijinki ne kadai ya rage a garin nan.
Amana tana cin magani tare da kukan gulma wai dan kar ace batayi kuka ba ta fito har jikin
motarsu taje Har khaleed driver yabi wata motar sun tafi cikin kano city,
Alim ne kwal a wajen,key din mota ya mikawa Amana me kuka,a ranta tace wato baima
daukeni Amarya ba kenan, karbar key din tayi Alim ya Shiga gaba,ta zauna mazaunin driver ta
fara tuki har suka bar garin Amana tukinta takeyi Hawayen karya nata sharara a fuskarta harda
shesheka, Har sukazo airport Amana bata daina kuka ba,Alim yana ta satar kallonta,ga driving ga
kuka,frnds tuni suna jirgi ango da Amarya ma shiga jirgi sukayi khaleed ya juya gida da motar,
Amana ana lungu a kujerar jirgi har yau kuka takeyi tare da cewa Ashe tana kaunata,me
sonace,Ashe kaunace zunzurutu Na dinga zaginta a banza,Ashe uwata ce nima,
Nima ina kaunarki ta kara fashewa da kuka,Alim bai gane kan zancen Amana ba,
Ashe Amana duk kukan takaici takeyi rannan da taji Mum zatayiwa Alim aure ta kwana tana
zaginta kala kala,ashe ma itace amaryar,ashe Mum din Alim tana matukar kaunar Amana tunda
har ta iya hada jininta da Na Amana.
Amana tunanin halin Mum ta shigayi yanda take sa Alim yana auri saki,kawai sai Alim ya kara
jin kukanta tace shikenan bazanyi lasting ba,bazanyi inganci ba,
Shi dai baya gane me Amana take nufi,masu kula da cikin jirgi sai lallashin Amana sukeyi
tunaninsu ko bata da lafiya,
Har suka zo lagos bata sani ba,motocin Alim Jere sun kai bakwai su suka kwashe tawagar
ango,har gida wajen Mum dinsa aka rakasu,Har Amana sai wani rufe fuska takeyi saboda
kunya
Mum cike da nuna murna da farin ciki Na karya ta tarbi Amana,
Yata kiyi hakuri kinji anyi aure ba tare da amince warkiba Na yaba da halayenki matuka shi
yasa naji kwadayin hadaki da Dana,kuma shima Alim ya fada min yana sonki,haka Mum Alim ta
dinga shiryawa Amana zancen karya iri iri,har sai da Amana taji ta yarda da Mum,
Su hajiya Talatuwa kawar Mum sun dawo suma,Talatuwa ita kadai tasan dalilin da yasa Mum
tasa Alim ya auri Amana,Aabid yana makale a jikin amarya Amana, Mum ce ta sa ma'aikata
suka fito da lefen Amana Na gani Na fada har akwati 9 babu abinda babu,wasu ma a Holland
Mum ta hadosu,har mota aka shigar da akwatuna,Mum ta kalli Amana tare da kallon ledar da
Amana tazo da ita,da wasa da dariya Mum tace wannan kayan fa daughter,Amana murmushi ta
saki tare da cewa Umma Na ce ta bani nima ban San mene ba, Mum ce ta karba tare da
dubawa kayan gyara Na mata ta gani,ingatattun magunguna,fakar idon Amana tayi ta dalla
mata wata uwar harara tare da maka mata banzan kallo,a ranta Mum tace za a mallakemin
yarona tsinanniya zaki ga yanda zan mai da rayuwarki,a fili kuwa cewa tayi yata wannan ai
sunyi araha da yawa sai su lalata miki mahaifa,ki bari ki zauna yanda Allah yayiki sai mijinki yafi
sonki,Amana baiwar Allah to Mum kawai tace,
Bayan sunyi sallar isha Abban Alim ya nemi Alim da Amana yayi nasiha ta gaske sannan
yayiwa Alim tasu ta sirri,Asiya ma sai yabon irin kyan Amarya takeyi har sai da Mum ta maketa,
Aabid Alim da Amana haka aka rakasu har mota suka tafi gidan Alim,kowa yana murna da
fatan alkhairi banda Mum da kullum cikin kulla sharri take,
Ma'aikatan gidan Alim kaf sun sa ido suga an kawo amarya su ga kalarta su sami abin
gulma,sai sukaji shuru kawai Amana suka gani da Aabid da Alim,sai suke tunanin ba yau za a
kawo Amarya ba,amma wasu maza daga ma'aikata sunzo da gulmar cewar sunji ance Amana
itace matar da Alim ya aura,amma aka karyatasu ba a yarda ba ganin babu wata alama data
nuna Amana Amaryace,kuma sunga da safe da ita Alim ya tafi gidan biki,
Amana kuwa suna shiga Palo Alim yace ina ledar hannunki da aka baki a garinku? Mum ce
tace Na bata basu da inganci Amana ta fadi,mene a ciki?Alim ya tambaya,hmm nima ban sani
ba amma naji Mum tace wai kayan gyaran matane,nan take Alim ya gano wato Mum kwacewa
tayi dan kar ma ko ya kusanci Amana yaji wani dadi,
Baki ya tabe tare da cewa ke kuma sai kika tsaya sototo ta karbe ko?gaki da wayo amma
kuma baki dashi,sai kiyi tayi ai.ga Aabid karbeshi yayi bacci zanje Na huta
Wanka sukayi gaba daya suka kwanta baccin gajiya Kowanne a dakinsa yake,washe gari
dukkansu babu Wanda ya fita,haka sai ga yan aiki sun shugo da lefen Amana gaba daya,Suna
zaune sai ga Mum da sassafe tayi sallama a gidan,da sauri Alim yacewa Amana dauki Aabid ki
koma dakinki,saida ya tabbatar Amana ta shiga dakinta sannan ya budewa Mum kofa ta shigo
tana faman baza ido,ko gaisawa basuyi ba tace ina Amarya,yatsina fuska Alim yayi tare da tabe
baki yace Mum pls ki daina hadani da wannan yarinyar bana kaunarta,
Tana can dakinta nifa Mum duk cikin matan da kike aura mun babu wacce Na tsana kamar
wannan yarinyar,bana kaunar ganinta Sam,da nasan zakisa Na aureta da bazan taba daukanta
aiki a gidana ba,yanzu wlh kin jawo mata masifa da bala'i aiki zata sha ta zama baiwata kawai,.
Wani sanyi da dadi ne ya ziyarci zuciyar Mum,nan take tayiwa Alim sallama driver ya maidata
gida,
Wata ajiyar zuciya Alim ya saki tare da kwankwasa dakin Amana ta fito tana fitowa ya sakar
mata kayataccen murmushi tare da cewa Amarya yau bazaki hada mana break ba ko hutun
Amarcinne,Amana dai kunya ce ta lullubeta,harda nunawa Alim Aabid karfa yajika tare da
fadawa kitchen sai Murna takeyi
AsmaBaffa
Ina godiya kwarai readers luv u all,ina ganin sakonninku ta ko ina tnx.
[6/27, 9:25 PM] +234 808 968 1079: ✳CIRANIN AMANA✳
75-80
By
AsmaBaffa
Alim suna ta game da Aabid har Amarya Amana ta gama shirya girke girkenta a dining
sannan ta koma dakinta ta shige toilet ta feso wanka tare da cancada kwalliya cikin shigarta ta
yau da kullum amma yau ta dabance wani burmemen wando 3qtr red da wata Riga T-shirt
karama ko dankwali bata daura ba ta fito,su Alim ta hango a dining tun kafin ta karaso wajen
Alim ya mata alama da hannu cewar ta juya ta canja kaya,
Tasan kayan da yake nufi dan haka ta cuno dan bakinta ta juya tana kunkuni ta canja shigar
atamfa wata lemon green dinkin Riga da skert sosai tayi mugun kyau ta fito a Amaryarta,yau
Amana cewa tayi sai ta daura dankwalinta nan ta fara kici ciki ta kasa kawai sai ta Dora
dankwalin kawai a kanta kamar gyale ta fito haka,
Tana zuwa Alim yace ko kefa,zo...zo..da sauri taje wajensa,dankwalin ya zame a
kanta,habawa nan yaga zallar baiwar gashi baki sidik yana kamshi da kyalli,
Amana kuwa gabanta sai faduwa yakeyi kasancewar namiji bai taba yi mata haka ba,
Shi kuwa Alim daurin dankwali ya shiga tsantsarawa Amana harda rera wakar barmani
choge ....sakarai... bata da wayo,ai Amana dariya ta fara kyalkyalawa,Alim bai taba ganin
dariyarta haka ba domin Amana ba komai ne ke bata dariya ba,
Tsayawa yayi har ta gama dariyar sannan ya daura mata daurin zamani kamar ta daura
goggoro haka Alim ya Nada mata dauri,da sauri ta shiga bedroom din Alim ta kalli kanta yanda
ta zama kamar sarauniya,
Fitowa tayi tare da cewa dan Allah a ina ka koyi dauri haka,ko a mata ban taba ganin wannan
kalar ba,ba kin maida kanki namiji ba ta ya zaki San da wannan sakara kawai cewar Alim.tun
daga wannan rana Amana ita ba abinda ke birgeta irin ta zauna taga Alim yana nannada mata
dauri abin birgeta yakeyi yana bata sha'awa.sabi da haka yasa Amana kullum burinta tasa
atamfa ko lace ko shadda ko material tazo wajen Alim tace Daddy ayi min dauri,shiko Alim ya
zauna ya tsantsara mata dauri,kuma tayi tayi ya fada mata a ina ya koyi dauri yaki fada mata,
Amana tare da Aabid zaune a kujera tana taje masa gashi,Aabid ne yace Anty ki siyo min
icecream gobe idan munje schl,Amana ce ta bige masa baki kar ka sake Na kara ji kace min
Anty as from today Na zama your Momy, kunji fa Amana,Aabid kuwa ya rike gam Momy yake ce
mata Yau Amana sauri tayi kafin Alim ya fita Office tayi wanka tasha wani dakakken lace a cikin
kayan lefenta ta fito main Palo Alim ma ya sakko cikin shirin sa zai wuce office da sauri tasha
gabansa Daddy...Daddyn Aabid pls ayi min dauri,me zakiyi da dauri yanzu ke